25

57 2 2
                                    


    Inallillahi wa Inna ilaihi rajiuun. Shine Kalmar da Sultan yake maimai tawa, yarasa nutsuwar sa, yakai gwauro yakai mari, yarasa wata hanya da zaiyi yaji sanyi, hawayen kansa ya k'afe yakasa fita ga Abban sama a yau tausayi yabashi, tabbas yasan aikin sihiri ke d'awainiya da shi.
   A yadda kowa ya shaida soyayyar Saleema wajan Abban ta, ace lokaci d'aya ya juya mata baya da ayar tambaya. A yadda Abban su keji da Alhaji Raheem yau gashi bashida makiyi kamar sa.
    Wayar sa ya janyo, Maman sa da Yayun sa ya bugawa, kasa gaya musu komai yayi, Illa cewa da yayi suyi maza su zo Asibiti, Saleema jiki ya tashi.
   Ai Mama daga wanka ta tafi to, to kaya batasaka ba, ta janyo hijab sai compound, driver take kwalawa kira da sauri yata so, maza d'akko Mota ba lafiya Saleema ciwon ta ya dawo nashiga uku, kuka takeyi bilhaqqi.
     Haka ya janyo motar sai Asibiti, anan ta tarar da Maman Deen da su Shehu, suna kuka suma,(already lokacin da Sultan yayiwa Maman sa waya, Deen shine na biyu, so Shehu shine ya d'aga phone d'in shiyasa yazo).
    Wajan Yaya Na'eem tai babban d'anta, jikin sa tafad'a tace Na'eem Abban ku ya kashe mun 'ya koh?, yayi sanadiyyar raba numfshinta da jikin ta koh?. Hawaye shima Yaya Na'eem ya share yace Mama relax mana we ar all under Proverbility tunda bamusan abinda ake ci ba, an shigar da Ita theatre room tun d'azu amma Saleema bata mutu ba Mama ki kwantar da hankalin Ki.
    Inaji ajiki na saimunga jikokin Saleema ma, kasa tsaida hawayen ta tai, illa jingina da bango da tayi tana kuka.
   Alhaj Sani shine ya shigo, ba yamai jiki daima magana da yayi akan yazo suje akwai abubuwa da ba'a gama ba, gashi gobe d'aurin aure so kaga abar matan a asibitin suyi jinya kafin gobe ko bataji sauqi ba, taji a d'akin mijin ta.
    Abba baice komai ba saima mik'ewa da yayi zalo zalo ya bishi a baya, Mama kam kuka taqara fashe wa dashi. Yaya Na'eem baisan lokacin daya furta hasbunallahu wa ni'imal wakeel, tsiya da wasulanta, wanga duniya inazakije damu?.
     Suna zaune babu mai cewa qala, illa Sultan dayake ta kiran Deen, shi kam yana sane yaqi Picking, yasan cemasa zaiyi yazo shikuma bai Iya zuwa, a gaban su akayi komai d'azu.
     5:30 aka fito da Saleema daga d'akin idon ta biyu tana arba da iyayen ta, nan tasaka kuka akwance datake a haka take kiran Deen ina yake, har waige takeyi amma babu shi, daidai zasu shiga da Ita resting room bakinta ya furta Deen tana fad'a gudan jini ya biyo baya k'asa tafado tim da gudu aka zagayeta aka d'auketa sai d'akin da aka fito da ita.
    Mama ganin abinda yasami yarta, itama anan ta yanke jiki ta fad'i, sultan kam da gudu ya fita sai gidan su Deen.
     A balcony ya hango shi, da sauri ya haura saman, ganin sa yayi dafe da kansa, Wanda tun d'azu yakejin kamar wani abu zai same shi, gashi zuciyar sa tana bugawa da sauri sauti, salati kawai yakeyi shiyasa ya fito balcony ya zauna.
  Deen!Deen plx kazo nayita kiranka a waya shiru, Deen Yaya Saleema kaitakeson gani, batada matsala saita ganin ka, aman jini takeyi plx com nd save my sisters life.

   Kuka ne ya kwace masa saikace ba namiji ba, saurayi kamar Sultan amma Idan ka ganshi yazama abin tausayi saboda halin da yayar sa take ciki.
    Duk maganar dayake Deen baice komai ba, illama mik'ewa dayake shirin yi, a sanyaye Sultan yace Deen Saleema ce fa, akanka take komai fa, bazakaje ba ko hankalin ta ya kwanta?
   Kafad'ar sa Deen ya dafa, yace sultan a gaban ka Abban ku yace kada naqara zuwa, bani ba Yaya Saleema kuma agaban ka yakiramun police a gaban ka ya maren ya kirani da maka shi zankashe Yaya Saleema, Sultan bazan Iya zuwa ba.

    Da baya da baya Sultan yafara tafiya harya fita. Deen kam kansa ya dafe yamarasa wani irin tunani zaiyi, shifa hankalin sa ya tashi, damm yaji zuciyar sa ta buga, bai farfad'o daga jinyar zuciyar ba, yaji waya, yana dubawa Shehu ne.
  Cikin kasala ya d'aga, daga can part d'in Shehu ne yace Deen kana inane?, ina gida yanzu Sultan ya tafi ma, Allahu Akhbar kabeeeran, kullu nafseen za'ikatul maut, mutuwa dole gaskiya kuma Idan lokaci yayi baka isa ka d'ara ko nan da can ba.
   Mik'ewa yayi cikin tashin hankali yace Shehu mene haka?, kuka ya b'arke da shi yace nayiwa sultan jaje baigana da yar uwar saba, nayimaka jaje bakayi ban kwana da masoyi yar kaba, Allah yayiwa Saleema cikawa ta mutu da sunan ka abakin ta, Bayan nan Kalmar shahada tabiyo baya.
    Sak Deen yayi bai ajiye wayar ba, yajiyo salatin Mom nasa da yan gidan su, d'aga kan da zaiyi saiganin Abban sa yayi ya fito daga k'ofar main parlour ya fita a guje.
    Tass ya saki wayar, a d'ari ya dirga baijira ya sauka takan steps ba, saigashi a waje keke napep ya hau sai Gate well asibitin da akayi charging Yaya Saleema
*Allah kaji kanmu badan mum mutu ba, mutuwa, mutuwa*
@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now