DUNIYARMU-32

375 19 0
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA.

BABI NA TALATIN DA BIYU.

Kwana biyu tsakani da kama su Saudat ba karamin tashin hankali ta shi ba domin yarda Dsp.Avva Omar Yhero ya hana a duba mata kafafunta ba yarda likita bai yi da shi amma yace shifa bai ga amfani taimaka mata ba, domin in har aka taimaka mata tamkar an bata lasisin kara cigaba da aikin da take yi kenan.
Kwana take yi tana zumduma ihu dalilin kafafuwanta da ta ji suna wani irin kwankwasa daga ciki kamar an samu gatari an dandatsa mata su kowa na cikin asibitin marasa lafiya da masu jinya cikin kwana biyu sun san Saudat domin hana mutane barci take yi litikta har an lura barci yake yi mata amma a banza domin ko minti biyar ba ta yi take farkawa ta hau zunduma ihu tana neman dauki amma ba wanda yake kulata ko ma mutum ya so taimaka mata Dsp.Avva na nan domin shi ya kasance mai kula da ita yake ganinta azaba kala-kala ba wacce baya gana mata a boye ba tare da kowa ya sani ba domin ya tsanane ta tsana mai tsanani a zuciyarsa bai taba tsanar wani mutum a duniyarsa ba kamar Saudat.
wani lokacin in ta isheshi da ihu yayi mata magana taki daina sai ya sa kafarsa ya take tata kafar nan za ta zunduma ihu kamar wacce za a zare wa rai wannan azaba da yake gana mata mutane da yawa da suke tunanin ciwo ke nukurkusarta har hawaye suke zubda mata saboda tsananin tausayi da take ba su.
ta wannan hanyar yayi amfani ya dinga tambayarta duk wani abun da yake bukat ya sani game da aikin assha da sukeyi tun tana taurin kai in ya tambaye taki bashi amsa sai ma tayi banza dashi tana faman zubda hawaye hakan da ya gani ya sake sabon salon mugunta da cizguna mata takaici ya hanata abinci ko da kuwa wasu masu cinyane suka ji tausayinta suka bata to sai ya amsheshi kuma yayi wa wanda ya bata gargadin in ya ga an sake bata sai mutum ya ji ajikin sa.
Ganin da tayi yana shirin kashe ta da ranta nan ta shiga ba shi labarin komai da suke aikatawa ba karamin mamaki yaji lokacin da ya fuskanci tana cikin yan fashin da suka addabi mutanan garin Minna da Abuja musamman da ya ji wai ita ce Oga haka ya kara tunzura shi amma ta wani bangare ba karamin dadi ya ji ba da wannan gaggarumar nasarar da sukayi domin su Saudat an jima ana fakonsu amma ina ba a yin nsarar kama su sai gashi ta wata hanya saukakka Allah ya tonu asirin su.
Bai gama tsinkewa da lamarin ta ba sai da yaji wai ita ce mamallakiyar lambar wayar da suke neman mai ita da zargin satar mutum zugudum takaicin duniya ya ishe Dsp,Avva ya shiga dubanta da idanunsa jajaye msu dauke da tsananin bacin rai da kiyayya ya sanya kafarsa ya take mata kafa wacce a wannan lokaci ta kumbura kamar za ta fashe wani irin gigitaccen kara ta saki lokaci guda ta dauke wuta.
Ko a jikinsa bai nuna alamun tsoro ko wani fargaba akan yanayin da ya ga ta kasance a ciki zuciyarsa cike da takaicin labarin da ya ji ta bashi abubuwa da dama da ake ta hakilon a san su wanene suke aikatawa ashe ba wasu ba ne illa kafiran majunanun mata nan tabbas Allah ya ragewa aya zakin ta da wadancan sauraj na raye sai ya shayar da su mamaki amma tun da sun samu babbar cikin su za ta fada wa yan garin su da wannan tunanin ya fito daga dakin da ya kasance Saudat ce kawai a cikin sa ya sanya makulle ya datse ya kama gaban sa ko ina yabi kowa bin sa yake da kallo maza da mata har da yara domin cikin kwanaki uku duk sun san shi da kuma abin da yake yi a cikin Asibitin kallon mugu suke yi masa maras imani da tausayi wasu kuwa wanda suka san komai burgesu yake yi tare da shi masa albarka domin da yayi shi ne daidai da dacewa barin irin su Saudat cikin kasar nan tamu ba karamar illa ban ce domin annoba ce take yawo cikin al'umma ba tare da masaniya ba.
Tunda ya fice daga cikin Asibitin bai zame ko ina ba sa Hedkwatarsu ta yan sanda nan ya ba su labari komai sun yi matukar cika da mamaki kuma sun ji dadin labarin sosai a ran su.
Cikin kanƙanin lokaci suka zurfafa bincike don tabbatuwar komai bayn komai ya zama daidai sun samu gamsassu baya nan daga bakin Saudat wanda wuya ta saka sakin baki ta dinga kora bayani tiryan-tiryar ba kankautawa domin iya wuya ta sha wuya har taji ina ma za ta mutu da tafi son haka kafafuwant kuwa ba a maganar su zuwa wannan lokacin har sun fara fidda wani ruwa mai dan banzan wari shi kan sa Dsp.Avva ya fara rangwanta mata akan izayar da yake gama mata tun da dai sun samu Information a gareta.
--------------@--------------
KAUYEN GURMANA.

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now