DUNIYARMU-12

675 54 0
                                    

DUNIYARMU
Na
KAMALA MINNA

BABI NA SHA BIYU
zaune suke cikin inuwar anburela dake girke cikin bayaro mall yanayi su kadai zaka kalla ka tabbatar da su na cikin muradan fariciki da na jindadi hejat ta dubi mubasheer da ya kai wa bakin sa farmaki da sanyayyan lemun inimi mai sanyi matuka "gaskiya wajan nan ya kayatar dani matuka gaya ina ma ace a nan kano nake zaune ina ga a kullum sai nayi zuwa Biyar ko fiye ma da haka" murmushi yayi mai dauke da jindadi ya margayar da kai cikin nuna yayi na'am da abin da ta ce nan yace "nima haka shiyasa na kawo ki nan don nasan zakiyi farin ciki da nan din kusan kullum in har na fito nan nake yada zango" duban da tayi da mamaki ba tare da tayi magana ba ta dauki robar ice-cream da ke gabanta ta sa cokali ta kamfato ta sanya  a bakin ta sanyin ta ji ya ratsa mata makoshi ta yi ajiyar zuciya gami da nisawa "kace nan kake zuwa kana sheke ayar ka son ran ka" kwalalo idanuwa yayi gami da dafe kirjin sa"laaaa rufani ki saya ni wallahi tun da muka zo har yau ba budurwar da na tunkara da sunan muyi wata mu'amala yar da ki kasan Wanda akayi wa ture" ya karashe maganar cikin alamun bai so haka ba hakan da hejat ta gani ya nuna ya tabbatar mata da gaske har zuciyar sa maganar da yake gaya mata hakan ba karamin dadi yayi mata a rai ba saboda tasan halin mubasheer ba hakuri gareshi ba bata taba zaton zai iya wannan juriyar ba amma kuma yarda ta San mubasheer akan lamarin mu'amala da mata anya zai iya hakuri har tsawon kwana biyar bai bibiyi wata ba gaskiya da wata a kasa amma dai bari ta barshi su tafi a haka din ajiyar numfashi tayi gami da duban sa "ya kama ta mu koma gida da wuri faaa" ta ka rashe maganar cikin sauri da kara sauti dalilin abin da idanuwan ta suka gane mata Wanda ba tayi zato ko tsammani haka ba jikin ta da magudanar jinin ta da taswirar tunanin ta da bugun zuciyar ta suka tsaya cak! mutuwar zaune na wucin gadi ya ziyarce ta ta rasa a wacce duniya take wani yanayi take ciki mai kokarin hasko mata wasu lamura marasa tsari da da kyan gani mai take shirin gani cikin wannan ranar wannan wacce irin rana ce anya tana da sa'a a fitowar da tayi...mubasheer ya kira sunan cikin amsa kuwa ganin halin da tashiga hankalin sa ya tashi ya mike ya shiga jinjiga ta kamar wacce mutuwa ta dauke mata rai hakan ya dawo da ita duniyar ta amma da guzurin tashin hankali masu dauke da kayan bakin ciki da na rashin kwanciyar hankali numfashi ta saki yi cikin sauri-sauri kamar zai tsaya da aiki kanta ta ji yayi wani irin nauyi kamar an daura mata goron dutse da dala wani tururin mai dauke da makakin yaji taji ya saukar mata cikin idanuwa har ganin nata ya fara daukewa zuwa dishi-dishi zuciyar ta na faman lugudan bugu kamar za ta faso kirji ta yo waje jikinta ya shiga kyarma da Mazarin kamar wacce ake kadawa gangi ba karamin tashin hankali mubasheer ya shiga ba cikin yan mintuna sai ambatar sunan bahijjat yakeyi amma ina ba alamun wani karfi ko kuzarin da zai bata Samar amsa kiran sa ko wani kwankwarar motsi iyakar karfin sa ya rike kafadun ta ya girgiza tare da Kiran sunan ta da karfi kamar zai dauke mata jinta har zuwa wannan lokacin ba wani kwankawarar motsi da tayi da sauri ya sake ya dauki gorar ruwan SWAN dake girke a kan teburi ya balle muffin ya shiga kwarara sai da ya juyo mata shi tas! amma duk da hakan bai sanya ta dawo hayyacin ta  da sauri mubasheer ya isa wajan gets security cikin rawar murya ya mai cewa su taimaka masa matar sa ba ta da lafiya da sauri suyo wajan da take ganin halin da take ciki su ma sun yi matukar firgita da sauri suka ce ya dauke zuwa mota tun kafin su ida zancen su ya surkuce ta kamar 'yar tsana ya falla a guje sai cikin motar ya watsa ta ya shiga gidan direba ya fizge ta kamar Wanda zai tashi sama gudu yakeyi na fitar hankali kallo daya kayi mubasheer ka tabbatar yana cikin yanayi na rashin dadin rai kan sa yayi matukar daurewa da shiga duhu mamaki da tu'jibi sun yi matukar tafiya dashi tambayar kasan yakeyi 'shin me ke faruwa mai ya saka bahijjat cikin wannan yanayi har ranta ke kokarin fita daga  jikinta tabbas ba banza ba in har ba wani abu akayi mata ba to akwai abin da ta gani Wanda ya firgita da hautsuna mata kwanya' ajiyar numfashi yayi mai karfi sannan ya juyo ya dubeta har yanzu ta na cikin wannan halin ba alamun wani motsi a gareta hakan da ya gani ya kara tsorata shi ya kara gudu na fitar hankali gani yakeyi kamar wa zai iya zuwa asibitin da yayi niyar ba gani yake kamar ba gudu yakeyi ba  gabadaya jikinsa yayi jagaf da gumi yarda kasan Wanda aka sa wani mugun aiki mai Dan karan  cikin lokaci kankani ya isa asibitin malam aminu kano tun daga bakin get ya yi parking motar sa ba tsaya Neman malaman asibiti ba ya bude gidan baya ya sunguma hejat yayi cikin asibitin da ita da gudu tun daga bakin get mutane ke bin sa da kallo cikin halin tausayi da jajantawa don sun San tabbas ba kayan kwanciyar hankali ga duk Wanda ya shiga cikin wannan yanayin har yadanganta da asibiti ya na isa harabar asibiti a lokacin wani babban likiti ya fito shi kuma da alamun akwai in da za su ganin mubasheer ya  sanya shi saurin tsaya ya shiga duban sa har ya iso gareshi da sauri likitin tan ya tare shi da cewa"yaya dai malam meke faruwa ne?"ai mubasheer ka sa magana yayi kawai dire ta yayi gaban likita jikin sa nq karkarwa ya shiga nuna masa bahijjat yana son yin magana amma ina maganar taki yuwu wa hakan da likita ya gani yayi saurin Kiran wasu nas guda biyu tare da basu umarni su taho da keken daukar marasa lafiya cikin lokaci kankani suka dawo suna gunguroshi likita ya yayi wa mubasheer nuni da ya dauke ya dorata akan keken amma bisa yanayin da ya shiga ba zai iya ba dole sai nas sukayi wannan taimakon gangawa da gudu suka gunguwa ta sukayi ciki bangaren taimakon gangawa suka nufa da ita(emergency) cikin kankanin lokaci likitoci kusan su gudu suka hadu akan ta domin samun daidatuwar numfashi ta aka Sanya mata abin taimakawa tafiyar numfashinta (oxygen) domin ya daidata zuwa matakin da ake bukata mubasheer tun da aka shigar da ita yaka sa zaune ya kasa tsaye duk da abin da likitan yace masa na ya kwantar da hankalin sa in Allah ya yarda komai zai daidai ta amma ina ya kasa bai zai iya ba gani yakeyi kamar bahijjat mutuwa za tayi in kuwa haka ta kasance shi kam ya ga takansa domin kuwa yasa bashida mafita ko madafa akan mutuwarsa don ya San tabbas shi za a dorawa alhakin kisan kan za a iya cewa shiya kashe ta bisa lakari da shi ba kowan kowa bane agareta ba wata alakace a tsakanin sa da ita ba ya San kuma asirin sa zai iya tonuwa don komai zai ya faruwa don sai abin cika yarda akayi ta rasa ranta ko da yake matakin direba a gareta ba zai hana a tuhume shi ba.kai ya shiga girgiza zawa kamar Wanda aka gayawa  mutuwar mahaifiyar sa yake kokarin karya tawa hannun sa duk biyu ya hada yana bugun sa ya na numfarfarshi yakai gwauro ya kai mari haka ya cigaba da yi tsayin lokaci yana duban kofar dakin da aka shigar da bahijjat amma ina ba wani alamun za abude hakan yana kara tayar masa da hankali matuka. karar budar kofar ce ta dawo dashi hayyacin sa ya baro duniyar tunanin tashin hankali da sauri ya durfafi kofar jikin sa na 6ari ya na isa likita daya na sanyo kai waje da azama mubasheer ya cakumeshi likita"ya ake ciki,ta farfado kayi min magana likita wani hali bahijjat ke ciki"dau gumin da ke karyo masa ya fara yi kafin yace"kwantar da hankalin ka komai ya zo da sauki da izinin allah"ajiyar numfashi yayi sannan yace"zan iya ganin ta likita?" Girgiza masa kai yayi"a'a saboda yanzu tana cikin halin bukatar natsuwa dalili kuwa kwanyarta firgita tayi sanadiyar haka zuciyar ta ita ma ta tsorata"cikin rashin fahimta mubasheer ya shiga duban likita mamaki dauke a fuskarsa "ban fahimta ba likita don Allah fiddo ni cikin duhu kai na ya kulle ban gane zancen da ka keyi min ba" riko hannunsa likita yayi gami da matsala alamun ya dawo cikin hayyacinsa ya nisa"ba wata matsala bace mai karfi wacce za tayi nasarar tayar da hankalinka ba kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka" cikin yanayi na rashin yarda mubasheer yace "amma dai matsalar akwai ta ko au ita matsala ba karama ba babban duk matsala matsala ce" gyada kai likitan yayi gami da murmusawa don ya lura har yanzu bai yi amanna da abin da ya gaya masa ba hakan ya sanya shi cewa"eh akwai matsala amma.." da sauri ya katse shi"amma me kawai kace matsala ta tabbata ka daina wani walagigi da abin da zaka ce mani"murmushi likita ya sake yi gami da dafa kafadar mubasheer" akwai abin da tagani ya tsorata ta wanda yayi mata zuwan bazata duk shi ya sanya cikin wannan halin har numfashin ta ya dauke amma komai ya dai data yanzu in Allah ya yarda yanzu barci takeyi amma in ta farka normal za ta dawo"a bazata murmushi yayi wa fuskar mubasheer tsinke ya shiga duban doctor cikin alamun son bayyanar jindadi"har naji natsuwa dake kokarin guduwa tafara dawowa gareni" gwalo doctor yayi gami da cewa"au ita natsuwar har guduwa takeyi" "sosai ma kuwa sai da baka shiga halin tararrabi bane doctor" gyada kai yayi sannan ya riko hannun mubasheer suka nufi ofishin sa.
***  ***  ***
Sama da awanni biyu bahijjat ta kwashe amma ba alamun za ta farka tun mubasheer na hakuri har hakurin sa ya fara karewa tagumi ya zabga hannaye biyu idanunsa kuri kan kofar dakin da bahijjat take tun da yadawo daga ofishin doctor ya neme wajan zama a nan saboda doctor bai bashi izinin shiga ba har zuwa wannan lokaci tashi yayi tsaye ya shiga kai wa dakomowa kamar Wanda aka tsikara wa allura haka ya zabura tunanin mahaifin bahijjat ya fado masa cikin rai ya san izuwa wannan lokaci yana can yana rububin cigiyar in da su ka fada yanzu meye abin yi tambayar da yayi wa zuciyarsa kenan kai ya daga sama kamar mai son tuno wani abu da ya shige masa duhu kamar daga sama yaji an dafashi da sauri ya juya don ganin wanene doctor ya gani ya yi masa kuri da idanu da sauri cikin barin baki yace"ya dai doctor ta farfado ko?" dariya yayi masa sannan yace"wai mai yasa kafiye shiga firgici ne kana matsayin namiji gaskiya kana shirin ba da maza" sosa keya yayi sannan ya dubi doctor yana yak'e"kadai doctor kawai ayi sha'ani ni kadai nasan tashin hankalin da zan shiga in har bahijjat ta shiga wani hali na rashin armashi"cikin rashin fahimta zancen sa doctor ya dubeshi"ba matarka ba ce?" tambayar tayi masa zuwan bazata don sai da yayi zillo kamar wanda aka tsikara ya gwalo idanuwa waje gaban sa ya shiga duka alamun rashin gaskiya hakan da doctor ya gani ya tabbatar akwai wata a kasa cikin nuna komai ba komai ba ya kau da kai daga Barin kallon mubasheer hakan ya ba mubasheer damar saita kan San cikin murya karyayya yace"ba mata ta ba ce yar uwa tace" murmushi doctor yayi don alamun rashin gaskiya sun gama bayyana ga mubasheer kawai dafa kafadar sa yayi gami dacewa"zo mu je ta farka" ba tare da ya tsinka ba ya bi bayan doctor cikin sanyi jiki gumi duk ya gama karyo masa a fuska a haka har suka isa cikin  dakin.zaune suka tadda ita ta hada kai da guiwa ba abin da takeyi sai zabga kuka da gunji da sauri mubasheer ya isa gareta ya zauna bakin gadon cikin alamun rashin kwanciyar hankali ya dube ta baki na 6ari"BAHIJJAT" yakira sunan cikin muryar son rarrashi da janjantawa ba ta dago ta dube bashi ba sai sautin kukan ta da ya karu hakan ya kara tayar da hankalin sa da sauri ya dubi doctor alamun son Karin haske yake yayi tare da margaya kai sannan yace dashi"tun da ta farka cikin yanayi na tsoro da razana dakyar muka samu ta daina shikenan kuma ta shiga kuka ba yarda ba ayi da ita ba amma yarda ka ganta a haka ko dago kai ba tayi juyin duniya anyi amma ina ba wani abu da ya sauya"gwalo idanu mubasheer yayi cikin fargaba yace"to me ya sa me ta mai ya sanya ta shi wannan yanayin?" Watsa hannu sama doctor yayi sannan yace"Allah Mani sani ga ka ga ta nan kila kai ta kula ka don mu dai mun yi iya bakin kokarin mu na taimako"juya wa yayi da sake duban bahijjat ya kira sunan ta wannan karon ba ta amsa ba sai dai ta tsagaita da kukan da takeyi hakan ya kara masa armashin magantuwa"bahijjat dago kan ki ki kalle ni" ba musu ta dago kan na ta Wanda ya rine yayi jajir hawaye sun yi wa fuskar tata faca-faca hakan ba karamin razana mubasheer yayi ba da sauri ya ja baya gami da sakin wata yar siririyar kara juyawa yayi ya dubi doctor shi ma shi ya ke kallo nufin sa doctor ya ce da shi wani abu amma ga bi sa alamu ba wata kalma da za ta fito daga bakin sa hakan ya sanya juyawa ga bahijjat"duk mai ya sanya hakan ta faru dake me ya San ya ki cikin wannan yana yi mai tattare da tashin hankali?"matsa idanuwa tayi wasu zafafan hawaye su ka kwaranyo mata ta dubi mubasheer da ya kafe ta da idanuwa yana sauraron abin da za ta ce dashi ta yi ajiyar zuciya mai karfi sannan tace"ta shi mu tafi gida mubasheer" zaro idanuwa yayi don bai taba zaton abin da za ta ce dashi ba kenan ya saki jiki da baza kunnuwa domin jin abin da ya sanya ta cikin wannan yanayi amma sai ya ji sa6anin haka"ba abin da nake bukata ba kenan da ga gareki so nake nasan matsalar da ta assasa miki shiga halin rudu"kau da kan ta tayi daga Barin kallon so zuciya sai faman ta farfasa take da suya ji take kamar za ta faso kirji tafi saboda tsakar takaici da bakin ciki da yayi wa zuciyar katutu kan ta yayi mata wani mahaukacin nauyi kamar an daura mata dala da goron dutse "mubasheer ba na bukatar ka sake yi min tambaya makamanciyar haka kawai ka bar ni" yanayin haushi ha bayyana a fuskar sa "dalili mai ya sa za ki ce da ni haka,? na dauka Ina da matsayin sanin duk wani abu da ya same ki na dadi da akasin sa..." da sauri ta tare shi cikin yanayi na rashin son jin kalaman sa a zafafa tace"in ka na yi wa Allah ka tashi mu tafi ka mai da ni gida"mamaki ne ya cika shi baki ya saki ya na duban ta shi mq kan sa doctor da ya zuba musu idanuwa ya fara shiga tararrabi akan ta ko dai matsalar hankali ya ke kokarin samun ta don ya lura ta fara zafi zafi da sauri ya ta shi ya iso gareta cikin muryar rarrashi yace"bahijjat bai ka mata ace kina cikin wannan halin ba kuma kina halin ba ace kuma ina irin haka sai ki kara sanya kan ki cikin rashin kwanciyar hankali" shi ma katse shi tayi "ka ga doctor in har ka gama abin da ka keyi min kawai sallame ni in kuma ba zaka sallame ni ba ni zan tashi na sallami kai na da kai na" ta na gama fadin haka ta shi ga kokari tashi amma bi sa alamun jikinta ba kwari sosai sai ma jiri-jiri da take gani hakan bai sa ta saduda ba ta mike hannun ta rike da karfen gado.sakin baki sukayi duk kan ninsu aka rasa mai yi mata magana akan abin da take kokarin aikata wa har ta fara kokarin Barin dakin a nan ne mubasheer ya kasa hakuri da sauri ya taso ya tsare gaban ta cikin fuskar shanu."wai wani irin taurin kai gareki bahijjat da alamun ba kya gudun haifar da matsala da kan ki cikin rayuwar ki?" Tsaya tayi tana duban sa ba tare da tayi magana ba kuma ba sa yanayin da take sam!ba ta da niyyar cewa komai idanuwa tashiga matsala ruwan hawaye na gangaro wa hakan da mubasheer ya gani ya kara bata masa rai"bahijjat mai ya sa wai kike kokarin dauko wa kan ki wahala cikin rayuwa ne?"nan ma ba ta ce komai ba dago idanuwan ta tayi wadanda suka kasa sukayi jajir ruwan hawaye jage-jage ta ja hannci sannan ta nisa"mubasheer ka mai dani gida tun kafin bugun zuciya ta ya tu'azzara ya kai ni ga faduwa kasa matacciya"furucin ta yayi matukar karyar da zuciyar mubasheer bisa la'akari da yarda tayi maganar cikin muryar kuka da ban tausayi.gyada mata kai yayi gami da matsawa ya bata hanya ba tare da yace da ita komai ba ya bi bayan ta har ya kai kofa don ita tuni ta fice ya juyo ya dubi doctor da ya ke zaune ya na kallon ikon Allah yace dashi "afuwan doctor ka tsumaye ni ina dawowa please" murmushi yayi masa gami da gyada kai hakan da mubasheer ya gani ya bashi tabbacin doctor ya amince jinjna hannu yayi alamun godiya da sauri ya juya ya fice yana isa ya tadda ita tsaye bakin reception din asibitin sai rarraba idanuwa take kamar mai son hango wani Wanda ya bace mata muryar mubasheer ni tayi mata tsinke da sauri ta juya ta dubeshi gami da kau da kai fuskar nan tata a jagule kamar wacce aka aikowa da sakon iyayen ta duk sun mace. ganin irin kallon da tayi masa shi ma sai ya ba banza ajiyar ta ya doshi in da yayi parking din motar sa yana isa ya bude ma zaunin direba ya shiga ya ja kofa ya kulle hakan da bahijjat ta gani ya sanya sauri ta isa wajan motar gidan baya ta bude ta shiga ba tare da ta ce da shi wani abu ba ta na shiga ya fizgi motar su ka bar harabar asibitin.tun da su ka cilla titi ba Wanda yayi kokarin tsinkawa cikin su kowa ka kalli fuskar sa ba alamun wata fara'a musamman Bahijjat wacce gabadaya fuskar ta canza launi har wani jaja da kore-kore takeyi idanuwan kuwa ba a maganar su yarda kasan an dama barkono aka zuba matashi acikin idanuwan gwauron ajiyar numfashi tayi wamda har sai da hawaye suka gangaro mata samman kunci duk abin da takeyi mubasheer na kallon ta amma magana ta gagara yayi mata tafiya sukayi sosai har sun kusan isowa gida daidai makarantar malam aminu kano legal mubasheer ya ja burke ya tsaya ba har zuwa lokacin ko duban ta bai yi ba ya kashe motar ya hada kan sa da sitiyari kamar mai son yin barci alamun ke nan ko a nan za a iya kwana duk abin da mubasheer yake yi bahijjat duk ba ta kula ba saboda duniyar tunani da ta afka tayi ni San zango sosai karar mai adaidaita sahu ne da ya gilma ta kusa da shi ya katse mata tunani firgigit ta dawo hayyacin ta ta kai duban ta ga mubasheer cikin yanayi na fiddo ido alamun tsoro duk azaton ta hatsari sukayi nan ta shiga sallallami da ambaton ta shiga uku da sauri ta kai hannunta ta na kokarin ta6a mubasheer shima a daidai lokacin ya dago kan sa karaf ya kama hannunta ya na kokarin ta bashi ya juyo da idanuwan sa ya watsa mata kallo Wanda yayi matukar Bugar mata da zuciya amma sai ta kinkimo jarumtar duniya ta yafa wa kan ta ba ta bari ya gane hakan ba kallon ta sosai yayi ita m idanuwa ta zuba masa ganin da tayi bashi da niyyar sakin ta ko ya ce wani abu sai tayi kokarin tsinkawa kau da kan ta tayi daga Barin kallon sa sannan ta nisa"lafiya ka shanyamu bakin titi sai kace kayan sai dawa?" Shiru yayi yana sauraro har sai da ya ji ta datsa aya sannan ya shima ya nisa"ki nafin a haka za mu isa gida mahaifin ki ya jidadin tabbatar da abin da yake zargi a kai na" da mamaki falla a fuskarta ta dubeshi jin abin da ya ce da ita"ban fahimce ka ba ?" "au ba za ki fahimce ni ba ni dai don allah ki gyara fuskar ki don wallahi ba zamu da wannan fuskar taki kozai-kozai da ita ba"
gyada kai tayi don tabbar maganar mubasheer kan gaskiya take don ta San tabbas dole Abban ta yayi zargin wani abu in har ya hanya haka cikin halin damuwa cikin sauri ta cire mayafin kan ta ta janyo gorar ruwan da tagani gabar motar ta balle murfin ta zura kan ta ta kofa ta wanke fuskar ta gas! Sannan ta tsane da mayafin ta gani tayi ya cillo mata jakar ta kallon su tayi don ta San abin da yake nufi bude jakar tayi ta dauka kayan make-up ta gyara fuskar ta sosai yarda kasan ba wani Abu da ya taba samun ta na dabuwa sai dai idanuwan ta za su tona mata asiri don har yanzu suna cikin kalar ja "mu tafi" abin da tace dashi kenan bayan ta kammala komai sai da ya juyo ya ga yarda tayi sannan ya tayar da motar ya dauki hanya cikin mintina dalilin su ka isa unguwar su ta dorayi a daidai kofar gidan sukayi parking tun daga cikin mota bahijjat ta hango mahaifin ta yarda ya zuba ma motar ta su ido hakan ya sanya gaban ta bugawa da sauri ta fito tayi wajan sa cikin yanayi na 6arin jiki ta na isa gareshi ya tare ta da cewa...
Heyy wai ya dai na ji ku shiru ne anya tafiyar nan za tayuwu😠😠😠😠

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now