17

142 6 0
                                    


    Abban Saleema daga gidan sa baizarce ko'ina ba, sai gidan su Deen, A mota sai maganganu yake yana lallai gaskiyar Alhaji Sani dayace yarabani da yara na, dubi Saleema maganar data gayan kwafa yayi ya cigaba da tafiya.
Horn yayi maigadi yazo ya bud'e masa, da gudu ya shiga cikin compound d'in parking yayi, sannan ya fito daga ciki leda bak'a ya d'akko yakama hanyar shiga gidan.
Yafara tafiya naga ya juyo wani part naga yayi, na Abban su Deen d'in. Shi kuma adaidai lokacin Deen ne da Abban su da yayun sa suna zaune anata hira coffee ne a hannun kowa da alama suna jin dadin yanayin.
Ba sallama ya shiga, saima tokarewa da yayi a jikin k'ofar yafara binsu d'aya bayan d'aya da kallo kana ya sauke idonsa a kan Alhaji Raheem wanda shima Ido ya zuba masa.
Deen ne ya tashi yace Abba sannu da zuwa bismillah mana ka tsaya a nan ga mutanen Cyprus ma ya dawo yanzu yake cewa zaizo nace yabari gobe maje.
Harara ya watsa masa, kana ya shiga daga ciki bakar ledar dake hannunsa Ita ya ajiye agaban Abban Deen, yace Alhaji Raheem ka tsiyar ka nan bani ba kai ba yarinyata ba yaron ka.
Haske ya bayyana duhu ya yaye, idona ya bud'e hankalina ya dawo, bayan juyar mun da tunani da kayi, na d'aukeka mutum mai amana, amini, Hamimi d'an uwa kuma ashe ba haka abin yake a wajan kaba, cuta ta kake kurum, dukiyata ka rik'e da sunan zaka ajiyemun, to nazo abani kayata.
Kuma dakasaka d'anka a harkar kuje can kuyi, amma bani ba kai, y'ata kuma nan da rana Ita yau wato juma'a zan d'auramata aure da wanda ba macuci ba
Ga kud'in ku nan, ka d'eban duk wasu decument da files nawa
Yaran da suke tsaye kaf hankalin su ya tashi, tun tashin su basu tab'a ganin irin haka a tsakanin iyayen su ba.
Shi Deen jikin sane ya saki, sai yanzu yaji yanada k'arfin yin magana. K'arasa wa yayi kusa da Abban ya kama k'afar sa yace Abba dan Allah kayi hak'uri komene ya shiga tsakanin ku , mu ba ruwan mu koda yankan naman jikin ku mukaga kunayi Wallahi saidai mubaku hak'uri amma babu wanda zai shiga tsakanin ku.
Tare muka tashi muka ganku, Iyayen mu mata tare suka ganku, babu wanda yasan tsakanin ku sai Allah, amma yau gashi da kanka kake gayawa d'an uwanka bakai ba shi, nidai Abba wannan matsalar taku ce kada kusamu cikin ta.
Kada kamana yankan k'auna, kada ka d'auki laifin da ba namu ba ka d'ora mana, kada ka yanke hukunci cikin rashin sani
Yaya Saleema bata Iya rayuwa Idan bani ba, zuciya guda ke aiki a jikin mu, ruhi guda ke aiki a tsakanin mu, kada karaba soyayyar da Allah ne ya had'a ta.
Kuka yaji yazo masa, meke shirin faruwa da su?, menene ya shiga tsakanin Abban su da Abba da har abin yayi tsamari haka?.
K'afar sa ya kwace, yace Idan kaga nacanja ra'ayina cene mutuwa nai, amma Idan ina raye Saleema batada miji sai Sagir d'an mutunci da maci amana ba, ubanka yarabani da yara na, mata ta akansa mukayi sa'insa.
Kayi shiru mana, d'ebon takarduna ina jira bani ba kai, Deen wallahi kada naga k'afarka a gida nayiwa 'yata miji Saleema bata dace da d'an maci amana ba da kuma maci amanar kansa
Kuka Deen yafara mai sauti, wajan Abban sa ya matsa yace Abba kabashi hak'uri Idan kaine da laifi Wallahi ban Iya rayuwa ba Saleema itama nasan haka, dalilin ta nasauya course wanda dashi na rayu da burin zama banker.
Banda burin kowanne aiki Indai bana office ba nacike takardu ko aiki kan System, amma akan Saleema nacanja kaf ra'ayina.
Itama da burin zama lowyer ta rayu, kuma baifi mata 1 years ta gama amma akan banaso ta canja, Abba kai kanka shaidane akan son da mukewa juna Idan kuka rabamu baku mana adalci ba, kayiwa rayuwata adalci kabani Saleema Abba.
Kuka yake mai fidda sauti fuskar nan tayi ja, kan hancinsa kaikace red colour aka saka
Yayunsa suma abin tausayi hawaye ne ke zubar musu, amma Abban Saleema ko ajikinsa illa kara d'aure fuska da yayi. Duk wannan maganar da akeyi Abban Deen yana zaune yana kallon komai baice k'ala ba
Illa mik'ewa da yayi, wani d'aki ya shiga jaka ya fito da ita, yabashi yace gashi duba abinda babu kamun magana, karb'a yayi yafara dubawa kalas sun cika
Yaran Abban Deen ne sukace Abba kunsamu aduhu nufinku kun rabu Wallahi baku isaba, so kuke duniya ta zagemu Abba mene haka?
Kai Nazeer kada kamun hauka, ba sa'an kane ni ba, saboda haka ka kiyaye ni, abota nace banayi
Zai k'ara magana Abban sa yace Nazeer yi shiru, komai na Allah ne kabarsa yayi abinda yake so
Aure dai ko yau zai d'aura to Wallahi ko ba'ayi da IMAM ba baza'ayi da Sagir ba
Yana gama fad'a, yajawo hannun Deen wanda yake kuka yana rok'on kada a rabasu, ayimusu adalci basuda laifi
Haka yaja shi, yakama kafadarsa sukai cikin d'akin
Suma yaran zaman d'aboro sukai, suna al'ajabin meke faruwa
@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now