DUNIYARMU-30

402 12 0
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA.

BABI NA TALATIN.

"ga gidan nan".
Tk ya fadi cikin mutuwar jiki da tsoron abin da zai je ya dawo a wani bangare kuma tunani yake yi akan halin da suka baro Adam domin ya yanke tsammani ba tabbacin za su koma su same shi cikin numfashi a duniyar nan.
Gidan Mansoor su ka zo domin Alhaji Kabeer ya birkice ala dole sai an nemo Bahijja ko a ina take ganin da ya yi ɗan nasa na kokarin barin duniya hakan ya kara tsoratar da Tk ganin da yayi komai na iya faruwa a ko wani lokaci kawai sai ya yanke hukunci kai su inda yake da tabbacin zai samu Bahijja don ya hakikance nan ne gidan da take don nan ne ya same ta kuma ya ga tashiga amma abin da ke fadar masa da gaba shine yarda ya ganta da wani kuma ya tabbata zai iya kasancewa mijin auranta ne amma kuma a wani bangare na zuciyarsa yana kokwanto akan hakan domin kuwa duk wata matar aure ba yarda za ayi ta je club har ta kai tsayin dare kamar yarda ya ga tayi amma kuma ai yanzu ZAMANI YA CANJA matan aure tamkar yan mata su ka koma in ba wai ka sani ba ba ka ganewa sun daukarwa kan su JARRABAR DUNIYA sun daurawa rayuwarsu...
Muryar Alhaji ce ta katse masa tunanin zuci da yake yi da sauri ya shiga saita kan shi yana duban sa cikin yanayi na alamar fargaba da tsoro.
"kace mana ga gidan kuma ka zauna kayi shiru ko dai ba nan din bane?".
Abin da Alhaji ya fadi kenan ya na duban Tk da yake cikin wani yanayi jiki a sanya ye Tk ya shiga gyada kai kamar mai son fashewa da kuka ba abin da ke dawainiya dashi sai fargabar in Bahijja ta kasance matar aure ce ya san komai ya gama lalacewa ba yarda kuma za ayi kuma tabbas wata matsalar ce za ta kunno kai.
A sanyaye Tk ya tun kari get din gidan Mansoor gabasan sai faman bugi yake yi har ya isa ya kwankwasa ya jim yana jiran a bude amma ba alamun haka din ya sake kai hannu zai kwanƙwasa sai ga maigadi ya bude ya bi Tk da kallo na ban san ka ba cikin yaƙe Tk ya gaida shi gami da tambayarsa ko mutanan gidan na nan sai da maigadi yayi jim cikin alamun tunani da kuma rashin yarda da Tk sai faman bin shi yake da kallo can dai ya nisa.
"Uhmm ba sa nan sun tafi aiki...".
da sauri Tk ya katse shi.
"gaskiya nake so ka fada min, wallahi ba wani mugun abu nake tafe dashi ba, don Allah in yana ciki kayi min sallama dashi".
gani yarda Tk ya marare ce kamar mai son fashewa da kuka ya sanya maigadi tausayin sa gyada kai yayi gami da cewa "ina zuwa". Ya juya cikin gidan.
Wata irin ajiyar zuciya Tk yayi ganin an samu sa'ar masu gidan suna nan sai dai fargabar sa daya da zuciyarsa ke yi akan Bahijja da mutumin da ya gan su tare yana tsoron ace mijin ta ne.
Karar buɗe get din ne ya sanya shi dawowa hayyacin sa daga duniyar tunani,Mansoor ya gani tsaye gaban sa jikinsa sanye da kananun kaya wanda sukayi matukar amsar sa su fiddo masa da suffarsa ta cikakken ɗa namiji mai jini a jika da kuma kuruciya wani irin bugu gaban Tk yayi ganin Mansoor domin komai ya dame Adam ya shanye kyau,kudi,hutu,wayewa duk ya na da su cikin rawar zuciya ya mika msa hannu amma sai Mansoor ya ki bashi hannun illa wani irin kallo da yake bin sa dashi na alamun naso na gane ka haka ya kara tsoratar da Tk cikin sanyi jiki ya janye hannunsa ya na faman yake kamar wanda aka cewa dole sai yayi.
"kai ne mutumin da aka ce yana nema na?".
Mansoor ya fadi yana mai nuna Tƙ da hannu.
Ba bakin magana kawai ya shiga gyada kai alamun haka ne.
A daidai lokacin Alhaji da Hajiya Laila suka iso wajan nan Mansoor  ya bi su da kallon rashin sani da kuma son sanin abin da ya kawo su gareshi si dai ban san su ba kuma ba wata alaƙa da yake tunanin za ta hada su.
Alhaji ya iso gareshi tare da bashi hannu Mansoor ya bi hannun nashi da kallo kamar ba zai amsa ma mai kuma ya gani sai shima ya mika masa nashi a yanayi na ban so ba. Alhaji yayi gyaran murya sannan ya fara magana cikin yanayi nan rashin mai ma.ya dace ya ce.
"Sunana Alhaji Kabeer Tanga mahaifin Adam".
wata irin zillo zuciyar Mansoor tayi yana maimata sunan Adam cikin zuciƴarsa da ƙasar ruhin sa abubuwa  biyu ne suka zo masa zuciya a lokaci guda Bahijja da kuma Tk nan ya tabbatar da zargin sa wani irin haushi ne ya ziyarce shi cikin zuciyarsa ya rasa ma abin da ya dace yayi kan wadannan mutanan ma cuta zuciyarsa ta far tsalle tsalle yana mai kankantar da idanuwansa jira kawai yake yi ya ji abin da su ka zo dashi ya keta musu rashin mutunci don jin zuciyarsa yake tana zabi da raɗaɗi ba abin d ke masa yawo sai in ya tunani wadannan mutanan dake gaban sa iyayen ɗan  da ya bata rayuwar Bahijja ne numfashi ya aje gami da gyada kai yana yake can ya nisa cikin muryar ɗaci ya fara magana. "ina jinka mai ke tafe da kai".
Jin yarda yayi maganar ya sanya Alhaji Kabeer dan razana domin ba abin da ya jiyo a muryarsa illa ɗaci da fitina haka ya sanya shakku a zuciyarsa amma haka ya danne damuwarsa  ya saki yake shima kamar dole.
"Maganar ba za ta yuwu a nan ba inda da dama da mun samu wajan zama domin mu fahimci juna sosai".
Haushi ya sake turnuke Mansoor don gani yake yi sun zo da iskanci ne ba wani abu ba cikin tunkudar zuciya da haushi ya kau da kai cikin alamun son keta rashin mutunci yace.
"kawai muyi maganar da zamuyi anan don bana mukatar komawa cikin gida domin nafito kenan akwai in da zani".
ya karashe ya na mai cin cin magani alamun yazo wuya haka shima Alhaji Kabeer ganin Mansoor zai nuna masa ɗanyen kai nan da nan zuciyarsa ta fara daukar zai da alamun shima tsohon kan nashi zai tashi nan ya shiga numfarfashi  da hirje hirje yana mai tsuke fuska kamar bire ya samu lemon tsami Hajiya Laila ce ta lura da yanayin da Alhaji ke ciki ta san komai zai iya faruwa in kuwa haka ta kasance abubuwa da yawa za su lalace abin da suka zo nema kuma a rasa shi bai kamata ace a matsayin su na masu nema suna daukar zafi ba musamman in suka lura da halin da suke ciki matsowa tayi gami da dafa kafadar Alhaji.
"nema fa mukeyi kawai muyi maganar anan domin da cikin da nan duk daya ne".
ta fadi tana mai duban Mansoor  wanda taga ya hada girar sama da ta kasa kamar bakin hadarin dake kokarin zubda ruwa.
jin abin da hajiya tace yasan ya alhaji saukowa daga zafin da ya fara hawa ya marare ce murya kamar gaske ya yafawa fuskarta yanayin tausayi.
Nana ya shiga korawa Mansoor bayani komai har izuwa maganar da Tk ya fada masa ya karashe yana mai kara yin rauni da muryarsa kamar mai son fashewa da kuka.
Mansoor da ya gama kulewa da takaici da bacin rai tun lokacin da ya gama tabbatar da zargin da yake yi ya shiga cin-cin magana bakin sa sai mutsu-mutsi yake yi yana kankantar da idanu zuciyar sai faman tunkudo masa wasu tawagar ashar take tana umartarsa da ya dan na masu Alhaji kabeer haka ne kawai zai saukaka masa zafin ran da yake kai amma ganin manyan mutane sai ya hakurkurtar da kan sa amma duk da hakan sai ya dubi idanun Alhaji Kabeer yace.
"Uban wa ya ce muku don an ganni da yarinya da kuke nema kuma aka ce muku nan gidan uban ta ne in ban da tsabar rainin hankali irin naka Alhaji ta ya ya ɗan ka zai hadu da budurwa a club amma sai ku kwaso tsiyarku ku zo nan niman ta akan wani dalili?".
Duk kan su sukayi mutuwar tsaye jin irin kalaman da Mansoor yake sanar da su zuciyar Alhaji Kabeer ta zo wuya ya shiga jan numfashi dakyar masifa na tsingulinsa ji yake kamar ya zabgawa Mansoor mari amma ina ba zai iya ba domin ya san kwa6ar sa ce za tayi ruwa sosai nan dai ya sake hakurkurtar da kan sa ya shiga duban Mansoor.
"kayi hakuri naga alamun baka ji dadin zuwa wajanka da mukayi ba amma ba yarda muka iya ne wajan ka shi kadaina ne hanyar da muke da ita ina mai rokon ka don Allah in kasan in da take ko in da zamu sameta ka sanar damu nayi maka Alkawarin ko mai kake so zan baka shi".
Yanayin da ya ga sun nuna sun dan bashi tausayi amma kuma hakan ba ya na nufin zai rangwanta musu bane domin kuwa su ba abin a tausaya musu bane ba abin da zuciyasa ke yi sai tsallan murna jin halin da Adam yake ciki wannan ba karamin abun murna bane ga Bahijja domin ga hanya mafi sauki ta daukar masa cikin ruwan sanyi ba sai t wahaƙar da kan ta wajan daukar rai ba balle zunuban da ya daukar wa kan sa su hau kan ta nan ya shiga murmushi lokaci guda duk ya ji bacin ran da yake ciki ya ragu ya dubi Alhaji.
"gaskiya ban san gidan su ba nima kawai haduwa mukayi da ita kamar yarda ɗan ka ya hadu da ita sai dai wata alfarma daya zan yi muku shine in har na ganta zam sanar da ita kun zo neman ta".
Ya na fadn haka ya juya ya koma cikin gida abin sa nan aka shiga kallan kallo tsakanin Tk dake can gefe tallabe da haba yana kallon abun da ke faruwa sam ya rasa abin yi domin tunanin sa gabadaya ya kulle.
jiki a sanyaye suna fara tafiya domin halin da suke ba su da abin yi sam haka suka isa motar su cike da tashin hankali suka bar wajan ko a motar ba wanda yƴai kokari tsinkawa har sukayi tafiya mai nisa sannan Hajiya Laila ta numafasa cikin matsannciyar damuwa .
"Alhaji yanzu meye abin yi?".
Gyada kai yay da alamun ran shi a matukar 6ace yake.
"ni ban taba ganin tsinannan yaro mai tsaurin ido ba kamar wannan yaron wallahi ya mai damu kamar mara hankali sai balla yake damu kamar ya samu bayinsa kina kallon yarda yake shan kamshi kamar uban sa ne shugaban kasa Allah ba don na kai zuciya nesa ba da buge shi zan yi".
maganganun Alhaji sun yi matukar  bawa Hajiya Laila dariya amma sait kanne damuwar da take ciki tafi karfin a ga dariya a garet ganinn yarda Alhaji ya hakikan ce yana IHU BAYAN HARI kai da kake nema amma kai ne zaka nuna iko ba ta ga laifin yaron ba domin kuwa yana da damar yin haka don nema aka zo yi wajansa.
" Kai Tukur ba cin wajan dan iskan yaron nan ba ka san in da zamu je ba ko zamu sami wannan SHU'UMAR YARINYAR dama alama 'YAR DUNIYA ce".
girgiza kai Tk ya shiga yi alamun bai sani ba Alhaji ya ja kwa6a gami da sakin tsaki mai tsayi yana mai dauke gumin da ya tsantsafo masa a goshi ita kuwa hajiya ganin ikon Allah take yarda Alhaji ya hakiƙance sai tsinew yaran mutane yake yi ya manta da nashi ɗan mai hali dai ba ya fasa halin sa a ko ina yake.
"nikam ban ga amfanin ta ja jijiyo yin wuya ba a wannan lamarin Alhaji duk fa wandannan da kake tsinewa sune maganin matsalar ka".
Duban ta yayi cikin haushi.
"to meye don an tsine musu duk ba su bane suka haifar mana da wannan bala'in mai kokarin kashe mu cikin wahala".
kau da kai tayi tana kallon titi tana mai cewa.
"ai dama kasan ance duk wanda ya bata shine ya fi cancanta da ya gyara don haka tun da su kake tsammanin sun saka muku cikin tashin hankali to kadaina tsine musu tunda su ne masu gyara domin kuwa tsine musu da kake yi zai iya ruguza hanyar gyarar".
shiru Alhaji yayi jin abin da  tace ya shiga nazari tsayin lokaci amma ba wanda ya sake magana a cikin su sai karar mota da na bugun zuciya kawai ke tashi.
-----------@------------
Numafashi take saki kamar wacce aka makure jikin bango ake kokarin rabata da ran ta idanuwanta sun kada sunyi jajir kamar wacce akayi wa shake da barkonon tsohuwa sai faman hirji take da tana murkususu kamar wacce take kokarin dire ɗa cikin duniya bakinta sai motsi yake zuciyarta na wani kartawa da zafi da raɗaɗi kamar za a zareta daga kirjinta sautin bugun da kirjin nata keyi shi ya haifar mata da sakin wasu zafafan hawaye.
Duniyar taji tana juya mata kamar za ta mai da ita ta baibai ta shiga duban Mansoor da idanuwanta da suka ƙankance saboda tsabagen shiga wani irin hali wani na ɗaci da takaici ba abin da taji na amsa mata kuwwa sai kalaman Mansoor da suke barazanar kona mata zuciya da ruhi ji take kamar ta shakoshi ta makure don takaicin wannan bakin labari mai matukar muni da ya sanar da ita ji take kamar ita ce rashin nasara da sa'a a rayuwa ya kare a kan ta ji take kamar ita kadai ce baƙar kaddaa mai muni take wanzuwa cikin duniyarta ta na walagigi da rayuwarta ta na buguta kamar kwallo.
Sai da ta gama numfarfashinta da kayan takaici sannan ta dubi Mansoor da shi takaicin nasa ya bayyana karara a fuskarsa da kuma tausayinta da yake ji tun daga kasar ruhin sa ganin yanayin da ta shiga dalilin fada mata abin da ya afku tsakanin sa da mahaifin Adam.
ba ta san lokaci da ta kwaso wasu tawagar ashar ba ta dire sannan ta dora da cewa,
"ban taba ganin tsinannun mutane lalatattu ba irin wandannan mutana nan".
ta karashe maganar cikin sakin wsu hawaye da suka taru a idanuwanta ta dora da cewa,
"da alamun ni a bakin cikin rayuwa zan kare Mansoor ban taba ganin mara sa'a a rayuwata ba kamar ni, shiyasa tun farko naso ka barni na dau fassar da zuciyata ta yarje min amma ka hanani ga shi yanzu suna kokarin kasheni ni kuma wani irin bala'i ne wannan mai yasa yawan mutanan duniya ba su da imani ne, shi dan uban sa Adam din da yake iyayensa haihuwar titi sukayi masa, saboda gantalalle ne watsantsa wanda tsinuwar Allah da ta mala'iku take walagigi da rayuwarsa, saboda gantalalliyar rayuwarsa da rashin saa da rahama a rayuwa sun gama hauka tashi, shi har zai iya bude maki ya tabka babban sa6o irin wannan, domin nidai sa6o zan kira wannan abin da ya aikata ya kama cutata ya kama kashe min rayuwa ya gama kashe min farinciki yayi sanadin gurbacewar duniyata shi har yake da  wani baki na furta kalma wanda tun da nake a rayuwata ban taba jin an faɗa mani kalmar da ta illa ta min zuciya da ruhi ba kamar wannan kalmar kaicon wannan duniya kaicon wannan zamani kaicon rayuwa da irin su Adam".
Kuka ne take yi wanda ba shi da sauti hawaye na fili da na zuciya sai zuba suke yi ba kankautawa komai ta ji ya dawo mat sabo fil kamar yanzu komai ke afkuwa da ita kamar yanzu mummunar ƙaddararta ke shigowa cikin duniyarta kuka take yi wanda take tsammanin ba shi da lokacin daukewa kuka take yi da bakin cikin dake nukurkusar zuciyarta kuka take wanda take so a sandin sa ruhinta ya bar gangar jikinta Adam ya shigo mata rayuwa da BIYU BALA'I wanda suka kasance sanadin lalata rayuwar ya keta mata haddi DAYA BALA'I gashi yanzu wai ya zo kuma da wani DAYA BALA'I ba ta san ya zata kasance nan gaba ba in ya haifar mata da UKU BALA'I dole ne ta kashe Adam dole ne ta dauki mummunar fansa akan sa dole a yau din nan Adam ya ji zafi da raɗaɗi kamar yarda ya haifar mata da raɗaɗi a zuciyarta dole ya san ita ma mutum ce mai daraja da kima dole ya san ba kowa wacce mace bace ake nasara wajan cuta da ita dole ya ji ajikinsa.
mikewa tayi cikin hanzari ta dubi Mansoor da ya tallabe ha6a yana kallon ta cikin tsananin tausayi tun daga kasar ruhinsa yake jin wasu abubuw suna kaiwa zuciyarsa fizga da kwakwalwarsa jiki yake kamar ya fashe da kuka ya ta ya ta yi ko ta sanadin haka za ta samu saukin zafin zuciya.
Wani murmushi ya ga ta sakar msa wanda ya tabbata in da za a fasa kirjinta ba abin da zai hana a ga zuciyarta na hayaki zata kama da wuta gabansa yaji ya buga ganin ta suri jakarta da mukullin motar da sauri ya mike cikin rawar jiki ya sha gabanta ya kura mata idanu da sauri ta kau da kanta jin yarda zuciyarta ke bugu ta san tabbas in ta cigaba da kallon Mansoor zai iya kashe mata hanzarin ta raɓashi tayi za ta wuce nan ya sake shan gaban ta cikin tsananin takaici ta fara magana.
"Na roke ka don Allah Mansoor karka cutar da zuciyata ta hanyar hanani abin da nayi niyya".
ta karashe tana mai hada hannayenta duk biyun alamun roko idanuwanta sai shatatalar da ruwan hawaye suke ba tsaya wa.
Tabbas ya san tana cikin wani yanayi sai dai ba zai so ta aikata abun da take da niyya domin yasan hakan ba zai haifa da ɗa mai idanu ba a gareta.
"ba zan cutar da zuciyarki ba amma ina rokon ki da karki yi abin da zaki zo kina nadama".
"NADAMA".
ta fadi cikin wata irin murya mai zafi tana duban Mansoor ta dora da cewa.
"wallahi na rantse maka da Allah in dai akan Adam ba zan taba yin nadama ba don na aikata masa wani abu. Kawai zan yi nadama har in ban samu nasarar daukar fansa akan sa ba".
ta karashe tana kokarin kauce masa ta wuce bai tanka mata ba kuma bai hana ta wuce wa ba da gudu ta isa ga motarta ta buɗe ta shiga cikin hanzari ta yi mata key ta fincike kamar zata tashi sama ran ta na matukar kuna. hakan da Mansoor ya gani ya san shi saurin isa gun motarsa shi ma.ya shiga ya bi bayanta.
Gudu take yi wanda da ka gani zaka gane ba cikin hayyaci ake yin sa domin kuwa motar gaban ta har daga wa yake yi wuta kawai take baiwa motar gani take yi kamar ba za ta isa ba gani take yi kamar  za ta iya hadiyar zuciya ta mutu kafin ta isa ga in da tayi niyya tafiyar minti goma tayi ta isa Asibiti Malam Aminu Kano tun daga kofa ta fara kokarin yin parking amma masu kula da get din suka hanata ba dan ta so ba ta isa ciki sannan tayi parking shima ba a inda ya dace ba cikin sauri gudu-gudu ta yi cikin Asibitin sai faman rarraba idanu take yi kamar wata zautacciya mutanen wajan sai bin ta da kallo su ke yi ganin irin halin da take ciki idanuwanta sun kumbur sunyi jajir alamun taci kuka har ta godewa Allah cikin Asibitin ta shiga sosai tana duban in da za ta ga alamun bakin mugu kamar yarda take nasawa a zuciyarta wani matattakala ta fara hawa cikin sauri kamar daga sama sukayi kacibus da Tk shi kuma ya na saukowa cikin yanayi na ma tsananciyar damuwa ai suna hada idanu ya ji wata irin faduwar gaba ta ziyarce shi ganin Bahijja wanda bai taba zaton zai ganta ba kuma cikin yanayi na tashin hankali hannu ya daga yana nuna ta dashi bakin sa na rawa yana kokarin yin magana amma taki fitowa ita kuwa wani irin kallon tsana da kiyayyace take daskare cikin kwayar idanunta sukarta ta shiga ya mutsewa cikin tsananin takaici  kunar rai wani wawan cafka ta kaiwa wuyar Tk wanda ban yi zato ko tsammani ba ta dauke shi da wani mari wanda karansa sai da ya amsa kuwwa cikin asibitin cikin wata irin murya mai cike da masifa ta dube shi.
"ina tsinane la'anannan Allah yake ina bakin kumurcin mamaguncin yake ida bakin kunama yake ina wanda tsinuwar Allah ke dawaini ya dashi nace ina yake!!!".
ta ida cikin kara wanda tayi matukar razana Tk sakin wuyarsa tayi gami da hankaɗa shi sai ga shi baje akan matattalakan wajan wani irin bugu kan shi yayi har sai da ya fashe hakan ya kara firgita shi matukar cikin gigita yayi mike yayi sama da gudu ganin haka da Bahijja tayi ta bi shi cikin hanzari domin ta tabbata inda Adam yake ya tunkara aiko sai ta kwasa a guje yana isa kofar dakin ya shiga ya na kokarin kullo kofar don ya hango yarda ta fallo da gudu kafin ya kai ga rufe ta bangeshi kamar wata ingarma ta fada cikin dakin gabadaya sun suka ta shi a firgice duk tsuka tsume a tsaye saboda tsabar tsorat da sukayi Alhaji Kabeer ne da Hajiya Laila sai Nurse dake tsaye kusa da Adam ta na kokarin yi masa Allura ba ta san lokacin da tayi cilli da allurara ba ta yi tsalle can gefe saboda tsoro duk Bahijja ta shigo cikin dakin sosai tan bin su da kallo daya bayan daya shi kuwa Tk yana can baya kofa da ta hada bango dashi Hajiya Laila zani a hannu jiki sai bari yake yi Alhaji Kabeer kuwa kure Bahijja yayi da idanu kamar wanda ya ga BAKUWAR FUSKA ko kuma ya san fuskar yake tunani a inda ya santa....

😁😁😁😁😁gham gham lahira must go Adam..lolz

DUNIYARMU (Compelet)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon