DUNIYARMU

6.4K 207 9
                                    

DUNIYARMU
       Na

Kamal Muhammad Lawal
   (Kamala Minna)
  07039355645
2017
BABI NA DAYA
Tafiya take sannu a hankali kamar mai jin tausayin kasa hannunta duk biyun rike suke da guntayen karare ta na kada su su na ba da sauti mai matukar kayatarwa. Kamar daga sama taji sautin murya na ambatar sunan ta. Cikin sauri ta ja birki ta tsaya gami da juya wa dan ganin wanene mai ambatar sunan nan
"Shukaranu!" Abinda ta ambata kenan fuskar ta na bayyanar da lallausar murmushi mai matukar k'awa da kara fuskar armashin kyau. Kafe shi tayi, da manyan idanuwanta tana kara faɗaɗa murmushin fuskarta, har ya iso in da take lokaci guda suka sakar wa juna wani shu'umin murmushi mai ciki da amo da armashin daɗi da kayatar da zuciya da ruhin da suka juma cikin kaunar juna.  Cike da kulawa atausashe cikin sautin murya mai jan hankali Shukuranu  ya dubi Salma wacce gaba ɗaya ta gama dulmiyewa cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa. Hata idanuwanta gaba daya sun tsaya cak! Bisa kan masoyin nata ko kiftawa ba tayi.
"Salma kafar yawo daga ina kuma ake cikin wannan zafaffiyar ranar mai kokarin dauke fatar jikin dangin rai ta aza masa ciwon gaɓai da tafasar kwakwalwa?"
Ya fadi cikin sigar zolaya da wasa, tsuke fuska tayi kamar wacce ba ta taba yin wani abu wai shi murmushi ba sannan tace. "Gantali naje yanzu na dawo."Cikin ja baya alamun tsoro ya kwalalo ido waje
"Me kike ce?"
"Cewa nayi daga gantali nake!"
Ta bashi amsar tambayar cike da nuna ciwon rai. Shiru yayi na dan dakiku kamar mai nazarin wani abu  sannan ya sake duban bayan ya yi ajiyar rai cikin marairecewar fuska
"Yi hakuri."
Cikin rashin fahimta ta dubeshi, "hakuri kuma? me kayi min kake ba ni hakuri?"
"Na ba ta miki rai" ya faɗa a gajarce.
"Na ce maka?" Ta fadi cikin kafeshi da idanuwanta masu kama da maganaɗisun majayin janye zuciyar wanda aka yi wa kallon. Shima idanuwa ya zuba mata. "Gani nayi maganar da nayi miki kamar ba tayi wa rankin dadi ba." Gyada kai tayi sannan tace, "a ganin ka kenan."
Ta faɗa tana ɗauke kai daga kallon da yake jefa mata, "tabbatuwar haka na gani bisa lakari da amsar da kika bani."
Murmushi tayi sannan ta juya ta na kokarin wucewa. Da sauri ya sha gaban ta cikin tsumewar fuska ta ce,
"Mene ne haka?"
"Me kika gani?"
Ya faɗa yana mai  watsa mata harara, "gani nayi kina kokarin wuce wa ba tare da kin jira ni ba." Sake tsare gida ta yi ta kau da kai  "ai ba tare muke tafiya ba hanyace ta hada mu." Sakin baki yayi, ya na duban ta cikin murmusawa sannan yace,
"Kuma dan hanya ta hadamu ko ma shikenan ba za muyi tafiya tare ba?"
Shiru tayi alamun ba ta da niyyar yi masa magana.
"Ina jin ki." A shagwaɓe ta turo baki tayi gaba tana faɗin, "ni dai yasin ba zan shiga cikin gari da kai ba mu jera muna  tafiya ai sai ayi mana wata fassarar ta daban ace ba mu da kunya." Bai san lokacin da dariya ta kunce masa ba ya shiga sheka ta har ya na dafe cikin sa ya shiga nuna ta da hannu ita ma dariya ta kama yi masa haka suka zama kamar wasu kwasar dawanau. Shi ya fara tsagaida tawa sannan ya dubeta.

"Ke yanzu dan Allah baki ji kunyar abin da kika fada ba?" Hannu ta sa ta rufe idon ta sannan tace, "su Malam fa na nan kofar gida lokacin da na fito kuma yanzu in na koma su ga mun taho tare ai da kunya."
Kuri yayi mata da ido, shi dai hallayan Salma suna matukar burgeshi musamman kunyar ta da kawaici a matsayin ta na 'ya mace gyada kai yayi tare da watsa hannu sama
"Shikenan..
"Ba dai fushi kayi ba?"
Ta fada dalilin gani da tayi yayi magana cikin sanyin murya.
"Ko daya ta yaya zan yi fushi da ke Salma? Akan me? Ni abin da ma ki kayi burgeni yayi sossai." Da sauri ta bar wajan saboda maganarsa ta  bata kunya. Kaɗai kai ya yi yana mai bin ta da kallo fuskar sa da zuciyar sa na bayyanar da tsantsar murmushi da muradan jindadi, sai da yaga ta bacewa ganin sai sannnan ya sauya hanya ya bi wata ba in da Salma ta  bi ba.

***   ***    ***
"Na shiga uku! Ni 'yasu mai na ke shirin gani cikin duniyar rayuwa ta?" Inna Luba ce ke fadin haka cikin tsananin tashin hankali da kakabin zance. Ta tallabo Salma da ke kwance magashiyan cikin jini ba alamun rai a jikin ta ta girgiza sosai amma ina ba alamun motsawa cikin gigita ta kwashi kafafuwa tayi waje da gudu ta na kurma ihu tana kururuwa ta ba ni ta lalace ta ɗakin Malam tayi wa tsinke cikin tashin hankali zaune ta sameshi ya na lazimi  a firgice ya dubeta ya na ambaton,
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Cikin gigita  gaban sa ta zube tana rusar kuka mai ciki da tashin hankali da yakewar farinciki rayuwa. Murya na rawa cikin shakakkiyar murya mai dauke da kuka "Malam an kashe Salma an kashe min ita an rabani da ita an yanke min farin cikin  rayuwa na shiga uku!" Cike da sauri ya ɗago cikin ambato,
"Me ki ke cewa Lubabatu? Kalau kike kuwa ko dai mafarki kika yi ya firgita?" A zafefe ta tare shi, "wallahi  ba mafarki bane zahiri kuma ta so ka zo muje ka gani wallahi an kashe ta!" Cikin nuna alamun yarda ya dubeta.
"Ya kamata ki natsu ki mai do da hankali da nutsuwa jikin ki."
Ya fadi yana mai girgiza ta lokaci guda tayi shiru amma jikin ta bai bar karkarwa ba,
"Alamun mafarki kika yi wanda ya firgita shi yasa kika gasgata abin."
"Kasan Allah Malam da gaske na ke", ta fadi ta na mai kokarin tashi  shima ta shi yayi su ka rankaya suka yi dakin Salma tun da ga kofar dakin su ka fara cinkaro da jini a kasa dalilin hasken farin wata da ya haska sosai. Duk kansu gaban su yayi matsanancin bugu da sauri Mlam yayi cikin dakin. Amma abin mamaki wayam bai ga kowa ba Salma kanta ba alamun ta sai yanayin dakin da ya hargitse ga jini ta ko ina ya yi faca-faca.
Wata irin katagar tashin hankali mai dauke da rugugi ta saukarwa Malam lokaci guda ya shiga tashin hankali, shi ma ba abin da bakinsa ke ambato sai sunan Allah da addu'o'i da su ka zo bakin sa na neman a tsari. Wani hsrgitsatsan gumi.shiga keto masa cikin kan kanin lokaci ya ya yi jagaba Inna Ƙuba da ke girke bakin kofar cikin yanayi na yanke tsammani da muradan kwanciyar hankali ta fado dakin. Numfashin ta ya fara safa  da marwa  yana kokarin dauke wa ganin da tayi ba Salma in da ta bar ta wani ihun kuwwa ta saki ta zube kasa numfashi ya fice da ga jikin ta.

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now