DUNIYARMU-20

564 25 0
                                    

DUNIYARMU.

NA.
KAMALA MINNA.

BABI NA ASHIRIN.

Tsayin minti na fiye da ashirin suka shafe cikin wannan yanayin ba tare da wani dayan su a ciki ya tsinka ba.
tun Heejat na daurewa da yanayin shirin har zuciyarta ta fara uzurta mata akan gangancin zama da makiyi a inuwa daya
lokaci guda ta ji ranta ya kara baci ba kadan ba cikin hanzari ta mike ta suri jakarta tana kokarim ficewa.
hakan da Adam ya gani yayi saurin ajiye kwalbar barasar dake hannunsa ya zuba mata rinannu idanuwan sa da sukayi jajir matuka gaya.
"me kike kokarin yi haka?"
Ya fadi cikin muryarsa mai dauke da tsantsar gushewar hankali.
Jin abin da yace ya kara bata mata  rai a duniyar nan ba abin da ta tsana bayan mutuwar kamar ta ji muryar Adam ba karamin ganganci da wautar kan ta ta gani ba akan abin da ta aikata tasan ta aika ta babban kuskuren da zuciyarta ba zata yafe mata ba ita kan ta ba zata yafewa kan ta ba.
shirun da yaji ne ba amsa ya bashi damar sake magantuwa.
"ki zauna mana"
"ba zan zauna ba"
ta fada cikin wata murya mai dauke da tsawa wacce ita kan ta ba ta san tana da ita ba.
Hakan yayi matukar jan hankalin mutanan wajan ainun.
kowa ya zuba mata ido tana tsaye ba abin da jikin take yi sai rawa kamar wacce ake yi wa gangi.
gabadaya hankalin ta ya tashi natsuwarta na kokarin barin ta idanuwanta sun kada sunyi jajir hawaye kokarin zubowa suke sai yanzu ta san abin da tayi sam bai da ce ba bai kamata ace ta nuna maitarta a fili a haka domin kuwa duk wani bajat din ta zai tarwatse muddin Adam ya fahimci inda ta dosa.
a raunane ta koma ta zauna cikin saurin saita kai.
yarda taji fargabarta ta ragu shine ganin yarda Adam ba ya cikin hayyacin sa da sauri cikin kissta wayance gami zaro wayarta daga cikin jakarta ta shiga lallatsawa in ka kalleta sai ka rantse da cewa hankalin ta kacokan na kan eayar ne amma ina zuciyarta da kwakwalwarta cunkushe suke duniyar taji tana juya mata kamar waina a tanda wani tukukin takaici da tarin haushi ya zo wuya ya tokare ta ji take kamar ta hadiyi zuciya ta mace amma ina in tayi haka kan ta yiwa asara.
bata ankara ba taji wasu ruwa masu dumi na sauka saman fuskarta wato hawaye da take boyewa sun fi karfin jarumtar da ta janyo wa kanta.
ba ta wani firgita ba don ta san za ta iyayin fiye da hakan in dai akan bakin cikin dake cin duniyarta ne ai ba yau farau ba amma kuma ai an kusan zuwa karau akan zubar hawayenta.
wani murmushi ta saki wanda ita kan ta ba ta san ya suɓuce mata ba ta dago kai da wani irin kallo na jan hankalin ko wani ɗa namiji mai cikakkiyar lafiya ta kashe murya cikin salo da kara kash jikin duk wanda yake sauraronta.
"ADAM"
ta ambata cikin wani irin salo wanda ita kadai ta san ma'anarsa wanda kuma ba ta so ko a ranta hakan ya faru ba ta so ace wani ɗa namiji tayi wa wanda ya zama mallakinta ita ma ta zama mallakinsa a matsayin ma'auratasuna rayuwa cikin jindadi da kwanciyar hankali cikin inuwar ma'aurata.
dago kan sa yayi cikin yanayi na baye ya zuba mata manyan idanuwansa wanda hakan sai da ya fadar mata da gaba matuka da sauri ta dauke kanta daga ganinsa cikin kunar rai.
wata irin dariya ya saki hadi da buga tareburin dake gabansu yana fadin,
"tabbas kece"
wata irin zabura tayi cikin matsanancin faduwar gaba jin abin da ya fadi akan ta.
nan ta shiga saƙar zuci
'anya Adam bai fahimce ni ba anya bai tabbatar ni ce bahijja ba in kuwa haka ne na shiga uku'
ji tayi kamar ta dora hannu aka tai ta kurma ihu amma wani bangare na zuciyarta ta shiga gargadin ta akan abin da take kokarin aikatawana sauyin karaya 'a kul! din ki shin ba ki lura da halin da yake ciki bane, ba fa tare da hankalin sa yake ba zai iya aikata komai da yazo masa cikin tunaninsa kila yana ganin taswirar wata kilakinsa ne a fuskarki'
wani irin gwauron numfashi ta saki lokaci guda tayi amanna da zancen zuciyarta.
Kuri tayi masa da idanu gabanta har yanzu bugawa yake yi amma azahirin fuskarta ta kinkimo jarumta ta yafawa kanta ta shiga salon kissa tana faman sakin murmushi wanda hakan ya kara jefa shi cikin yanayi na nishadin da giyar da yasha take gwada masa.
"tabbas kece wacce take zuwa mik kullum cikin mafarkina ta na sakar min murmushi gami da tattali na so da kwantar da hankali"
ina wuta Hejjat ta jefa Adam zuciyarta tayi bakinkirin jin kalaman da yake saki wai ita Adam yake yi mata irin wadannan maganganun tabbas bai da hankali kuma bai san wacece ita ba.
ajiyar numfashi tayi cikin kunar rai da takaicin kasancewarta da makiyin ta lamba daya a inuwa daya mai yafi wannan kashe rayuwa anya kuwa tayi wa kanta adalci in har ta cigaba da zama da Adam cikin wannan yanayin ba tare da ta aiwatar da abin dake ranta ba 'Ina!'ta fadi cikin zuciyarta ta na mai girgiza kai.
hakan da Adam ya gani ya sanya shi tasowa ya iso gareta ya na mai cewa.
"karki yi min haka baby ki amsa min ke ce kike zuwa mani cikin barci na ki amsa min don Allah"
yanayin da ya karasa maganar kamar mai son fashewa da kuka hakan ya tabbatar ma da cew giyar maye ce kawai ke masa sukuwa akai.
wani murmushin muguta ta saki cikin wani yanayi na tabbatar da cewa burin ta ya kusa cika kudirin zuciyarta na kashe makiyin ta gaf yake da tabbatuwa in kuwa hakan ya kasancewa da a duniyar ba ta ga wanda zai kai ta farin-ciki ba.
kamar wata mai tausayin kan ta haka ta mike ta isa wajan da yake durkushe gaf da ita ta tsaya har suna jiyo numfashin juna duk irin hamamin dake tashi da ɗoyi na giya hakan sam bai kashe jinta taba duk da dai ba so takeyi ba.
dafa kafadunsa tayi gami da dagoshi cikin sarkewar idanun juna tsuka fuskanci juna hannunta daya ta daura kan laɓɓansa dayan kuma da daura saman kafadunsa ta shiga jefa masa kallo mai rikitarwa da fidda mutum daga hayyaci tana liliya masa laɓɓa da hannunta daya hakan ba karamin tasiri yayi ba akan Adam nan da nan jikin sa ya kara saki sai ya zambato tamkar rakumi da alaka sai yarda tayi dashi hakan ya bata damar duban sa cikin kashe murya ta ce,
"ni ce wacce ka daɗe kana nima nice wacce ta jima tana maka shawagi cikin duniyar rayuwarka badini da zahiri yau gani gaban ka zan dauke maka duk kan wani abubuwan nishadi da farincikin dake cikin duniya rayuwarka naji ma ina cigiyarka na jima ina mafarkin hadu da kai naji ina sanar da zuciya ta kai kadai ne mutumin da take burin suyi arba dashi domin wani SIRRIN BOYE irin naka da kake kokarin cin ma wa ka kwantar da hankalin ka"
wani irin ihu ya saki don tsananin jin dadi da annashawar da ta cika masa zuciya ba zato ba tsammani kawai sai Heejat ta ga yana kokarin dake ta cak! ya daga sama cikin hanzari ta tare shi cikin tura dan yatsanta cikin bakin sa tana jujjuyawa cikin wani salo na sake kashe jiki tayi kamar zata kai masa sumbata sai kuma tayi saurin gocewa tana mai kyalkyalar dariya shima sai ya biye mata nan waje ya dauka ba muryar da kake ji sai ta Adam ma goya bayan sa sai ambaton sunansa suke suna yi masa kirari hakan ya kara kular da Heejat ba kadan ba amma sa ta ki nuna hakan a fuskarta don ita a duniyar nan ko mai son Adam ne to ya zama mikiyinta na gaban abada.
sun shafe tsayin lokacin cikin club din dare ya tsala sosai gari yayi tsit ba abin da kake ji sai sautin wakoki da dukan manyan sifiku dake tashi hakan ya kara tabbatar da dare yayi dare sosai izuwa wannan lokacin kowa ni matashin da duniya ya tsarke hannun abokiyar burmin sa sun yi makwanci a hankali a hankali wajan ya ragu sosai sai yan tsararu wanda suka sha sukayi mankas suka kasa tabuka komai irin su Adam.
Heejat kuwa izuwa lokacin tunaninta ya ta'allaka akan abin da za ta aiwatar ta shiga nazarin hanyar da zata bi don cin ma burinta zuciyarta ta shiga sanar da ita kawai tayi masa kisa na wulakanci tunda dama ce ta same ta amma kuma in har tayi sake da wannan damar wata damar kafin ta same ta za ta ji ajikin ta nan ta shiga girgiza kai akan wani kisan za ta yi masa dame za tayi kisan gabaday ta daburce sam ta manta da ajiyar ta dake jaka wato bindiga hankalin ta gabadaya ya gama tashi duk wani jarumta da burin da ta dauko duk a yanzu ta rasa in da ya tafi zuciyarta na dukan uku-uku.
'wai ita za tayi kisa'
ta fadi cikin ta rarrabi da shiga wani irin hali wanda ita kan ta ta kasa fassara shi.
Zuciyarta ta yin kuro mata a zafafa.
"baki da hankali ne Heejat mai yasa kike kokarin dauko tausayi ki saka wa kan ki a wajan da bai dace ba! Kin man ta ke wace ce shin kin manta illar da Adam yayi miki ne kike kokarin jinkiri akan abin da kika san zai gusar miki da tashin hankali da kunar rai dake makale da zuciyarki tun wuri ki aje tausayi ko wani imani akan Adam don bai cancanta bai dace ba bai dauko ko da hanyar aji tausayin sa ba ina mai rokonki da kiyi gaggauwar daukar fansa wannan lokaci shi me yafi dacewa da ki dauki ko wacce irin fansa"
cikin hanzari kwakwalwarta ta katse maganganun zuciyarta da cewa.
"ina sam wannan ba hanyar da ta dace bane da daukar fansa ya kamata ace yana cikin hayyacin sa za ta aiwatar da hakan domin kuwa ya san wace ce ita yasan kuma illar da yayi mata ba karama bane kuma ya gane bawai ta barshi bane tsayin lokacin da ya dauka yana harkar rayuwar kuma ya sani bawai bagas ya ci ba akam cutar mata da rayuwa da yayi"
Nan zuciya ta sake dauka ita ma
"me yasa zaki ce haka wannan ai guntun tunani ne kuma bahago wanda bai da wani tasiri idan akace za a aikata shi don haka kawai ki barta ta aika komai a yanzu shi ne mafitar ta"
da sauri ta sanya hannayenta ta kulle kunnuwanta don ji takeyi maganganun zuciyarta da kwakwalwarta suna kokarin zaunatr da ita duniyar taji tana juya mata kamar wacce aka daura a majajjawa ta rintse idanuwanta kam lamarin duniyarta gabadaya ya zama a haukace komai ya kwance mata ta rasa mafita ta rasa ina ta dosa abokan tunaninta wato zuciya da kwakwalwa suna kokarin haukatar da ita ta rasa shwarar wa zata dauka batun bangaren zuciya in tayi duba akan sa ta wani bangaren kamar ta sanya hannu ta amsa lura da tayi lokacin da ya cimma manufarsa akan ta ba ta cikin hayyacinta amma kuma in tayi nazari ga batu na kwakwalwa za ta ga matukar amfanin barin shi ya dawo cikin hayyacin sa domin hakan zai tabbatar da ita wacece a gareshi kuma zai san illar da yayi mat ba karamar nakasta mata rayuwa tayi ba cikin hanzari ta amince da batun kwakwalwa akan ta bari sai yana cikin hayyacin sa san nan ta aiwatar da komai amma kuma anya ba tayi ganganci ba shin za ta iya dashi in ya dawo hayyacin sa ta wacce hanya zata bi domin tabbatuwar hakan?
da sauri Kwakwalwarta ta bata amsa 'duk wannan mai sauki ne ke fa 'ya mace ce akan me zaki damu kan ki akan ɗa namiji ai shiga hannu ba wuya bane in dai kin sa ke 'ya macece cikakkiya ai duk wani ɗa namiji sai ya sha mamaki akan ki ki bar shakka ke dai kawai sawa kan ki komai ya tabbatu akan kudirin ki'
Lokaci guda taji wani umarni daga kasar zuciyarta akan ta tashi ta bar wajan tun kafin ya dawo cikin hayyacin sa lamarin kuma ya kwaɓe tunda ba ta shirya daukar fansa a yau ba.
cikin hanzari ta mike ta dauki jakar ta gami da wayarta da ke yashe har ta juya ta fara tafiya wani tunani na daban ya fado mata cikin zuciya da sauri ta juyae da dubanta ga Adam da izuwa wannan lokaci wani shiriritaccen barci ya fara awon gaba dashi wayarsa ta dauka cikin sauri ta saka lambar ta kira cikin sakanni wayarta ta dau ruri hakan da ta gani ya tabbatar mata lambarsa ce ta shigo ta katse kiran sannan ta tura wayar ta cikin jaka gorar ruwan Faro ta dauko mai matsakaicin sanyi ta balle murfin ta kwararawa Adam akai cikin yanayi na fita hayyaci ya fafado gami da sakin sambatu da zage zage hakan ya kara tabbatar mata bai dawo hankalin sa ba murmushi ta saki gami da cewa,
"ta shi ka tafi gida mana ai dare yayi"
cikin muryar maye ya tare ta
"bar ni a nan kawai ke dai zo mu kwanta"
wani takaici ne ya kume ta jin abin da ya ce amma sai ta yi yaƙe kawai  gami da tura masa wayarsa ta bar wajan cikin yanayi na rashin dadi ta na isa wajan da tayi parking ta bude motar ta shiga bayan ta zuge gilasan mota bakaƙe wuluk wanda sam ba a hango wanda yake ciki in har ya rube su har tayi wa motar key taji an kwankwasa mata glass hakan ba karamin mamaki ya bata ba kamar ba zata bude ba can kuma sai tayi kasa da glass din wani matashin saurayi ta gani tsaye fuskarsa dauke da murmushi hakan ya sanya ta tsuke fuska gami da kokari zuge glass din duk tunaninta ya bata irin yan kalan'dangin nan ne a bari wanda tashin balangar kyankyasai ke yi musu amo akai zai zo ya raina mata wayo da guntun iskancin sa
jin ya sanya hannu ya tare glass din yana dariya ganin yarda ta tsuke fuska hakan yasanya shi gane abin da take nufi yace,
"y hakuri mana ba wani abu ya kawo ni ba gani nayi kin bar oga shi kadai kina kokarin guduwa"
mamaki cike a fuskarta ta dube shi gami da ajiyar zuciya sannam ta ce "ban fahimci in da ka dosa ba?"
ta fadi cikin yatsine fuska.
"ni yaron sa ne tare muke nayi tunanin tare za ku kwana ai a zato amma sai kuma naga kina kokarin tafiya kuma ga dare yayi sosai ko dai ya bata miki rai ne"
'Kwana'
kalmar da ta tsinta kenan cikin batun ta wai ita zata kwana da Adam habadai ai ko kanta akwance yake yayi warwars ba abin da zai sata ta kwana da makiyinta can ta nisa gami da sakin wani murmushi mai dauke da yaƙe
"No ba wani abu akwai abin da zan yi ne shiyasa zan tafi zaka iya zuwa ka ja shi ku tafi ma kwancin ku is ok"
ta na gama fadin haka ta zuge glass din ta tayi wa motar ki ta bata wuta ta fice abin ta.
matashin natsaye har sai da ya ga bacewar ta sannan ya isa izuwa wajan Adam wanda barci yayi masa dukan tsiya wajan dauka ya shiga kokarin tayar dashi amma ina yayi nisa da yawa hakan da ya gani ya bashi damar daukar wayarsa da sauran tarkasan ya dagoshi a kafada yana janshi domin kuwa ba zai iya daukar sa cak ba domin Adam ba karamin ingarman namiji bane kallo daya zakayi masa ka tabbatar tsayin ɗa namiji mai cikar zati da kwanji duk Adam ya mallake su haka yayi ta jan sa yana nishi har suka usa ga motarsa ya bude gidan baya ya watsa shi kamar wani kayan wanki don jikin sa yayi matukar saki ya mai da kofa ya rufe gami da sakin ajiyar zuciya mai karfi sannan ya bude gidan gaba ya zauna yayi wa motar key suka fice daga cikin club din.
-----------------------------------
Tunda ta dawo cikin dakinta ta kwanta take ta faman juye-juye gabadaya hankalin ta ya karkata ga tabbatuwar fansan da take kokarin dauka ba abin da take hango sai hanyar da za tabi domin aiwatar da hakan.
sai yanzu take ganin wautar da tayi na kin aitawa tun a wannan damar da ta samu anya WATA DAMAR za ta sake zuwa mata ko dayake ba abin ace ta damun kanta ba ta san ba abin da zai hana tabbatuwar hakan sai ta kashe Adam ita ce hanya daya da zata bi don daukar fansa amma kuma ya kamata ace tayi matukar bashi wahala da kuma kunsa masa bakin ciki kafin ta hallaka shi sai yanzu taga ne ranar shawarar da kwakwalwarta ta bata
da sauri ta mike ta zaro wayarta daga caji da ta jona tun dawowarta lambar Ayshanty ta dannawa kira cikin rashin sani wanda aka ce YA FI DARE DUHU in da ta san halin da Ayshanty da yanzu hankalin ta in yayi duba ya tashi kira take yi amma wayar na kururuwar neman agaji ba a daga ba tun tana kira da doƙi har ta fara tsaki tana dannawa Ashanty ashar da tuna ai Ayshanty Matar aure ce yanzu haka kila tana tare da mijinta shi yasa taki dauka take mat wulakanci da sauri ta sauke wayar daga kunnan ta gami da zubawa fuskar wayar kallo agogon wayar ya nuna karfe uku na dare tsaki ta ja gami da mai da wayar caji tayi ruf da ciki ta fada duniyar tunani wanda kawai yin sa take amma ba wani alamun mafita da take nima sai kara cushewa da kwanyarta ke yi ta shiga birgima kamar wata mai aljananu ta na faman sakin nishi da jiyar zuciya idanunta sun kada sun yi jajir cikin hanzari ta mike tana fama layi kamar wacce tayi tatil da barasa ta nufi hanyar toilet.
ta jima a ciki kafin ta fito bayan ta gama sakarwa kanta ruwa hakan ta fito tawul daure a jikinta da wani a hannu ta na faman tsane jiki a daidai wannan lokacin kuma aka fara kiraye-kirayen Sallah asubahi hakan sam bai ɗaɗata da kasa ba don tasan wannan dare sam bai zama na wani jindadi a gareta ba gabadayan sa takaici ya zame mata da tarin damuwa bayan ta gama tsane jikinta ta sanya doguwar rigar jallabiya mai kalar sararin samaniya ta sake komawa toilet ta dauro Alwala bayan ta fito tashiga ramuwar sallolin da ake bin ta tajera su (Kara'i) bayan ta idar ta shiga gyar kanta ta hanyar kwalliya wacce ba wata ta a zo a gani bane kawai dai ba ta saba barin kan ta ba kwalliya bane ya rigaya ya zamema ta jiki shiyasa.
misalin karfe bakwai daidai ta dan na kararrawar neman masu otel din bayan sun iso ta sanar da su abin da take bukata na breakfast ba a dau tsawon lokaci ba a kawo mata ruwan lipton ne kawai sai wainar kwai su kadai take tunanin za ta iya kawai cikin ta a halin da take ciki na rashin kwanciyar hankali da nutsuwar rai.
wayar tace ta dau kururuwar neman a gaji daga in da take zaune ta zira hannu ta janyota a tunanin ta Ayshanty ce ta kira ta amma sai akasin haka lambar Mubasheer tagani hakan ya dan bat haushi har da tsuke fuska da jan tsaki sai da ta gama ja masa rai sannan ta daga wayar ba tare da ta ce dashi kala ba.
daga can bangaren cikin yanayi na zumudi ya fara magana.
"mutuniyar ya ya dai"
banza tayi dashi da alamun ba tayi niyyar yi masa magana ba
hakan da yaji sa ya sake magantuwa.
"Heejat me yake faruwa ne ina magana naji ki shiru kuma nasan kina jina ko wulakancin naki da miskilanci ne ya motsa"
jin abin da yace ya kara bata haushi don ita taki jinin takura irinta Mubasheer.
"wai kai mai yasa ko yaushe in zakayi wa mutum magana sai ka sako rainin hankali ne?"
ta fadi cikin cin magani kamar ya na kusa da ita
murmushi ya saki har tana jiyo sautin sa sannan yace
"ni kuma matsala ta dake shegen korafin tsiya abu kadan sai ki hau fushi da mutum Allah ya baki hakuri"
"meye ka kira ni da safiyar nan?"
ta fadi cikin daskarewar murya
shi ya tare ta
"nayi laifi kenan daga kawai na kira ki don naji yar kika tashi ke fa ba a abin dadin rai dake"
"naji na gode da kulawa sai anjima"
ta na fadin haka ta katse wayar tayi cilli da ita saman gado gami da jan guntun tsaki

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now