DUNIYARMU-7

982 45 0
                                    

DUNIYARMU
Na
Kamala Minna
BABI NA BAKWAI
cikin mintina da ba su haura biyar ba muka isa bakin get din makarantarmu a daidai lokacin kuma ake kokarin kullewa alamun lokacin yayi duk Wanda ya zo a latti ne da sauri na dire na suri kaya na na falle da gudu na fada ciki ina Shiga a ka kulle wata irin ajiyar zuciya mai karfi nayi domin da an kulle da na bani nikam.
da sauri nayi hanyar ajinmu ina isa na tadda har malamin ingilishi ya shiga tunga na ja na tsaya ina rarraba idanuwa gabana sai faduwa yakeyi bakina yashiga ambaton sunan Allah cikin sanyi na doshi ajin har da sallama kai na a kasa ba Wanda ya tankamin shima malamin kawai kallona yayi ya cigaba da bayanin da yakeyi kujerar zama ta na dosa na tadda Baseera Haruna Sa'ad ita kadai dama daga ni sai ita muke zama murya kasa kasa ta dubeni
"Heejat yau kin makara dafatan lafiya?"
kai kawai na girgiza mata alamun ba wata matsala tun daga nan ba wanda yasake tsinkawa hankulanmu duk mun mai dashi kan Malam musadiq sai kwararo bayani yakeyi cikin iyawa da gwanancewa a bangaren ingilishi awa daya da zuwa na ya kammala darasin sa ya fice malamar food and nutrition ta shigo ita mata tayi na ta awa daya da rabi ta fice a lokacin ne kuma lokacin tashi break yayi duk kowa ya fice a ka barni dama wannan al'adatace ba na fita in har na shigo makaranta ko da kuwa break ne cikin aji nakeyin kaya na domin ina zuwa da komai na bukata
bayan min dawo break sai kuma aka fara bangaren arabiya malamin TAUHIDI ya shigo bayan yafita malamin FIKHU shi ma ya shigo bayan fitar sa sai malamin ALKUR'ANI wanda za mu shafe awanni uku munayin sa
haka muka cigaba da daukar darasi har lokacin tashi yayi a ka tashi kowa ya firfito bakin get Wanda suke da wanda zasu dauke su su na tsaye masu hawa napep kuwa sun hau sun yi gida
Ina cikin wanda ba a zo dauka da wuri ba sai rarraba idanu nakeyi domin hango Aliyu ta ina zai fito ne amma tsayin min talatin da tashin mu ba alamun Aliyu gashi har an watse an bar ni Wanda ba za dauka ba kalilan ne
kamar daga sama naji ana horn duk hankalina bai kai dani akeyi ba nidai kaina na sunkuye duk hankali na ya fara tashi don sam bana so a tashi in gan ni bakin titi a tsaye bana jin dadi sai naji rai na na baci
Ina cikin wannan duniyar tunanin na tsinkayi muryar mutum akai na da sauri na dago don ganin wanene, kuri nayi masa da idanuwa ina son sanin inda nasan fuskar sa don ba tantama nasan wannan fuskar sanye yake cikin shiga ta manya kaya shadda kalar ruwan ganye sai maiko takeyi kan sa sanye da hura kalar shaddar sa kayan sun yi matukar yi ma kyau da kara masa kwarjini ga wani murmushi dake bayyane akan fuskar sa..
ban kai ga kare masa kallo da suffantashi ba na kara tsinkewa jin yakira sunana da Sauri nayi kasa da kai na sake dago wa wannan karon kallon ido cikin ido muka yi dashi gabana ya ba ras ya fadi da sauri na kau da kaina ina neman tsari ga wannan mutumin sai addu'a nakeyi cikin zuciyata
"bahijjat zaman me kike yi anan, naga an tashi makarantar amma ki na zaune ke kadai"
shiru nayi masa kamar ban san anyi ruwan sa a wajan ba can kuma sai na ga rashin kulawa da zan nuna masa kamar wulakanci ne kuma wulakanci ba kyau
kai na akasa cikin murya kasa kasa nace dashi
"Aliyu ne bai zo ba har yanzu mai dauka ta ya mai dani gida"
da mamaki sai naji yace
"to tashi ni in mai da ki gida tun da nima gida nayi amma zaman ki anan haka sam bai kamace ki ba rana duk zata dakar mini wannan jikin naki mai tsada"
ban fahimci abin da yake nufi ba illah duban sa da nayi don har zuwa lokacin ban tuno in da na sanshi ba
gani da yayi bani da niyyar tashi kuma ba zan tsinka ba ya San yashi sake magantuwa
"bahijjat dake fa nakeyi ko ba zaki bini bane?"
girgiza ma sa kai nayi sannan nace "dama ka bar shi na San yanzu haka ya na kan hanya ka ra so wane kawai bai yi ba"
fahimtar da yayi kamar ban yi amanna dashi ba ya Sanya shi sakin murmushi har sai da naji sautin sa
"Tsorona kikeyi ko bahijjat ba ki gane ni ba ne ko, nine fa Adam na unguwar ku dan gidan alhaji dan-kasa"
da sauri na dago kai na ina kara kallon sa sai yanzu na gane  in da na San shi 'ADAM DAN-KASA' abin da zuciya ta tafadi kenan Adamu dan kusa da mune layin mu daya mahaifin sa shahararran mai kudine  sosai domin kuwa duk cikin dorayi da wuya a samu Wanda zai kamo kafar sa a dukiyarsa domin yana da kamfanoni cikin unguwar sharada har ma da unguwar panshekara ga shaguna da yake da su a kasuwannin kano.
gwauron numafshi na sauke na daga kai na dubeshi har zuwa lokacin idanuwan sa na kai na da mamaki a fuskata nace dashi
"da ka bar shi wallahi nagode sosai da karamcin da kayi min.."
Hannu ya daga min fuskar sa ta canza launi zuwa fushi
"Haba hijjat kamar baki san ni ba sai kace Wanda zai cuce ki matsayin kanwata fa na daukeki ko wani naga zai cuce ki ba zan lamunta ba ai ko ba dangantakar unguwa da ta hadamu akwai dangantakar addani please don Allah karki ce baki amince dani ba tashi mu tafi"
Maganganunsa sun yi matukar sanyaya min jiki domin kuwa abin da yafadi gaskiya ne in har ban yarda dashi ba to ina zargin sa kenan da aikata wani mugun abu
ba yarda na iya haka na mike amma zuciya ta har yanzu ba ta gama AMANNA dashi ba na dauko kayana nayi tsaye kamar ban zan tafi ba hakan da ya gani ya sanyashi sanya hannu zai amshi kayan da ke hannuna da Sauri na goce ina murmushin yake
"Na gode ka barshi kawai zan iya rikewa"
Hannnu ya watsa sama alamun ba damuwa ya yi gaba ina biye dashi har muka isa ga dankareriyar motar sa sai daukar idanu takeyi ta na zuba kyalli gidan gaba na ga yabude sannan ya dubeni alamun wai na shiga idanuwana na dan zaro waje ina dubansa kai na ga ya girgizamin alamun ba ya so nace komai ba yarda na iya haka na fada cikin motar wani irin kamshi mai dadi shaka ya daki hancina har sai da na dauke numfashi ban lura ba ashe har ya kulle bangaren da nake  ya juyo izuwa ma zaunin direba ya shigo ya zauna yayi mata key ya zuge gilasan motar masu launi baki irin wanda sai kai da kake cikin motar kake hangen mutane amma su ba za su taba sanin wanene a ciki ba.
Na ji mun fara tafiya wani sanyayyan sanyi naji ya na ratsa duk kannin sansan jiki na sai wani lumshe idanu nakeyi shi sai hankalin sa na kan tuki ya saki sauti sai bin wakar yakeyi tafiya tayi tafiya ban San lokacin da wani irin rikitaccen barci ya zo yayi awan gabani dani ba
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un
Aka ce K'ADDARA TA RIGAYI FATA to itace ta yo min dirar bazataa
Tun da barcin nan ya dauke ni a motar Adamu ban tashi barkawa ba sai a gadon asibiti cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali da rugujewar farincikin rayuwata da na iyaye na Ina kwance shame shame cikin halin na rashin hayyaci ba abin da idanuwa su keyi sai zubar hawaye na takaici tunani na ya fara dawowa duk abin da ya wakana duk yafara dawo min cikin zahirin rayuwata wani gunjin kuka na saki na shiga kokarin tashi amma ina tun daga marata zuwa kafafuwana ba abin da sukeyi sai zafi da radadi kamar anyi min wanka da barkono
mahaifina naji ya rike ni ya na ambaton sunana da Sauri na kai dubana gareshi yanayin da nagan shi aciki da yanayin da fuskar sa ta sauya idanuwansa sun kada sunyi jajir hakan ya kara dugunzuma tashin hankali na wani irin kuka na saki ina ambaton na shiga uku na lalale rikon da mahaifina yayi min na lura jikin sa ba abin da yakeyi sai rawa ya koma ya kwantar dani cikin muryar lallashi ya dubeni kwalla ta cika masa idanuwa
"Bahijjata kiyi hakuri komai ya faru da bawa DAGA ALLAH NE(Rashkardam) ki dauki komai a matsayin kaddara domin tun fil'azal Allah ya rubuta sai hakan ta faru"
Ya karashe cikin karayar zuciya ya koma kan kujera ya zauna ina lura dashi hawaye ke ta faman surnanowa daga idanuwan sa ya nasanya babban rigar sa ya na daukewa.
"abba an kashe min rayuwa an rugurguzamin farin cikina an dasamin mummunar tabo cikin duniyar rayuwata  na shiga uku ni bahijja ya ya zan yi da wannan rayuwa mai ya sa kaddara tayi min haka mai yasa ba ta tashi zuwa min ba sai ta wannan hanyar mai cike da muni da hargitsi da kayan barinciki kaicon wannan rayuwa kaicon wannan duniya da mugayen wasu al'ummar da ke cikin ta"
Wani kuka ya kufce min mai cike dacin bakin ciki tun daga zuciya har makogoro na abin da nake ji sai wani makakin dacin Wanda yafi madaci daci sai da  nayi kuka na nakoshi amma abbana bai hanani ba don shi nashi kukan ya kasa tsayar dashi
fuska ta jage jage da hawaye na dubi abbana cikin rawar murya
"abba ina mami shin taji wannan abin da kayi min mai tawatsa rayuwar farincikin da dasa bakin ciki da takaici da sanya ciwon zuciya?"
bai bani amsa ba a daidai lokacin likita ya shigo yanayin da ya gamun aciki yayi matukar tausaya mana da sanyi jiki ya kara so garemu fuskar sa na bayyanar da tsatsar nuna takaicin sa matuka akan abin da akayi min
Ya dubi abbana bayan ya janyo kujera ya zauna cikin muryar lallashi
"ba yarda za muyi Alhaji dole hakuri za mu bai wa kan mu rayuwar yanzu da muke ciki kenan rayuwa ta lalace al'umman cikin ta sun lalata ta sun ta garyata sun dauko munana halaye wanda za su kai mu ga rashin samun rahamar Allah sun dora ma duniyar nan sun dauko munana halaye Wanda Allah yake fushi ga duk mai aikatasu sun kawata rayuwarmu da su DUNIYARMU ta lalace al'umman cikin sun lalata ta wannan rayuwa da muke cikin sai dai muce innalillahi wa inna ilaihir raji'un"
likita ya dafa kafadar mahaifina bayan ya gama maganar sa cikin takaici da bakin cikin wannan rayuwa
"ayi hakuri alhaji wannan lamari ya rigaya ya faru ba yarda zamuyi sai sai fatan Allah ya tsare mana rayuwar mu ta nan gaba domin kuwa rayuwar yanzu yin ta kawai akeyi son zuciya da son daukaka ko ta halin yaya ne  an manta da ranar alkiyama ranar da Allah zai yi HISABI(AUYO) ga duk kan wani dangin rai akan rayuwar da yayi a duniyar nan duk ba ma tuna haka kawai rayuwa ce akeyin ta ta son zuciya da muradan jindadi ko ta halin kaka ne"
cikin bacin rai abbana ya dubi likita
"an ya muna bukatar samun rahamar Allah a DUNIYARMU da lahirar mu kuwa, ace munanan aiyuka su ne muka mayar abokanan rayuwarmu ba mu da wani aiki na yabo da Allah zai duba ya ji muradan birgewa sai sai kayan da Allah zai yi fushi damu da shi mukayi wa rayuwar kawa gaskiya to ba a yi wa rayuwar adalci ba kuma a haka kowa yake so ranar alkiyama ace ya shiga aljanna gaskiya son zuciya da son jindadin duniya bai yi ba"
Ya karashe cikin tsananin takaci da bakin cikin
likita yace"ai lamarin rayuwar nan sai du'a'i kawai irin wannan mummunar aikin da akayi wa wannan yar taka shine  ta zama ruwan dare cikin rayuwarmu ba kakana ba manya har fa da jaririn yan watanni shida sai kaji wai anyi musu fyade wa'iyazubillah abin takaici da ban haushi in ka duba Wanda yayi wannan aiki ashekaru ya hau ra sittin amma saboda mutuwar zuciya da rashin imani da tausayi..kai jama'a kai jama'a WANNAN RAYUWA muna cikin musifa kuma ba Wanda ke janyo ta mune da kan mu muke dauko ta ba ruwan kaddara son zuciya ne kawai da mutuwar ta amma ina amfanin haka mutum kaganshi magidanci mai iyali da 'ya'ya amma shine yake wannan mugun aikin shin ba ya tunani wata rana hakan za ta iya fadowa kan sa ko ga 'ya'yan sa ko cikin dangin sa sai ya ji anyi wa wani ba ya tunanin halin da zai shiga ne na rashin kwanciyar  hankali"
a kule abbana yace "ina yake tunanin haka idanuwan sun rufe imanin sa ya bar zuciyar sa ba abin da yake hange sai mugun nufin da ya kudira azuciyar sa"
Haka likita da abbana suka ci gaba da maganganu kan irin wannan bakar rayuwa da muke cikin mai cike da rudun rashin hankali nidai zuciya ta sai tururin bakin cikin take ji nake kamar in hadiyi zuciyata na mace don kuwa duk naji rayuwar ta isheni cikin duniyar nan ba na muradin in cigabada WATA RAYUWA a cikin ta
sai da na shafe kwana hudu cir a kwance asibiti ana bani kulawa sosai har zuwa lokacin ban ga mami na ba hakan ya kara tada min da hankali don tunanins fushi take dani ta na zargi na da zubar musu da martabar su sai dai ban Sani ba ashe wannan tashin hankali da na shiga karami ne tashin hankali na gaba
rana ta biyar aka sallame mu har zuwa lokacin ba Wanda ya tambayeni wa yayi min wannan mugun aikin hakan kuwa bai dameni ba don sam bana so a tambayeni domin kuwa hakan kara tayar min da hankali yakeyi
misalin karfe biyar muka isa gida tunda muka iso gaba na ke bugawa lokaci- lokaci yanayin da naga unguwar tamu da yanayin kofar gidan namu ya tsanata faduwar gabans domin kuwa shinfidu nagani da tsirarin mutane akai alamu yanuna kenan akwai abin da ya faru kuma daga gani ba na armashin dadi bane da sauri na juya na dubi mahaifina
"abbana mai ya faru ne?"
na tambaya shi idanuwana kur a kan sa yanayin da na ga yanuna a fuskar sa lokacin guda naji gabana yayi wani irin mugun bugu har sai da na dafe kirjina ina ambaton innalillahi
da sauri na yi cikin gida shi kuma abbana ya tsaya kofar gida wajan mutanan da suke zazzaune tun da nasa kafata daya cikin gidan naji gabadaya duniyar na juyamin kamar Wanda jiri ke kokarin yarfar da ita kasa da sauri na dafa bango a haka har na isa cikin gidan bakowa a cikin sa hakan yayi matukar ba ni mamaki da Sauri cikin Jan kafa na isa dakin mami na da dage labule amma ba ita ba alamun ta da gudu nayi hanyar bayi ina kwala mata kira nan ma shiru kake ji nayi kicin bangan taba na koma dakin abbana nan ma ban gan taba  na dawo tsakar gida na tsaya kerere kamar wacce aka dasa na shiga raba idanuwa a daidai lokacin abbana ya shigo fuskar sa bayya ne da damuwa
Ya janyo ni cikin jikinsa muka zauna
"Hijjata  kin ga yarda rayuwarmu ta koma ko kin ga yarda Allah yayi da mu ko shi yasa a kullum ake cewa kar ka sakankance da duniya domin ba ma tabbata bace hijjata kiyi hakuri ki dauki komai da ya faru a rayuwarki a matsayin kaddara ce daga Allah gwada imaninmu yakeyi yake jarabtarmu da irin wannan kaddarar ki daure hijjata ki baiwa zuciya hakuri ki taushe ta domin hakan zai matukar taimaka miki daga gujewar duk wani halina fadawa  tashin hankali kiyi hakuri hijjata kin ji"
maganganun abbana sun yi matukar dugunzuma tashin hankali da nake ciki da sanyaya min jiki matuka gaya
na dubeshi cikin rashin fahimta
"Ina mami abba"
shiru yayi kamar ba zan yi magana ba can ya nisa
"wannan mugun aikin da akayi miki hijjata aka keta miki haddi aka ci zarafin ki a ka rabaki da martabar ki da darajar ki shine SILAR AJALI ga mamin ki"
ban san lokacin da na daura hannu aka ba na kurma ihu na fadi kasa sumanmiya sai farkawa nayi na ganni yashe kan abbana yanayin da nagani a gareshi ya ci kuka har ya godewa Allah
tun da ga wannan lokacin na yankewa kai na da wata rayuwa wai ta farinciki cikin duniya ta tashin hankali da rashin jindadi da kayan damuwa sune suka zama abokan rayuwa ta nayi Allah ya isa ya fi a kirga ga Adamu dan-kasa domin kuwa duk shine silar komai da ya faru a rayuwa ta abbana ya yayi tambayar duniya in gaya wanda yayi min wannan mugun aikin amma naki sai dai nace nima ban san shi ba da mahaifina ya fuskanci ba na son maganar sai ya je baya da tambaya ta ya barwa Allah komai domin shine zai mana sakayya
haka rayuwa ta cigaba da guda na cikin rashin armashin dadi sai da na shafe sama da shekara daya amma ban canza ba daga yanayin da nake cikin kullum mahaifina rarrashi na yakeyi da in hakura domin kuwa na sanyawa kaina damuwa abin da yafaru ya Riga yafaru ba baya za a kuma dawowa ba a wannan halin na kammala karatun firamare dina lokacin cikin ikon Allah na samu sakamako mai kyau don sai da nayi mamaki don ban taba zaton zan samu wani abin yabo ba don sam lokacin karatu na kaurace masa ba na sha'awar sam makarantar ma sai mun kai ruwan rana ni da abban sannan nake zuwa
bayan wani lokaci abban ya tuntubeni da zancen cigaba da makaranta maganar gaskiya lokacin ban da ra'ayin wani cigaba da karatu dan shima ya fice min rai sam ba na kaunar sa don a nawa haukar har da sanadin zuwa makaranta rayuwata ta lalace
lokacin da abbana yaji na sanardashi ba na son cigaba da karatu na ga bacin ran sa Wanda tun da aka haifeni ban gani ba don rufe idon sa yayi ya shiga surfamin fada kamar zai dakeni gada karshe ma ya daina kulani sai da muka shafe kwana uku ba ya min magana ko na gaidashi ba ya amsawa ko wajan sa naje a shago korata yakeyi ya ce na tashi na bashi waje tun da ni sakarya ce  ban san ayi min abin yabo ba ban san abin da zai taimakawa rayuwa ta ba
ganin da nayi fushin da ya dauka da gaske ba shiri naje ina kuka na shiga bashi hakuri na dauki alkawarin cigaba da karatuna to tsakanin d'a da uba nan da nan ya sauko muka dawo kamar da cikin kankanin lokacin yayi min komai na makaranta na cigaba da karatu na a matakin sakandiri to shiga ta makaranta sakandire itace sanadin lalacewar rayuwa ta kuma anan na hadu da mubassheer shine mutumin da ya kara iza wutar lalacewar rayuwata ban iya soyayya ba shine ya koyar dani so ban san menene shan kwaya ba shine ya koyamin ita ban San menene zuwa club ba shine ya koyar dani yana da babban kaso wajan kashe min rayuwa ta kuma nima na bashi goyon baya don anawa tunanin ba abin da  yayi saura a rayuwa ta nafarinciki da jin dadi ban da wata daraja ko wata martaba da za a kalleni da ita da duk wata 'ya mace ke da ita hakan yakara ba ni damar fadawa cikin harkar banza da kashe arayuwa mun kasance da mubassheer har lokacin da muka gama makaranta duk mahaifina bai san halin da nake cikin ba domin kuwa akwai fuskar salihanci a gareni a cikin gida amma in nafice waje kwalluwar shegiya ce so da dama mahaifina na lura da Dan sauye sauye da nayi na hali yana yawan ankarar dani da zaunar dani yayi min nasiha sosai a wajan zan nuna masa na dauka amma kwana biyu zan koma ruwa ban san ina  shaye shaye ba hakan bai san ina fitar dare ba domin kuwa dakina daban nashi daban sai yayi barci nake fita gaf da assalatu kuma na dawo gida
ban san abin da mahaifina ke kitsawa kai na ba ashe a bayan fage shirin aure yake min ba tare sa na Sani ba sai satin da za a dauramin aure sannan naji labari hakan yayi matukar tayar min da hankali ba kadan ba nasami mubassheer na sanar dashi sai yanuna min kar nasake na nuna turjiya domin in har na nuna ba na so hakan zai iya bankada halin da muke cikin da wannan shawarar nayi amfani ta mubassheer nayi amanna na yarda da auren a ranar wata asabar aka dauramin aure da mijina Adam wanda sam ban San shi ba ban san wanene ba haka akayi shagalin biki a ka watse nidai a wajena da shi da babu duk daya ne ban damu da gani mijin ba a ranar da aka daura auren a ranar aka dauke ni zuwa gidan miji na a ka kawo nan jahar Niger Minna in da yake aiki.

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now