DUNIYARMU-11

703 31 0
                                    

  ***
DUNIYARMU
Na
KAMALA MINNA.
BABI NA SHA DAYA
misalin karfe biyar na yamma suka isa cikin Birnin kano kafin su isa gidan su Heejat sai da suka biya ta otal suka ci abinci sukayi nak  sannan suka dauki hanyar Dorayi domin isowa gida tunda suka shigo layin Heejat take zuba idanuwa ta na kallon unguwarsu wacce tayi rayuwa irin biyu ta dadi da akasinta murmushi ta saki lokacin da ta tuna da mamin ta hawaye su dan kwaranyo mata ta sa hannu ta dauke su mubasheer na lura da ita amma bai ce da ita ko mai ba illah kai da ya girgiza domin kuwa duk ya San akan me ta shiga wannan yanayin lokaci guda parking din da yayi ne ya dawo da ita hayyacin ta ta dubeshi cikin alamun tambaya kai ya gyada mata tare da yi mata nuni da kofar gidan su da sauri ta kai duban ta kofar gidan yana nan yarda ta san shi ba abin da ya sauya sai lalacewa da wani sashin ya fara yi na alamun tsufa shagon mahaifinta ya na nan yarda ta san shi ba abin da ya sauya ya na bude da alamun yana ciki shiru tayi kamar mai nazari akan wani abu wanda yayi mata dirar BAZATA cikin sauri ta balle murfin motar ta fice batare da tace da mubasheer komai ba yanayin unguwar ba wasu mutane sai yan tsiraru hakan bai hana a shiga kallo ta ba ita ma bin mutanan unguwar ta su take yi da kallo har ta isa kofar shagon maihaifin nata ya na shingide hannusa rike da casbaha yana ja idanuwan sa a rufe kamar mai barci da sallama tashiga cikin shagon ta na bin sa da kallo har yanzu yana nan da kayan sa cike ba alamun aci baya sai ci gaba da aka samu hakan yayi mata dadi sosai har sai da tasaki murmushi mai kayatarwa ta kai duban ta ga mahaifinta wanda izuwa wannan lokaci ya bude idanuwan sa ya na duban ta cikin mamaki ganin ta fuskar sa na bayyanar da yalwataccen murmushi mai cike da muradan jindadi tashi yayi ya zauna da kyau tare da kafeta da idanuwasa sannan ya ni sa "Bahijjata ce yau ta zo gareni ba zato ba tsammani" murmushi tayi tare da isa gareshi ta zauna ta kwantar da kan ta kan kafatarsa cikin shagwa6ar6iyar murya tace"Abbana nayi kewarka sosai wallah shiyasa ma ko da zan taho ban sanar da kai ba don nayi maka zuwan BAZATA" ta karashe cikin kyalkyalar dariya shi ma dariya ya shiga yi irin ta su ta manya ya dube ta lokaci guda wani abu ya dalsu a zuciyar sa ba Wanda yake gani a wannan lokaci kan fuskar Bahijjarsa sai mami ya kura mata idanu ta na yi masa wani kayataccen murmushi mai cike da muradan jindadi shima martani ya shiga mai da mataa bahijat da ta lura da irin halin da mahaifinta ya shiga duk sai ta tsargu domin kallon da yakeyi mata tamkar mai son gano wani abu a game da ita da sauri ta daga kanta daga kafatar sa tare da hure masa idanuwa firgigin ya dawo hayyacin sa fuskar sa ta dan sauya izuwa halin damuwa hakan yasan hejat cewa"Abba lafiya na ga ka canza lokaci guda?" girgiza mata kai yayi tare da murmushi mai kama da yake "bakomai bahijjata"tashi tayi ba tare da tace dashi komai ba har ta fara tafiya sai kuma ta ja burki ta tsaya ta juyo ta dubeshi idanuwan ta sun kada sun yi jajir" abbana mami ka tuna ko" ta fadi ta na goge idanuwan ta da hawaye sukayi mata marhabin shiru yayi ba tare da yace da ita kala ba har ta kusan barin cikin shagon "ki shiga cikin gida ki zauna gani nan shigo wa" kai ta gyada masa ta koma wajan motar ta tayi wa mubasheer magana dacewa"fito Ku gaisa da da abbana sannan kuma ka buds but ka kwaso kayan ciki ka shigo da shi cikin gidan" ta na gama fadi ta juyo da sauri  ta fada cikin gida dakin mamin ta tashi ga abin mamaki har yanzu ya nan yarda ta barshi zaman dirshan tayi tsakar dakin idanuwan ta suka shiga zubar hawaye zafi da radadin zuciya ya turnuke mata kirji abin da ya faru da ita wanda ya zama silar rugujewar kwanciyar hankalin rayuwarta da jindadi Wanda ya kasance silar rasa mahaifiyarta kuka ne ya kunce mata tashiga yin sa ba kankautatawa kamar ranta zai bar jikin ta cikin wannan halin mahaifinta ya shigo ya same ta yayi matukar mamaki ganin abin da ke faduwa da hejat da sauri ya isa  gareta " me na ke shirin gani cikin rayuwa ta Mara kyan gani"/da sauri ta dauke hawayen jin furucin da mahaifin nata yayi"yi hakuri Abba wallahi tun da na shigo dakin nan zuciya ta ta karaya gabadaya na kasa daurewa ban San ban lokacin da hawayen su ka fara zuba ba" margaya kai yayi cikin yanayi na jimami"amma dai kin sa kuka ba naki bane ko?"shiru tayi gami da sunkuyar da kai domin ta lura mahaifin ta bai ji dadin abin tayi ba amma ya za tayi dole ne rashin mahaifiyar ta ya dame ta domin kuwa ba ta dadin rai ta bar duniya ba ta bar duniya da bakin ciki da tarin takaici Wanda ta sanadiyyar abin da akayi mata ne ya assasa haka cikin murya raunan na ta dubi mahaifin na ta "na dai na" shiru yayi na tare da yace da ita wani abuba dakin ya dau shiru a daidai lokacin mubasheer yayi sallama da sauri Abba ya dubi hejat ba tare da yayi magana ba hakan da ta gani alamun kallon tuhuma ne da sauri tace"direba na ne Wanda muka taho dashi" da mamaki ya dubeta "direba kuma?" Gyada kai tayi cikin yanayin rashin gaskiya don yanayi da ta lura da kallon da mahaifin ta ya ke mata na tuhuma da rashin gamsuwa da abin da tace "kamar na san fuskar sa amma dan ina ne shi" wani bugu taji kirjin ta yayi da sauri ta sabura kamar wacce aka tsikara duk yana lura da ita a dubeshi " nima ban San dan ina bane a dai can garin adam ya sa man min shi a matsayin direba" "shikenan" abin da yace kenan da ganan bai kara ba da sauri ta mike cikin yanayi na rashin gaskiya jikin ta sai 6ari yakeyi ta fice daga dakin tsaye ta tadda mubasheer tsakar gidan duk ya zube kayan duban tayi a Dan wulakance cikin salon rada tace dashi"hala ba kayi wa Abba magana ba ne?" girgiza kai yayi alamun eh da saurita sake duban sa cikin yanayi na takaici"to wallahi ka Ku San tona mana asiri don kuwa yanzu maganar da akae ciki yace kamar ya San fuskar ka"cikin nuna ba maganar tata rashin muhimmancin yace" to meye don ya sanni baki gaya masa ko ni wanene a gareki ba" da mamaki ta dubi mubasheer ba tare da tace dashi komai ba ta kwa6e fuska gami da Jan tsaki ta juya ta koma cikin dakin har yanzu ya na zaune in da ta barshi ta koma ta zauna ta dubeshi cikin dardar "abba ga shi adam yace na baka" ta ciro kudi a jakarta  dami guda ta mika masa sai da ya dube ta sannan ya dubi kudin kamar ba zai amsa ba mai ya gani  kuma sai yace aje su a nan zan dauka"maganar sa tayi matukar dukar mata zuciya ba yasan lokacin da ta furta"abba lafiya kuwa na ga kamar ka sauya" kan sa a kai yayi shiru tsayin mintina biyu sannan ya dago ya dubeta "kin fara canza wa bahijja gabadaya rayuwarki kin sauya ta ba tun yanzu ba na lura da haka tun kafin kiyi aure halayenki gabadaya ki ka canza su rayuwarki gabadaya kin sauya kin siyo wa kan ki WATA RAYUWA ta daban wacce sam ba ta dace dake ba cikin duniyarki" tun da yafara kwararon zancen sa gabanta ya shiga bugu ba k'ank'autawa gumi mai dauke da kayan tashin hankali ya shiga karyo mata ba abin da take wassafawa a zuciyar sai tashiga uku ta lalace asirin ta dake binne shikenan ya bankadu dama duk abin da takeyi mahaifinta na lura da ita,in kuwa haka ne ta gama yawo domin kuwa ta San abin kunya dana takaici su ne za suyi wa rayuwarta lale marhabin ji tayi kamar ta nitse cikin kasa don kunya yanzu ita ya zatayi me ya dace tayi dan kubutar da kanta da abin kunyar dake shirin yiwa rayuwar ta tsinke.."bahijjat ban yi zato ko tsammani haka rayuwarki za ta gurbace ba cikin kankanin lokaci ki Sauya tunani da damuwa cikin duniyarki kin kasa yarda da kaddara duk yarda ta zo miki na lura tun lokacin da wannan kaddarar ta fado cikin rayuwarki sam kika canza duk wasu kayan alheri da birgewa kika ja baya da su damuwa da kulafici akan abin da yarigaya ya faru kuma ba dawowa zai ba shi kika saka a ranki yake kokarin salwantar miki da rayuwa me ya haka mai ya sa kika kasa kwantar da hankalin ki ji beki duk kin je me kin kode kamar ba bahijjar da na sani a can ba ya ba" abin da kunnuwanta kenan suka jiye mata daga furucin mahaifin nata hakan ba kamar dakar mata da zuciya yayi ba domin abin da take tunani bashi ne ya tabbata  ba ajiyar zuciya tayi mai karfi ta dago ta dubi mahaifinta fuskar ta kamar mai son fashewa da kuka tace"ba haka bane Abba na yarda da kaddara kuma na dauke nasani duk abin da ya faru da ni daga Allah ne tun fil'azal ya kaddara sai hakan ta faru.."da sauri ya daga mata hannu "ban yarda ba bahijjat baki yarda da ita ba da kin yarda da ita da rayuwarki ba ta canza lokaci guda ba" shiru tayi ba ta sake tsinka masa ba hakan shi ma bai yi kokarin tsinkawa ba sai da suka shafe dakiku fiye da hudu a haka ganin da tayi ba shi da niyyar cewa wani abu hakan ya Sanya ta mikewa ta koma tsakar gidan in da mubasheer yake har zuwa wannan lokaci tsaye yake suka shiga shigo da kayan cikin daki amma shi mubasheer bai shiga ba sai ya aje mata a kofar dakin ta kara sa dashi a haka har su kammala Abba ya tashi yafito ya dubi mubasheer cikin nuna kualawa sosai"sannu da kokari ko ka sha gajiya"yake mubasheer yayi Dan ya irin kallon da Abba keyi masa sai ya Sanya shi shan jinin jikin sa ya shiga Sosa kewa"yawwa Abba dafatan mun same Ku lafiya"kai kawai ya gyada masa ba tare da ya sake tsinkawa ba yayi hanyar waje.
**  **   **
kwanar su bahijjat sati daya da zuwa kano ba in da ta leka ko da ko kofar gida domin Abba ya ce bai amince ta dinga fita ba tunda yanzu ba da bane dole komai za tayi sai ta sanar da mijinta tunda shine da hakkin komai na ta komai za tayi dole sai da yardar sa da amince wa maganganun Abba sun yi matukar bata mata rai saboda ita bata ga amfanin Dan zata yi Abu sai ta sanar da adam ba saboda bai da wata abin da zai sanya ta sanar dashi da kuwa ya na amsa sunan mijinta to ita ba za ta iya ba sam! Tun da akayi haka ta kulle kan ta a daki ba in da take fitowa ko da tsakar gida sai da uzuri mubasheer ba yarda bai yi da ita ba ko da satar hanya ta dinga yi amma ta nuna kin yarda da haka in ya matsa mata ma har kusan fada sukeyi in ya yi nacin ya ga ta ki yarda sai ya fita shi kadai ya gama walagigituwar sa sa warshagare walle din sa ya dawo ko abu take bukata sai dai ta ba mubasheer sautu ya taho mata dashi sam jinin Abba bai gauraya da na mubasheer ba tun da suka zo kawai kallon sa take amma zuciyar sa na zargi ba mai gaskiya bane kawai yana nuna azahiri ne  ya aminta dashi tun da bahijjat tace direban  tane amma fa akwai tarin SHAKKA da yakeyi akan sa.
Kwance take hannunta rike da faskekiyar wayar ta kallo daya zakayi mata ka tabbatar abin da takeyi ya na matukar sanya nishadi da muradan jindadi yanayin murmushi fuskar da da walwala da suka yi wa fuskar k'awa kamar wacce aka tsikara ta mike a hanzarce tare da kallon waya cikin zare idanu alamun mamaki ganin Kiran da taga ya shiga da sauri ta danna maballan amsa kira ta kai kunnan ta cikin sigar wasa tace"hegiyar gari ai na dauka ba zaki kirani ba ne"daga can dayam Barin aka kyalkyale da dariya ayshanty tace "ke dai bari duniyar ce ta zo min da muradai masu matukar burgewa cikin yan kwana kin nan jin kai na nake a sama-sama kamar wacce aka zunduma gidan aljanna"hejat ta kara gyara zaman ta dauke tare da cewa" fe samin don Allah me ke faruwa ne?" Cikin dariya ayshanty tace"anki yariya da kin tsaya da kin kwashi shawarma mai lasisi don wallahi ba karamin kamu mukayi gidan alhajin nan ba don har sai da naji tausayin sa ya so dalsuwa a zuciya ta wallahi saboda tatsar da akayi masa ba ta wasa bane mun talauta shi don ina tunanin mutum nan ko banyi hauka tuburan ba to sai yayi ta wucin gadi" hejat ta numfasa kamar ba zatayi magana can sai kuma tace"yanzu ya ake ciki kun gama komai kenan""tun yaushe har kowa ya yagi rabon sa ya kama gaban sa"cewar ayshanty ta fadi cikin zakuwa cikin sigar wasa hejat tace"dafatan an aje min ka so na.." A hanzarce ta tare "kutumar ubara can ai wallahi karya ki kikeyi yarinya ko sisi ba zaki ci ba uban wa ya hanaki ki tsaya ayi da ke wato so kike mu zama kura da shan bugu gardi da amshe jaka kenan?" Kyalkyalar dariya ta shiga yi "ke fa shatu ba mutunci gareki in dai akan kudi ne" "to ce miki akayi ni irinki ce mai sakaki da abokan rayuwa" shiru hejat tayi jin ayshanty na Neman ya6a mata magana a fakaice da sauri ta tsinke zaran zancen da cewa"ina SAUDAT" yatsine fuska tayi gaban tana ganin ta sannan tace"ni tun ranar da aka gama wannan aikin rabona da ganin ta ai ni lamarin ta ya fara ba ni tsoro wallahi" da sauri ayshanty ta tare ta"dalili?" Sake yatsine fuska tayi sannan tace"kin fi kowa sani hejat ba sai na tunatar dake ba" shiru tayi kamar mai tunanin wani abu na daban can sai ta numfasa sannan tace" gaskiya Saudat tana cikin takaicin rayuwa da rashin rabo tsakani har ga Allah duk lalacewar iyaye ba ka ma ace ka zama silar ajalinsu ba a matsayin ka na d'an da suka Haifa wannan wani irin ASARAR RAYUWA ce gaskiya tana cikin TSAKA MAI WUYA" "uhmm ke dai bari hejat nima har yanzu zuciya ta tarardadi take akan ta wallahi tsoron ta nake duk mutumin da ya iya kashe iyayen sa aiko zai iya kashe kowa dan kuwa imani da dangin tausayi sun rabu da rayuwar sa" maganar Saudat ta fara gundurar hejat don haka tace "don Allah mu bar wannan zancen kayan takaicin ni fa ina ga ko na dawo ba zan sake tu'amali da ita ba gaskiya" "nima abin da nake tunani akai kenan amma kafin mu zartar da haka mu lallaba ta mu samu labarin abin da yasa ta aikata wannan BAHAGON HUKUNCIN ga iyayen a domin hakan zai ba mu damar gudanar da abubuwan akan ta da salin wace ce ida don kar muyi lalube a duhu" gyada kai hejat tayi alamun hakan yayi nan suka cigaba da hirar su har zuwa wani lokaci sukayi sallama ajiyar wayar hejat kamar da mintina biyu mubasheer ya shigo cikin gida tun daga tsakar gidan ta tsinkayo shi yana kwala mata kira tsaki ta ja gami da koma wa ta kwanta ta kulle idanuwan alamun kamar mai jin barci haka ya shigo ya same ta tokarewa yayi bakin kofa ya zuba Mata idanuwa yana kare mata kallo jikin ta sanye take da doguwar Riga mai ruwar madara takama jikin ta sosai ga santsi da take dashi hakan yakara bayyanar da yanayin suffar jikinta yanayin kallon da yake cilla mata zai tabbatar maka da ya kwadaitu da ita matuka don har hadiyar yuwu yakeyi ji kake makwat hakan ne yasanya hejat saurin bude ido gami da tashi zaune wata uwar harara ta cilla masa gami da Jan tsaki"kallon na lafiya ne?" Karasowa yayi cikin dakin ya samu waje kusa da ita yana kokarin zama da sauri ta jakin ta can gefe tana wurgamasa wani malalacin kallo "ka ga mubasheer ba na son irin wannan abin da kake min wai shin ka man ta a ina muke ne?"dariya yayi San nan yace" yau gaskiya so nake mu fita wannan zaman kurkukun da ki keyi ya na fa takurawa rayuwa ta gaskiya ya kamata ki San abin yi don wallahi yau sai mun fita dake" mamaki dauke a fuskar ta ta dubeshi ba tare da ta tsinka ba kai ya gyada mata alamar tabbatar da haka kwa6e baki tayi sannan tace"kai ma kasan abin da ba zai yuwu ba ne don Abba sam ba yarda zai yi ba" murmushi yayi sannan yace"ai na gama da Abba don ya amince da yarjewa mu fita tare din" kwale idanuwa tayi tana duban sa da mamaki dauke a fuskar ta tana tattama akan maganar mubasheer hakan da ya gani kamar ba ta yi amanna da maganar tasa ba ya sake duban ta cikin yanayi da gaske yake magana"ki yarda wallahi Abba ta yarje mu fita tare don cewa nayi zaki asibiti awo" wata irin zabura tayi tare da dakin kara tana duban sa hannunta aka"mubasheer kalau kake kuwa kasan abin da kake kokarin yi wannan fa abin da kayi bai da Mara ba da daukar wuka ka da6a min aciki" ta karashe maganar cikin halin jin haushi mubasheer baki ya saki yana ta babbaka dariya kamar wanda ya ga wani abu na ban dariya sai da yayi dariyar sa ta isheshi sannan ya dube ta har zuwa lokacin fuskar sa dariya na bayyane"na ga duk kin wani birkice ne da ga fadin wannan dan abin Wanda bai ta ka kara yakarya ba.."da sauri ta tare shi cikin tsawa ta nuna shi da hannu "a na ka shegen tunanin kenan ka ke ganin ba wani  abu ba ne a ciki ni na san halin da zan shi ga" duban ta yayi yana mai yatsine fuska "hali fa kikace ke kuwa wani irin hali zaki shiga a kan wannan yar maganar" tashi tayi tsaye tayi taku kamar biyu sannan ta juyo ta fuskance shi"kasan abba zai iya bugawa adam waya akan wannan maganar awon a tunanin sa ciki gareshi ka na ganin in har adam ya ji me kake tunanin zai faru kasan tun da muka yi aure ko dakin sa ban ta ba zuwa da sunan kwana ba to in har yaji zancen ciki ka na ganin ba zan shiga tashin hankali uban wa zan ce yayi min cikin?" shiru yayi yana nazarin maganganun hejat ya dago kai ya dube ta sannan yace"karki damu duk wannan ba abin tashin hankali ba ne in dai ta adam ne mai sauki ne sai kace ke ba mace ba ce kin fi kowa sanin hanyoyin da zaki bi wajan kwatar kan ki duba da yanayin da kuke zama fa ba zaman lafiya kuke ba tsakanin Ku don haka don Allah bar zancen kawai shirya mutafi don nace masa ba dade wa za muyi ba" komawa tayi ta zauna ta buga tagumi hakan da mubasheer ya gani yakara matsala gareta"karki ba da mata mana ke fa daban ce cikin su" juyo tayi da idanuwan ta ta dubeshi"ba kasan halin Abba bane har yanzu fa kallon rashin gaskiya yake yi min ka ga kuwa idanuwan sa nakai na kiris yake jira ya ji wani abu wallahi na kade ni har gayye na in ya ji wani abu" hannnun ta ya jayo ya shiga matsawa cikin salon na narkar da jiki da kwantar da hankali idanuwan su suka hadu da na juna da sauri ta kau da na ta ta mike a hanzarce ta fada bandaki tayi wanka ta shirya tsab! ba wata kwalliya tayi ba sosai ko hoda ba ta saka ba kawai lotion ta muntsuka sai lip-rose ta mai da doguwar rigar ta ta gyara saurin Dan kwalin kan ta sannan ta dauko zabgegen hijibi ta zurma tun da ta fara shirya wa mubasheer bai tsinka ba sai da ya ga ta zurma zabgegen hijabin nan da sauri ya dubeta"meye haka don Allah sai kace wacce take takaba"dariya ta tuntsire da ita ta dube shi"saboda halin tsaro" ta daga masa gira hakan da tayi ya ganar dashi karatun nata shima dariya ya kama yi haka ta kammala suka fito tare har kofar gida ta isa wajan Abban ta dake zaune bakin shagon sa murmushi dauke a fuskar ta ta karasa har kasa ta durkusa "Abba sannu da hutawa" duban ta yayi shima ya murmusa"har an fito bahijjata mubasheer yace zaki asibiti ko?" Kai ta gyada masa "dafatan kin gayawa mijin naki" an zo wajan ta fadi a zuciyar ta gaban ya muga da sauri ta dago ta dubi Abban nata tace"eh ya sani ai" ya gyada kai to shikenan a dawo lafiya a kula sosai bahijjata" ta amsa da to Abba ta mike tayi wajan da mubasheer yayi parking ta bude gidan baya tashiga suka muka ta na daga wa Abban nata hannu shima ya na daga mata. tun da suka hau titi ba Wanda ya tsinka a tsakanin su sai da sukayi tafiya sosai daidai danja din kofar famfo duk tsaya hejat tace"yanzu da ka ce mufito ina muka dosa?" ta glass gaba motar ya dubeta sannan yace" duk in da kike da muradan zuwa can mukayi" kwa6e baki tayi "nan fa daya wallahi kadai kawai kai mu in da ka San zamu huta" gyada kai yayi gami dacewa "shikenan" a daidai lokacin aka basu hannu ya dauki hanyar titin da za ta sada su da kofar gadon k'aya...

DUNIYARMU (Compelet)Onde as histórias ganham vida. Descobre agora