DUNIYARMU-10

808 35 0
                                    


DUNIYARMU
Na
KAMALA MINNA.
BABI NA GOMA
Zaune suke kimanin su goma sha biyar kowacce kallo daya zakayi mata ka kau da kai dalilin irin rikitaccen shiga da sukayi Wanda shi da babu duk matsayi daya za a aje su domin kuwa ilahirin jikin su a bayyane yake komai na jikin su ana gani tsab! Fuskar nan ta dauki make-up na fitar hankali  har wata canza launi takeyi saboda goguwa da kwalkwale da akayi mata.
Gaban su babban teburi ne mai dauke da kayan shaye-shaye kala daban daban ba abin dake tashi cikin falon sai k'auri da tashin hayakin sigari da hamamin kwalaben kayan maye  yanayin da suke ciki zai tabbatar maka ko waccen cikin su ta banka har ya kai mata geji yarda take so kwanya ta dau tururi da caji.
Hamshakiyar cikin su wacce mazaunin ta ya zama na daban acikin su ta dubi ko wannan su hannunta rike da wata karamar bindiga baka wuluk sai kalli takeyi ta shiga juya ta fuskar ta na bayyanar da wani shu'umin murmushi mai cike da ma'anoni masu matukar yawa ta kai wa bakin ta farmaki da guntuwar sigarin dake hannunta cikin salo na gwanancewa a harkar ta zuka sosai ta tada kan ta sama tare da sakin hayakin yayi cili sosai sannan cikin wani salon da hayakin ta rubuta kalma S tare da sakin wata mahaukaciyar dariya lokaci guda kuma kamar daukewar ruwa tayi tsit duk sauran Matan suka bita da kallo ba tare da dayansu ta tsinka ba ta nisa sannan tace"ina so nasar daku cewa a ranar laraba goma ga watan Biyar misalin karfe biyar na safiya ina son ko waccen Ku ta kasance anan domin a ranar zamu kai farmaki gidan Alhaji Sha'aban mai-nasara" tun da ta fara maganar ba wacce tayi ko da tari har ta dasa aya  ta shiga duban su daya bayan daya ta Dora da cewa"ko da akwai mai abin cewa?" duk suka girgiza kai a lokaci daya Heejat dake can gefe guda yanayin fuskar ta ta sauya da alamun akwai damuwa game da ita Ayshanty da ke kusa da ita ta lura da haka ta zungure ta cikin rada tace da ita"ya kamata ki ce wani abu domin na lura akwai damuwa game dake"
mirgida kai tayi sannan tace"Shatu maganar tafiya ta Kano kin san nace miki zan je kuma zanyi kamar sati guda kafin na dawo kin ga wannan aikin da Saudat ke fadi za ayi zai yi matukar gurguntar min da tafiya ta nikuma ba zan so haka ba gaskiya" ta karashe cikin yanayi na damuwa Aysahnty ta dubeta cikin yanayi na rashin damuwa"to meye na damuwa  kin ga ki gaya mata kawai ga abin dake gaban ki ba za ki samu damar fitowa ba domin kuwa mahaifinki ne bashi da lafiya kike son zuwa gareshi yanzun ma meeting din nan ne ya tsai dake amma a na tashi za ki tafi"
cikin yanayi na gamsuwa Heejat ta mirgina kai "hakan za ayi domin wannan hanyar ce mafita kadai amma ina tunanin sai mun fita daga meeting din sai na same ta"
"hakan yayi matuka domin kin san yanzu kina yin magana wata cikin nan za ta iya yi miki tungu a hanaki wallahi" nan dai suka rufe zancen a haka har aka kai karshen meeting su ka tashi ko wacce ta kama gaban ta yanayin su kadai zaka kalla ya tabbatar maka ko wacce jin kan ta takeyi a sama don ko tsakanin su ba wata gamsashinyar yarda bace ana dai zaune waje dayane duniyar  wata rayuwa ta hada su rayuwar da suka zabawa duniyar rayuwar su suna ganin itace ta fidacewa da su suna ganin ita ce kadai rayuwar da su ganin tafi cancanta da su Wanda sukayi amanna da ita ko wacce cikin su ba wacce ba igiyar aure akan ta amma saboda sun kasance masu son k'awar duniya da kyalkyal ya rude su su kasance zuciyar su ita ce ke jan ragamar su sai yarda tayi dasu kamar rakumi da akala haka su ka gama da zuciyoyin su cikin wasu kaddara ce ta afka musu suka kasa karbarta ta yarda ta zo musu wasu kuwa dadin duniya da rudin zamani ya jefa su cikin wannan gurbataccen halin mara amfani ga duniyar rayuwarsu burinsu da kudurin su su mallaki abin duniya ta ko wacce irin hanya sun manta haram da halas duk daya suke daukar sa SAUDAT ita ce shugaba a garesu ita ta kafa musu kungiya ta yaki da taddanci da miyagun kwayoyi da fashi da makami su ka kasance FATAKEN DARE ya wancin su a yawon club suka haduwa wasun su kuma a wajan SAFARA ta miyagun kwayayoyi su alakar su ta kullu tsayin shekaru biyu kenan suna tare sun yi matukar addabar al'umma sai dai abin mamaki duk yawan fashi da makamin da akeyi cikin garin Minna da abuja ba a ta ba kama su ba kuma ba a taba zaton 'YA'YA MATA ba ne keyin wannan ta'addancin yawancin su 'ya'yan masu kudi ne bahijjat ce kawai aciki mahaifinta ba wani mai tarin dukiya ba  lokacin da ta fara tu'amali da harkar safara ta kwayoyi mubasheer ne sila komai har haduwar ta da su SAUDAT duk shine sila a tunanin ta da hangen ta mubasheer son ta yake yi tsakani da Allah zai iya yin komai a tunanin ta ta yarda dashi ta bashi amanar rayuwar ta amma ina ashe ba ta sani ba amanar ta yake ci duk kuma YARDA CE SILAH (sanah ummu-beenah...lolz)
Bayan fitowarsu daga cikin hall din da suka gabatar da meeting din su ko wacce ta fada cikin luntsumemiyar motar ta tayi gaba a ka bar Ayshanty Baheejjat sai  Saudat.
Ayshanty ta dubi Heejat "ya kamata muje tun da kowa ya watse ko" gyada mata kai tayi ba tare da tace da ita komai ba Saudat na kokarin bude motar ta sukayi mata tsinke duban su ta shiga yi cikin wani irin yanayi na lamun tuhuma a gadarance tace"ya dai ko akwai mai magana ne?" duk Kansu suka gyada mata kai ta watsa hannu sama tare da kwa6e baki alamun za su iya yin maganar ta su wata uwar harara Heejat ta watsa mata batare da ita Saudat din ta lura da hakan ba sannan ta ce"dama kan maganar aikin da za aje nace nidai ba zan samu damar zuwa ba dalili kuwa mahaifina ne ba lafiya zan je duba shi a can kano kuma gaskiya ranar aiki za ta shiga cikin kwanakin tafiyar da zan yi" tunda ta fara magana Saudat ke duban ta cikin salon raini da nuna halin ko in kula har ta kai aya amma ba tace da su komai ba kuma da alamun bata da niyar cewa wani abu hakan yayi matukar kular da Ayshanty cikin nuna ita ma akwai IZZA a gareta ta dubi Saudat"yau fa zata ta tafi lokaci tafiya yakeyi ya kamata ace ta san matsaya" key din motar ta ta shiga kadawa ta na duban su daya bayan daya kamar wacce taga bakin fuskoki hakan yayi matukar kara kular da su Heejat ta zunguri Ayshanty cikin alamun fushi tayi mata alamun kawai su wuce girgiza mata kai tayi sannan ta sake kai duban ta ga Saudat"Saudat ke fa muke jira"ciki da mamaki Saudat ta shiga duban Ayshanty jin ta ambaci sunanta gatsal ba surki ko wani alamun girmamawa a gatsale tace "ban amince ba kuma in har zaki iya tafiya ba zan hanaki ba amma kisan da sani kamar ficewarki ne daga cikin kungiyar nan in har kika tafi" yanayin fuskar Heejat ta baci da damuwa cikin salon rarrashi tace"ki na ga hakan adalci ne Saudat mahaifina fa nace zan je dubawa Kuma na San ke ma kin san muhimmancin mahaifa cikin rayuwarki" wata irin dariya Saudat ta barke da ita kamar sabuwar kamu ta shiga nuna su da hannu lokaci guda dariya fuskar ta ta dauke kamar wacce murmushi bai taba wanzuwa a fuskar ta ba tayi kyarrr da idanuwata kan su sannan tace "wasu mahaifan na da kima da darajar da za akula da su amma wasu ko kashe su za kayi wallahi ba za'a taimaka musu ba" sunyi matukar razana da shiga halin rudu jin furucin da Saudat ke amayowa daga bakin ta Heejat ta juya ta dubi Ayshanty ita ma ita take duba don gabadaya sun yi matukar shiga mamaki da jin lafuzanta su ana su hangen komai lalacewar iyaye ko da kuwa suna yankar naman jikin ka su na ci ne to bai dace ace kana kin su ko wani aibata su ba ko da dai ba su san dalilin ta na fadin haka ba amma ai muhimmancin iyaye ya wuce a yi musu mugun fata lokaci daya sukayi ajiyar GWAURON NUMFASHI su ka juyar da kallon su gareta har zuwa lokacin idanuwan ta na kansu ganin yanayin da su ka shiga a dalilin maganar ta don ta san tabbas akan furucin da tayi  ne ya shigar da su wannan halin rudanin "nasan akan furucin da nayi ne duk ku ka shiga wannan halin ko to ba abin mamaki bane in har na sanar da Ku ni nan da hannuna na kashe iyayena duk kan su na raba su da duniyar rayuwar su na rabasu da jindadin duniyar nan.."ai ba ta kai ga dasa aya ba duk kan su suka shiga sallalami da ambaton sun shiga uku sun lalace zaman dirshan sukayi akasa kamar yar borin da ake kadawa gangi lokaci guda gumi mai tsanani tururin tashin hankali ya shiga karyo musu wata katagar tashin hankali da tada zuciya tsaye daga zaune ta rikito musu cikin tsumar jiki Heejat tace "TASHIN HANKALI.."Ayshanty tace"GOBARAR GEMU" ta shiga dauke gumin da yayi wa fuskar ta jagaf da rigar jikin ta idanuwan ta duk sun yo waje saboda tsananin faduwar gaba da bugun da zuciyar ta keyi ita kam Heejat suman zaune tayi hannu bibbyu ta daura akai jikin ta sai 6ari yakeyi da karkarwa cikin takun isa da gadara da nuna halin ko in kula ko shiga damuwa ga abin da ta fadi Saudat ta iso garesu ta durkusa hannunta a wannan lokacin bindiga ce rike sai wulwulata takeyi bakin ta na taunar cingam jikake kas-kas ta dube su tare da nuna su da hancin bindiga"duk me ya jefaku cikin wannan halin na rudu  karku bada mu mana ai wannan salon kawo raini da faduwa kasa ne a garemu don Allah Ku dai na"mirgina kai Heejat tayi cikin barin jiki tace"amma ke anya musulmace Saudat?" dariya tayi mata sannan tace"cikakkiya kuwa kuma jinsin Hausa Fulani yar asalin jahar kano"luuuu Heejat tayi kasa kamar wacce aka zarewa numfashi ta dago da idanuwan ta kamar wacce take cikin buguwa ta nuna Saudat da hannu amma ta kasa cewa komai ta juya ta dubi Ayshanty wacce a wannan lokacin mamaki ya kusan kashe ta Mike wa Saudat tayi ta tayi taku kamar uku sannan ta juyo ta dubi su ta nisa cikin gwauron numfashi"nice na kashe mahaifina da mahaifiyata da hannuna" da sauri Ayshanty ta tare ta"Saudat amma dai kin taba hauka ko?" dariya tayi sannan tace"ko daya hankalina garau yake ke dai yi shiru zan  sanar dake dalilin abin da yasa na kashe iyayena da hannuna" shiru sukayi suna zuba mata idanuwa duk ilahirin jikin su yayi matukar sanyi ba abin da ke dawainiya da su izuwa wannan lokacin sai rashin kwanciyar hankali da rashin dadin rai gani sukeyi kamar duk duniya Saudat ce wacce tafi kowa wauta da rashin hankali in ba rashin hankali da rashin rabo ba mai zai kai ta kashe iyayen ta kuma har take iya budar baki tana fadin ita ce SILAR AJALI ga iyayen ta wannan wani irin rashin tunani da rashin hankalin kwakwalwane wannan wata irin MATACCIYAR ZUCIYA gareta... ji sukayi ta katse musu zaren tunaninsu ta fara rattabo musu MAFARIN LAMARIN kisan iyayen ta da tayi"ranar wata talata bayan na ci kuka na nagodewa Allah na rasa mai ya dace nayi domin samun mafita ko zan samu sassauci zuciya daga radadin zafi da zugin da takeyi min ji nake kamar an dauko kasko wuta mai dauke da jan garwashi mai tsananin tartsatsi an kwarawa zuciya ta na rasa me ke min dadi cikin duniyar nan na rasa farincikina na rasa muradan jindadin duniyata takaici bakinciki kayan tashin hankali su ka maye gurbi lokaci guda a lokacin wani rikitaccen tunani ya bullo min cikin duniyar rayuwata zuciya da gangar jikina sukayi amanna da wannan tunanin a lokacin nima na yarda da wannan hukuncin saboda shi ne yafi cancanta kuma shine hanya mai dauke da mafita a gareni tashi nayi zaune daga kan luntsumeman gadona Wanda yaji kayan moriyar rayuwa na zuro kafafuwa na zu kan kilishin da yayi wa tsakar dakin adon birgewa da kayatar wa kicin na nufa ba abin da zuciya ta ke sanar dani illah in gabatar da kudirin da ta sanar dani wata zabgegiyar wuka na dauko sai kyalkyali takeyi kamar wacce rana ta haske na rike wukar a hannu sai jujjuyata nake yi ina kare mata kallo na dau kusan mintina ashirin tsaye tsakar kicin din ina abu daya wato tunanin mafita lissfe lissafe na shiga yi ko da zan samu wata mafitar ta daban ba wacce zuciya ta ke sanar dani ba amma ina har zuwa wannan lokacin ba ta canza zani ba duk nagama sakar tunani da nazarin wata mafitar amma ina abu dai jiya i yau gani da nayi lokaci na kokarin cin mani in har ban wanzar da abin da nayi kudira ba to tabbas lokacin mutuwata yayi domin kuwa zuciyata gaban take da bugawa na sake bin wukar da kallo idanuwa na tsiyayar da wasu zafafan hawaye masu matukar radadi zuciya na tunzurani gani da ingiza ni kawai in je in aiwatar cikin azama da yanayi na rashin hayyaci na durfafi dakin mahaifiyata ba sallama ko Neman izini na kutsa kai cikin dakin hankalina yayi matukar tashi a yanayin da na tadda mahaifiyar tawa zuciyata ta shiga tururi da Kunar rai hankali ya kara tunzura wajan tashi ba abin da zuciya ke sanar da illah kawai na farmata hakan zai yi matukar gusar da tashin hankalin da nake ciki da tarin bakin ciki da yayi wa duniya ta katutu ban San lokacin da na isa gareta ba domin kuwa idanuwa na a rufe suke na fice daga hayyaci kawai saukar wukar da ihun da ta kurma shi ya tabbatar min komai ya wakana da sauri na saki wukar wacce take saitin zuciyar ta ta nitsa cikin jikin ta tun da tayi ihu sau daya ba ta sake ko da motsi ba hakan ya tabbatar min da komai ya kammala ban yi wata wata ba na fice daga cikin dakin da sauri cikin tsanani rudani da shi ga wani yanayi Wanda ni kai na ba zan iya cewa ga halin da na shiga ba..." maganar Ayshanty ce ta katsa ta "na ga kin dauko wani dogon sharhi ne Wanda sam bai da wani armashi sai na tashin hankali bashi muke bukata ba so nake ki sanar damu gundarin abin da yasa kikayi ajalin iyayen ki wani irin mugun hali suke dashi ko wani irin laifi suka kundumamiki har ki ka zartar musu da wannan BAHAGON HUKUNCI (najnoor) haka Wanda sam ba wani abu dake cikin sai sai tashin hankali da yake Rabin samun rahamar ubangiji" murmushi Saudat ta saki sannan tace"na fara muku bayanin ne yarda zaki fahimta dalla-dalla" da sauri Heejat ta tare ta"ba wani bayani naki da zamu fahimta wallahi ke dai kawai kice son zuciya da kwadayin abin duniya ya sanyaki  kashe iyayen ki duniya ta rude ki ta gwada miki kayan k'awa irin nata da take rudar mutane dashi" ta karashe maganar cikin matukar jin haushi mikewa tayi cikin kunar rai ta dubi Ayshanty"kin ga malama tashi mu tafi in har muka tsaya sauraronta to wallahi sai azabar mummunar ta sauka akan mu iyaye fa ba abin wasa ba ne laifi ma kayi musu yakake kare wa in sun yi fushi balle kuma ka kashe su a matsayin ka na Dan su Allah karshen rashin rabo ma da rashin rahamar Allah ya tabbatar akan ka" Saudat ta dubi Heejat cikin tsananin bacin rai "ai bai dace kiyi gangawar yanke min hukunci ba ki bari na karasa baki labarin abin da ya faru" wani tsakin takaici Heejat ta saki gami da tsartar da yawu "Allah ya sauwake na tsaya sauraron ki wannan ma da naji ina rokon Allah kar yayi min hisabi akan sa domin kuwa bisa rashin sani naji shi" ta na zuwa nan a zancen ta da sauri ta dubi Ayshanty da jikin ta yayi matukar saki kallo daya zakayi mata ka tabbatar ta shiga rudani mai tsanani "ni kin ga nayi nan wallahi ba za ayi wannan aika-aikar dani ba" wucewa tayi ta shiga cikin motar ta ta bata wuta ta bar harabar wajan ita ma Ayshanty cikin azama ta fada cikin motar ta ta fizge ta ta bar wajan suka bar Saudat sake da baki don gani take sunyi mata mummunar fahimta ya kamata ace sun tsaya sun ji abin da yasa ta aikata haka amma suka nuna mata rashin gaskiya tsantsa a gareta girgiza kai tayi tare da cizar la66a  ta shiga motar ta tayi mata key ta bar wajan zuciyar ta cike da tarandadi da rashin armashi.
***       ***      ***
duban sa tayi cikin wani irin kallo na alamun raini da gwasalewa amma duk da haka bai nuna alamun damuwa ba illah wani gutun murmushi dake yawo saman fuskar sa ba yabo ba fallasa ya sake nisawa"ba dan ke na bada akai masa ba da ma kin kwantar da hankalin ki yarinyar" ya karasa cikin sigar alamun zolaya harara ta cilla masa cikin jin haushi musamman ce mata da yayi yarinya "ni ma ai bacewa wa nayi ka bayar saboda ni ba don wallahi ko da kace saboda ni ka bayar ba burgeni za kayi ba don haka dama kadai na wannan zancen naka" ta fadi tana mai kokarin kara daidai ta kayanta da ta gama shiryawa cikin jakar ta ta tafiya "Bahijjat" ya fadi cikin yanayi na halin damuwa juyo wa tayi ta dubeshi sannan tace"lafiya kake min wannan kirar haka sai kace wacce ta ci maka bashi ta kasa biya ni fa naki jinin mutum mai kulafici da naci a rayuwata in banayin mutum to ni ma bana so yayi ni cikin duniyar rayuwar sa hakan zai fi zama alheri" da mamaki a fuskar sa ya dube ta jin abin da ta fadi"yanzu in kika je wajan Abba ya tambayeki wani irin zaman aure mukeyi mai zaki sanar dashi?" da sauri ta dubeshi don bata taba tunani wannan tambayar za ta fito daga bakin sa ba ko a mafarkin ta me hakan ke nufi mai Adam ke nufi da wannan furucin nasa margaya kai tayi cikin nuna halin rashin damuwa tace"me kuwa zan ce masa illah in ce lafiya kalau nake zaune" murmushi yayi tare da cusa hannayensa cikin ajjihun wandon sa yace"in yace tsakanin ki da mijin ki fa" duban sa tayi da sauri Adam ya fara kuleta da alamun son kureta yake son yi da saurin ta kau da kai  ta koma bakin kujerar da ke cikin falon ta zauna ta shiga lallatsa wayar dake hannunta hakan da ya gani yasanya shi girgiza kai ya juya ya na mai cewa "dafatan zaki isar min da sakon da na baki don wallahi kina isa zan kirashi naji" ya na fadin haka yayi hanyar sashin sa ya barta nan zaune cike da takaicin zuci Adam ya rigaya ya raina ta ta rasa mai za tayi masa domin ya fita harkar ta gabadaya ta kai duban ta wajan da ya aje kudin ta sa hannu ta dauka gami da jan tsaki a daidai lokacin mubasheer ya sanyo kai cikin falon ba tare da sallama ba duban sa tayi ta watsar gefe "sai yanzu ka ga damar zuwa tun dazu nake jiran ka amma ka ba banza ajiya ta ka kyauta" da sauri ya karaso ya zauna gaf da ita ya kura mata idanuwa sannan yace"yi hakuri babyna tun da zu na iso har na sanyo kai cikin falon naji ki ke da gwani" ya fadi yana mai kashe mata ido daya tsaki ta ja gami da galla masa harara"kai kam Allah ya kyauta maka ashe la6e ka tsaya yi kenan?" hannu ya watsa sama tare da kwa6e baki "Allah ya sauwake in rasa Wanda zan yi wa la6e sai ke da wannan likanken mijin naki haka kawai in jiyo abin da zai kusa min bakin ciki azuci" me kewa tayi sannan ta dube shi "tashi mu tafi kaga lokaci tafiya yake yi" ba tare da yace da ita komai ba ya mike gami da daukar babbar Jakarta yayi gaba ita kuma ta dauki karama da wayar hannu sai Dan yalolon mayafin da ta rataya a wuya ita ma tafice gindin mota ta taddashi tsaye ya harde hannayensa a kirji ya zuba mata idanuwa har ta iso ba tare da ta kalleshi ba tace "muje ko" bai ce  da ita kala ba ya fada cikin motar ita ma tashiga ya yi mata key mai gadi ya wangame tafkeken get su ka fice yana mai daga musu hannu alamun a dawo lafiya..

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now