31

46 1 0
                                    


   Innalillahi Abba me kake shirin aikatawa hukuncin ubangijin zaka datse?, bafa mu muka kaddara auren juna ba, ikon Allah ne Abba.
   "Saleema itace me wannan maganar. Banzan kallo Abba yamata, zata kara magana ya daka mata tsawa tare da bata lafiyayyen mari a fuska.
   Kuka tasaka tana dafe da kuncin ta, Deen ne yayi k'arfin halin cewa Abba Idan wani laifi nayimaka ina rok'on ka gafara ka yafemun, amma kace zaka rabani da Saleema wani abune mara yiyuwa muna son juna.
   Tsawa yayi masa kana yace kai nizaka cewa abune mara yuyiwa, to tabbas Saleema tagama auranka Idan bazaka ban takardar taba to kaje amma zama da kai ya k'are.
   Bai saurari cewar saba ya janyo hannunta a haka ba mayafi suka fara tafiya tana kuka Deen yana kuka suka bar parlour d'in.
   Mayafi Deen ya d'akko mata da gudu ya yafamata, kana yace Saleema duk inda kike kituna da aurena akan ki, ina miki fatan alkhairi I love u.
  Yana gama fad'a a guje ya fad'a motar sa, sai gidan su.
    Yana isa a guje ya shiga gidan, Abban sa yana zaune magazine ce a hannunsa saijin Deen yayi a kansa yana kuka.
    Hankalin sa a tasha yace Deen menene?, Saleema wani abu yasamu kome?, Abba yarabani da Saleema ya d'auketa Abba kaikamun alqawarin zakaban Saleema, gashi yanzu ya d'auke ta.
   Kuka yakeyi sosai, Deen Abba yace saidaya kira sunan sa sau uku sannan ya d'ago da daradaran hawayen sa yaima Abba k'urii da ido.
   Kafadar sa ya dafa, a hankali yace Deen mezaihana ka hakura da Saleema?
    Da sauri ya d'ago yace rabuwa, dariya yai yace Abba SO BABBAR CUTA ne, Kuma cutar tamun kamu babba m, maganinsa shine Saleema amma maganar rabuwa da Saleema bata taso ba.
    Huum Abba yace, to dan me kake son Saleema?, nasan kana sonta dan kyaun ta, iliminta dirin hallitar ta, kamalar ta. Amma anawa ganin zakasamu wacce tafi Saleema komai.
   Kuma zaka samu wadda tafi Saleema kyau da ilimi da kamala. karabu da Saleema dan Allah da annabin sa.
    Abba bazan Iya ba, karabu da Saleema to kodan hanakan da mahaifin ta yai karabu da ita, ko zaka sami kwanciyar hankali nima nasamu.
    Abba wallahi koda da son danakewa Yaya Saleema zaka had'a ni bazan rabu da ita ba.
   Abba tabbas akwai wad'anda sukafi Saleema komai, amma SO daban kyau daban.
   Zan Iya ganin wadda halinsu yayi d'aya da Saleema amma wallahi a fuska bazan sami kamar taba. Zanga wadda kamarsu d'aya da Saleema amma halinsu daban dan haka Abba kamun addu'a son Saleema ajinin mu yake.
    Zan Iya hakura da Saleema amma Ita bazata Iya ba, tana komai akaina, to danme zanjanye bayan ni, namiji ne.
   Allah kad'ai yasan meke tsakani na da Saleema, kuma shi kad'ai yasan meya b'oye akan hakan, Insha Allah zan zauna nai addu'a da kaina, zan Kuma rabu da Saleema naga ikon Allah yadda zaiyi damu.
    Yana gama fad'a ya tashi ya haye sama yana share hawaye. Matuqar tausayi Abban Deen yaji tausayin yaran matuqa amma akwai Allah wataran komai zaiyi normal.
   Waya ya janyo, bugawa Maman Saleema yai akan tazo yanason ganin ta, itada yaran tunda yasan kaf suna gidan.
    To tace masa, basu jima ba, sai gata kuwa itada tawagar yaranta, sunzata wani abune amma fa jikin su yai sanyi.
   Shiga sukai nan sukaci karo da yaran gidan su Deen. Sallama Abba yai musu, sannan ya d'ora da yimusu bayani akan abinda ya faru da safe, kuka Maman tafara nan dai akayi ta lallashin ta da nunamata tai shuru kada tamasa magana ko d'aya, addu'a zasu fara yanzu.
   Kuma itama ta dage da addu'a, tunda kowa yasan saka hannu akayi ba wai yin kansa bane.

    Kowa wajan ya tausaya musu, Sultan kam ba'a cewa komai dan kamar yafi kowa shiga damuwa, a haka dai Abba yayita musu nasiha da nuna musu rayuwa wataran dadi wataran mad'aci.
    Maman batada ta cewa illa Allah yayimata maikyau yasaka duk inda taje Allah ya kareta, amma bataji damuwa sosai ba, haka suka mik'e sultan kam cewa yayi ya dawo nan da zama saboda Deen.
   Su Shehu a daran suka d'aga Egypt shida Halifa. Abba kam yaji dadi yadda Sultan ke nuna kulawa akan d'an nasa.
     *****
   Abba kam suna fita Court road sukayi gidan Abokinsa inda Alhaji Sani yace yakaita inda baza'a zata ba, ya ajiyeta harsaiya sake ta, yaso yace akaita gidan sa amma Allah baibashi ikon haka ba.
    Gidan sukayi sallama anan sukayiwa Alhajin bayanin qarya da wofi, akan Deen sukace gata nan amana, zata zauna harsai yanda hali yayi.
   Baiyi musu ba, ya amsheta tana kuka tanaji tana gani suka tafi suka barta bayan kashedin datasha akan Idan ta qarya tasu Allah ya isa bai yafemata ba
     Yini tai tana kuka, Allah yasa matar sa tanada kirki, itace taita bata baki, tana nunamata Allah da Annabi da kuma girman biyayyawa wa iyaye.
@ut@r h@jiy@

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now