1

984 24 0
                                    

Garin Kano garine mai cike da jama'a da unguwanni masu yawa garine na kasuwanci garine kuma na manyan Malamai da Attajirai cikin Attajiran garin ya had'a da Alhaji Raheem kwangila

   Duk wanda yake harkar kwangila ko ta meye yasan Alhaji Raheem da aminin sa Alhaji Abdulazeez, wanda suka taso tare tundaga k'aramar Makaranta har kawo babbar da jami'a

   Sun taso cikin aminci da k'aunar juna babu wanda yatab'a jin tsakanin su, kuma kowa zuciya d'aya yake zaune da d'an uwan sa

   Tare suke harkar su ta kasuwanci da komai, Iyayen su suma sun kasance Aminan juna ne, suma Allah ya had'a jinin su

   Lokaci d'aya sukayi aure, shi Alhaji Raheem a Maiduguri ya auro matar sa, macece kyakyawa da sanin yakamata gata da kirki da son jama'a kuma gata da ilimi na addini kowa natane

  Alhaji Abdulazeez shi a Yola landa of beauty anan ya auro tasa, itama ta kasance bafulata nace usul tsantsar bafulatana gata da haske sosai, bata da makusa itama tanaji da ilimi kowanne b'angare

    Yadda d'ayar keda kirki haka itama take dashi, kowacce dai dai tanada kirkin ta

  Yadda mazajen su keda kirki kuma suke zumunci suma haka suke, Kaya wataran ma tare suke d'in ka musu, basuda kyashi kowacce tana kiyaye abinda zaije ya dawo

   Alhaji Abdulazeez yaran sa tara maza hudu mata biyar, kuma a yanzu duk ya aurar dasu sai mazan, k'aramin d'ansa shine Imam Deen yana son sa matuk'a badan komai ba saidan

kasancewarsa sunan Mahaifinsa ne da shi, kuma kaf yaran sa shine yayi kama dashi Illa fari da gashi daya d'ebo na mahaifiyar sa

Kuma gashi yaro kamili nutsatse bashida hayaniya, kuma ga zumunci da sanin yakamata

   Alhaji Raheem yaran sa hud'u maza uku mace d'aya, macen itace ta uku tanada k'ani Sultan.
Saleema kenan yarinya yar gata tanada kirki da hankali batada son hayaniya amma duk da haka batada kyaliya, tana girma ma kowa, ita Saleema yadda Maman ta take haka take kyakyawar gaske ce ga gashin nan na Shuwa Arab akanta kamar gori

  Yaran kaf d'in su Kansu a had'e yake, bakajin kan kowa, kuma Makaranta dukkansu tare suke, Driver d'aya shine yake kaisu

  Abban Saleema yana zaune a unguwar Matan fada, shida iyalansa

  Abban Deen kuma suna zaune a Lamid'o crescent, kowa unguwar sa daban , amma Idan kagansu kace gida d'aya suke ma, tunda yaran wannan. suna wanccen gidan yaran wanccen gidan suna wannan

   Deen da Sultan k'anin Saleema abokan junane, sosai tare suke yin komai nasu, ba boyewa juna sirrin juna, Saleema ta girmi Sultan da shekara d'aya da rabi amma Idan kaga yadda yake respecting nata kamar irin shekara goma ko biyar ta bashi

   Wannan kenan

Wata motor ce k'irar Accord sabon yayi naga ta shigo layin, gidan su Saleema a hankali sai kace mai tausayin k'asa ko tayar motar sa, naga yana driving
Har zan wuce nace sainaga Waye wannan gayen ko wace?

  Sannu a hankali naga tayi parking a k'ofar gidan su Saleema, bai shiga gate d'in gidan ba anan ya tsaya

   K'afar sa d'aya ya fito da ita, wow masha Allah tab lallai dama ance daga k'afa zuwa farce ake gane tsaftar maza shi wannan zan iya cewa 100% ne

  K'afarsa kawai abin kallo ne, takalmi ne buffalo bak'i  mai d'an yatsa ak'afarsa, dogwayen 'yan yatsun sa na k'afa suka k'arawa takalmin nasa kyau

  K'afar sa ja maikyau, farcen sa farare k'al, a around suke, abin sha'awa

  Fitowar sa itace tasaka ni saurin kallon waye wannan? *Imam Deen* kenan yaro matashi da baifi shekara 28 ba, yadi ne milk colour ajikin sa sharara dan ga singlet dayasaka fara k'al ta bayyana ajikin sa ba hula akan sa, sai gashin sa da yasha gyara yana kyalli irin na Fulani Yola

SHI NAKE SOWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu