7

160 10 2
                                    


Bata k'arasa fad'ar abinda take so ta fad'a ba yayi saurin toshemata baki da hannun sa yana girgiza kai Plx Yaya Saleema kada kice baki sona Wallahi ni inasonki kada ki furta abinda zai kamun matsala kada kiyiwa rayuwata nak'asu
Ki yiwa d'an uwanki adalci mana ki amshi tayina, iyayen mu zasuyi alfahari da haka
Yaya Saleema kodan banida kud'i d'an Makaranta ne ni, kinada Dr Aliyu shiyasa koh?
Kiyi hak'uri zan barki kinji duk abinda yake hannun sa na kan bakin ta sai k'ok'ari take ta cire amma ya hanata
Sultan ne yazo yace haba Deen ya kake haka aisaika siyawa kanka raini duk da kaid'in k'anintane ko sa'anta amma baikamata kanawa mace haka ba
Idan ta amince fyn, if not kuma shikenan saika nemi wata
Harara ta galla masa ta funkice hannun sa daga bakinta tace tsaya malam ko ina ruwanka munafurci mata suna suka tara, kuma ba wasu yagani yace yana so ba ni yagani stupid kawai
Fice zaik'ara magana tsawa ta masa, yasan halinta fita yai
Dawo da kallonta tai gareshi tace Deen naji komai amma kaban lokaci zanyi nazari
Yaya Saleema nazari kuma? dan Allah ki agazan ki tallafan kice kin amince
Ita kunya yake bata sosai, jin yadda yake gayamata kalaman so. Huum nace kayi hak'uri mana zan baka answer nan da night
Ok naji shi Doctor fa ya zakiyi dashi?
A'a kaidai tunda nace kajira amsata bashikenan ba.
Tom Sweety na yana magana yana kanne ido d'aya
Tsayawa tai tana kallon sa lallai d'an duniya ne Deen data sani ne haka
Eh nine kuma son Yaya Saleema yamaidani haka, yamaidani raggo amma yanzu zanzama jarumin maza zanyi yak'i da duk maison rabani da farin ciki na yarabani da rayuwata Sai inda k'arfina ya k'are
Lallai kuwa kasan Dr kuwa?, koma Consulta ne Soja, zan iya ja da kowa akan ki tunda naga itama kamar Yaya Saleema na sona
Enyeh waya cemaka tana sonka?, a idonta kamar nagani Deen ne ciki ba DR Aliyu ba
Wata dariya tai maiban sha'awa wushiryarta ta bayyana tace gara dakace kamar amma Ita Saleema karatun ta shine a idonta
Basu lura da lokaci yayi ba saida Yaya Ummi tazo tace kai kai kai lallai yaran nan ba Sallah bare cin abinci kuma gashi lokaci yayi zamu tafi
Banda abinki So ai baya saka yunwa ba yasaka ka tuna kowa sai Ita ko shi, inazuyi tunanin komai Aunty Fatee tayi magana
Da gudu ta mik'e tana dariya suma dariyar suka saka, Deen kansa yake shafawa yana godiya ga Allah mai kowa mai komai daya bashi lokacin da ikon furtawa Yaya Saleema maganar datake damun sa
Wayyo k'afata wash Abba " Saleema ce garin fita ta bige da sauri ya taso yana Yaya Saleema menene? bigewa nayi nazo fita
Oh sorry dear k'ofa ta bigeki lallai Sai anmata bulala tunda ta sa Yaya Saleema ta bige
K'afar ya kama yana hurawa yanamata sannu, maimakon su tashi a'a sai aka b'ige da hira saida Abba ya shigo yace kowa ya fito za'a tafi
Motarsa yace tazo su tafi, a'a dasu Yaya Ummi mukazo fa
To kibata tayi driving da kanta mana, inayso gobe saina kamiki koh?
Kai ta kad'a key d'in ya amsa yabawa Aunty Ummi yayimata bayani, sultan kaikuma kabisu Abba mu biyu zamu tafi kawo jakar na rik'e miki
Dariya suka kwashe da ita Lallai Deen da Saleema anshan love ko dama kunason juna ko sabon na yanzu ne?
Hhhhh aikam hannunta yakama ya bud'e mata gaban motor tashiga shima yashiga yaja
Music yasaka mai sanyin kid'a ga k'amshin su ya had'e ya gauraye da AC a hankali yake tafiya yana mata murmushi
Itama sai murmushi take kamar gonar auduga tana wasa da 'yan yatsunta
Yaya Saleema Plx kice kina sona kinga ba wahala ko a gobe sai ad'auramana aure kinga daga yanzu nafara irga awowi nawa ya rage
Lallai saikace yar tsana haka ake biki?
To ai banson a d'auki lokaci gara dai ayi naganni kullum kusa da Sweety Saleema
Haka ne fa, daga haka sukaci gaba da hira harya kawota gida
Nan ma saida aka jaddadamata ana sonta kuma zai kirata yaji muyarta mai sanyashi walwala

@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now