13

145 2 0
                                    


Alhaji Sani cikin motar sa, qirar Ciana yana gaba ga tunbinsa agefe a ajiye waya yake latsawa da alama wani abin yake nema ko yake son kira amma baisamu ba
D'ansane yake driving d'in Sagir, wanda daga ka ganshi zaka tabbatar da cikakken Mashayi ne, danga idonsa jajawur kamar gauta
Magana yakewa uban akan wai menene ya d'aga hankalin sa haka, me Kuma zaiyi?
Dariya yai yace yaro aure zanmaka gidan daraja da kuma akwai, yarinyace kyakyawa badan uwarka ba, dakuma kai to tabbas da nizan aureta
Duniyar ubanta inaso ta dawo hannuna komai zaishiga inason Sani, shiyasa banyi k'asa a gwiwa ba naje wajan Malam yaban magani akan nayi nasara akan abinda nasaka agaba
Ina dawowa natafi Ikeja, nan ma nasamu wani mashahurin Malami shi arnene ma
Ajikinsa kamar yankan wuk'a, wata Leda ya d'aga yace kaga dukka menene aciki?.
Tumfafiya ce, yauwa Kasan ma'anarta?
A'a saika fad'a Baba, yauwa kaga Ita dai ba komai ajikin ta, amma wannan tawan anyi rubutu da Nonon raqumi akan ta, da kuma sirri ka sosai
Zan marmasheta ne gaba d'aya, sai nasamu hanya wadda takasu kashi hud'u kowacce na kallon ko wacce
Kaga kenan Mararraba, saina ambaci sunayansu duka ina watsawa iska tana kwashesu har saina gama zubar da ita tabi ko wacce kusurwa, sauran kuma saina zuba a ruwa mai tafiya
Gayan Idan nayi akace kud'i ne akayimusu haka, zasu dawo daidai za'a tsinci duka?
A'a ai ba yadda za'ayi wannan tumfafiyar ta dawo ta had'e, to shi zanyi Kuma kai bakason ka canja mota Ga mata sabuwa ga gidaje?
Inaso mana, to lallai kayi kawai
Amma kana ganin abin zai tabbata?, bacin kud'in ka Malamai keba? Kuma tabbas ka yadda shi sihirin zaiyi tasiri
Dariya ya saki yace yaro mankaza, ai Ita wannan abin Idan kayi shine ake cewa *FARRAK'U* dan saina raba Alhaji Abdulazeez da Alhaji Raheem, saboda Idan suna tare bazan samu damar ciga ba, Kuma zai samun ido
Kasan dai kud'in nan, nawa banawabane na mutane ne, ga bashi da ake bina nacincewa mutane kudin su shiyasa naga gara ayi ta wuce
Murna d'an yakama sosai, daidai nan suka shigo layin, motar Abban Saleema suka hango yana fitowa daga gidan, kafin su k'arasa yabi ta baya sun harba titi
OMG nazo da magana amma kalli Shege ya fita, indai kaza na yawo kare na yawo wataran sai an had'u, zakàyi danasanin rashin mutuncin da kamun
Haka yace d'an yaja su wuce, yana mai cike da tarin ta kaici na rashin nasara da baiyi ba
Washe gari 9am a k'ofar office na Abban Saleema tayimasa, ganin k'ofar arufe yasa ya zauna akan kujera yana danna waya da tunanin banza
Zama yayi sosai wajan 3 hours amma ba labarin Alhaji Abdulazeez, wayar sa yasaka ya kirashi tayita ringing ba'a d'aukaba, Massinger ya tambaya da wani lokaci zaizo?
Ai Alhaji baya zuwa office duk weekend, suna zama a majalisa ne, bakagayan shi kake nema ba dana gayamaka tun zaman ka
Ido ya bud'e yace ka tabbata bazaizo ba?
Eh mana k'aidar sace shida abokinsa basa zuwa ko'ina suna tare da iyalansu
Wata irin zufa ce tafara karyatomasa, ga cikinsa daya hautsine impossible ace nayi asara, nazuba wannan kud'i na amso magani ace yatashi abanza tsinanne kawai
Wayar sa ya wawura ya dannawa Matarsa kira
"Hello Hajiya kinyi abincin nan kuwa?
A'a Wallahi kayi hak'uri yanzu dai nake shirin d'ora wa, naman ma na wanke, sai rubutun da kaban da za'a zuba lemon nayi tunani kawai ayi zub'o shine zai b'adda kamar sa
Alhamdulillah dama haka nakeso, kibar komai kije Ki adanamun kayan kawai, nafasa sai gobe, goban ma sainaga yadda zamuyi dashi
Tom maigidan, Allah yadawo dakai lafiya, Ameen
Yau dukkan su yaran suna majalisa Saleema ba exam shima ba lecture ga su Shehu da Halifa suma antawo tare dasu
Su shehu basu tab'a zuwa ba, sai abin yabasu sha'awa sosai, baran da sukaga yadda yaran kowa ke girmama kowa
Ga barkwanci da ake, Yanzu ma magana suke akan wai shi yace lallai Saleema Dubai zata ta siyo abinda take so, Baban Kuma yace A'a
Ya siyomata ko menene sai tafi farin ciki da shi
Abba nidai kabarni, Wallahi ba'inda zata, Abban sane yayi maganar, Abban Saleema ya kalla yace kaji koh Abba kaikace muje
Deen ai hukuncin Abban ka shine nawa, hakan daidai ne, ko kuma kabari Idan akayi auren saika jata kuje a siyo
Aikam haka za'ayi, dan ni ba wanda zaikallamun kayan da Yaya Saleema zatasaka a ringa d'agawa haka kawai
Sudai iyayen abinma dariya yake basu, su basu tab'a ganin shirmen So ba irin wannan
Mik'ewa wai tsam ya kalli gefen da su Yaya Ummi suke, yaga basa kallon su da Ido yamata magana jinjina kai tai
Bayan wajan yayi, itama mik'ewa tai ta bishi
Yana kan kujera ya hard'e hannunsa a k'irji, k'afar sa ya d'orata akan wata
Daidai nan ta k'araso Marhaban biki Habeebaty, ya kike ya Exam
Lafiya lou, exam na dukan mu, danma ankusa gamawa duk nabi na rame
Kallonta yai ta gefen Ido, yace nibanga wata rama ba, saima kyau, koh? Eh mana
Hira suka fara, da labarin qawayenta saijin hayaniyar su Sultan sukai
A'a kaga Masoyan asali, ni dan Allah Ku bamu sirrin kullum kuna tare bakwa gajiya ne?
Yaya Saleema bani sirrin me kike masa ko ne kike cemasa ya mato haka dayawa, bashida zance saina Saleema haba saikace akan ku akafara love
Shehu shima yace A'a aiga wanda zaugayamana nan, yah to hiran me akeyi take k'ara donk'on love d'in nan?
Gaskiya da amana da rashin k'arya itake k'ara sawa muna son juna, tattalin juna da kare hakkin Allah shiyasa muke ganin girman juna
Magulmata, Yaya Saleema taso mutafi
Kut wai Yaya ake cewa?, eh mana haka yake cewa abin kunya
Takalminta ta cire tajefawa Sultan tace ya fad'i d'in ina ruwanka gulma ko me, kai Wallahi kaji kunya Ku kuma ya koyamuku koh?
Rabu dasu My choice tawo mu tafi, Yaya Ummi Kada suyi jiranki naga lokacin cin abinci yayi
Yana gama fad'a ya karb'i wayarta yace kawo kada ta wahalarmun dake
Sowa suka saka, suna tafi Soyayya gaskiya, Muma Allah yabamu masu sonmu haka
Lokacin da taje harsun zuba ma Ita ake jira, nan ta zauna Ga kwano kusa hannu tasaka ta wanke suka fara cin abincin
Monday yau Abban Saleema tun safe ya tafi office, saboda ayyuka yasan sunyi yawa, shigar sa keda wuya yaga Alhaji Sani a zaune d'auke kai yai ya wuce shi
Da gudunsa ya mik'e yace Alhaji mene haka?, da girman mu, ni hak'uri nazo baka nasan namaka laifi Kuma sharrin shaid'n ne
Yana magana shi ko sauraran sa baiba, nan fa yabi shi har cikin office d'in, kujera yasamu ya zauna nan ya ringa rattabo k'arya da k'arairayi yana cewa sharrin shid'an ne, amma badan haka ba tare naganku Kuma yaranku komai tare suke
Alhaji Raheem au mutum ne nagari, kayimun afwaa nima mazugane suka saka nace muku haka
Nan yayita lallab'ashi harya sakko anan ya zauna suka fara hira
Cikin hirar yake ta bugun cikinsa har yasamu wani abu da yake son sani
Wajan 1pm Alhaji Raheem ya shigo, ko kallon arzik'i baisamu daga gareshi ba, illa harara saboda yagama gane wannan mutum k'anin Shaid'an ne, ko tsaka tashafamasa lafiya wajan munafurci yaji labarinsa, akan munanan halayen sa, Kuma yayi alqawari saiya hanashi zuwa wajan aminin nasa
Bai cewa kowa kanzil ba, Illa wata loka daya bud'e yad'ebi wasu files ya fita
Lokacin Sallah yanayi suka mik'e akaje akayi, abinci tare sukaci amma shi Alhaji Raheem d'iba yayi ya haye sama office nasa
Alhaji Sani yaga fa abin ba sauk'i lallai saiya k'ara shiri, dama Daryanatu tace masa saiyasaka wani kwalli zaima Iya binsa har yasamu yaci naman
Itama Malama ce, ko nace bokanniya
Ka'ida 5 sun tashi haka sukai Yau, dubu goma Alhaji Abdulazeez yabawa Sani tunda yaga throughout suna tare sallama yayi masa kowa yakama gabansa
Abban Deen dai saida yayiwa Abban Saleema masifa akan maisaka yazo ya zauna masa, kada ya k'ara barinsa. To shidai yace nan sukai musabaha kowa ya shiga motarsa driver yaja
Alhaji Sani dai antafi karb'o kwalli, wanda zaisaka, dan neman buk'atar duniya dashi

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now