DUNIYARMU-15

638 39 0
                                    

DUNIYARMU
Na
KAMALA MINNA

BABI NA SHA BIYAR
Heejat ce zaune ita da Ayshanty ta na labarta mata abin da ya faru da ita zuwan ta kano da kayan bakin ciki da tashin hankalin da ta dauko Ayshanty tayi zuru tana sauraron.
ta nisa sannnan tace "lamarin yayi matukar daure min kai sam ban yi tsammanin zan sake ganin sa cikin duniyar rayuwa ta ba sai dai abin mamaki ba zato ba tsammin sai ga shi ya dawo rayuwa lamaarin ya duzunguma ni ta wani fanni amma in nayi nazarin baya sai na ga ai watan DAUKAR FANSA ne ya kama a gareni ya zama farilla ya zama dole ya zama tilas in dauki fansa ko da kuwa zan rasa rai na ne ko da kuwa zan yi yawo ba ni da sunturar sanyawa jiki wallahi sai na ga bayan sa" ta karashe maganar ta ta cikin tabbatar da taɓbatuwar haka har azuci da gangar jiki da gaske take.
Ayshanty ta shar ce gumin da yake to mata dan nan ta ja numfashi "kar ki yi gangawar bin lamarin Heejat ki bi komai a sannu domin namiji da kike gani ba a samun sa ko cin nasara akan sa ta dadi rai dole sai anyi masa shiri sosai domin kamar zuma yake in har kan son shan ta ta dadin ra dole ne ka nemi wuta don haka  mu bi komai a sannu"
Duban ta tayi cikin rashin fahimta sannan tace "Ayshanty kin san waye Adam kuwa ai ni ban ki a yanzu na gan sa ba wallahi sau na bude masa wuta"
"duk gajen hakurin dole ki tsya domin shiri tun karar namiji ba abin sauki ba ne"
"ke ki ke ganin ba abin sauki ba ne amma wallahi shan ruwa ma ya fi shi sauki a gareni don haka zuba ido ki sha kallo"
Shiru ayshaty tayi ta na duban Heejat cikin yanayi na mamakin lamarin nata na rashin saukar sa da sauki.
Haka su ka cigaba da hira har zuwa wani lokacin ya wancin hirar ta su duk akan abin da Heejat ke son aiwatar wane a haka har ayshanty tayi mata sallama ta tafi
***   *** ***
Adam ne ya shigi cikin falon sallama dauke a bakin sa amma sam ko kallon Heejat ba tayi ba sai ma kallon gefen ido da tayi masa waje ya samu ya zauna gami da numfasawa alamun ya gaji kusan minti biyu ba wanda yayi kokarin tsinkawa a tsakanin su sai da ya numfasa ya dube ta gami da cewa "a gaskiya nayi da nasani dauko Mubasheer a matsayin direba a gareki domin abin da na ga ya na guda tsakani ku sam ba da ce ba a matsayin ki na na matar aurena ya kamata ace duk wani abin da kika san zai sanya ki kau ce hanya ki gujeshi amma na lura sam bakin san hakkin aure ba ba ma kisan mai nene shi ba BAHIJJA na fara gajiya da lamarin ki tsakani har ga Allah ni fa mijin ki ne na sunna ya kama ta ace duk wata kulawa da mata ya kamata ta baiwa mijinta na hakki ya da ce ace kina ba ni amam sam ban samu wannan matsayin ba sam na rasa dalili ko don ba auran soyayya muka yi ba shiyasa duk wannan rashin jituwar ya gin ta tsakaninmu amma kuma in nayi duba ta wani fanni sai in ga ba kan mu farau ba kuma ba kan mu karau ba ya kama ta izuwa yanzu mu fuskanci ALKIBLA"
Tun da ya fara magana kan ta ke kasa ko alfarmar kallo bai ci ba in ran ta yayi dubu yq bace izuwa wannan lokacin jin ya dasa aya a batun ta ya san ta dagowa rai ba ce fuskar nan ta ta sam ba kayan rahama a jikin ta sai fama zuke idanu takeyi alamuɓ fita ne ce ke cin ta take son a mayar wa tun kafin ta sanya mata ciwon rai.
"Adam mai ya sa ka zabi rayuwa da ni mai ya sa ka shigomin rayu mai yasa tsautsayi da ganganci suka sa ka son zama da ni a matsayin mata mai ya sa ban san ka ko a mafarki amma ka zama mijin aure na mai ya sa ba ka nemi yarda ta ba kafin ka aure ne mai ya sa ba ka nemi amincewa ta kafin kayan ke hukucin zama  dani ka san wacece ni kafin ka yarjewa zucciyarka aurata ba kasan ni ba kawai ka nemi aure kuma hakan kana gani dacewa ne don haka wallahi tallahi yanzu ka fara gani kayan haushi da bakin ciki in dai ni ne sai ka sha mamaki musamman da ka kasance ADAM bakin suna sunan da ya tarwatsamin rayuwa ya kashe min farin ciki na ya rayamin bakin ciki cikin duniya don haka ka dai wani tunanin zaka same ni a rayuwarka domin ni ba abokiyar rayuwa ba ce!"
ta karashe maganar tata cikin dishewar murya mai son fashewa da kuka
Cikin rashin fahimta ya shiga duban ta da mamaki jin furuncin ta ya rasa in da ta dosa ya ji ta ambaci sunan sa kuma tace mai sunan sa ne ya kashe mata farincikin kenan ta na nufin dalilin da yasa ta kin yarda dashi kenan anya kuwa haka ne ina! akwai dalili
"ZAN RAYU DAKE!"
bai san lokacin da furucin ys fito daga bakin sa ba cikin wata irin murya mai taushi da sigar rarrashi
Wata tsawa da tayi ne ta tsinke mata zaren tunanin sa da sauri ya kai duban sa gareta tsaye ya ganta kan shi sai faman huci take kamar kububuwa idanuwan ta a warwaje fuskarta ta kada tayi jajir cikin kankausar murya ta fara magana a zafafe
"aiko in har kace zaka rayu da ni aiko ka na shirin mutuwa da bakin ciki a zuciyarka kaji na rantse maka ko SHAKKA ba nayi"
ta na gama fadin haka tayi cikin dakin fuuuu
bin ta yayi da kallo cikin yanayi na rashin dadin rai da armashi dafe kai yayi gami da fadin 'YA ILAHI' wani gumi ya ga shiga keto masa kamar wanda kayi wa wankar ruwan zafi ya kara nutsewa cikin kujerara da yake gami da cusa hannu cikin sumar kan sa haka ya jima cikin wannan halin na rashin dadin rai tsayin mintina talatin sannan ya mike bayan zuciyar sa ta lafa da zuki ya fada dakin sa toilet ya fada gami da sakarwa kan sa shawa ko ya ji saukin CIWON RAI dake ɗawainiya da zuciyar sa da gangar jikin sa yazai yi dai ita mai zan yi don ya sanya ta so shi tabbas ya lura ba ta son shi ko kadan mai yasa haka laifin waye nisa wa yayi gami da fadin laifin sa ne shi ne mai laifi ya tafka babban kuskure da yaki bin hanyar da ta dace domin samun soyayyar ta son ta ya rufe masa ido ya manta da komai shi dai kawai ya aure ta shi ne burin sa gashi ya aureta amma ya rasa so ya rasa farin ciki ya rasa muradin  ran sa ya rasa cikar burin sa shi yazai yi da ran sa ya zai yi da son sa dake nukurkusar zuciyar sa mai yasa zuciyar sa ba tayi masa adalci ba mai ya sa ta nuna masa son kai mai ya sa tun farko bai yi tunanin da zai yi masa dakyaua ba yayi aure don yana so amma gashi ba kwanciyar hankali kai jama'a kai jama'a shi kam ya ga ta kan sa ya zan yi da Bahijja dhi da yana son ta da ita yake so ya rayu ita ka dai ce 'ya macen da zuciyar sa tayi amanna da ita anya zuciyarsa ba tayi wauta ba wajan son abin da ba ta son ta ta kinkimo masa kayan tashin hankali in da ya san haka rayuwarbauren sa za ta kasance da Bahijja da bai faraba sai dai da yake komai na Allah ne da ma ya tsaka sai anyi auren koda kuwa za ayi rashin rayuƙa balle ma ba ayi amma har a zuciyar sa ya na tunani nan gaba za a samu jituwa da izinin Mai duka.
Da wanna tunanin ya kammala shekawa kan sa ruwa ya fito ya gyara jikin sa sosai tare davsanya kaya masu matukar kayartada jikin sa ya feshe jikin sa da dadadan turare mai matukar kamshi da sanyaya zuciya shi kan sa sai da ya ji sanyi amma zuciyar sa a cinkushe take ba wani walwala sosai hakan yafito falo ba kowa cikin sa ya dubi sashin ta ya girgiza kai wani guntun murmushi ya suɓuce masa ba tare da ya shirya ba har a ransa ya na kaunar Bahijja sai dai ita sam ta kasa sanin haka
"ZAN RAYU DAKE"
Ya fadi cikin suɓutar baki da sauri ya juya don tunani yake ko ta na kusa da shi ganin ba kowa har zuwa wannan lokaci ya san yashi saurin ficewa daga falon motar sa ya shiga gami da yi mata ƙey yayi wa mai gadi horn ya bude masa ya fice daga cikin zuciƴa cikin wani irin hali na rashin armashi.
***       ***     ***
A sukwane ta iso cikin falon ta zube kan kujera kamar wata kayan wanki sai sauke ajiyar zuciya take kamar wacce tayi tseran gudun duk abin da keyi khalil na kallo ta amma bai yi kokarin tsinka mata ba kamar yarda tashigo ba tare da ta yi masa ko da sallama ba ya ba banza ajiyar ta har ta gama shan sharafin ta ts dago ta dubi in dayake zaune cikin raunannun idanuwanta kamar wacce tayi wa cikin ta cushen Allah tsine ganin da tayi hankalin sa bai kan ta hakan ta sa ita ma ta yi banza dashi amma ba ta sani ba duk abin da takeyi ya na kula da ita haushi da takaici ne suka cika shi yarasa abin cewa abubuwan da Ayshanty takeyi masa ya kai makura yayi hakurin amma ina an kai shi bango ya rasa wata irin macece ita mai baudanden hali maras kan gado mata sai kace ba mai igiya uku akan ta ba yarda take daukar kan ta kamar wata mai zaman kan ta shi fa ya fara zargin wani abu game da ita domin sam rayuwar da takeyi yanzu ba irin ta da bace wacce ya san tada ita ko dai dama acan haka take lulluɓi tayi masa kura da fatar akuya saliha a fuska amma a zuci kwalluwar shegiya ne tabbas biri yayi kama da mutum ya kama ace zuwa wannan lokaci ya san wacece ya ke zaman aure  da ita yasan ainihin fuskarta don ya lura fuskar biyu ce ita  daga kai yayi ya kalle ta a daidai lokacin ta zare doguwar rigar dake jikin ta gabansa ne yayi wani irik bugu ganin irin shigar da tayi da wasi la'anannun kaya wanda su da babu duk daya suke zuciyarsa ta shiga bugu da tsalle tsalle ya rasa bakin cewa wani abu sai yau ya kara tabbatar da Ayshanty JARABAR DUNIYA ce ita ma tana cikin sahun matan aure masu ai kata fasiƙanci a waje kenan masu cin amanan auren su da na mijin su zuciyar sa tayi saurin ƙwaɓar sa akan bai dace ya ke zargin matarsa ba tun da ba gani yayi ido da ido ba tana cin amanar auren sa ZATO ZUNUBI ko da kuwa ya kasance gaskiya ne shiru yayi yana mai nazarin abubuwa da halayan Ayshanty na tsayin laokaci da ya san ta ya kamata ace yayu wani abu akai tun kafin lokaci ya shammace shi gyada kai yayi alamun tabɓatuwar haka da hanzari ya tashi ya sungumi Lipton din shi yayi sashin sa batare da ko kallon ta yasake yi bawacce a wannan lokacin ɓarci ya fara galaba akan ta bata san ma ya tashi ba ko da ya shi dakin sa kasa nutsuwa yayi zuciyarsa sai faman cigiye cigiye take sam ya kasa yarda da Ayshanty izuwa wannan lokaci ya na shakka akan ta zuciyarsa ta na gaya masa akwai wani BOYAYYEN AL'AMARI da bai sani ba wan da yake tunanin shi ake cutar wa zarya ya fara yi cikin dakin nas ya kai gwauro ya kai mari ya rasa abin da zai yi takamaimai zuciyarsa ta kasa kwanciya ta kasa nutsuwa waje daya iska ya kai wa bugu da hannun sa duk biyun sannan ya dafe kan sa gami da fadin 'Ya Allah' ya fada kan gadon sa yayi shiru kamar mai son canko wani abu da ya shige masa duhu.
***   ***    ***
HYDRO HOTEL.
cikin matsananciɓ gudu ta karo so cikin hotel yarda ka san wacce za ta tashi sama tayi fuka-fuki mutnan dake zaune a farfajiyar otel din sai bin ta suke da kallo kamar wadanda su ka ga bakon lamari wasu tsaki suke ja gami da kau da kai wasu kuwa kafe motar da ido sukayi don ganin waye mamallakin ta baka wuluk yar madaidaiciya da ita sai kyallin kyau take can nesa in da aka tana da don yin parking ta dosa gami da jan burki har sai da yar karamara kura ta tashi duk da wajan ba turɓaya bane amma sai da hakan ya nuna shafewar mintina sannan aka fara kokarin fitowa kafa ce maidauke da takalmi sau ciki amma mai matukar tsini kalar baki da ratsin fari a jiki sakanni kadan ta zuro gangar jikin ta izuwa waje sanye take da atamfa kalar maru da ratsin yalo wanda akayi wa dinkin siket da riga rigar tayi matukar kama ta musamman wajan kirjin ta don rabin kirjinta a waje yake da cikin ta kuma rigar an bude ta sosai haka siket din yayi matukar kamata a kugu kamar zai tsage haka yake daga kasar sa a buɗe an yi masa cin baki da wani zare mai ruwan gold din yayi matukar kyau kan ta dankwali ya ji dauri kamar injin ya naɗashi daurin fanka-fanka daga can baya jelar gashin tane wanda akayi wa ciko da na doki ke lilo fuskar ta kuwa ta ji make-up har wani kala-kala takeyi an saka gashin ido ga gira an feke ta sosai bakin nan ya ji janbaki purple-colour kamar a suɗe 😯 hannun ta rike da jaka mai ruwan hanta sai dayan hannnun nata ƙey da kuma taffatsetsiyar wayarta wacce kallo daya za kayi mata ka san ba daukar wasa akeyi ba ta ba domin na shaki kudi har sun koka don kan su ajiyar zuciya tayi sannan ta mai da kofar motar ta kulle ta fara taku ilahirin jikin ta ba inda bai motsawa musamman kirjin ta da kuma kugunta hankalin kowa sai yayo kan ta duk in da ta gifta sai ta bar musu tsarabar kamshin turaren ta wanda ya amasa sunan sa da turare dan uban su tayi nisa da tafiya har takusan take benen da zai sada ta da cikin otel din kamar daga sama taga an sha gabanta tare da ware hannu alamun ba za bar ta ta wuce ba da mamaki fal a fuskarta ta dubi wannan wanda zai nuna mata iko da gadara na hanata wuce wa abin da ba tayi tsammani ba wani banza zai yi mata tun daga yatsar kafarsa ta far kallon sa ba ta dire ba sai tsakiyar idanuwansa mamaki ne yakara cika ta lokacin da tayi arba da shi lokaci guda kuma ta janye mamakin ta hadi da daure fuska ba alamaun wasa a cikin sa ta yi saurin kau da kai sannan ta ni sa cikin izza ta ce dashi " wani irin akuyanci ne wannan kake kokariɓ yi min Sk lafiyar ka kuwa ko barasar da kake bankawa cikin ka ta fara haukata kwanyar ka ne?" ta karashe cikin tsiwa da tsananin bacin rai murmushi ya saki duk kalamanta ba suyi wani tasiri wajan ba ta masa rai ba ya shiga tafa hannu yana mai dariya kasa-kasa sannan ya watsa mata wani kallo wanda ya san zai iya kalaba akan ta sannan ya ce "zan iya amsa kowa ni suna za ki kira ni dashi domin nasan dai a iya baki ne ba har zuci ba na san ana so na kawai bacin rai ne ya sanya haka amm in har zaki iya kallo kwayar idanuwa na ki fadi haka zan iya amincewa Teemah!" ya karashe cikin salon barikanci irin nasa da rikita kwanyar duk ya macen da ta shigo hannun sa. maganar sa ta bugar masa da zuciya amma ba ta bari hakan yanuna a fuskar ta ba cikin shan kamshi ta dago idanuwan ta farare tas wanda a wannan lokaci sun fara rinewa zuwa ja "Sk ka  rabu dani ka fice daga rayuwa domin kai sam ba mutumin da yaka mata a din ga mu'amala da shi ba ne Sk kai kan ka ka san ina son ka amma saboda butulci irin naku na mazan bari ki na rashin tabbas da kalaman yaudara da cin amana shine a gaban ka ake ta min rashin mutunci amma ka ksa tabuka komai amma a hakan kira kake yi kana so na lura ba ni kake so ba gangar jikina kake so duk halin da kake ciki na sani Sk duk yaudara da  kake yi na harbo cikin ka tuni!" jin abin da ta fadi ya san yashi yin laushi amma a zahiri ba a cikin zuci da ya ke faman sheka mata dariya yana mai cewa 'kadan kenan daga aikin KADANGARUN BARIKI 'Yarinya har yanzu ke ba kin bariki" amma a fili sai cewa yayi cikin kashe murya da salon yaudara "in zan yaudari kowa ban dake in zan ha'inci kowa ban dake in zan ci amanar kowa ban dake Teemah har zuci ina son ki matuka ke ne dai har yanzu baki fuskance ni ba ba ki fuskanci rayuwar damu ke ba izuwa wannan lokaci ya kama tq ace kin yarda dani dari bi sa dari kamar yrda na amincewa kai na ZAN RAYU DAKE! ZAN MUTU DAKE!" idanu ta watsa masa sannan ta fara nazarin kalaman sa cikin ma'aunin mizanin kwanyarta da zuciya cikin kan kanin lokaci tayi amanna dashi amma duk da hakan ba ta nuna ba sai ma jan numfash da tayi gami da gyara tsayuwar da tayu hakan ya bashi damar fuskarta ta cikin ganɗoki don ya lura komai ya fada yarda yake so "ayi min afuwa Teemah na san nayi kuskure amma nayi alkawarin ba zan sake ba"kƴaɓe baki tayi gami da zakuda kafada tayi farrr😊 da idanuwan ta wanda suka dawo fari tas! Kamar madara Sk ya saki murnushi shi ma gami da amsar jakar dake hannunta ya yi mata nuna da su tafi haka suka jera kamar rakumi da akala ta na gaba ya bin ta mutanan dake harabar otal din sai kallo ikon Allah juyo yayi ya kalli abokanan sheke ayarsa yayi musu nuni da alamuɓ nasara suka sheke da dariya kasa-kasa suna mai yi masa jinjina suna isar su cikin otal din ke da wuya wata motar tashigo cikin otal din hankalin jama'ar wajan yayi kan ta cikin yan sakanni akayi parking gami da fitowa AYSHANTY ce abokan nan Sk da ke zaune su ka hango ta haɓawa duk kan su suka kwalalo idanuwa waje cikin tsoro da mamaki fal zuciya daya daga cikin su ya ce " ta faru ta kare Hisham ga ka ayshantƴ ta shigo kamar wacce a ka gayawa Sk zai yi bakuwa" wanda aka kira da Hisham ya nisa cikin halin damuwa "kasan kuma ba jituwa sukeyi da Teemah sam don kuwa haduwarsu ba tayin kyau a dalilin ganin Skda Teemah da ayshanty tayi watannin baya har fad sukayi ta uwa ta uba har fasawa Teemah kai tayi tun daga ranar Sk ya samu matsala da Teemah sai yu da suka sasanta junansu to kuma ga shi za a bar BAYA DA KURA" da sauri ya shiga lalubar wayar Sk domin ya sanar masa amma a bisa rashin sa'a sai ga wayar a wajan su ya man ta da ita Hisham ya ce "mun shiga uku Kabeer kaga wayar ta sa nan ya bar ta yanzu menene abin yi..." maganar Ayshanty ta sanya su saurin gimtsewa ganinta a gaban su sam ban su tsammanin ta iso garesu ba cikin yanayin yaƙe suka amsa mata kallo ta bi su dashi ganin alamun tambaya akan su taɓe baki tayi sannan ta dubi Hisham ya yai sumar zaune "Ina dear  Yake?"
Aka rasa mai bakin amsa matasai mazurai suke hakan ya kara tabbatar mata da akwai wata a kasa ba ta bi ta kan su ba tayi hannayar cikin otal din da sauri Hisham ya fara kokarin kiran ta amma Kabeer ya dakatar dashi gami da cewa "rabu da ita kawai wallahi su suka jiyo" shiru sukayi na dan lokaci ko wannan su yana nazarin irin abin da zai faru don sun tabbata ba za ayi ta dakyau ba...Ihun da a ka zunduma ne ya yadawo dasu daga barin tunani Sk ne ya fallo a guje daga shi sai gajeran wando kan sa sai zubar da jini yake yi yayo kan su Hisham ya na faman kururuwa da nema dauki hakan ba karamin tayar musu da hankali yayi ba zunbur suka miki suna masu faman zare idanuwa jiki na kyarma sauran mutanan wajan su a firgice su ka tashi matan wajan kuwa sai hannu suke daura aka su na zunduma ihu kalilan ne a cikin su wadanda ba suyi hakan ba Sk na isowa gaban su Hisham ya fadi warwasan yana numfarfashi ba su ankara ba kawai su ka ga Ayshanty akan su ta daga fasanshiyar kwalba ta lumawa SK a kirji ya saki wani ihu mai kara da amsa amo a take numfashin sa ya dauke...

Kamala din kune😍😍😍

Voter and comment line by line🙌🙌🙌

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now