DUNIYARMU-21

435 21 2
                                    

DUNIYARMU.

NA.
KAMALA MINNA.

BABI NA ASHIRIN DA DAYA.

Zaune yake ya zabga tagumi kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwar iyayensa yake zaman jajantawa kan sa gabadaya tunanin sa izuwa wannan lokaci ya gama gurguncewa ba shi da abin yi sai zaman tunani wanda kuma sam ba ya kawo masa abin yabo sai karin kasala da sanya kai cikin damuwa wacce yake da yakinin ba ranan karewarta cikin duniyarsa bai yi zato ko tsammanin lamarin rayuwa zai zo masa a hagugunce ba haka duk da dai ya san komai na duniya dake faruwa a rayuwar dangin rai MUƘADDARI NE daga Allah madauƙaƙin sarki mai wanzar da duk wata jarabawa da kaddara cikin duniyar dan'Adam mai dadi da akasinta
 
Ya hakikancewa kansa da zuciyarsa da take ta sanar dashi wasu lamarurruƙa masara ƙawa da kayan farinciki akan cewa farin cikin duniyar sa ya kare amma kuma tunanin kwakwalwarsa yana kwadayar dashi da cewa akwai burbushin fariciki da zai zo masa kar yayi saurin YAKE TSAMMANI akan sha'anin ubangiji domin komai tun Fil'azal rubutacce ne.

cikin wannan tunanin kanzon kuregen da yake yi ji wayarsa dake yashe gefen sa ta dau kuwwar neman a gaji amma Shukuranu sai yayi biris domin ya san ko ya daga kiran kuma ko wanene mai kiran ba albishir zai masa akan ganin Salma ba don haka bai ga amfani daukar ba.

wayar ce ta katse a karo na farko cikin sakanni kuma ta sake daukar kuwwa amma har wannan lokacin ko kallon banza wayar ba ta ci arzukin samu ba illa tsaki da yaja ya kara jan jiki daga kusa da ita kamar wata mugun abu.

Daga labulan dakin da akayi iska da haske suka iso cikin sa hakan ne ya san yashi saurin juya zuwa kofar Shukura ce tsaye ta kafe yayan nata da kallo cikin yanayi na tausayin rayuwar dake yi ba shi kadai ba har da ita ma domin kuwa duk abin da ya same shi kamar ita ya sama domin duk rayuwarsu daya ne JINI DAYA kuma ai ba wasa bane ni sawa tayi cikin murya mai sanyi kamar mai son fashewa da kuka duk da jarumtar da ta kinkimo ta daurawa kan ta domin kar ya gane halin da take ciki amma rauninta na ƊIYA MACE ya kasa barin ta da jarumtar.

"tun dazu naji wayarka na neman agaji amma ban ji an dauka ba shiyasa na biyo sawu na dauka ma baka cikin dakin"

ta ida maganar ta ta cikin gyada kai.

kamar ba zai tsinka mata ba can kuma ya nisa cikin jan hanci ya shiga gyada kai kamar wanda aka fadawa magana bai yarda da ita ba sam!.

  "ba ta da amfani shi yasa ban yi wa kai gangancin dauka ba"

ka rasa shigowa dakin tayi tana mai cewa,
"kasan dai ba a tabbatar da abu sai an gwada an gani ko?"

ta yi masa tambayar kamar tana rokon sa Allah da Annabi ya daga kiran da ake yi masa

"zuciyata da tunani na ba su amince min da na dauka ba domin sun hakikance ba shi da amfani komai gareni ko da kuwa na daga din"

"yaya.."

da sauri ya tare ta.
"Shukura"

dakin ya dau shiru tsayin mintina ba wanda ya sake kokarin tsinkawa zuciyoyi ne kawai ke ta aiki numfashi nafita da sauri-sauri kirji sai faman bugu yake cikin wani irin hali na yanke tsammanin jindadi a cikin wannan lokaci.

har zuwa wannan lokaci wayar ba ta daina kuwwa ba shi kuma Shukuranu bai sauka akan bakarsa nacewa ba zai daga ba tun abin na cin ran Shukura tana kokarin yin magana amma ganin ba halin hakan ya sanya zuba idanu tana kallon sarautar Allah.

abu yaki ci yaki cinyewa hakan ya kara tunzura ran Shukuranu da sauri ya sanya hannu ya dauki wayar yana kokarin kashe ta gabadaya
 
hakan da Shukura ta gani da sauri da isa gareshi gami da rike masa hannu idanuwanta izuwa wannan lokaci sun kada sun yi jajir kamar an yayyafa mata barkono.

"in kana yiwa Allah da Annabi yaya ka daga wayar nan karka yanke ta ba kasan kayan alherin dake tattare da kiran ba kar ka zobe alherin da ke cikin sa ko ya ya yake Alheri ba ya kadan"

DUNIYARMU (Compelet)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora