DUNIYARMU-34

374 23 1
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA

BABI NA TALATIN DA HUDU.

A firgice ya farka daga sumar da yayi yana faman ambaton sunan Salma cikin wani irin yanayi mai dauke da firgici da razana.
Nurse dake kula dashi ta shiga rarrashin sa akan ya koma ya kwanta amma ina ko ta kan ta bai bi ma zumbur ya mike sai faman tangaɗi yake yi kamar wanda yayi tatil da barasa idanuwansa sai ganin uku-uku suke yi yana hada hanya ya doshi kofar fita sai sakin numfashi yake yi mai dauke da matsanancin tashin hankali da hanzari Nurse din ta bi bayansa tana taimaka masa domin ta lura kamar faduwa zai yi.
A haka suka fito daga cikin dakin da yake ba nisa da inda aka shigar da Salm hango su Dsp yayi tsaye sai faman kai kawo su ke yi shi da Shukuranu wanda a wannan lokacin ya sarara da kukan da yake yi amma lokaci-lokaci yana dauke hawayen da suke zubo masa.
"Yallabai tana ina don Allah ku nuna min ita na sani 'ya ta mutu jikina ya bani tabbacin haka don Allah ko gawarta ne ku bani damar gani".
Magana yake yi cikin rawar jiki da rashin hayyaci Dsp ya dube shi cikin yanayi na tausayawa yana faman gyaɗa kai ya riko hannunsa can gefe ya ja shi suka zauna kan daya daga cikin kujerun dake girke a wajan.
Shiru ya ratsa tsakaninsu na tsayin mintina biyar ba abin da suke sai ajiyar zuciya mai dauke da tashin hankali Dsp ya nisa cikin yanayi na tausayi ya dubi Baban Salma.
"don Allah don Annabi ka gayyato natsuwa a ka sakawa kan ka...".
"ta ya ya zan iya haka yallabai".
Ya katse Dsp da fadin haka.
Girgiza kai yayi cikin matsannancin tausayin sa, cikin muryar mai dauke da laushi ya sake dubansa.
"Salma ba ta mutu ta nan a raye sai dai ba ta cikin hayyacinta, tana bukatar samun kulawa sosai daga likitoci domin samun daidatuwar numfashinta kayi hakuri ka natsu ka baiwa zuciyar ka hakuri da salama ka rungumu ƙaddara cikin yanayin da ta zo maka ka cigaba da Addu'a domin a halin da ake ciki yanzu ba abin da Salma take bukata illa Addu'a bai kamata ace har zuwa wannan lokacin ba hankalin ku a tashe yake tun da a rigaya an same an yi mai wuyar".
Shiru yayi yana cakuɗa maganar Dsp cikin zuciyarsa da yanayin da suke amsa amo a kwakwalwarsa sai dai yana ganin ba zai iya kasancewa cikin halin da Dsp din yake so ba kwanciyar hankalin sa da samun natsuwarsa shine ya ga 'yar tashi a cikin ko wani hali take domin har yanzu bai tabbatar tana da rai ba a yanayin da ya ganta a hannun Dsp kwalla ne suka ciko masa cikin idanu da sauri ya sanya babbar rigarsa ya dauke su gami da nisawa.
"Shikenan Yallabai zan yi kokarin kasancewa a yarda kake so, sai dai  natsuwar zuciyata shine ganim halin da 'ya ta take ciki".
Kafadarsa Dsp ya dafa gami da gyaɗa masa kai cikin yanayi na tausayawa sannan ya juyar da kallonsa in da Shukuranu yake tsaye gabadaya ya fice daga hayyacin sa sai faman kai kawo yake yi kofar dakin da Salma take lokaci-lokaci yana kai kallon sa jikin kofar ko zai ga an bude ta amma ba alamun haka.
Awa day suka shafe cur amma har zuwa lokacin ba wani labari har sun fara kosawa shi kan sa Dsp din ya kosa ya ga halin da Salma din take ciki mikewa yayi ya nufi kofar dakin ya dan leka amma ba ya hango komai saboda labulan da yayi wa kofar kawanya daga ciki nishi yayi yana mai faman goge goshinsa. a daidai lokacin ya fara jin motsi za a bude kofar da hanzari ya dire ganinsa jikin kofar daya daga cikin likitocin ne ya fito kallo daya zakayi masa ka fahimci rashin walwala a tattare dashi da sauri Dsp ya tare shi tare da kafeshi da idanu cikin son karin bayani Baban Salma Shukuranu suma a daidai wannan lokacin suka iso ga likita kamar za su shige cikinsa saboda kusancin da sukayi masa sosai.
Sai da ya dauke gumin da ya wanke masa fuska kafin nan ya fara kokarin cire safar hannun wacce ta kasance ta roba.
Dsp ne ya yi kokarin cewa,
"likita ya ake ciki dafatan dai komai ya zama Normal".
Gyada kai ya shiga yi kafin ya dube su su duka.
"amma don Allah me ya sami baiwar Allah nan haka?".
Nan suka shiga duban juna cikin rashin abin fadi nan dai Dsp ya nisa cikin kunar rai da tausayi.
"wannan maganar ba za ta yuwu ba yanzu likita kawai kuyi kokarin ceto mata numfashi shine muradinmu...".
"...shikenan".
Ni likita ya fadi cikin katse Dsp kafin ya dora da cewa.
"tana da rai sai dai tana cikin mawuyacin hali mai rikitarwa matuka dole sai ta samu lokaci kamar sati ko ma fiye da haka cikin ingantaccen kulawa yanzu haka an daura mata jini da ruwa zuwa anjima mu ga yarsa zata kasance kudai ku cigaba da addu'a".
ya gama bayanin yaja jiki ya bar wajan a hankali duk likitocin su kai ta fitowa daya bayan daya nan suka neme shiga su ganta daya daga cikin likitocin yacw ba damar haka ba don sun so ba suka koma kujerunsu suka zauna izuwa wannan lokacin zuciyoyinsu sun fara ficewa daga tsoro natsuwa ta fara ziyartarsu jin bayanin likita.
A wanni biyu suka Shuɗe nan likitan da ya musu bayani na farko ya sake dawowa ya shiga ya tarar ruwan da aka saka mata har ya kare ya dubi Nurse din dake kula da ita ya bukaci ta dauko masa wani ruwa da jini da yake can cikin loka a ajje da sauri ta mike ta dauko nan ya sake saka ma Salma wacce har wannan lokaci ba wani kwakkwarar motsi da take yi bayan ya kammala daura mata ya sake yan gwaje-gwaje ya tabbatar akwai numfashi game da ita kuma ya na ganin alamun tafiyar komai Normal yaji dadin haka don bai yi zaton Salma za tayi rai ba sai wani iko na Rabbani
Fitowa yayi ya ja Dsp can gefe sukayi yar kuskus din su akan Salma din da kuma yanayin da take ciki ba karamin dadi Dsp yji ba ya shiga hamdala ga Allah mai kowa mai komai nan ya shiga yi masa abin da ke faruwa ba karamar tsorata likita yayi ba ya shiga duban Dsp yana jin wani irin tausayin Salma na tsargar masa tun daga kasar ruhi har zuciya da gangar jiki
"ina fatan kuna yin list din komai da kuke mata amfani da shi ko?".
Dsp ya fadi yana mai duban likita, gyada masa kai yayi cikin yanayi na sanyin jiki alamun eh sunayi nan sukayi gaisuwa kafin likitan ya wuce shi kuma Dsp ya koma wajan su Shukuranu da suke zaune jugum-jugum kamar kurame...
Kwanan Salma uku kwance a Asibiti izuwa lokacin ta fara sanin halin da take sai dai ba ta iya cin komai illa ruwa da ake bata mai dauke da sinadaren magungunu domin kashe duk wasu kwayoyin cututtuka da ke barazana ga rayuwarta sai kuma jini da ruwa da ake ta faman saka mata izuwa wannan lokacin ta sha ruwa da jini sama da leda Ashirin amma har lokacin su Shukuranu ba a bar su sun gan ta ba domin har da Dsp ma yace kar a bar su shiga domin hakan zai iya tayar da hankalin su da ita kanta.
A rana ta hudu ne Dsp ya umarce su da su leka gida domin kar aji su shiru hankulan mutan gida su sake tashi ba don sun so ba haka suka ja jiki Dsp yacewa ya ran sa su kai su a mota shi zai kula da komai akan Salma haka kuwa akayi su Shukuranu suka shige mota cikin yanayi kadaran kadahan ba wanda ke magana a cikin su sai SAƘAR ZUCI  suke ta faman yi, tafiyar mintina talatin sukayi su isa KAUYEN GURMANA tun a bakin hanya suka fahimci an ji kewarsu domin kuwa da mutanan gari sun sai su fara daga musu hannu da barka da dawowa haka har suka isa kofar gidan su Salma aka sauke Baban Salma sannan suka kara sa da Shukuranu gida.
Da sallama dauke a bakin sa ya shiga cikin gidan sai dai bai tarar da kowa a tsarkar gidan ba ga gidan yayi tsit kamar ba kowa a cikin sa ajiyar numfashi yayi yana nazarin halin da Ummarsa da kanwarsa su ka  shiga na rashin sa ya san dole rashin natsuwa ya zama abokin zaman su cikin gidan yasan barci ma sai ya gagare su kamar yarda shi kullum cikin maganar su yake yi a zuci tunda ya tafi. Dakin Umma ya isa ya dage labule gami da sallama Umma ya hango zaune ta zabga tagumi Shukura na kan cinyarta ta kwanta cin yanayi na tsananin damuwa Sallamar da yayi ta farko ba su ji ba sai da yasake wata kamar wadanda aka tsirawa Allura haka suka mike a firgice Umma har ta na kokarin faduwa saboda yanayin jikin girma Salma kuwa wani irin tsalle tayi sai ga ta gaban sa ba tasan lokacin da ta rungume sa ba ta saki wani irin kuka mai cin rai da zuciya Umma kuwa ba abin da take yi sai akbara da hamdala fuskarta dauke da wani irin murmushi mai dauke da hawaye hakan da Shukuranu ya gani da sauri ya isa gareta har zuwa lokacin Shukura na manne jikin sa sai kace wacce aka ce in ta sake shi bacewa zai yi hannun Umma ya kamata ya zaunar da ita yana mai dauke hawayen da ya ga sun zubo mata fuskarshi dauke da murmushi shima tsayin dakiku suka dauka cikin Shiru sautin kukan Shukura ne kawai ke tashi mai hade da Shassheka Umma tayi kokarin sai ta kan ta ta dubi Shukuranu da yayi tsuru yana kallon Ummarsa cike da kauna da soyayya hannunsa na faman shafan kan Shukura cikin salon rarrashi.
"kayi matukar samu cikin yanayi na tararrabi Shukuranu zuciyoyinmu sun yi matuƙar yin rauni a dalilin shirun da muka ji game da kai mai ya sa haka"?.
ta karashe cikin yanayi na raunin murya murmushi yayi kafin ya fara magana.
"Umma kuyi hakuri zuciyata da ruhina gami da tunanin kwakwalwana suna tare da ku gangar jikin ne kawai ke wani waje can daban nasani kun yi kewata matsananciya, nasani kun shiga yanayi saboda rashin ganina amma kuyi min afuwa Umma ba a son raina komai ya kasance haka ba".
Shukra ce ta dako fuska cike da hawaye ta dubi Yayan nata tana mai kau da kai.
"Yaya Shukuranu mai ya sa kayi mana haka, mai ya sa ka guje mu kuma kasan zuciyoyinmu  ba za su iya zama ba tare da kai ba kuma ka sani idaniyarmu ba za su iya rashin ganin ka ba yaya mai ya sa ka mance damu cikin duniyarka kaje can wani waje ka zauna".
ta karashe cikin muryar son kara fashewa da kuka da sauri ya tallabo habarta ya kura mata idanu ba abin da take yi sai ZUBAR HAWAYE murmushi ya saki ya sanya hannu ya na goge mata hawayen da suke ta faman zuba.
"karki yanke mani hukunci bahago mana kanwata kin san ba zan iya guje muku ba ba zan iya zama ba tare da kuma ki sani zuciyata da tunani suna tare da ku gangar jikina ne kawai yake can ayi min Afuwa kanwata".
Ya karashe yana mai kama kunnuwansa ba ta san lokacin da ta saki dariya ba tare da hawaye tana kai masa dukan wasa a kirjinsa nan suka saka dariya su duka kai kan ka in ka gan su sai sun burgeka matuka domin SOYAYYA DA SHAKUWA ce tsantsa take yawo a tsakaninsu sun shafe lokaci a haka kafin Umma ta natsu ta dubi Shukuranu
"Sai kuma  ku kaje kuka samu waje kuka rashe daga cewa baru muje mu dawo".
ta fadi cikin kureshi da ido da murmushi a fuskarta, kasa yayi da kan sa kafin ya dago ya dubi ta
"Umma dole ce ta sa haka wallahi abubuwa ne suka tare mu wanda ba mu taba tsammani ba".
Da sauri Umma ta tare shi jin abin da yace cikin bugun zuciya.
"Kamar ya Shukuranu yi saurin sanar dani abin da ke faruwa ko zuciya ta rage tararrabin da ta shiga na kwanaki".
Sai da yayi shiru na yan dakiku ba abin da yake tunawa sai lamarin da ya kasance masa kamar BAKAR KADDARA cikin rayuwa nan ya shiga ba su labari komai tunda ga barin su gida har zuwa wajan Saudat da yarda ta kaya zuwansu gidan Saudat inda Salma take da samo da sukayi har dawowar su Asibiti ya kai wa karshe a bayanin wasu hawaye suka zubo masa su kuwa su Umma kuka sukayi da gaske har Shassheka ba abin da Umma take furta sai hamdala da godiya ga Allah sai da tayi mai isarta ta share hawayenta ta dubi Shukuranu cikin yanayi na matukar tausayawa junansu sai faman gyada kai take yi.
"Ikon Allah haka Allah ya so damu cikin duniyar rayuwarmu sai mun fuskanci wannan ƙaddarar da ta zo mana na lokacin da Allaha ya tsaga mana shiyasa aka ce komai yayi farko yana da karshe ƙaddara jarabawara ce kun kenan duk tsayin lokacin da muka dauka cikin tashin hankali ashe akwai ranar daina shi shiyasa aka ce dogaro ga Allaha jari ga duk lamuran dangin rai".
ta karasa tana mai dauke hawayen da suke ta zubo mata ta rasa wani irin farinciki za ta nuna a duniyar nan zuciyarta take ji ta tafara sauya ta fara samun natsuwa tashi tayi ba tare da tae da su komai ba ta fice daga cikin dakin ba su bi ba'asi ba Shukuranu ya juya inda Shukura ke zaune tayi kasake sai zubda ruwan  hawaye take yi ya sanya hannunsa ya janyota jikinsa ya shiga goge mata su yana mai rarrshinta cikin murya mai dauke da taushi.
"haba yar kanwata meye kuma abin kuka tunda komai ya dauka hanyar zama karshe kwanciyar hankali ya fara yi mana maraba lale".
"Yaya ba wai ina kuka bane don wani abu farinciki ne ya sanya ni yin sa".
Jin abin da tace sai ya sanya shi sakin murmushi tare da rungumeta sosai ajikinsa ya na bubbuga bayanta a haka Umma ta shigo ta same su Murmushi tayi tana gyada kai saboda jin dadin ganin farin ciki ya ziyarce su fitar da tayi Alwala ta dauro suna kallonta ta tada kabbara tayi raka biyu domin godewa Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai mai yin yarda ya so a lokacin da yaso mai rayawa mai kashewa addu'a sosai tayi a rakar ta ta karshe tana mai zubda hawaye zuciyarta taji ta fara washewa daga yanayin da ta shiga tsayin lokaci ba na dadi ba bayan ta shafa ta dube su kuri su kayi mata da kallo.
"Kallon na me nene kuma haka malamai ku tashi kuje kuma kuyi godiya ga Allah ba wai ku zauna kuna faman murmushi da kare min kallo ba".
Ba wanda ya tanka mata sai murmushi da suke ta faman yi suƙa fice daga cikin dakin.
A bangaren Baban Salma kuwa yana isa gida bayan an sauke shi ya tadda Inna Luba zaune bakin kofa kamar yarda ta saba kullum tunda lamarin batar Salma ya shigo rayuwarta yanayin da ya ganta ya san abin yayi mata yawa ya zame mata biyu yasan damuwar shisa ya kara hautsi na mata tunanin duniyarta tayi matukar bashi tausayi ba kadan ba sai da ya tsaya ya kare mata kallo sosai yana lura da ita lokaci-lokaci idanuwanta suna cika da kwalla tana shafe su yasan duk adalilin rashin ganinsa ne musamman lura da yayi lokacin da ka zo daukar su bai sanar da ita abin dake faruwa lura da yayi in har ya fadi mata tayar da hankalinta zata yi kuma ta ce dole sai ta bi su shi kuma ba  zai so ya ga tashin hankalin ta ba girgiza kai yayi lokacin da ya tuno yarda ya ga Salma da yarda ta kasance a gareshi ya san da Lubabatu ta ganta tabbas sai zuciyarta ta bugu ta mutu shima namiji ya aka kare balle ita mace mai rauni ga kuma halin da take ciki gyaran murya yayi amma ba ta jishi ba da alamun tayi nisa cikin duniyar tunani isa yayi gareta tare da durkusawa a daidai lokacin wasu hawaye suka zubo mata hannu ya sa ya dauke su jin an taba ya sanya saurin zabura saura kadan ta wuntsila cikin dakin ta baya ya rikota cikin tsananin gigita da rikita ta ta dube shi ba ta san lokacin da ta saki wani irin kuka ba jikinta na rawa ta shiga nuna shi da hannu ta na son yin magana amma ta kasa domin harshenta taji yayi mata nauyi sosai hakan da ya lura dashi nan ya shiga rarrashinta yana sanar da ita ta natsu ta dawo cikin hayyacin ta amma ina kuka take yi hawaye sai shatashata suke yi cikin rawar jiki ta shi share hawayen domin ta rasa bakin magana ta dube sosai kamar wacce aka cewa in ta rintse idanu zai ba ce mata ta shiga sakin ajiyar zuciya mai karfi sai kara rikeshi take yi domin gani take kamar gizo yake yi mata, ba shi bane. Nisawa tayi cikin gwauron numfashi,
"haba malam mai yasa haka mai ya ka aikata min haka kasan zuciya ta gaf take da buguwa amma ka sake turani cikin tashin hankali laifin me nayi maka da zaka biyo min ta wannan hanyar da hukunci".
Ta fadi tana mai kara sautin kukan da ya ci karfinta ta nisa wasu hawaye suka zubo.
"sanadin ka na zama kamar wata mahaukaciya a gari na zama abin kallo da nuna nawa a layi ko wani mutum na cikin garin nan ya san ni dalilin rashin ka saboda rikita dda ka je fani a ciki da wanne zan ji malam batar Salma ko taka".
ta karashe cikin dacin rai da tsantsar takaici yayi matukar jin tausayin sa ya san haka dama zata faru domin ba hakuri gareta ba, ba ta iya shiga tashin hankali ba sam cikin karyayyiyar murya ya fara magana
"Nasan ban kyauta ba, amma ina neman afuwarki akan abin da nayi na rashin sanar dake in da zani nayi haka ne domin karki tayar da hankalin ki don na tabbata ki kasan in da zani a lokacin ba za ki taba kwantar da hankalin ki ba".
duban shi ta shiga tana mai tsayar da kukanta sai sakin ajiyar zuciya take kamar wacce tayi gudun ceton rai
"yo ai an yi ba ayi ba kenan malama. Yanzu rashin fadin naka ai bai hanani shiga tashin hankali ba".
"nidai nace kiyi hakuri ki daina wannan hirjin don Allah".
yayi saurin tararta ganin tana kokarin tayar da rigima.
"fada min in da kaje".
ta fadi cikin murya mai cike da neman ba'asi da tuhuma tsuru yayi mata ya na kare mata kallo kamar wacce ya ga ta sauya masa ko dayake ta rame to dama yaya lafiyar kuka balle ta saki gudawa
"natsuwarki nake bukata".
"ai natsuwata tana tattare da sanar dani abin da ya sanya ka barin gida".
Nisawa yayi gami da zare babbar rigar dake jikin sa ya miki ya shiga dakin sa dakiku kadan ya fito har yanzu tana nan in da ya barta gyada kai yayi yana mai cewa a ran sa 'mai hali ba ya fasa halin sa a ko ina ya samu kan sa'. a haka ya kara so wajanta ya dube ta bayan ya nisa
"Daga wajan neman Salma muke".
galala tayi da baki cikin rashin bawa zancen nasa muhimmanci tana mai yatsine fuska.
"Hmmm naji amma bai kai zuci ba...".
"Allah da gaske nake".
ya fadi iyakar gaskiyarsa fuskarsa na wanzar da murmushi.
Wata irin zabura tayi har zaninta na kokarin barin jikinta ta rike da hannu daya tana mai dafe kirji da yo waje da idanuwanta".
Ganin yanayin da ta shiga ya san yashi saurin janyo hannunta ya zaunar da ita ya yi mata kuri da idanu kamar yarda tayi masa sai zuciyarta sai kai kawo take yi ta daure cikin gayyato jarumta.
"Malam ko dai an ga Salma ne da alamun akwai wani abu dake wakana wanda ka boye mani don Allah malam fada min gaskiya ko zuciyata ta rage raɗaɗin firgici".
yanayin da tayi maganar cikin yanayi na rashin natsuwa ya sanya shi nisawa,
"kwantar da hankalin ki ki gayyaci natsuwa sannan muyi magana".
jin ya fadi haka yasan sauri gyara daurin dan kwali da daurin zani kamar a nan natsuwar ta ta take ta gyara zama gami da tankwashe kafafuwanta kamar wacce take shirin cin abinci,
"Malam kasan Allah zuciyata rawa take yi don ZULLUMI na matsu naji ka gaya min farin zance ko ya yake ban son jan rai malam  ka tausaya min ka tuna halin da na shiga abaya ka kuma tuna halin da na shiga barin gida da kayi har mahaukaciya an ce dani amma ban dauki hakan a zuciyata ba ya dame ni damuwata 'ya da mijina".
ta karashe maganar har da yar kwallarta hakan ya kara sanya shi tausayin ta ya san duk abin da ta fadi gaskiya ne nisawa ya yi gami da gyada kai fuskaraa da murmushi,
"Ki godewa Allah 'yarki ta bayyana...". Tun kafin ya rufe baki ya ga ta dauke numfashi idanuwanta ta akan shi amma ko motsawa ba sa yi hakan ya fadar masa da gaba da sauri ya girgizata ai zumbur ta tashi tsaye tana dubansa jin maganganunsa take kamar a mafarki ba a zahiri ji take kamar kawai maganar ba gaskiya bane tsokana ce ji take kamar ba kunnuwanta bane suke naɗo mata wannan labarin lokaci guda sai ga hawaye suna shatata
"don Allah kace min gaskiya ne wannan maganar da kake gaya min karka ce ka fada min ne don ganin kwanciyar hankali na in kuwa kayi min haka ba kayi min adalci ba zaka kara jefa zuciyata wani hali".
tana karasa tana mai dukursawa gabansa ba karamin tausayin ta ya ji ba ya san dole ta ji wani iri a ranta musamman a matsayin ta na Uwa kuma mace mai rauni a rai jan ta yayi ya zaunar da ita sosai ya shiga rarrashinta sai da ya ga ta samu natsuwa ya shiga ba ta labarin abin da ya wakana ba karamin firgici da razana ta shiga ba da taji halin rayuwar da 'yarta ta kasance tausayi da raunin yarta ya san ta fashewa da kuka mai cin rai yi take kamar za ta sheɗe sai da Malam yayi da gaske sannan ya samu tayi shiru...

Woooh hw Fah Inna Lubabatu😁😁😁😁
It'x Kamala Minna😍😍😍

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now