DUNIYARMU-35

413 16 0
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA.

BABI NA TALATIN DA BIYAR.

Tun sanda Bahijja ta samu kufcewa daga cikin Asibiti ba ta zarce ko ina ba sai gidan Mansoor cikin wani irin yanayi na farinciki domin ta tabbata hakarta ta kusan cin ma ruwa. Yanayin da ta ga Adam aciki ta tabbata sai wani ba dai shi ba cikin duniyar nan.
da wannan tunani ta isa cikin gidan tayi Parking ta fito sai dai kuma ba ta ga motar Mansoor ba alamun shi ma ya fice daga cikin gidan da sauri ta koma wajan mai gadi ta tambayeshi nan yake sanar da ita lokacin da Mansoor ya fita ita ba ta dade da fita ba gyaɗa kai tayi tana nasawa a ran Mansoor ita ya bi kenan karasawa tayi cikin gidan a falo ta zube sai faman numfarfashi take kamar wacce tayi gudun fanfalaki. Idanuwanta a sama kamar mai kallon silin da fankar dake aiki amma ina tunani ya ziƴarci zuciyarta lokaci guda ba tare da tayi tsammanin haka ba abin da ta tuna sai gidan aurenta tun da ta baro shi ko sau daya ba ta taba zama da sunan tayi tunani akan sa wani hali yake ciki ina Adam yake izuwa wannan lokaci. Tsaki ta ja kamar wacce aka yi wa wani mugun abu zumbur ta mike ta isa gaban firijin dake girke cikin falon ta buɗe tare da zaro gorar ruwan EVA mai dan rangwamin sanyi ta balle murfin ta shiga kwararawa cikin ta har sai da ta kusan shanyewa sannan ta dire tana faman ajiyar zuciya sai kaɗa idanu take yi kamar wacce take gaban mai son ta natsuwar zuciya ta fara ziyartarta tana ji a ranta lokacin ta yayi lokacin huce takaicin ta yayi lokacin rage raɗaɗin zuci yayi duk da dai ta san rayuwarta ba za ta taba komawa kamar da ba komai nata ba zai taba dawowa kamar yarda take yin sa ba a shekaru goma baya hakan ba zai taba faruwa ba ko da kuwa a baɗini ne.wasu hawaye ne su zubo mata hannu ta sanya ta shafe su kafin ta ko kan kujera ta zauna wani irin abu ne taji yana yawo a zuciyarta da gangar jikinta wasu lamura na ziyartar kwakwalwarta lokaci guda ba za to ba tsammani wani hargitsantsan tunani ya ziyarce ta zumbur ta mike kamar wacce aka tsikara Abbanta ta tuni yashe rabon da su ga juna yaushe rabin da ta kira shi a waya yaushe rabon ko da gaisuwa ne ta mika masa ko ta hannun wani ne anya kuwa ta kyauta anya kuwa ba tayi wa kanta wauta ba ta mance da mahaifinta da duk wasu lamura nashi a dalilin son daukar fansa gaskiya ya kamata ta san abin yi ya kamata ta kai wa mahaifin ta ziyara. da sauri ta mike ta sure jakarta ta yi waje ta shiga motarta face tana mai sanar da mai gadi in Mansoor ya dawo ya sanar dashi ta dawo amma baya amma za ta je Dorayi ta dawo ba ta tsaya jin amsar sa ba ta fice cikin hanzari tun da ta hau titi take ta faman zabga gudu cikin kankalin lokaci ta isa hotel din da take zaune da sauri ta isa dakinta wanka tayi sosai ta canza kaya cikin kwalliya mai armashi kallo daya kayi mata sai ka rantse ba abin da ke dawainiya da ranta a haka ta kammala komai ta fito ta shige motarta ta ja ta tafi sai da tayi tafiya mai nisa ta tsaya sani Super-Market tayi wa Abban nata sayayyar tsaraba sosai sai da ta cika bayan but din ta nan ta sake daukar hanyar Dorayi cikin SAƘAR ZUCI da yanayin da za ta samu kallo da ga mahaifin nata ta san ita mai laifi ne sosai dole kuma ta dauki laifinta dole ta je a matsayin mai laifi babba kuma ta ne mi afuwa ta san mahaifinta mau yafiya kuma ba zai kullaceta ba sai dai ta san dole ya shiga damuwa sai a rashin jinta kwana biyu sama da sati biyu tana cikin garin kano amma ko sau daya ba taba tunani kai masa ziyara ko kira a waya ba ko dayake ba ka safai take barin waya a kunne ba za iyayuwa shi ya na neman bai ya samu tabbas zai nema ta ta san halin mahaifin nata da irin so da kulwa da yake yi a gareta, gabanta ne taji ya fadi dalilin tuna mijin ta Adam tabbas mahaifinta zai iya kira Adam in kuwa hakan ya kasance da matsala tabbas da matsala nan da nan wani tashin hankali ya ziyarce lokacu guda ta ruɗe ba abin da take tsoro illa Abban ta ya kira Adam ya tambaye ya nuna ba ta nan ya san dole ya nemi ba'asi tabbas zai iya fada masa gaskiya 'innalillahi wa inna ilaihir raji'un' abin da ta shiga ambata kenan cikin zuciyarta da kasar ruhi wani irin bugu zuciyarta ke saki kamar zata faso kirji ta fito guda ta karawa motarta ji take kamar ra tashi sama ta isa wajan mahaifinta rokon Allah take akan kar hakan ta faru domin in har hakan ta faru ba karamar matsala zata fuskanta ba cikin duniyar rayuwarta cikin wannan yanayin ta isa Dorayi nan ta ji wani irin faduwar gaba ya dirar mata lokaci guda saura kadan sitiyari ya kufce mata cikin hanzari tayi sa'ar saitawa ji take yi kamar akwai abin da ke faruwa ji take kamar akwa wani tashin hankali da za ta tadda in taje mara dadi da firgita zuciya jikinta yayi matukar sanyi lokaci guda a hankali ta cigaba da can motae kamar wacce kwai ya fashewa a ciki faduwar gabanta sai kara hauhawa yake yi gabadaya ta shiga wani yanayi na rashin hayyaci karfin zuciya ne kawai ya isa da ita kofar gidansu kallo daya tayi wa kofar gidan nasu ta firgice lokaci daya Parking ma kokarin gagararta yake yi sai da tayi da gaske sannan ta samu natsuwar da ta taimaka ta kashe motar mutanan da ke layin nasu yan majalissa sai faman kallon ta suke amma ita ba ta san su nayi ba cikin hanzari ta zare key din motar gami da kulle ta fara tafiya cikin wani yanayi na rashin kwarin jiki sai faman tangaɗi take yi motar dake can gefe ajje take bi da kallo in har ba gizo idonta ke mata motar Adam take hange to meke faruwa mai ya kawo Adam gidan su ko dai ita ya zo nema in ƙuwa haka ne ta fadi ba nauyi kamar wacce aka tsiraka haa ta kwasa da gudu tayi ciki gidan tana shiga tsakar gidan ta ja birki ta tsaya zaune ta hange shi saman tabarma hannusa rike da waya gabadaya hankalinsa yana kan wayar kallo daya tayi masa ta ga duk ya zube ba kamar da ba sai taji ya dan bata tausayi kadan amma bata bari tausayin yayi tasira a gareta ba domin har zuwa wannan lokaci ba ta ji wai za ta iya zama dashi ba ko na dakika daya ne a matsayin igiyar aure na tsakanin su za ta so ace sakinta ya zo yi amma sai dai matsala daya mahaifinta ta san dole ta shiga tashin hankali in har ya san abin da ke faruwa da ita...muryar Adam ce ta katse jin yana waya firgigin ta dawo hayyacinta ta dago shi a sa'ilin ya dago kan sa ya nuna alamun firgici sai dai bai bari ta ga hakan ba sai ma kau da kai da yayi kamar bai ganta ba ya cigaba da wayarsa amma a zuciyarsa hankalinsa da natsuwarsa duk suna gareta ita kuwa mamaki da fargaba duk suka cika ganin irin kallon halin ko in kula da Adam ya nuna mata tabbas ta san akwai wata a kasa gyaɗa kai tayi cikin mazawa da nuna ita halin shagulatun bangari a garesa tana faman cin-cin magana amma zuciyarta ji take kamar katangar rusau ce a zubo mata akaia saboda tsabar fargaba da lamuran da suke shirin afkuwa gareta a hankali ta fara tafiya cikin guntuwar jarumtar da take tsammanin ta rage mata ba in da ta nufa sai tsohon dakin mahaifiyarta ta shige ba tare da tsake kallon in da Adam yake ba mamaki ne ya cika shi bayan ya kammala wayar ya ga yarda ta shigo ba alamun wani abu na damunta koma ganin sa da tayi bai haifar mata da komai ba hakan ya kara sanya shi karaya da lamarin ta nan ya shiga ajiya zuciya kamar wanda akayi wa dole yana faman bin kofar dakin da ta shiga da kallo  a daidai lokacin shikuma Abban Bahijja ya fito daga bandaki buta rike a hannunsa kallo daya zakayi masa ka tabbatar da tashin hankalin da yake ciki idanuwansa sun kaɗa sunyi jajir kamar wanda akayi surace da hayaki can gefe ya dungurar da butar cikin yanayi na mutuwar jiki yayi tsaye kikam kamar wanda aka dasa hannayensa a hade guri guda duniyar ya ji tana juya masa wani lamari da bai taba tsammanin sa ba zai faruwa a gareshi ko a mafarki shi yake gani a zahirin sa yana afkuwa wata kaddara mai wuyar dauka gareshi ya ga tana tunkaro duniyarsa a halin da yake ciki anya zai iya dauka kuwa zuciyarsa ba za ta buga akan bakon lamarin da ya zo masa lokaci guda wanda bai taba kawo haka ba Bahijja 'yarsa guda tilo da ya mallaka cikin duniyar rayuwa ita ce take shirin wargaza masa zaman lafiyar duniyarsa mai ya sa haka mak yasa Bahijja za tayi masa haka mai ya sa take kokarin kashe da tashin hankalin da yaji a dalilinta ba zai taba son haka ya tabbata ba zai so ace mafarki yake yi ba gaske ba zai so ace wannan lamarin a baɗinance ne ba zahirance ba nisawa yayi cikin matukar kunar rai da zafin zuciya ya dubi Adam da tashi ya zuba masa idanu yana kallon yanayin da tsohon ke ciki yayi matukar tausaya amma hakan ba wai yana nufin fasa abin da ya zo yi bane kau da kai yayi domin zuciyarsa kara narkewa take yi a tausayinsa
"kace tsayin sati biyu kenan rabon da gidan auranta, in kuwa haka ne to ina Bahijja ta nufa?".
ya fadi cikin rawar murya da yanke tsammani da farinciki.
Gyada kai Adam ya shiga yi cikin wani irin yanayi na rashin dadi kafin ya kokarta magantuwa.
"lokacin da za ta fita kano ta ce za ta zo amma ban san inda zata zo akano sai dai a lokacin nayi tunanin ko nan za ta zo".
girgiza kai ya shiga yi.
"haba Adam ta ya ya kake tunanin zan bar Bahijja tsayin satika zaune a gidan nan alhalin ma wata matsala ke faruwa da ita ba".
Ya fadi cikin yanayi na kunar rai da zafin zuciya idanuwansa sun kara kadawa sun yi jajir ji yake ina ma wannan lamarin mafarki ne ba gaskiya ba ina ma ace ba da gaske bane.
"ni dai maganar zama da Bahijja ya kare domin har ga Allah nayi iya bakin kokarina amma abin ya ci tura ban san haka take ba da tun farko ban yi gigin shiga rayuwarta ba don haka ni kam na sauk...".
Da sauri ya tareshi cikin rawar jiki.
"karkayi min haka Adam na roke karƙa gayyato min abin da zai saka zuciya ta buga ka raka min lokaci zan yi duk abin da ya dae domin ganin komai ya daidaita".
Yanayin da yayi maganar yayi matukar sanyaya jikin Adam amma bai bari hakan ya kashe masa hanzarin da ya dauko wa kan sa ba ya shiga kokarin magana adaidai lokacin ita kuma Bahijja ta fito daga cikin dakin wani irin kallo da take yi wa Adam shi ya kashe masa baki dubanta ya shiga yi ita ma dubansa take yi cikin takaici wai Abbanta ne yake baiwa Adam hakuri da kar ya fadi abin da yayi niyya wani kunci taji wai mutumin da bata so shi abbaɓta ke roko da kar ya zartar da hukunci akan ta cikin wata irin murya ta dube shi sosai.
"Da ka daina bata lokacin ka wallahi kuma kadaina sanya baba na ya baka hakuri akaina ka zartar da abin da kayi niyya kawai kai ka sani ko sau daya ko da na dakika da ban taba jin wani abu game da kai ba kuma bana fata naji haka din".
Wata irin razana yayi jin muryar Bahijja a bayansa domin tun da ta fito sam bai lura sa ita ba mamaki yake yi yaushe ta shigo gidan ko dai dama tare da Adam din suke amma bisa alamun yanayin maganar ta ya tabbtar masa ba tare su ke to yaushe ta shigo gidan.
"wai ba ka ji abin da nace bane Adam?".
Bahijja ta fadi cikin daga murya sosai sake dubanta mahaifin ta yayi gani yake yi kamar ba Bahijjarsa ba 'yarsa daya tilo gabadaya ya ga ta sauya masa kamar ba ita ba komai ya canza tabbas Bahijjar ce wani irin zabura yayi ya dauke da mari ya sake dauke da wani sai da yayi mata guda hudu a jere hantsilawa tayi ta baya ta fadi kasa warwas har ta buge kai jikin bango bin ta yayi ya damko sosai  yana mai dubanta idanuwansa na zubda hawaye zuciyarsa da kasar ruhin sa sai raɗaɗi da zafi suke kamar za su tarwatse murya mai cike da daci la66ansa sai rawa suke yi
"Bahijja kece haka Bahijja kece ki ka zama haka Bahijja mai ya same ki mai ya sami rayuwarki mai ya sa kika cuci kan ki da ni kai na mahaifinki dama abin da kika shirya yi min kenan a matsayin ladan kula da rayuwarki da nayi mai nayi miki Bahijja laifin mai nayi miki a matsayina na mahaifin da zaki dauko min wannan bakin lamarin".
Muryarsa ta sarke idanuwansa suka shiga kadawa numfashin sa na kai kawo kamar zai fice daga jikin sa Adam ne yayi hanzarin zuwa gareshi ya shiga kuciyar kwatar Bahijja wacce ita ma ta fara ficewa daga hayyacin domin shakar da Mahaifin ta yayi mata ba karamar shaƙa bane da kyar ya amshe ta ta zube a kasa shi kuma ya fara tangadin faduwa da sauri Adam ya rike shi tare da kai shi kan tabarma ya zaunar dashi ba abin da idanuwansa ke yi, sai zubar hawaye zuciyarsa tayi zafi ran shi ya baci yana jin yar kirjinsa ke bugawa.
"me yake shirin faruwa dani ne yata ta ciki na ta zama haka ina tabiyya da kulwa da rayuwarta da na bata ina ta ajje su ina ta cillar da su ta dauki wata rayuwar daban ta daura wa kan"?.
"TARBIYYA DABAN SHIRIYA DABAN".
Abin da Adam ya fadi kenan ya na duban sa bayan ya dire kalamansa cikin yanayi na rashin hayyaci girgiza kai ya shiga yi.
"kaicon wannan rayuwa, kaicon wannan zamani, kaicon DUNIYRAMU a yau kaicon Al'umman wannan zamani ni nasani ba abin da zai ruɗi Bahijja illa zamani da kayan cin sa tabbas batayi mani adalci ba a rayuwa ba tayi wa kanta Adalci ba TA CUCE NI kuma ta cuci kan ta da rayuwarta tun har ta fifita wanu abu daban akan gidan auran gidan da zai neman mata aljanna gidan da zai kawo mata daraja da kima gidan da zai kawo mata mutunci a idanun kowa na duniya amma ta hanbare ta fice ta tafi cikin duniya kaicon wannan rayuwa".
ya karashe ya shafe hawaye cikun rawar jiki ya kalli in da take yashe ba abin da take yi sai zuba hawaye wani kallon takaici ne ya ke jifanta dashi.
"da na san haka za kiyi da ban auran dake ga Adam ba, da nasan abin kunyar da zaki dauko min kenan wallahi ba zan fara hakan ba, na dauka ni Uba ne mai hakki akan zaba miki Mijin Aure hashe ba haka bane ban kai wannan matsayin ba, bani da wannan martabar ko darajar, kin nuna min ban isa dake ba kin nuna min ba ka matsayin da zan zaba miki miji ba".
Magana yake yi cikin yanayi na kunar rai da zafin zuciya ji yake yi kamar ya hadiyi zuciya ya mutu da wannan BAKAR RANA da bai taba zaton za ta kawo rayuwarsa farmaki ba bai taba zaton Bahijja zata aikata haka a gareshi ya dauka tarbiyyar da ya bata da kulawa ta isa ta inganta rayuwarta ashe ba haka bane tarbiyya daban shiriya daban shikam Allah na gani ba zai iya kasance da bahijja cikin rayuwarsa ba domin in har ya kasance da ita to tabbas zuciyarsa bugawa zata yi ya mutu a banza a wofi ba damuwarta bane.
"wallahi in har ki ka kashe auran nan naki ba dai ki zauna cikin gidan nan ba sai dai ki nemi wani uban bani ba".
zabura Adam yayi jin abin da ya fadi ya shiga duban sa ya na mai girgiza kai.
"bai kamata kace haka ba baba sam wannan ba shi bane abin da ya dace kayi in zuciya ta bace bai kamata ace hankali ya goshe ba yarka ce kai ne sanadin kawo ta duniyar nan ko min abin da zai faru da ita ba zata taba zanjawa a matsayin 'yarka ba ni dai ina baka hakuri Allah na gani na so Bahijja so mai tsanani na so zama da ita na rayu da ita har karshen rayuwa ta amma sam hakan ba zai yuwu ba domin ni ne nake shiga hakkinta domin tun farko ba ita ta ce ta gani tana so ba ni ne na ce  NA GANI INA SO ban bi yo ta hannunta ba sai na biyu ta hannunka a matsayinka na uba lokaci daya ka amince ba tare da yarjewarta ba ka ga kenan dole matsala ta afku ni so ya rufe mani ido na dauka in har ta kasance a gidana matsayin matata komai zai daidaita ashe ba haka bane Bahijja ba ta so na ko kadan ta fadi min ta sake fada min karo ba adadi amma  ni ban nuna wani abu akan haka ba saboda son da nake yi mata...".
Nisawa yayi cikin tafasar zuciya wani irin yanayi yake jin kansa aciki game da Bahijja sai dai ba yarda ya iya ya zama dole ya rabu da ita ko da kuwa hakan na nufin yankewar numfashin sa ne domin zama da ita ba abin da zai haifa masa sai ta shin hankali zai hakura da ita har abada zai yi kokarin cire son da yake yi mata daga zuciyarsa zai amshi ƙaddara da yarda ta zo masa zai mikawa Allah lamarin sa shi kadaine zai masa magani. Juya wa yayi ya dubeta har yanzu ta na nan zaune sai faman rabsar kuka take yi kamar ranta zai bar gangar jikinta tausayinta ya tsargar masa sosai cikin zuciya da kasar ruhi yana jin yarda sautin kukan ke amsa amo cikin kunnuwansa kukanta yana matukar haifar masa da wani irin yanayi na rashin dadi a baya ya furta zai rayu da ita sai dai hakan ba zai yuwu ba dole ya rabu da ita domin kwanciyar hankalu yake bukata cikin duniyarsa ya sani Bahijja ba ta son shi amma bai san meye dalili ba ya sani ba abin da ba shi dashi na jindadi rayuwa amma ita wannan duk bai tsole mata idanu ba sai yau ya kara tabbatar wa kudi ko mulki ba sa taba siyan soyayya a mai cike da dadi da armashi numfashi yaja wanda yake ji kamar zai dauke gabadaya ya dubi Abban Bahijja.
"Abban kayi hakuri zan aikata abinda baka so sai dai ba wai zan yi bane don na kuntata maka a,a zan yi domin hakan ne kawai hanyar da ta fi daceqa ta kawo mafita kayi hakuri na sauwakewa Bahijja in ta samu wani mijin tayi aure domin ban daura mata IDDA ba".
Yana gama fadin haka ya mike cikin hanzari ya fice daga cikin gidan zuciyar sa na kuna d raɗaɗi duniyar yaji tana juya masa kamar zata jirki ce dashi bai so furta kalmar saki ga Bahijja ba sai dai ba yarda zai yi dole ya taushi zuciyarsa ya rarrasheta.
Mutuwar zaune Baban Bahijja yayi jin furucin Adam wata katanga tashin hankali yaji ta ruguzo masa akai tana barazanar dauke masa numfashi sai da ya shafe dakiku kafin ya dawo hayyacin sa idaniwnsa na zubada hawaye zuciyarsa na raɗaɗi da zafi ya shiga duban Bahijja da har lokacin ba ta ba zubar hawaye ba, ba karamin razana da firgita tayi ba ita ma jin abin da Adam yace akan ta zuciyarta ta shiga zillo da wani irin yanayi wanda yake nuni da ita kanta ba ta ji dadin hakan ba ko da dai ba ta son shi amma kalmar sakin jin ta tayi kamar an buga mata gudama a tsakiyar kai ji tayi duniyar ta shiga juya mata wasu lamura masu firgita tunani sai ziyartarta sukeyi ji take kamae ba ta kyautawa Adam ba ji take kamar ta dauki Hakkinsa ji take kamar bai dace da tukuici haka ba amma ba yarda zatayi zuciyarta ba za ta taba amincewa dashi a matsayin mijin aure kwanciyar hankali ba zai taba wanzuwa ba in har suna tare dashi rabuwar shi ne mafita sai dai ha kasar ruhin ta ba ta ji dadi ba.
Hannu ta sanya ta dauke hawayen da suk zubo mata  ta dubi in da mahaifinta yake zaune jiki a sanyaye ta rarrafa ta isa gareshi jiki na rawa ta fara kokarin yin magana da sauri ya dakatar da ita cikin kunari rai.
"bana bukatar jin komai daga gareki kin yi yarda kike so kin nuna min ke kike iko da kan ki don haka ni ba wani bane gareki bani da daraja ko kima a wajanki don haka ki san in da dare yayi miki in kuma ba zaki tafi ba ni zan bar miki gidan domin ba zan iya zama dake ba hakan zai iya haifar bin da bugun zuciya a dalilin bakin cikin da kika kirkira min a rayuwa".
Bugun zuciyarta ya karu tashin hankalinta ya linka wanda take ciki jikinta ya shiga rawa da kyarma kamar wacce aka zaro daga cikin kankara ta shiga girgiza kai da rawar baki.
"Abba ka ji kaina ka tausaya min halin rayuwar da tan shiga ka tunani Abba ni mai biyayya ce gareka ban taba saba maka ba ban taba gudun maganar ka ba...".
"bana bukatar jin wata kalma daga bakin ki kawai ki rufe min baki in ba haka ba wallahi zan iya bige ki a banza don ban ga amfanin rayuwarki cikin duniyata ba ashe akwai abin da Allah ya gani shiyasa ya dauke Mahaifiya ki domin nasan tabbs ba za ta iya daukar wannan tashin hankalin ba cikin duniyarta na godewa Allah da bata raye".
ya fadi yana mai dauke hawayen da suka zubo mata nan da nan mutuwar Ummu-Bahijja ta dawo masa sabuwa kamar yarda ta dawo wa Bahijja sabuwa nan da nan sabon kuka ya balle mata ta fara tunano abin da suka afku da ita da silar ajalin mahaifiyarta kuka takeyi kamar ran ta zai fita Adam take tunawa bakin mugu macici wanda duk shine sanadin faruwar komai cikin duniyar rayuwarta da ta iyayenta tsine masa take ta na karawa Adam ya cuce ta ya cuci rayuwarta ya saka mata mikin da ba zai taba barin zuciyarta ba har karshen numfashinta a dalilinsa ta rasa uwa a dalilinsa ubanta na fushi da ita a dalilinsa mijin da aka aura mata  ya sake ta gaban mahaifinta wannan wani irin bala'i haka Adam ya sayo mata UKU BALA'I ya saka ma rayuwarta duk sun rikirkita mata tunani sun kashe mata duk wani farinciki da kwanciyar hankali sai yau ta kara tabbatar da a rayuwarta ba ta da abin yabo duk A DALILIN ƊA NAMIJI ɗa namiji yayi mata illar da ba za ta taba goguwa a duniyar rayuwarta taba har numfashin ya dauke nisawa tayi cikin zubar hawaye ta dubi mahaifin nata.
"Abba na boye maka abubuwa da dama da suka kamata ace ka sani wanda ta dalilin su ne duk na fada cikin ko wani hali na rashin dadi a duniyata ba ni kadai ba har ta kai da mahaifiyata".
ta yi shiru ta na dauke hawaye shi kuwa dubanta yake cikin rashin ba zancen nata muhimmanci don yanaji a zuciyarsa ba komai baɓe zata fada wanda zai yarda dashi.
"Fyaɗen da akayi min tun ina karamar shiɓe silar ruguzewa rayuwata wanda ya kasance ban fadi maka wanda ya aikata min haka ba a lokacin na yi alkawarin kin gaya maka domin ni da kai na nake so na dauki fansa".
ta sake yin shiru izuwa wannan lokaci ya fara nitsuwa da kalamnta abubuw suka shiga tariyo kan su kamar yanzu suke gudana muskutawa yayi cikin kaduwar zuciya ba tare da yace da ita komai ba.
"Adam dan gidan Alhaji Kabeer Tanga shi ne ya zama silar komai...".
nan ta shiga bawa mahaifin nata labarin komai da ta boye masa tun da ga farko har izuwa auranta da Adam da kiyayyar da ta nun amasa na rashin so a matsayin na mai sunan wanda ya illata mata rayuwa.
Tun da ta fara bashi labarin ya shiga girgiza kai yana mai jin wani iri tun daga kasar ruhinsa har zuciyarsa numfarfashi ya shiga yi kamar wanda ake kokarin zarewa rai yana duban Bahijja cikin wani irin yanayi na Al'ajibi da kuma haushin yarda ta boye masa abubuwa masu muhimmancin da ya kamata ace shi ne da kan sa ya dauki mataki na kara hakki a matsayin sa na ubanta sai dai ta barar da damar ta tun farko ta bata komai ta lalata komai ba shi da abin cewa illa Allah ya bi msa hakkinsa domin ancuce an nakasta musu rayuwa ba kadan ba amma kuma anyi amfani da son zuciya da ruɗin shaidan sosai cikin lamarin wanda ita da kan ta Bahijjar ta janyowa kan ta
"BAHIJJA!".
ya kira sunanta cikin sauti da sauri ta dube shi kafin tayi kasa da kai don ta tabbata kallo da yake yi mata na tuhuma ne.
"sam ba ki kyautawa kan ki da rayuwarki ba har ni baki kyauta min ba naji takaici nay bakin ciki matuka da abin da ya faru na so ace tun waccan lokaci kin fadi mani gaskiya amma kika ki akan wani kudiri naki wanda kikayi amfani da shi ya bata miki rayuwa ya illata miki duniyarki kin yi amfani da son zuciya da zance zuci wajan aikata komai kin guji iyayenki wanda ya kamata ace duk wata matsala taki sun sani kin boye su wani SIRRI da ya kamata ace sune mutanan farko da za su sani Bahijja mai yasa haka mai ya sakika aikata haka ban ji dadi ba ban so haka ba ni ji takaici da ɗaci a raina har kasar ruhina Allah nagani".
Ya karashe yana mai girgiza kai  fuskarsa ta nuna tsananin ɗaci da yake ji a ransa da takaicin lamarin ita kuwa Bahijja kuka take yi sosai ta iso gareshi tana dafa kafafuwansa tana mai rokon sa afuwa da neman yafiya akan abin da ta aikata na ba daidai ba wanda ba taba zaton haka kin gayawa iyaye illa bane sai yau sai yau ta tabbata in da ta nemi shawarar iyaye hakan ba za ta faru ba yau ta tabbata iyaye babban jigo a rayuwar 'ya'ya yau ta tabbata gudun iyaye ba karamar illa bace rayuwa ba zaka taba samun abin da kake so ba in har ka guji  iyaye.
"kin ga amfani rashin bin maganar iyaye ko in da kin sanar da iyaye duk haka ba zata faru ba amma Allah na nan yana ji kuma ya na gani zai man sakayya akan hakkin zarafin da aka ci mana da izinin Allah za su gani a kwanonsu in dai cin mutunci da keta haddi abin yi ne  DUNIYARMU a yau ba abin da ya fi karbuwa a cikin ta illa son zuciya da shiga hakki son kai da cin amana shi ya zama ruwan dare cikin DUNIYARMU amma ba komai Allah na nan ke kuma sai  ki san abin yi cikin duniyarki biyewa son zuciya duk ba ya kai mutum ga abin kirki illa halaka".
Su jima zaune cikin yanayi na matsanancin damuwa Bahijja hawaye sai zuba suke yi cikin idnauwanta lamarin gani take kamar ba gaske ba kamar ba ita ba ce komai ke faruwa akan ta...

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now