DUNIYARMU-29

343 12 0
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA.

BABI NA ASHIRIN DA TARA.

Safah da marwa kawai Alhaji kabeer ke yi jikinsa ba abin da yake yi sai mazari kamar wanda ake kaɗawa gangi lokaci lokaci ya na sanya babbar rigarsa yana dauke gumin dake wanke masa fuska duƙ da halin sanyi da ake ciki amma tashin hankali da rashin natsuwar da yake ciki ya shanye duk wani alamu na sanyi daga jikinsa lokaci lokaci yana juyar da kallon sa zuwa dakin da yake hango an shigar da ɗan nashi ckin wani irin hali wanda yake tsakanin RAYUWA KO MUTUWA.
Hajiya Laila kuwa zaman dirshan tayi tana ta faman rafsar kuka ba ƙanƙautawa kamar so take ruwan hawaye ya kare daga jikinta gabadaya ya gama fita daga duniyar hayyacinta zuciyarsa ba abinda ke wulwulata sai tashin hankali da tsananin firgici gami da fargaba.
Tun lokacin da Tk ya fuskanci halin da Adam yake ciki ya falle da gudu bai dire ko ina ba sai gabansu Alhaji da suke cikin halin damuwa marashin misali.
Fadowarsa a firgice shi ya assasa dawowarsu cikin hayyacin su gabadaya suka miki zumbur kamar wadanda aka zungurawa allura a jiki ba tare da sun sani ba.
Jikin Tk na rawar tashin hankali ya shiga sanar da su abin da ke faruwa bai kai aya ba Alhaji ya tashi a razana ya yi dakin Adam Tk da hajiya suka rufo masa baya suma dai duk cikin yanayi na firgici.
Sunyi matukar kaɗuwa da yanayin da su ka ga Adam a ciki nan Alhaji cikin rawar jiki ya fara kokarin daukar Adam yana baiwa Tk Umarni da yaje ya fidda mota ita kuwa ajiya sumar tsaye tayi jikinta gabadaya ya daina motsi sai kirjinta dake ta faman bugu fat-fat kamar zuciyarta za ta faso ta yo waje tashin hankalin duniya ji take kamar ita aka juyewa shi ba ta taba zaton lamarin Adam zai kai ga haka ba ba ta taba zaton damuwar tashi takai haka ta rasa mai yake damunsa tayi tambayar duniyar nan amma ba wata gamsasshiyar amsa da za ta dauka ta yi amfani da ita.
Tana cikin wannan tunanin zucin Alhaji ya zungureta ganin ba ta cikin hayyacinta a firgce ta dube shi ba tare da yayi magana ba ta ga sunyi waje da Adam wanda a wannan lokacin gabadaya ya gama ficewa daga hayyaci ba abin dake aiki a jikinsa sai zuciya dake bugawa kana hango bugun da take yi ta saitin kirjinsa.
Da hanzari ta mike zaninta a hannu dan-kwali na kokarin zabewa ya yi kasa cikin janki ta faratafiya tana harɗe hanya a haka har ta fice ba ta tsaya daukar wani abin yafawa ba tayi waje tana isa ta tadda har Tk ya yiwa motar ki lura da yay Alhaji ba zai iya ba domin baya cikin hayyacin sa.
Baya ta bude ta shiga inda Alhaji ke rungume da Adam cikin wani irin mawuyacin hali mai firgita mai imani da tausayin zuci.
Gudu Tk ke zabgawa kamar za su tashi sama amma duk da gudu nan Alhaji gani yake kamar ba tafiya suke fa sai faman cewa yake "Tukur don Allah yi da jiki mana, kana kallon halin da ɗana yake bana so na rasa shi, rashi kamar ni na rasa rayuwa ta ne".
Duk da hajiya na cikin rashin hayyaci amma maganganun mijin nata ya sun dan bata mata rai domin kuwa karara ya bayyana rashin tawakkali da daukar ƙadddara ko wacce iri ce kallon sa tayi sannan ta kalli Adam da sauri ta kau da kai zuciyarta na faman yi ma ɗan ta addu'a samun warakar wannan tashin hankalin da yake ciki mai kokarin tafiya da numfashin sa da ruhi. Tafiya mai nisa sukayi sosai kafin su kara Asibitin Malam Aminu kano Tk nayin Parking ya fita a guje yayi cikin asbitin domin nemo likitoci a hanya ya fara cikin karo da marasa lafiya yan dubiwa da kuma wanda suke jinya da masu jiran likita Nurse yake karo da su amma yana tambayarsu cikin yanayi na firgici hakan da suka gani suka gane yana cikin yanayi da sauri wani namiji mai sanye da kananun kaya da farar riga ta ma'aikatan asibiti ya tare shi yana tambayar sa abin da ke faruwa nan ya shiga sanar dashi sda sauri ya ja shi sukayi can in da su Alhaji suke ko da isar su har Alhaji ya sabo Adam a wuya da yake shima akwai girman jiki sa suffar mazantaka da kwanji nan su ka rufa cikin asibiti Emengancy kana nufa dashi lokaci guda Nurse suk je suka gayyato likito ci kusan uku duk suka rufa a kan sa domin ganin halin da yake ciki na rai kwakwi mutu kwakwai.
Dr,Kamal ne ya fito hannunsa sanye da safa da suke amfani da ita fuskar sanye da madubin idon da yayi matuka karawa fuskar tshi kwarji dogo kakkaura yana da manyan idanu da hanci tsaka tsakiya wanda shi ba a baje ba kuma bai yi tsayi sosai ba yana da baki daidai misali masu dauke da jan La66a baki ne amma ba can ba za a iya kiransa da wankan tarwaɗa ya tun karo in da su Alhaji suke fuskarsa ba yabo ba fallasa duk ba su lura da shi ba har ya iso ya dafa kafaɗar Alhaji firgigin ta juyo ganin likita ne da sauri ya damki hannunsa cikin ɓarin jiki da rawar murya ya fara magana.
"Doctor wani hali ɗana yake ciki don Allah kace dani komai zai zo da sauki ina son ɗana shi kadai na mallaka bana so na rasa shi in na rasa shi tamkar ni ne na rasa rayuwata".
Tun da ya fara magan Dr,Kamal ke duban sa cikin wani irin yanayi ajiyar numfashi yayi sannan ya nisa.
"Kwantar da hankalin ka Alhaji komai zai zamto Normal Amma ku cigaba da adɗu'a wannan firgicin ba shi da Amfani gareku".
Hajiya ce ta janyo jiki ta iso gareshi tana mai sharbar majina.
"Doctor ya jikin nasa".
Yanayin yarda tayi maganar ya tabbatarwa da Dr,Kamal ita ba ta fice daga hayyacin ta ba tasan abin da take yi hakan ya san yashi dubanta gami da gyada kai ya nasa kin murmushi ta gefen baki mai kama da dole akayi masa.
"da sauki za ace Hajiya Amma in ba za ku damu ina son ganin ku a Office dina yanzun nan".
Da sauri Hajiya Laila tace.
"muje likita domin ina bukatar sanin halin da ɗana ke ciki"
Bai sake tanka musu ba yayi gaba suna biye dashi har suka isa Office din sa wanda yake dauke da komai na bukata da duk wasu abubuwa da za su tambarda cewa shi cikakken likita ne Teburi ne famfaɗa mai dauke da fayil fayil can gefe kuma wani dan karamin abu mai kama da Allo an rubuta sunan DOCTOR KAMAL GWADA da ruwan gold sai daukar idanu yake yi. da kan sa yayi musi izini da su zauna kan kujerun dake girke kusa da teburin shi kuma ya tafi ya zauna saman tashi kujerar mai jujjuyawa ajiyar numfashi yayi tare da zare glass din idanunsa ya zuba musu kallo tausayin su yake ji ganin yarda duk suka rikice suka shiga halin damuwa akan rashin lafiyar ɗan su sai da suka dau minti biyar cikin shiru ba abin da ke tashi sai sautin ajiyar zuciyoyinsu. Sannan Doctor Kamal ya fara kokarin tsinkawa cikin taushin murya da sigar rarrashi.
"kuyi hakuri nasan zaku ji ba dadi matuka akan abin da yake damun ɗan ku sai dai ina so ku kasance masu yarda da ƙaddara a ko wani hali kuka tsinci kan ku komai da ku ga ya faru da bawa dama can tun Fil'azal Allah ya rubuta haƙan sai ya faru...".
Hajiya ce ta katse shi cikin zakuwa da son jin abin da ke fauwa domin maganar Doctor ta kara sanya ta cikin wani hali.
"mu musulmai ne Doctor mun yarda da ƙaddara mai kyau da akasin don Allah sanar damu abin da ke damun ɗan mu ko zuciyoyyin mun samu dawo wa hayyacin su".
ta karashe furucin cikin roko har tana hada hannunt biyu hakan ya kara sanya tausayin su a zuciyar Doctor kai ya sunkuyar tare da sanya hakicif ya goge goshin sa
"ɗan ku yana dauke da ciwon zuciya wanda cikin kankanin lokaci ta kamu kamuwa kowa mai tsanani ba cin haka kuma...".
"Innalillahi wa inna ilair raji'un Allahumma ja'alni fi musibatin..."
Hajiya ce ta katse Doctor da fadin haka tare da mikewa zumbur hawaye na shatata a idanunta shikuwa alhaji mutuwar zaune yayi gami da kafe Doctor da idanu ba alamun kiftawa tagumi Doctor yayi cikin tsananin tausayin halin da suke ciki ya mike yana mai cewa,
"Hajiya hakuri zakiyi koma ki zauna mana ke fa yanzu kike sanar dani kin yarda da ƙaddara mai dadi da akasinta to ina so ki nuna min hakan".
Jiki a sanyaye ta koma ta zauna tare da girgiza Alhaji ganin halin da ya shiga wani gwauron numfashi ya aje wasu kwalla suka zubo masa yayi kasa da kansa ya na dauke su zuciƴarsa sai faman harbawa takeyi cikin sauri-sauri ba abin da ke masa yawo sai maganar doctor wai ɗan sa ke dauke da ciwon zuciya garin yaya haka ya faru mai kuma ya haifar masa da haƙan meye sila. Nan ya shiga jero tambayoyi wa kan sa amma ba shi da amsar ko dya haka ya daure ya dago yana duban Doctor da ya fara kokarin cigaba da bayani a gare su.
"gaskiya ɗan ku na cikin mawuyacin hali ba ma wannan ba ya kamata na sanar da kuma muhimmin abu ma da yake kara shigar da ɗan kuwa ni mataki na kashe rayuwa nan gaba kadan".
ya nisa yana mai jinjina maganar da zai sanar dasu zuciyarsa na daci matuka akan lamarin yarda son zuciya da wani buradan banza can suke kokarin kashe rayuwar matashin ɗan wadannan mutanan don ya tabbata son zuciya ne kawai da kazamin buri ya nisa ya dora da cewa.
"a gaskiya ɗan kuwa yayi matukar bata rayuwar sa ba kadan ba domin kuwa kayan mayen da yake sha cikin rashin tsari sun yi matukar cutar dashi ba kadan ba yanzu a halin da ake ciki ma komai zai iya faruwa dashi".
ya kara she yana mai takaicin lamarin yana gyada kai.
Lokaci guda Office din ya dau shiru tashin hankali da su Hajiya Laila suk shiga fadarsa ma bata baki ne don ji suke kamar duk wani tashin hankali na duniya da tarin damuwa da bugun zuciya da caja kwakwalwa duk kan asu aka dire ba abin da suke sai innalilahi cikin zuciyarsa don gabadaya duniyar ta su ji suke tana juyin waina da su.
Nan dai cikin wannan halin ya shiga yi musi bayani da matakin da dan su ke ciki da hanyoyin da za su bi in har suna bukatar cigaban rayuwarsu wanda ba tabbas gareta ba rayuwar gareshi sai wani iko na Allah.
Yawan maganganunsa duƙ ba su fahimta ba domin sun kai makura cikin wani yanayi na rashin hayyaci
gani da yayi ba sa wannan Motion din na natsuwa ya sa shi tsagaida tawa da bayani ya zabga tagumi yana ganin ikon Allah da irin son da kauna da yake gani game da su wand suke nunawa dan na su tabbas iyaye abin a so ne a kula da su a daraja su ayi musu duk wani abu da zai saka su farinciki da kwanciyar hankali...
Kofar da aka bude ne duk ya dawo da su hayyacin su har dashi likitan da yake tunani Tk neya shigo jiki a sabule domin tun da aka shigar da Adam cikin dakin da za a duba shi Alhaji ya Umarce shi da ya je gida ya dauko duk wami abu da za a bukata domi. Baya so a bukaci wani abu ba tae da yana kusa da su ba.
Gaida su yayi sannan ya mikawa Alhaj wata jaka karama da alamun kude danƙare acikin ta. Cikin jan hanci Alhaji ya dubi Tk cikin raunin murya,
"Tukur wai shin ko kasan abin da yake damun Adam, a halin da ake yanzu haka ciwon zuciya yana barazanar kashe masa rayuwa"
wata irin zabura Tk yayi cikin tsananin faduwar gaba gabadaya sai suka shiga duban sa lokaci guda jikin sa ya fara ɓari ba abin da ya zo ran sa adaidai wannan lokacin sai maganar Bahijja da ya hakikan silar ta ne ya shiga wannan halin tabbas suna cikin matsala babba ya kamata ya sanar da su Alhaji abin dake faruwa domin ya tabbata ba su dan meye sanadi ba shiyasa suka nemi jin ba'asi daga gare shi...
Alhaji ne ya katse masa zaran tunanin zucin da yake ta hanyar damko hannunsa yana girgiza shi
"Tukur kayi magana mana!".
ya fadi cikin daga murya wamda ta kara tsorata Tk cikin rawar jiki da ɓarin maki ya dube su.
"nima ban sani ba Alhaj..".
"karya kake wallahi ta ya ya ma zaka zo mana da wannan banzar maganar tunda Adam ya shiga wannan halin kai ka daine mutumin da yake kulawa ka ga kenan dole kasan Sanadin abin da ya je fashi cikin wannan tashin hankali kaji na rantse maka in har kasani ka ki fadi mani wallahi zan yi maka hukuncin da har ka koma ga mahaliccin ka ba zaka mance da ni ba".
ya karashe yana mai sakin sa ya dafe kan shi ya yaji yana kokarin rabewa gida biyu jagwaf ya koma ya zauna kan kujera wani irin yanayi yaji yana kara ziyartar sa na tashin hankali.
Ba karamar razana Tk yayi ba zuciyarsa ta fara kar gadin sa da ya fadi abin da ya sani domin ya san halin Alhaji akan dan shi zai iya daukar ko wani mataki akan sa
Cikin barin jiki ya fara magana.
"Alhaji wallahi ni dai abin da nasani kuma ya sanar dani shine..."
Sai kuma yayi shiru yana faman rarraba idanu kamar mi tsoron fadin maganar dake bakin sa.
Dukkan su suka zuba masa ido Doctor ya dube shi cikin alamun son ya fadi yana mai kara masa gwarin gwuiw don ya lura Tk ya tsoraa da maganar Alhaji.
"yi maganar ka Tukur ka kwantar da hankalin ka ba abin da zai faru dakai ka zama namiji magana".
ya karashe yana kara masa kaimi.
nishi Tk yayi sa'annan ya cigaba da cewa,
"Wata yarinya ya hadu da ita yake so to tun ranar da suka hadu din ban sake ganin ta".
Haushi takaici bakin ciki duk suka turnuke Alhaji bai san lokacin da ya mike ya kwashe Tk da wasu maruka har biyu ba lafiyayyu.
"wata irin maganar banza ce wannan kake fadi Tukur kana da hankali kuwa ina nufin kan WATA MACE ɗana ya shiga wannan halin kana nufin saboda son WATA MACE yake kokarin kashe kan sa wacece ita kuma yar gidan uban wanene a garin nan?".
Tk da ke tsaya jiki na ɓari jin maganar da Alhaji yake fadi ya fra sanya shi ka da baya domin tsoron sake shan mari
Hajiya kuwa sakin baki tayi tana jin irin maganar da Alhaji ke furtawa mai hali dai ba ya fasa halin sa ta shiga gyada kai takaicin duniya ya gama kashe mata zuciya.
Shima Doctor mamaki ne da tu'jibi suka cika shi jin irin maganar da Alhaji yake fadi ta tsantsar son zuciya da son kai.
Cikin targagi Alhaji ya juyo yana duban Likita. "kaji wata banzan magana ko kaji wata bahaguwar magana mara kan gado ko..".
"a,a Alhaji". Hajiya ta tare shi ta dora da cewa cikin jin haushin maganarda yayi.
"Kar ka ga laifin Tukur Abin da ya sani ne ya fadi don haka yanzu kai ne abin yi ya rage gareka dabara ta ragewa mai shiga rijiya".
da sauri ya juyo ya dube ta cikin tsananin tashin hankali ba tare dya ce komai ba ya juya ga Doctor.
"Zan iya ganin ɗa na Doctor"
Gyada kai yayi gami da cewa.
"Eh zaka iya ganin sa amma kuma ba ya bukatar hayani domin an samu an tsayar da aman jini da yake an saka masa ruwa yanzu haka ya samu barci yan jira muke ya tashi muga halin da yake ciki da matakin kuma da ya kamata ace mun bi domin ceto shi".
Komawa yayi ya zauna gami da dafe kai duk yaji lamura sun sake kwance masa ba abin da ke msa yawa akai sai maganar Tk wai son wata ne ya sanya dan shi cikin mummunar yanayi wanda bai taba zaton ko tsammani ba bai taba zaton Adam zai sanya kan shi cikin matsala ba akan So ya dauka yana da damar da zai so ko wace 'ya mace ce, ya dauka ba macen da ɗan shi zai nuna ya na so taki amincewa dashi mai ya rasa kudi suna da su komai najin dadin rayuwa ya mallaka to me yasa har wata mace zata shigo masa rayuwa akan so kuma take kokarin kashe masa ɗa wacece ita a ina take yar gidan waye dole ya binciko ko wacece ita domin dawo wa dan shi da farincikin sa ko zai rasa komai nashi da ya mallak sai yayi nemo wa dan shi farinciki rayuwa ko da kuwa shi zai kasance cikin damuwa ba abin da ya fi kauna da so kamar ya ga ɗan sa Adam cikin dadin da farincikin rayuwa.
Mikewa dauke da sanyi jiki ya dubi Doctor ba tare da ya yi masa magana ba, amma da alamun ya gane abinda yake nufi mikewa yayi gami da duban hajiya yace "Hajiya tashi muje ko"
Gyaɗa kai tayi gami da mikewa Alhaji na gaba yarda kasan shine likitin su koma suna biye dashi har suka fice daga cikin Office din suka nufi dakin da Adam yake tunda daga bakin kofa suka fara jin numfarfashin sa kamar wanda rai ke ƙokarin ficewa daga jikin jin haka da sukayi ai gabadaya su ka runtuma a guje gabadayan su har hajiya har tana kokarin tuntsurewa saboda zaninta da ya kusan ballewa ya fadi kasa.
Adam suka tadda sai faman mika yake kirjinsa na wani irin tunkudowa kamar zai tarwatse wani Nurse sai faman dandanne shi yake wani kuma na dannan masa kirji da alamun zuciyarsa ne ke bugu da sauri Doctor,Kamal ya kara yana mai tambayarsu ba'asi nan Nurse daya dake rike dashi Adam sai faman girgiza yake kamar wanda aka jonawa wutan nepa kan shi gadon da yake kai sai wani rawa take yi kamar zai balle guda biyu.
"wallahi muna daga waje muka ji ihun sa muna shigo muka tadda shi dai faman fizge-figze yake"
Doctor Kamal ya dube shi yana mai jin wani iri a ransa akan Adam.
"ba kuyi masa Allurar da nace kuyi masa bane?".
Da sauri ya Amsa.
"Wallahi munyi masa har barci ma ya fara yi amma kuma ko minti ashirin ba ayi bq muka ji ihunsa".
Shiru Doctor Kamal yayi kamar mai tunani wani abu can ya dubi Nurse din yace da shi yayi maza ya dauko masa wata Allurar cikin azama ya saki Adam shi kuma ya rike shi har zuwa lokacin bai dai na fizge-fizge ba yana wani irin numfashi kamar wanda ake kokarin zarewa ruhi.
Hajiya,Alhaji,Tk duk daskare a tsaye sun rasa mai ke yi musu dadi cikin ran su tashin hankali dai gashi nan suna gani wanda tun da suke a rayuwarsu ba su taba fuskanta matsala mai kamanceciya da wannan ba aduniyar na suna ganin kamar sun fi kowa tashin hankali.
Doctor, Kamal ya amshi allurar da aka kawo masa ya sake yi masa sannan ya duba ruwan da ya daura masa sai ya lura ya daina tafiya ma sam nan ya shiga gyarawa cikin kankanin lokaci sai Adam yayi lakwaf kamar ba shi bane mai fizge-fizge ba nan duk sukayi ajiyar zuciya doctor ya dubi su hajiya da suka gama yanke tsammani da Adam.
"ya kamata tun wuri kusan mafita akan wannan lamarin domin Adam na matakin da komai zai iya faru a ko wani lokaci zuciyarsa gaf take da bugawa ina mai bako shawara koyi gangawar neman abin da zai kawo masa sauki cikin rayuwarsa ina mai baku shawara kuyi amfani da abin da Tk ya fdi domin maganar sa abin dubawa magana ce mai muhimmanci sosai domin zai iya kasancewa akan son yarinyar da ya gani ne duk ya shiga wannan halin domin kuwa wannan lamarin ba kan sa farau ba in dai akan So ne so da kuke gani ba karamin Shu'umin abu bane a rayuwar dangin rai a dalilin so Dangin rai na shiga mawuyancin hali wanda ba ku taba tsammani ba so da kuke gani ba abin da ba zai iya sanya Dangin rai ya aikata ba So na gusar da hankali da natsuwa so na saka mutum yayi abin da daga baya ya zo yana dana sanin aikatawa Alhaji ko taimaka ko ceci rayuwar ɗanku duk da dai an san rayuwa da mutuwa duk suna wajan Allah amma wata wahalar tafi gaban kwatance".
Ya karashe cikin matukar tausayin su kowa na cikin dakin ba karamin sanyi jikin sa yayi ba zuciyoyi suka shiga harbawa cikin ko wani sakan dauke da damuwa matsananci gabadaya su Alhaji kan su ya kulle sun rasa abin da ya dace su yi kan lamarin tsayin lokaci suna halin shiru can Alhaji ya kokarta gayyato jarumta ya yafawa kan sa ya dubi Tk da shima ya ke cikin tashi damuwar bai taba zaton so haka yake ba bai taba zaton so na wahalar wa da yawa ya ga ana soyayya kala-kala mai cike da kayan ruɗani amma bai ta ba zaton halin so har ya kai haka tabbas ya kara tabbatar da SO SHU'UMI ne a rayuwar dangin rai tamkar ZUMA DA MAƊACI yake cikin duniyar dangin rai shi kam in haka so yake an ya zai iya kuwa..
Alhaji ne ya katse masa tunanin daya faɗa ta hanyar cewa,
"Tukur ina ne gidan su yarinyar?"
Wani irin bugu yaji kirjin sa yayi domin kuwa ko WUKA A MAKOSHI za a sanya masa ba zai iya cewa a gidan su ba da kyar ya kakalo abin da zai fadi.
" BAN SANI BA"
nan kowa yayi tsit zuciyoyi suka shiga shawagin tunani aka shiga kallon kallo a tsakanin juna Doctor,Kamal ne ya kokarta duban Tk ya ce, "a ina kuka ganta?"
nan wani bugu ya ji kirjin sa yayi yana ta rarrabin amsar da zai bayar shi dai ba zai iya furta a Club suka hadu ba to in yaki bada amsa to yace me cikin lokaci kalilan ya fara safa da marwa da zuciyarsa domin samo amsar abin da zai ce amma ina gabadaya tunaninsa ya cushe ya rasa tashar ma da zai kama.
"a CLUB"
abin da bakin sa da harshen sa kenan yaji sun furta ba tare da basu damar haka ba.
'CLUB'.
abin da kowa ya shiga ambata kenan cikin zuciyarsa da mamaki.

Hmmm Tofa wata sabuwa
CIWON SO😱😱😱

OHHHH NI kamala Minna ina ganin abu ....lolx😁😁😁
😍😍😍😍😍

DUNIYARMU (Compelet)Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ