DUNIYRMU-26

415 22 1
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA.

BABI NA ASHIRIN DA SHIDA.

Duk hannayenta biyuta zabga tagui da su, ba abin da ke ɗawainiya da ita sai kalaman Mansoor da yake furta mata kafin su rabu da juna.
Tayi matukar shiga halin damuwa da rashin madafa akan lamarin.
Ta rasa in da ya dace ta dosa kwanyarta sai faman tariyo mata kalaman Mansoor take kamar yanzu sukayi su a tsakanin su.
  "ki yarda da ƙaddara Bahijja hakan ne zai kara imani da kusanci da ubangijinki ba a son bawa ya kasance mai mayar da sharri akan sharri".
da sauri ta juyo ta dube shi sa'annan cikin sanyin murya ta fara magana.
  "kana nufin kenan na rabu da Adam akan cin zarafi da KETA HADDI da yayi min a rayuwa kana nufin in yafe masa kenan ya ci bulus"
Girgiza kai ya shiga yi cikin yanayi na son ta fahimce shi, amma da alamun zuciyarta ta rigaya ta kullaci Adam in ba fassar ta dauka ba ba za ta ji saukin raɗaɗin zuci ba, sai dai kuma in har ya bar ta ko kuma ya koya mata baya ta aiƙata son ranta to tabbas za tayi NADAMA a rayuwa ya kasance bata ga wan balle kanin tayi biyu babu ko kuma ta gamu da Uku Bala'i cikin duniyar rayuwarta wanda ba ya fada hakan ya kasance.
nisawa yayi cikin kwantar da murya da sigar rarrashi.
"Bahijja duk wani dangin rai da kika gani cikin duniyar nan to tun kafin Allah ya wanzar dashi ya rubuce duk wani abu da zai faru dashi da kuma har yarda da abun zai faru dashi kamar ke yanzu dama can tun Fil'azal a kudin kaddararki hakan a rubuce yake ta sanadin Adam zaki fada halin kunci da damuwa a rayuwa"
Yayi shiru kamar mai son jin abin da zata ce ya nisa gami da dorawa.
"nasan dole kiji ba dadi amma HAKURI DA ƘADDARA shi yafi cancanta a gareki ki yafe masa..."
Tun da ya fara magana ba taji yayi furucin da ya tunzura zuciyarta kamar kalmar 'ta yafe masa ba'.
duban Mansoor ta shiga yi cikin wani irin yanayi na ban karbi maganar taka ba da muhimmancin cikin tsananin takaici ta dubeshi
"in kana yiwa Allah Mansoor ka kyaleni da wannan batun don ba abin da yake kara mani sai takaici da kunar rai na rokeka kayi shiru zai fi zama Alheri maganar wata kalma wai ita yafewa duk ba ta da muhalli a cikin duniyar rayuwa in dai akan bakin azzalumi mamuguncin can ne Adam wallahi ba zan yi masa afuwa ba ko sssauci ko da kuwa hakan na nufin daukewar numfashi na ne".
zuciyarsa ta yi matukar rauni akan tausayin Bahijja ya san dole taji ba dadi domin keta haddi ga 'ya mace ba  karamar illa bace domin kuwa hakan na kashe musu rayuwa ya jefa su cikin wani hali a tsangwame su gami da kyara da aibatawa da mugun alkaba'i duk mace na shiga wannan sahun ne in har rayuwarta ta fada gagari na halin keta haddi.
  "Bahijja ki tuna kina da aure a kan ki, baki san abin da kike aitakawa kuskure bane babba, hakan zai iya jawo miki matsala da fushin Allah cikin rayuwarki domin kina aikatawa abubuwa ba tare da izinin mijinki ba..."
hannu ta daga masa hakan ya sanya shi sauri yin shiru don ya lura ta kai makura.
"ban dauki wannan a Aure ba domin bani nace ina so ba kuma ba da amincewata akayi shi ba nifa a rayuwa in akwai wanda na tsana to d'a namiji ne domin maza ba su da hali da yawansu macuta ne".
Gyada kai yayi cikin aminta da batun ta.
"duk da hakan Bahijja Aure ba abin wasa bane a addinance domin aure abune mai muhimmanci da daraja da kima ga duk kan wani jinsi na Dan'adam ya kamata ki san wannan na rokeki da ki rike darajar auranki kisan ke matar aure ce kamar yarda kike fada".
Shiru tayi tana nazarin kalamansa suna yi mata shawagi cikin kwakwalwa da zuciya ta san gaskiya ya fadi amma kuma sam ita ba ta iya amfani da wannan maganganun nasa domin in har tayi abin da ce to tabbas ta cuci kan ta da kan ta.
"Bahijja ke nake sauraro ki ce wani abu".
Mansoor ya fadi yana mai dubanta
shiru tayi da alamu bata da niyyar cewa komai gareshi bata da wata kalma da zataiya furtawa gareshi duk wani azancin ta da kumajinta ya yi sanyi sai dai har yanzu zuciyarya na nan ba ta canza ba akan daukar fansa.
duban sa tayi cikin yanayi na sanyin jiki.
"ina son zan tafi domin samu natsuwa tunani ya cushe gabadaya"
bai ce da ita komai ba illa gyada kai da yayi ya fara kokarin ficewa daga cikin motar.
Ajiyar numafashi tayi jin abubuwan da suka faru tsakaninta da Mansoor sai yawo suke yi mata a kwakwalwa sam ta kasa sukuni akan lamarin ta rasa mai ya dace tayi duk maganganun Mansoor sun gama karya mata kwarinta.
Wayarta ta jawo tashi bincike cikin majiyar lambobi lamar Ayshaty ta lalubo ta shiga nema amma ina abun daya ne dai wayar a kashe take hakan ya kara sanyata cikin rudani tun da ta zo take cigiyar Ayshantƴ amma ba ta samunta ta rasa dalili abun da ba ta taji ba kenan ta kira Ayshanty a waya ba ta same ta ba.
Tsaki ta ja gami da yin cilli da wayar can gefeta sake girka wani abun tagumin ta fada kogin tunani
----------------------
Ayshanty ne zaune gaban teburun ofishin yan sanda gabadaya ta gama lalacewa tayi baki ga wata uban rama da ta zabga kamar wacce ta shekara tana amai da gudawa can gefe kuma Khaleed ne zaune ya zabga uban tagumi yana kare mata kallo kamar wanda ya ci karo da Bakuwar fuska  daga bakin kofa kuma wani dan tsukanken kurtu ne yake tsaye kamar bishiyar da ta dauko hanyar mutuwa sai faman mazurai yake yi da alamun jira kawai yake yi lokacin da ya debar musu ya cika ya daura aikin sa.
Khaleed ne ya numfasa idanuwansa sun yi jajir kamar wanda ya fito daga dakin hayaki ya nisa cikin kunar rai da tarin bakin ciki da takaici.
"Ban taba zato ko tsammanin haka daga gareki ba Aysha na dauke ki mace mai mutunci da kima da daraja amma ashe ba haka bane ban san abin da ya shiga zuciya ya lullube min ganina ba har da na kasa gane aibun dake tattare dake haba Aysha meye amfanin irin wannan rayuwar da kika daukarwa kan ki ina amfaninta illa kawai kashe kai da barin abin fada cikin zuria"
ya tsagaita jin da yayi kirjinsa na wani irin bugu kamar zuciyarsa zata faso kirji ta fito waje.
"kamar ki har za ki iya daukar ran mutum kamar ki da auran ki a matsayin ki na 'yar musulmai amma ace kike yawo zuwa club da hotel hotel mai yakai wannan asara a rayuwa ai da in yi irin wannan rayuwar taki na gwammace in roki Allah ya dauki rai na hakan zai fiye min Alheri..."
Dan tsukaƙƙen kurtu ne yayi gyarar murya da alamun lokaci yana gaf da karewa ya dube su fuska a turbude " yallabai lokaci fa ya iso"
Gyada kai khaleed yayi cikin yanayi na kunar rai zuciyar sa na zafi da radadi wani irin yanayi yake jin sa aciki wanda bai taba tsammanin ta dalilin Aysha zai shige shi ba ya  nisa gami da sukoyar da kai kasa kamar mai son tunano wani abu daban ya dago da rinanun idaniwansa ya sauke su kan Aysah wacce a wannan lokaci ba abin da gabanta keyi sai dukan uku-uku don ta gama haƙiƙan cewa rayuwar ta ta gama lalacewa cikin duniyar nan bata da kowa iyaenta sun yi fushi da ita duk dangi an kaurace mata akan abin da ta aikata wanda izuwa yanzu take da na sani da cizon yatsa mijin ta shi kadai ya rage mata wanda ta tabbata shi ma din nan da yan dakiku zai gille duk wata alaka dake tsakaninsu wanda hakan ke tabbatar mata da cewa ita rayuwarta ta karewa ba ta ga amfanin rayuwa irin wannan ba na son zuciya da kazamin buri tayi da nasani biyewa zuciya da kawayen zamani tayi da nasani bin rudin da zamani ya zo mata dashi ya illata mata rayuwa ba ta da wata daraja ko kima a wajan kowa yanzu rayuwarta ta zo karshe don ta tabbata ba ta da wani lokaci a yanzu domin tasan hukuncin ta da za a yanke mata kisa ne kawai ba ta tunani zata fice daga wannan gidan har abada sai dai gawarta...
Maganar Khaleed ne ta dawo da ita dag duniyar rudanin tunanin da ta fada da sauriɓta dube shi ba abin da ta gani cikin idanuwans sai hawaye da zallar kauna da so da yake mata wanda ita kan ta ta san haka tun ba yanzu khaleed na son ta amma ina rudin zamani ya ja ta ta fada cikin JARRABAR DUNIYA mai cike da kayan tashin hankali da bakin ciki da takaici tayi da nasanin wannan rayuwa da tayi wani kuka ne matsananci ya kufce mata ta shiga rusashi kamar ranta zai fice daga jikin ta hakan ba karamin kara sanyaya jikin Khaleed yayi ba amma duk da haka bai bari jarumtarsa ta guje shi ba mikewa yayi yana mai duban duban da ya tabbata daga shi  ba ya tsammani zai sake ganinta wanda yake ganin shine kallo na karshe a tsakaninsu dan duk son da yake yi mata ba zai taba iya zama da ita ba ba zai iya ba Allah ya gani kuma yasan duk wanda yayi kisa ba shi da wani hukunci illa a kashe shi balle iata da ta kashe rai ba guda daya ba.
  "Ayshaaa".
ya fadi cikin wata murya wacce ta sanya ta kara razana da sauri tayi kasa da kodaddun idanuwanta gaban ta na tsanar ta bugu jiya kawai take taji hukuncin da zai yanke akan ta.
"kiyi hakuri da abin da zan fada miki kisan ina son ki tun da nake a rayuwa ban taba son wata ya mace sama dake ba na nuna miki so da kulawa da kauna cikin duniyarki na fifita ki akan ko wacce ya mace cikin duniyar nan amma ina Aysha kin yi wasa da damarki kin kashe mana rayuwa don zan ce kin kashe rayuwarki ke kadai ba har da tamu kika kashe"
shiru yayi gami da jan numfashi na tan dakiku zuciyarsa sai faman safa da marwa take yi can ya nisa
"Aysha na sauke miki hakkin aurena da ya rataya akan ki kuma na yafe miki duk wasu laifuka da kika yi min har zuciya ta Allah ya sada mu da Alheri".
ya na fadin haka da sauri yayi hanyar fita cikin yanai na takaicin rayuwa idanuwansa sai zubar hawaye suke yi kamar an bude famfo.
Ita ko Aysha durkushewa tayi cikin yanayi na tashin hankali ta daura hannu akai kuka take son yi amma ina kukan yaki zuwa wani abu ne taji ya toƙare mata makoshi ya hana sautin kukan nata fitowa waje.
shi kan sa kurtun yayi matukar jin tausayin ta a ran sa sai da kuma in ya tuna ta'asar da ta aikata sai yaji a ransa bai kamata aji tausayinta ba domin duk mutumin da zai iya kashe rai na dan'uwansa aiko ya cika maras imani da tausayi a cikin zuciyarsa a matsayinta na 'ya mace mai rauni da tausai ace tana aikata irin wannan ta'addancin aiko abu ba karami bane tabbas ana cikin wani yanayi na sauyin zamani mai cike da abubuwa na tashin hankali da AL'AJABI.
"DUNIYARMU"
abin da ya fadi kenan cikin sigae yanayi na jin dadin duniyar rayuwa dangin rai a yau da ta lalace da abubuwa na kashe kai da sace-sace cin amana da hassada yaudara duk sune suka zama RUWAN DARE a duniyarnan bat kananan yara ba ga mata balle maza ba wanda aka bari matan aure masu cin amanar aure mazaje masu cutar matansu 'ya'ya masu kashe iyayen su akan wani dalili da ba shi da wani amfani duniyar gabadaya ta lalace domin kuwa Al'ummar cikin ta su suka lalata suka tarwatsa duk wani kwanciyar hankali ta hanyar dauko kayan son zuciya da sabon Allah suka zama abin ado a garesu ya za ayi kuwa ace za a zauna lafiya duk wasu masifa da bala'o'i da suke faruwa cikin duniyar nan Al'umman ciki duk su ne sila da sanadi.
gyada kai yayi cikin rashin kuzarin jiki a can kasar makoshin sa ya furta. "Allah ka iya mana cikin Duniyarmu ta yau".
duban Ayshanty yayi dake tafaman rafsar kuka kamar ranta zai fita sai dai sam ba alamun hawaye a idanun nata gabadaya ta gama fita da ga hayyacin ta nadama ce ke ta shigarta ta ko ina najikinta da mugudanar jininta zuciyarta na suwa ba abin da take sai zafi da radadi takaicin rayuwar da tayi da bakin ciki suke ta nukurkusar ta ba abinda take bukata a wannan lokacin sai mutuwa 'ina ma ace zata mutu ina ma ace numfashin ta zai dauke a cikin yan dakiku da tafi kowa bukatar haka ta bar duniyar nan mai cike da kayan kƙawa da rudanin zuciyar da take dauke da KAZAMIN BURI mara amfani ina ma ce ba ta zo duniƴar nan ba da duk wannan bala'o'in ba za au faru da ita ba cikin rayuwarta kaicon ta kaicon  wasiyyar zuciya mai cike da son duniya kaicon zuciya irinta ta",
haka ta cigaba da sambatu ita kai a can kasar ruhin ta idanuwanta sai faman radadi suke kamar za su zubo kasa don zafi.
Cikin wannan yanayin kurtun nan ya iso gareta yana mai bata umarni da ta tashi ta koma ba musu ta mike sai faman tangadi take kamar wacce ta kwankwadi baras ta kai ma.
Yana bin ta da kallo harta shiga (Cell) din wanda ta tabbatarwa ran ta wat sabuwar duniya ce gareta da ƙaddara gami da son zuciya suka bude mata wanda take da yakinin rayuwar da za tayi acikina har abada ne ko tantama ba tayi ta san dai hukuncin duk wanda ya kashe to a kashe shi balle ita ba rai daya tayi sanadi barin su duniya ba sai yanzu take ganin kuskuren da ta tafka a cikin rayuwa wanda bata tsammanin zai taba gyaru cikin duniyarta ta sadakar da rayuwar ta zo gabar karshe.
Kowa ya gujeta iyayenta, danginta, mijinta, gami da Al'ummar gari wanda ta tabbatar in dai sukaji abin da ta aikata tsinuwa ce da la'anta kawai za suyi ta bin ta da su ba ta tsammanin akwai mutum guda wanda zai yi mata fatan rahama.
tana ji ta na gani, aka kargama jibgegen kwado ajikin kofar (Cell) dinda take idanuwanta sun ga kekeshewa HAWAYEN ZUCIYA ne kawai ke aikin su.
Juyawa tayi ta kalli sauran matan da suke zaune cikin dakin kusan sun haura goma ko wacce kuma da laifinta da ta aikata na rashin tunani da imani yawancin su duk kisa ne ya sany su zaman wannan bakin dakin wasu kuwa tsautsayi ne kamar yan da wasu su bata labari sharri ne akayi musu wasu kuwa zuciya ta kwashe su ta dulmiyar dasu a kogin dan sani wasu mazajansu suka kashe wasu kishiyoyi wasu 'ya'yan roko wasu kuwa abokanan huldar su suka zama sanadi ga rayukan su.
Kamar daga sama taji an furta.
"DUNIYA TAFI BAGARUWA IYA JIMA".
juya tayi, tana kallon daga in da maganar ta fito.
daya daga cikin abokan nan zaman tane ta furta hakan idanuwanta na zubda hawaye.
Cikin shasshekar kuka ta ji ta fara magana.
"kalmar nan taji ma tana amsa min kuwa a kunne an gaya min ita yafi a kirga amma ina sam ban lura da abin da ake guje min ba nukuma ina kara likewa sanadin Ɗa NAMIJI na shigo wajan nan ta dalilin sa rayuwata ta gurba ce ta sanadin irin mahaukacin son da nake masa yayi amfani dashi ya jefa ni ga halaka ni ban sani ba so ya rufe min ido gabadaya na daina jin maganar kowa na daina sauraron kowa na dai jin zantukan kowa, kawai abin da wanda nake so ya fadi dashi zan yi amfani munyi aure dashi cikin so da kauna da kulawa yana yi min duk abin da nake so cikin amarci ba ashe ban sani akwai wani salo da yake kokarin billo min dashi wanda ban sani ba na yaudara wanda nayi masa lakabi da SABON SALON ƊA NAMIJI cikin duniyata likita ne shi amma na bogi mai safarar jariryar yana saidawa ma bukata masu MATACCIYAR ZUCIYA marasa imani masu sabon Allah domin wani bukata tasu ta daban, na samu ciki ya kai sau biyar amma kuma sabida mutuwar zuciya da rashin tunani da salon da mijina yayi amfani dashi na kalaman yaudara ya kasance in na haihu sai ya dauki ɗan dana haifa ya biya bukatar sa da shi tun ina jin tsoro har na daina har ya kasance da kaina nake tunata dashi komai domin kuwa bana son bacin ran shi da na samu ciki zan sanar dashi kamar masu sai da kayan sakawa haka zai sanar da mutane wanda ke so sai yayi kamu har na haife ya biya a bashi abin sa saboda rashin imani da tausayi da mutuwar zuciya haka muka kasance da miji yan uwa tun ba sa damuwa har suka fara damuwa domin kuwa abin ya shanlake tunanin su da na haihu zan sanar da su ɗan ya mutu tun su yarda har suka fara zargin akwai wani abu a kasa da yake Allah ba azulumin bawansa bane  muna cikin wannan ganiyar aka kama mijina dumu-dumu da safarar 'ya'ya jaririyar lokacin da lamarin ya faru ba karamar shiga tashin hankali nayi ba miji aka kulle tare da gana masa azaba kala-kala domin ana so ya tona asirin duk wadanda suke harkar tare farkon wanda ya fara ambata ni ce domin sai da ya sanar da su komai daga nan ya dinga ambato mutane manya-manya wanda ni kai na da ji sunansu ba karamin tashin hankali na shiga na din ga mamaki da tu'jibi akan lamarin tashin hankali gabadaya na rasa shi domin mutane ne manya masu dafun iko a kasar mu har da su ake wannan banzar harkallar ta kazamin buri..."
kuka ne ya ci karfin ta ta kasa ci gaba da labarin da take ba su duk matan da suke ciki kowacce ta zabga tagumi tana jin wannan irin rashin imanin ko da yake ko wannansu a nan akwai kalar rashin imanin da ya shuka sai da tayi kuka ma ishinta sannan ta dora da cewa.
  "...iyayena da sukaji labarin ba karamin tashin hankali suka shiga ba don a take a wajan mahaifina ya fadi zuciyar sa ta buga mahaifiyat kuwa sai da ta kwana biyar ba tare da numfashi a tare da ita ba sannan ta farka gami da samun matsalar cutar barin jiki na shiga tashin hankali matuka gaya yan uwana da kan su suka ba da damar a kayan ke mun hukunci koma kotu ba ta yanke mun hukuncin kisa ba to in har nafito sai sun kashe ni da hannunsu mutanan gari kuwa tofin Allah ya tsine sun yi min shi yafi a lissafa in da tsinuwa da fitowa a jikin mutum da tuni na kasa ganuwa nayi da na sani nayi nadama mara amfani a lokacin da komai ya kwance min mutane da yawa sun jima suna furta min kalmar duniya tafi bagaruwa iya jima in dai duniya ce gani ga ita.
Kuma hakan ce ta kasance yanzu so bai yi min rana ba bai amfane da komai illa shiga halaka da tashin hankali mai dauke da ajalin rayuwata".
ta ida labarin tana mai dauke hawayen da suke ta faman zuba a fuskarta.
daya daga cikin su ne ta muskuta cikin sanyin jiki ta ce "yanzu ina mijin naki?"
Murmushi tayi mai dauke takaici da tarin kunar zuci sannan tace
"ai shi bai tsira ba domin a ranar da aka shiga kotu da shi domin yin shari'a ba a kai ga farawa ka ga zugar mutane sun shiga sun yi kan shi ba zato ba tsammani suka cilla masa taya a kan sa tare da kwara msa fetir gami da kesta Ashana cikin lokaci kankani ya kama ci da wuta nan kotu ta rikice da ihu da neman a gaji amma ina kafin a an kara ha wutar ta kusan cinyeshi numfashin sa da ruhin sa sun bar gangar jikinsa"
Tana kaiwa nan ta sake sanya hannun ta na dauke hawayenta cikin yanayi na nadamar rayuwar da tayi.
Ba wanda ya sake tsinkawa dakin ya dau shiru zuciyoyi ne kawai da kwakwalwa ke aikin su cikin yanayi na tashin hankali kowa sai juya lamarin sa yake domin ba su da damar daukar nawa ni su daura kan su na su ma ya ishe su.
Ayshanty dake zaune can gefe ta hade hannaye duk biyu ta rafka tagumi tanajin irin ta'asar da ake aikatawa cikin duniyarnan duk sai taji jikinta ya kara yin la'asar komai ya kwance mat gabadaya komai na duniyar taji ta tsane shi muradin ta kawai ta bar cikin duniyar nan domin tashin hankalin dake cikin ta yafi karfin tunanin duk mai tunani wanda ya kasance kuma al'ummar cikinta su suke haifar da kowani tashin hankali da bala'o'i rayuwar da tayi abaya ce kawai ke ta yi mata gizo tana ganin irin rashin imani da rashin zuciya da kazamin buri suka yi mata illa illar da ba zata taba magance ba har duniya ta naɗe gabadayan ta ina ma ace ana tariyo rayuwar baya ina ma ace ana tariyo mugayan aiyuka a magance su da kayan alheri ina ma duniyar zata sake sabunta kanta da ta sauya abubuwa da yawa cikin ta da kayan Alheri amma ina abin da ya faru ya rigaya ya faru ba zai taba maimaita kan sa ba wasu guntayen hawaye ne masu dumi da zafin raɗaɗi suka zubo mata kan kumatu wanda ta ji su tamkar ruwan damar amma a wani bangren zuciyarta ta rage zuba nata hawayen da ta dau lokaci tanayi wanda yafi na bayyane zafi
Hawayen zahiri ma rahama ne...

Uhmmmm tofa wata sabuwa in ji yan caca

Itx'Kamala Minna😘😘😘

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now