23

46 1 0
                                    


  Da gudu iyayen suka ban kad'a k'ofa jin hayaniya da kuma k'arar fad'uwa, warwas suka Saleema a k'asa tana wani irin numfashi kamar wadda za'a zarewa rai.
    Kuka suka fashe dashi baran sultan da zuwan sa kenan, wajan ta yayi ya rik'e mata hannu Yaya Saleema mene haka?, kitashi Wallahi wanda kike so za'a baki, kada kibari ki mutu zamuyi rashin yar uwa tagari, kuka yake wasu Doctors suna shigowa akayi waje da su, gaba d'aya sun saddak'ar mutuwa zatayi
    Duk wani taimako da drip da injuries da ake bata, basu karb'i jinin taba, bacci ake son tayi amma ina shi d'in ma takasa, su kansu likitocin komai tsaya musu yayi, illa zubawa sarautar Allah ido da sukayi
   A can d'aki wajan Deen firgigit ya farka yana Mom Saleema tazo ina bacci koh?, dubawa yayi ba kowa a d'akin nan yaji wani k'arfi yazo masa da hanzari ya mik'e ya fita, wata hanya ya yabi inda yaga kamar wasu doctors sunbi.
   A hankali yana dafe bango ya k'arasa har wajan, iyayen su yagani a zaune kowacce idonta taf da kwalla kansu a sunkuye, da sauri ya je wajan Mom !, a razane suka d'ago, Mom ina Saleema meyasa meta mutuwa tai kuke kuka haka?
    Yaya Na'eem ne yadafa kafadar sa yace haba d'an samari lover boy Saleema tana nan yanzu zata fito ma, je ka zauna. Har ya juya zai zauna inda Yaya Na'eem ya nuna masa saiyaji murya kamar ta Saleema tana Deen kana ina gani kazo plx kada ka bari Abba ya rabamu kaji?, da gudu yatafi saitin d'akin dayaji muryar ta
Bankawa yayi ya shiga, Saleema yagani a kwance tana duban saitin daya ke, doctors nacikin d'akin ne suka juyo
  "Lafiya zaka shigo, waye kai?, baice musu komai ba, Illa ma k'ara tafiya da yayi zuwa gaban gadon ta, tsayawa sukai dukkan su har iyayen da suka shigo ganin yadda ya tawo da gudu shiyasa suka biyo bayan sa.
   Yaya Saleema suka gani ta mik'e zaune tana wani sanyayyar murmushi wushiryarta da dimple nata duk sun fito ras saboda ramar da tayi
   Karasawa yayi d'ofana d'uwawun sa yayi akan gadon datake, my choice bakida lafiya, meya sameki Abba ne jiya koh?, hannun sa takama tace Deen kaji Abba yace jibi zai aurar dani, Deen ya zamuyi banson rabuwa dakai.

   A hankali ya k'uta yace yi shiru kada kisaka damuwa, Allah na kowane, mu rok'eshi zai amsamana kukan mu, bamuda mafita tunda Abba ne, amma Allah ya fishi yafi munafukin abokin sa maisashi a hanya.
   Uban Kane munafuki bani ba, wato danace narabaku saida ku kuka saka yazo, to gobe I yanzu na aurar da yata, kai ko tsaka nan ta barka a munafurci sultan ya nuna da hannu wanda hawayen dad'i sukaiwa sallama lokacin dayaga Saleema na magana.
   Abba hannu yasaka ya fincike hannun Saleema ana Deen ya dank'a hannun wajan Sagir wanda suka tawo tare, yace Sagir zauna kaizakayi jin yarta
   Sultan da uwarka Ku wuce mutafi gida, Na'eem Abbas ku shekara marasa jin magana, kaikuma kada naganka koda a hanyar asibitin nan ne, bare ka kara shigowa marajin magana, wallahi naganka sainayi k'arar ka kaji koh wuce mutafi.
    Yana gama magana ya fita Mama tanaji tana gani ta tafi, Sultan kam cewa yayi ya yadda akan hakan Abba ya sallamesa a gidan sa, amma bazai barta da wannan azzalumin ba.
   Shehu abokan Deen sune suka kama hannun sa suka fita dashi, yana wani irin kuka Mom nasa kasa jurewa tai, kukan tasaka, Saleema ta zama mutum mutumi dan batasan inda kanta yake ba ma, bare aje a zancen tai kuka ko magana.
   Haka kowa yakama hanya, Sultan da Yaya Na'eem Sai Yaya Ali wan Deen su suka zauna a waje, likitocin kuma aikin su, suka fara kowanne yana al'ajabin mene haka, masifa sabuwa ana neman gyara shi yana neman b'ata wa.
   Deen tunda yakoma gida Sallah yafara akan Allah ya bashi Saleema, Allah kuma yabata lafiya abinci bai Iya ci ba, Illa addu'a dayake tayi.

   Yayun sa mata, suma sunzo duk kansu sun jajanta akan haka, sunyi jimami sun tausaya wa Saleema, yadda suka ganta yanzu ba uhm ba uhmumh.
    Mom kiransa tai d'aki nasiha da nuna masa yayi tawakalli shi take ta gaya masa, su Shehu kansu addu'a ta neman mafita Ita suke, kaf gida jen biyu, kaikace gidan mutuwa.
   Maman Saleema taso gayawa danginta abu d'aya take tsoro, kada suma abin ya shafe su, suna ganin mijin ta da mutunci yayi musu ba daidai ba, shiyasa takasa gaya musu, sai a yau da aka aika da card suka gani, shine tayi musu bayanin komai.
    Wantane yace tayi shiru tadena kuka suma zasu tayashi da addu'a, a yanzu haka kaf wasu takaddu na Abba yabawa Alhaji Sani, office kam yazama nasa, abinda yakara d'aga musu hankali kenan
@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now