DUNIYARMU-KARSHE THE-END

886 33 0
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA.

BABI NA ARBA'IN DA DAYA
KARSHE.............THE-END

A hankali ya sauka daga kan keke-Napep din yana mai cizon laɓɓa da alamun yana cikin yanayi na zafin ciwo da yake damunsa ne. kallo daya zakayi masa ka kautar da fuskarka musamman yarda ya rame wasu kuraje duk sun bata masa fuska da jiki tafiya ma da kyar yake yi. juya wa yayi zai wuce ba tare da ya baiwa mai Napep din kudi da sauri mai Napep din ya turo gami da shan gabansa.
"Malam ya haka, ya zaka wuce ba tare da ka ban hakkina ba".
ko kallon sa bai yi ba ya cigaba da tafiya hakan ya kara tunzura mai Napep ya roko wuyar rigarsa wacce duk ta gama fiyewa daga hayyacinta T-shirt ce mai ruwan toka amma saboda tsabar datti da rashin tsafta duk ta rine ta koma baka.
"malam wai ya haka ne kudina fa zaka bani wallahi ko kuma wallahi nake ta maka rashin mutuncin".
Wank irin kallo ya yi masa cikin cizon laɓɓa.
"bani da kudi kuma ban san inda zan same su ba don haka sakar min wuyar riga".
zaro idanu mai Napep yayi yana dubansa cikin takaici da dacin zuciya bai san lokaci da ya dauke shi da mari ba ya hambarar dashi can gefe guda ya zube mutanan dake wucewa ne suka lura da sauri suka shiga tsakani suna tambayar ba'asi nan mai Napep ya kora musu bayani nan suka bashi hakuri tsaki ja ya dauki Napep dinsa saura kadan ya take masa kafa ya wuce abin sa.
Sai da ya ga ma numfarfashinsa sannan ya mike ya cigaba da tafiya har ya isa kofar gidan wanda kallo daya zakayi wa kofar kasan akwai abin da ke faruwa a cikin sa can gefe guda ya rabe ya kira wani Almajira shi kasan Almajirin so yayi ya fice ganin yanayin da mutumin da ya kira shi yake yana ɗarɗarya isa gareshi.
Nan yace dashi "shiga nan gidan kace ana Sallama da Bahijja".
kuri Almajirin yayi masa kamar bai ji abin da yace ba sai da ya sake maimaitawa sannan ya ja jiki ya shiga cikin gidan mutane cike sai faman aiki ake yi yan'uwa da abokanan arzuki Almajira ya shiga rarraba ta inda zai hango Bahijja domin ya san kuma ya san bikin ta ake yi amma mamaki yake yi yarda waccan mutumin yace ya kira ta to waye shi yana cikin wannan tunanin ya hangota ta fito daga cikin daki jikinta sanye da hijabi har kasa fuskar nan ta ta tasha gyara sai kalli take yi da daukar ido cikin sauri ya isa gareta yana mai sanar da ita ana kiran ta da mamaki ta dube shi tana tambayarsa waye kai ya girgiza mata alamun bai sani ba gaban ta ne taji ya fadi lokaci guda amma hakan bai hana son ganin waye idon mutane ta fakaita ta ja almajirin kamar zata aike shi sukayi waje turus ta tsaya a bakin kofa lokacin da Almajirin ya nuna mata mai kiran nata zuciyarta ce ta buga kallon mutumin take kamar mahaukaci amma ba mahaukaci bane da alamun dai ba mai lafiya bane kamar ba za tahe ba amma zuciyarta ta shiga tunzura ta domin zuwa cikin jan jiki da faduwar gaba ta nufi wajansa har ta isa ba ta gane waye ba saboda kan sa a sunkuye yake motsin da yaji ne ya tabbatr masa da akwai mutum akan sa tun daga yatsun kafarta ya fara kallo sun sha kushi na jan lalle sai daukar idanu zara-zaran yatsunta suke da sauri ya dago kai gabadaya ya dire akan ta wa zata gani wata irin karamar kara ta saki gami da furta "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un MUBASHEER".
ta dafe kirji gami da zazzaro idanuwa waje ta dora da cewa.
"me zan gani haka mai ya sa meka?".
jikin sa na kyarma ya fara magana cikin hawaye.
"Bahijja kin ga yarda na zama koma kin ga yarda rayuwa ta juya min baya ko kin ga yarda na zama abin gudu da kyankyami a rayuwa ko saboda halin da zuciya ta jefani".
shiru tayi tana jin sa can kasar zuciyarsa ba abin da take yi sai Allah ya kara saboda Mubasheer yana sahun mutane manya-manya da suka baiwa rayuwarta damar lalacewa Allah kenan maji kan bawansa murmushi tayi kafin ta dube shi.
"rayuwa kenan Mubasheer in dai mutum ya dau duniya da zafi to da zafi zai gani Allah na gani Mubasheer kana cikin mutunan da sukayi sanadin lalacewar rayuwata ba tare da na sani ko na farga ba".
Da mamaki ya shiga dubanta idanuwansa cike da hawaye.
"Haba Bahijja mai ya sa zaki ce haka kin sani fa ina son ki ina kaunar ki yanzu haka zuwa nayi ki taimaka min mu rufawa juna asiri MUYI AURE".
wata irin zabura tayi kafin ta dubeshi ji take kamar ta shake shi ya mutu.
"baka da hankali Mubasheer kan ka rawa yake yi to kasani wallahi ba zan iya auranka ba ji bi ka sauran kiris ka mutane nasani wajan jajibe jajiban ka kaje ka kwaso kamayamaya shine zaka zo ka jona min ka kara illa ta min rayuwa to bari kaji yanzu halin da ake ciki ma yau za a daura min aure baka ga sai tashin kamshin amare nake yi ba don haka malam ka ja ki  ka bar mana layi ba kar a ganka ka jazami bala'i".
ta na gama fadin haka ta juya tayi cikin gida abin ta tana ji yana kiranta tayi banza dashi kamar ba ta ji sa hawaye ne suke zuba a fuskarsa kowa ya tsane shi kowa ya ki yarda ya rabeshi ya zo in da yake zaton nan kadai ne zai samu kulawa nan ma ta nuna wulakanci da rashin arzuki a gareshi sau yau ya kara nadamar rayuwar da yayi wacce sam bata amfaneshi da komai ba bai ga amfani kwadayi da buri a rayuwa ba ya ga illa zamani da ruɗin sa hannu ya sa ya dauke hawayen dake zubo masa ya miki cikin jan jiki yana tari ya bar layi tafiya yake wacce bai san in da zai dosa ba bai san ina ya nufa ba.
   Misalin Karfe biyu da rabi bayan an sauko juma'a ak daura auran MANSOOR YUSUF GALANDANCI da BAHIJJA ALHAJI NASEER a babbar masallacin dorayi na Sheikh Ja'afar Mahmud Adam bisa sadaki nai dubu dari biyu dandazon mutanan da suka halacci daurin aure ba a magana kamar shugaban ƙasa ne ya dire ranar sabon titi cika yayi makil sai kusan karfe biyar san nan aka samu raguwar jamaa kamar yarda Alhaji kabeer yayi wa ɗan sa Alkawari kawo shi wajn dauran Bahijja ya kawo shi har gaisawa sukayi da MANSOOR wanda ba karamin mamaki yayi ba da ya gan su nan Alhaji kabeer ya nema yafiya da afuwa sagalo yayi yana kallonsa gami da yatsine fuska abu daya zai hana shi yi masa rashin mutunci shi yau rana ce ta musamman gareshi magana ya yaɓa masu sannan ya wuce nan suka sami mahaifin Bahijja shi kuwa ko kallon su bai yi ba bai san ma an yi ruwan su a wajan ba haka aka watse har kowa ya  kama gabansa kowa sai san barka yake yi da fatan zaman lafiya da zuria ta gari.
Suna komawa gida Alhaji nasuru ya tadda su Adam da mahaifinsa har da Hajiya Laila zaune cikin mota suna jiransa fuska yayi kamar bai gansu ba sai haba haba yake yi da mutane da kyar da sidin goshi har sai da wasu yan uwansa suka sanya baki akan ganin da sukayi Alhaji Kabeer sai bin sa yake yi amma yaki kula shi ko da ya kula shi din Alhaji kabeer ke ta kwarara zance amma shi keya ya bashi hakuri yake ba shi da ban mamaki da neman afuwa amma ina ko gezau har sai da Adam ya yazo ya zube a gabansa yana faman kuka sannan ya juye ya kalle shi yanayin da ya gansa zuciyarsa ta dan raunana musamman da ya ga halin da yake ciki kamar wanda ya shekara yana jinya ya san tabbas duniya ta koya masa hankali da nutsuwa kuma ya ga alamun yayi nadamar abin da yayi ganin za su tare masa jama sanya shi cew komai ya wuce ya yafe musu nan suka ne mi ganin Bahijja nan fa Alhaji nasuru ya dire yace bai san zance ba 'yarsa ba za ta ganu ba saboda ta zama matar wani in ma yafiyarta suke nema ya ari bakin ta yafe musu ba yarda suka iya haka suka ja jiki suka bar wajan zuciyarsu cike da abubuwa masu dauke da kayan nadama jikin su yayi matukar yin san yi ba kadan ba duniya kenan tafi bagaruwa iya jima.

Shagali akayi sosai bayan daurin aure anyi bidia na kin karawa amarya ta tare a gidan ta dake Sharada phase tsararran gida na gani ma fada kallo daya zakayi masa kasan nera tayi kuka a cikin sa zuciyoyi da yawa sun damu natsuwa musamman zuciyoyi uku
Bahijja Alhaji Nasuru Mansoor ango
Sai fata alheri a rayuwa...
------@@@--------

Kana shigo cikin garin Kauyen gurmana zaka san ana shagali na kece raini wanda zaa iya cewa ba a taba yin sa ba a garin ko ina ka bi yan sanda sai zirga-zirga suke yi ba abin da ke tashi sai sautin taken su gari ya cika makil kowa ka gani cikin farin ciki da annashawa Dsp Avva kuwa ba a magana sai faman yake baki ake yi tun da yaji an daura auran sa da Shukura yake ta faman hamdala da godiya ga Allah haka dayan Ango Shukuranu Majnun😁 baki har kunne sai kai kawo yake yi ya rasa ma ina zai sa kan sa don farinciki da jindadi abokanansa si tsokanarsa sukeyi shi kuma sai kara yashe baki yake yi biki akayi na gargara kowa sai som barka yake yi sun Inna Lubabatu da Umma uwayen amarya jeka ka gan su anci kwalliya sai haba haba ake da mutane masoya.
Misalin Karfe hudu motoci daukar Amarya Shukura suka dire jerin gwano sukayi sai busa akeyi na taken yan sanda lokacin da Shukura taji wai za a tafi da ita nan hankali ya tashi ta yi tsuru tsuru da idanu kwalla take faman yi tana gogewa gabanta sai faduwa yake yi wai ita yau za a raba da ummanta da yayanta shukuranu za ta koma can wani wajan in da babu su ta rayuwa da wani daban amatsayin mijinta ba ta san lokacin da ta fara kuka ba tun tanayi kadan kadan ana rarrashin ta ta ga da gaske tafiya za ayi da ita haba ai sai ta kware baki tana kuka Umma tana jiyo ta amma ta ki zuwa domin itama zuciyarta tayo rauni sosai gaf take da fashewa da kuka tana zaune can kuryar daki aka shigo da Shukura nan ta shiga yi mata nasihi akan bin miji da hakkin miji da hakuri da gidan aure a duk yarda ta riske shi ta na tunatar da ita gidan aure bauta ake zuwa yi ba wai zaman jindadi ba ne komai ta gani mai dadi da akasin sa ta rungume shi tayi tattalin sirrinta tsakaninta da mijinta.
Nasiha sosai take mata muryarta na rawa kwalla sun cika mata idanu ita kuwa Shukura kuka take yi kamar ranta zai fice daga jikinta Umma ta taso ta rungumeta tana kara rarrashin da kyar aka raba su kana nufi dakin Shukuranu nan shi yayi tasa nasihar a matsayinsa na yaya zuciyar cike take da kewar kanwarsa daurewa kai yake yi da kan sa ya kama hannunta yana rarrashin ta har ya fice da ita daga gidan yana mai kara tunasar da ita tayi hakuri tayi hakuri akan komai da ta samu a gidan auran ta da kan sa ya saka cikin mota ya kulle tana hango Umma a bakin kofa tana daga mata hannu ita ma tana daga mata Shukuranu shima yana daga mata nan motaci da suka cika da yan kai amarya suka fara tafiya motar amarya ita ce a tsakiya suka dauki hanya Shukura sai faman rusa kuka take yi ana rarrashinta
A bangaren Salma kuwa kwarama aka kwasa da Inna Lubabatu duk murnar da take yi da ɗoki ta aurar da 'ya duk sai da ta daina ganin da gaske raba za ayi da Salma karo na biyu tun kafin ta gama jajan rabuwar farko da sukayi ji take yi kamar wacce za a rabata da ita har abada ba za ta sake ganin ta ba sai da akayi da gaske sannan ta saki Salma tana kuka ita ma tanayi sai da suka baiwa kowa na wajan tausayi har shi Baban Salma sai da yayi kwalla domin sun shaku da 'yar tasu soyayya ce mai girma da kaunar juna a tsakaninsu  amma ya za ayi rabuwa ta zama dole zaman mace dakin mijinta shi yafi dacewa su dai fatan su zaman lafiya mai daure har gaban abada
  AURE YAKIN MATA.
haka abin yake amare dai duk sun tare a gidan su sai fatan zaman lafiya mai dorewa

KARSHE
ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALIN

GODIYA GA ALLAH MAI KOWA MAI KOMAI MAI RAYA DA KASHE WA ALLAH YAI DADIN TSIRA GA ANNABIN DA NA KARSHE GODIYA GA ALLAH DA YA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DUNIYAMU ALLAH YA YAE MANI KURAKURAN DA NAYI ACIKI ALHERI CIKI KUMA ALLAH YA YI MASA KAYAN ALHERI DA SHI DUNIYA DA LAHIRA

GODIYA MARAS DADI GAREKU MAKARANTA NA MASU JIMIRIN BIBIYA TUN DAGA FARKON LABARIN NAN HAR ZUWA ƘARSHE NAGODE SOSAI ALLAH YA BAR ZUMUNCI DA AMINCI A TSAKANI

GODIYA GAREKU READS MY WATTPAD INA GODIYA HAR DA KU YAN LA6E...LOLZ

MY WATTPAD WTTRS

BEIBE ISA
UMMU ABDUOL
SANAH MATAZU
RASH-KARDAM
LUBABATU MAITAFSI
KHADIJA CANDY
JEEEDO LAWAL
UMM-YESMIN
RUFAIDA OMAR
AYSHA YA'U KURA
AYSHA CHU-CHU
SANAH SHAHADA

Allah ya kara basira da hazaka

My lovely GROUP
ZAMANI WTTRS
INA GODIYA GAREKU SOSAI DA SOSAI
ALLAH YA KARA HADA KAWUNANMU CIKIN AMINCI DA NAGARTA YAKAREMU DA SHARRIN ABIN KI INA GODIYA SOSAI

WANNAN LABARIN SADAUKARWA NE KACOKAN GAREMU RABIN JIKINA

NASEER MUHAMMAD LAWAL
NAZEERA MUHAMMAD LAWAL
NAJA'ATU MUHAMMAD LAWAL
BASHEER MUHAMMAD LAWAL
NANA HAFSAT MUHAMMAD LAWAL
Allah ya kara hada kawunan mu ya bar mu cikin aminci da nagarta

TUKUICI NAKI NE

BASEERA HARUNA SA'AD
MAMAN KHADEEJA
ALLAH YA RAYATA YA ALBARKCI RAYUWAR INA GAISUWA GAREKI YAR UWATA TA KAINA

MASHA ALLAH! MASHA ALLAH!! MASHA ALLAH!!!.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 12, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now