DUNIYARMU-24

468 30 2
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA.

Wannan shafin nakune aminan kwarai kuma yan uwa abokanan cin mushe..lol

RASHEEDA ABDALLAHI KARDAM
SANAH S MATAZU UMMU-BEENAH

FATAN ALHERI NAKE MUKU A CIKIK RAYUKAN ALLAH YASA KU GAMA DA DUNIYA LAFIYA YA CIKA MUKU BURIN KU NA ALHERI YA KAIMU LOKACIN AURANKU AMEEN SUMMA AMEEN😍😍😍😍

BABI NA ASHIRIN DA HUDU.

Gudu take yi kamar wacce za ta tashi sama,ko ina ta gifta sai mutane sun bita da kallo saboda ganin irin gudun wuce sa'a da take yi.

Zuciyarta ta zafafa matuka. ta rasa mai ke mata dadi cikin duniyar rayuwarta lamura sai kokarin tuntsire mata sukeyi tunanin ya na kokarin gurguncewa kwakwalwarta na kokarin dauko mata kayan shirfe da shiririta.

Ta sani kuma ta tabbatar in har ba tayi kokarin daukar fansa ba karamin illa zata janyowa duniyar rayuwarta ba. ya dace izuwa wannan lokaci ace komai ya kammalu amma ina! ba ta hango hakan ba, Adam Tanga da alamun sai ya wujinjiga rayuwarta in har ba tayi da gaske ba.

"ban yiwa kaina adalci ba, in har ban dauki fansa ba akan Adam nayi wa kaina cuta mafi girma cikin duniyata."

Abin da tashiga fadi kenan, cikin yanayi nason ficewa daga hayyaci, idanuwanta sun kada sun yi jajir kamar wacce aka watsawa barkono.

Tafiya mai nisa tayi daga otel da take zuwa gidan wani shaƙatawa na musamman dake cikin birnin kanon dabo can gefe inda aka tana da don yin (Parking) ta nufa bayan ta saita komai sai da t shafe tsayin mintina kafin ta balle murfin motar tayo waje cikin shiga ta isa da kasaita ta zuro kafafuwanta masu dauke da wasu ta kalma kalar pink da ratsin fari yana da tsinin dunduniya da igiyoyi wanda suka taimaka wajan zaman takalmar a kafarta dodar jikinta kuwa ta riga Arabiya-grow mai ruwan Ash-colour anyi mata kwalliya da duwatsu masu ratsin fari da ruwan gold rigar tayi matukar zaunawa ajikinta kamar don ita akayi ta.

sannu a hankali ta doshi cikin Resturent din ba tare da wani abu ba a bakin kofar da zata sada ta da cikin Resturent din ba zato ba tsammani sukayi kaci bus dashi da sauri ta ja jiki gefe tana faman yatsine fuska kamar wacce ta ga kashi.

shi kuwa murmushi yayi gami da mamaki har yana tafa hannayensa ya shiga dubanta da idanuwansa yana mai gyada kai sa'annan ya nisa.

"is not a Dream dafatan ke din ce a zahiri".

yana fadi yana mai kara kusantowa gareta.

Ita kuwa sai faman tsuke fuska take kamar wacce take shirin fshewa da kuka sam ba ta so haka ba, ba ta so ace ta sake haduwa da wannan mutumin ba cikin rayuwarta...

Maganar da ya sake yi ne ya katse mata dan guntun tunanin da ta fada yi.

"Oh yaaa meye kuma haka ba fa wani abu zan miki ba ba cewa nayi zan rama marin da kikayi min ba naga alamun duk kim rikice".

ya fadi dariya dauke a fuskarsa yana kara kusanto ta har suna jin saukar numfashin juna hannunsa ya kai yana kokarin ta6a da sauri ta kauce gami da watsa masa wani irin kallo mai cike da gargadi.

Amma hakan bai hana shi yin abin da yayi niyya ba jakar dake hannunta ya amsa cikin yanayi na kiciniya don bata so ba amma ganin yana kokarin tara mata jamaa kuma yana kokarin yi mata ta'adi sai ta sakar masa gami da jan tsaki.

"wai mai yasa kuma maza ba ku da kunya ne ya wancin ku sam ba kusan abin da ya dace da wanda bai da ce ba agaban kowa sai ku tsinka mace".

Tsuru yayi mata, yana kallon yarda take sarrafa harshanta da la66ant wajan yin furuci hakan ba karamin tafiya da imaninsa yayi ba sai ya koma sakin baki yana yake mata hakora kamar wanda aka ce an bashi sabuwar budurwa kyauta.

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now