DUNIYARMU-33

354 16 0
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA

BABI NA TALATIN DA UKU.

Dsp ne ya nisa cikin tsananin tashin hankali ya dubi Saudat wacce ta gama ficewa daga natsuwarta tausayinta ya dalsu a zuciyarsa jin irin rayuwar da tayi mai cike da kayan tashin hankali da rikita tunanin wanda ya ji labarin.
"da wannan dalilin kenan kikayi amfani kika kashe su?".
Dsp ya fadi cikin murya mai cike da Tuhuma.
Shiru tayi kamar ba za tayi magana ba can ta nisa ta ce,
"Na rasa hanyar da zan bi ne domin ganin sun daina, na iyakar kokarina amma kamar kara tunzura su nakeyi, kuma ni kaina rayuwata ta shiga cikin wani hali wanda na kasa bambance kaina a matsayi yar Adam domin kuwa sai da na kasance kare ma yafini Albarka cikin duniyar rayuwata mutane da yawa kallon kalar iyaye na suke mani gani suke kamar nima haka nake an sha kawo min hari da banzan harkar maza da mata amma ban yarda ba domin nasan hakan ba karamin naskatamin rayuwa zai yi ba, duk da dai nasan rayuwata a lalace take domin rayuwar da nayi da iyayena ba ta da amfani komai a gareni zaman garinmu sai da ya gagareni domin ko fitowa nayi yara ihu suke min suna tsinemin tare da iyayena hakan ya kara kunci cikin duniyata, nan na tattara inawa inawa na baro gidan iyayena na samu waje na daban na kafa wata rayuwar wacce ashe ban sani ba bakar rayuwa na gaba ashe da yawa mutanen da suka san abin da ya faru da iyayena su na biye dani da wani KAZAMIN BURI nasu ban ankara ba sai da sukayi wa rayuwa ta illa sosai ta sanadin su na fara harkar fashi domin na lura rayuwata ba ta da wani amfani cikin duniyar nan kare ma ya fini arzuki ban yi nadamar abin da na aikata ba ban yi dana sani ba domin nasan ko mai ya faru dani IYAYENA NE SILA".
dakin ya dau shiru sosai kowa zuciyarsa sai harbawa take cike da tsananin mamaki da Al'ajabin labarin Saudat, kusan minti sha biyar suka shafe a haka, ba wanda ya tanka a tsakanin su sai da Dsp yayi gyarar murya sannan yace,
"ki na ganin hukuncin da kika daukarwa rayuwarki shi ne daidai a tunanin ki".
Cikin jarumtar zuci ta dube shi idanunta cike da hawaye.
"shi ne yafi cancanta dasu wallahi domin ban ga amfanin iyaye irin nawa ba in da nasan rayuwa haka zata kasance dna roki Allah bai halicce ni cikin duniyarnan ba domin ba abin da ke cikin ta sai tashin hankali da son zuciya da kazamin buri kowani dan 'adam ka gani cikin duniyar nan da yawa cikinsu son zuciya da buri ke hallaka su, ni nasan haka kai ma kasani. don haka ni bana wani da nasanin aikata abin da na aikata akan iyaye. barin su cikin duniyar nan ba karamar illa bane. don Allah kadai ya san mutanen da suka jefa cikin BAKAR RAYUWAR da suke yi, mutuwar ita tafi dacewa da su".
Baban Salma ne ya muskuta cikin yanayi na kara tsorata, da duniyar nan. ya dubi Salma cikin tausayinta da BAKAR ƘADDARAR da take gani a rayuwa.
"Iyaye fa aka ce miki, ko mai sukayi ba a taba canza su a iyaye".
Da sauri ta tari hanzarin sa.
"ai ba wai na canza su a iyayena ba ne, a,a ko daya, kawai dai gani nayi rayuwar ta su ba ta da amfani ko daya a garesu har dani ma kuma, ba ni da wata hanyar da zan bi don fiddo su daga bakar rayuwar da suke ciki nayi iyakar kokarina amma abin ya ci tura shiyasa kawai naga mutuwarsu shine abin da ya fi cancanta a gare su".
Shiru yayi, yana jin yarda take maganar cikin iyakar gaskiyarta, har kasar zuciyarta. kai ya shiga gyaɗawa yana mai duban Dsp da shima yake cikin wani yanayi na rashin abin yi. Shukuranu kuwa ba a maganar sa fargabarsa ce ta karu matuka, zuciyarsa sai faman zillo take tunaninsa daya Allah yasa Salma dinsa ba ta cikin jerin yan fashin domin ya lura da Saudat, komai za ta iya aikatawa duk wanda ya kashe iyayen sa da suka kawo shi duniya aikuwa zai iya kashe kowa...
Maganar Dsp ce ta katse masa tunani, da ya ji yayi batun Salma. da sauri ya dago kai ya shiga duban sa yana kallon bakinsa da maganar da yake yi.
"Lamarinki Akwai daura kai ni na rasa ma ta ina zan fara, da Al'amarin naki...ba ma wannan ba, yanzu ki sanar damu in da zamu samu Salma domin fiddo da ita".
ba ta dube su ba tashiga kora musu bayani akan Salma da irin cin kashi da BAKAR IZAYA da ta dinga gana mata.
ba karamar razana Shukuranu yayi ba, don ji yake kamar ya tashi ya makureta ya kashe banza, don bai ga amfanin ta ba, cikin duniyar nan ita ANNOBA CE.
Baban Salma da Dsp ne suka fara kokarin tashi, bayan sun mike Dsp ya dubi Saudat.
"za mu tafi domin daukota, kafin ke kuma mu zo domin sanin abin yi game dake".
ko kula shi ba tayi ba, illa kara abin da take tunanowa azuciyarta hukuncinta bai wuce kisa ba, ita kuwa a shirye take domin mutuwar, ita ce za ta fi dacewa da ita, da zaman wannan duniyar ta wannan zamanin rikitacciya.
Ba wanda ya sake tsinkawa tsakaninsu, suka mike dukkan su cikin yanayi na sanyi jiki matuka, da kara tsoron lamarin duniya. Dsp a gaba sai Abban Salma sai Shukuranu bayan su kuma kurtun da ya rako su ne, kallo daya zakayi masa ya baka tausayi da alamun LABARIN SAUDAT yayi matukar girgiza masa zuciya da ruhi, idanuwansa sun kaɗa sun yi jajir kamar mai shirin fashewa da kuka, a haka har suka fice daga cikin dakin Dsp ya kargama kwado kamar yarda ya saba, sai da suka biya Office din Doctor, Kamal ya ba shi dan key tare da Umartasa da ya je ya duba Saudat, ba karamin mamaki yayi ba amma bai bari haka yayi tasiri a zahirancen sa ba, domin ya lura duk jikinsu yayi sanyi da alamun akwai abin da ya faru ya haifar musu da hakan. Dsp suna barin Asibitin Doctor,Kamal ya kwasa a guje kamar wanda aka cewa in har bai je ba to a bakin aikin sa. tun kafin ya isa ya kira Nurses su uku domin su taimaka masa, don ya san aiki ne gundumeme za suyi da azama su isa, ya saka key din ya bude suna tura kai kamar ko yaushe in sun samu sa'ar Dsp ya bar su sun shiga. warin kafar Saudat ke musu maraba yau ma haka ce ta kasance. nan ko wannan su ya sanya hankicif ya toshe hancin sa. a haka suka isa gareta, kan ta nakas. ba abin da take yi sai zubar hawaye, da shassheka kamar ran ta zai fita hakan ba karamin rauni ya sanya wa zuciyoyin su ba. musamman Nurses din wasu har da yar kwalla domin Saudat taci ace an tausaya mata a cikin halin da take domin lokaci guda ta zabge ta rame kamar ba ita bace mace mai kamar maza mai dakakkiyar zuciya ba ta fargaba ko wani tsoro na duk wani dan'adam na duniyar nan. amma wai ita ce yau a haka rayuwa kenan kana taka Allah na nashi kuma kowa yayi dakyau zai ga da kyau cikin duniyar sa, abin da zuciyoyin su ke ta fadi kenan.
Cikin dan kankanin lokaci Doctor,Kamal yayi duk wani taimakon da ya san zai iya yi mata, a matsayin sa na likita, don ya lura dole ne sai an yi mata dauri kafin a kula da sauran ciwunwukan da suke jikin nata. wani irin tausayi yaji yana ta kaiwa zuciyarsa da kasar Ruhin sa farmaki mai tsanani, domin daurin da za ayi mata ba karamar azaba zata sha ba. lokaci guda ya ji idanuwansa sun kawo kwalla da sauri ya sanya hankicif da ya toshe hanci dashi ya dauke su ba tare da ya bari wani cikin su ya gani ba.
Ihu take zundumawa lokacin da Doctor,Kamal ke saka hydrogin yana goge mata ruwan dake fasowa daga jikinta, da bushassahan jinin da duk ya samu wajan zama jikin kafafuwan nata, hakan ya kara mata wasu sinadaran ciwukan ba wai zafin wankin take ji ba a,a kawai yanayin da take ji in an taba kafar ne ke haifar mata da wani irin zugi da raɗaɗi, ji take kamar a sassara kafar za ta fi samun salama. da wannan zafin da yake hawa mata har kai da kasar ruhi ji take kamar a na yinkurin zare mata numfashi. Sunyi matukar kara jin tausayinta, jin irin ihun da take zundumawa nan da nan zuciyoyin Nurses din ta kara karaya, hawaye suka shiga zuba a idanuwan su a haka har suka kammala amma ba ta daina kuka ba. magani ya dauko ya mika mata amma sai tayi banza dashi gami da kau da kan ta gefe. saida yayi da gaske sannan ta amsa ta hadiye girgiza kan sa yayi gami da tashi daga bakin gadon da take. ya dubi Nurses tare cewa su tafi yana gaba su na bin sa a baya, har suka fice daga cikin dakin. zuciyoyin su sai harbawa suke cikin matsannancin tausayin Saudat.
-------@@@--------
Tafiya mai dan nisa sukayi sannan suka isa Unguwar daji. nan Dsp ya shiga bin kwatancen da Saudat tayi masa, ba su sha wani wuya ba suka gane gidan. sai dai sunyi matuka lokacin da suka ga gidan, domin tunda suka shigo Unguwar ba su ga gida wanda ya kai shi kyau da tsare ba, yafita daban cikin Uguwar. Parking sukayi suka fito suna lura da mutanan layin sai kallon su suke, kamar sun ga bakin fuskoki. ko da yake duk abin da aka ga ya danganci jami'an tsaro dole a zuba ido, domin an tabbata akwai abin dake faruwa. Dsp ne ya kwankwasa gidan, domin ta sanar dashi tana da maigadi. sai da ya kwankwas sau uku sannan yaji ana tambayar 'waye ne'. daga can cikin gidan. Dsp yace "bude ka gani mana, bakin uwargijiyar kane".
Shiru ya ziyarci wajan, kamar ba wanda zai sake magana. can sai kuma aka fara kokarin buɗe get din. wani matashine wanda ba zai haura shekara talatin da biyu ba, ya wanzu a gabansa. kallo daya zakayi masa ka gane shima tattire ne, wani irin kallo ya shiga yi musu, lokacin da ya ga Dsp cikin kaki ba karamar razana yayi ba, da yake dan duniya ne sai yaki nuna hakan a zahiri, sai yaƙe da ya shiga saki kamar wanda aka yiwa dole. nan suka gaisa yana faman bin su da kallo, har suka shiga cikin gidan sosai. nan suka kara tsinkewa da lamarin gidan, domin ba suyi tsammanin cikin gidan ya kai haka ba, gida ne sosai wanda za a iya kiransa da ALJANNAR DUNIYA. domin komai na more rayuwa ga shi nan birjit, kamar ba gidan mutum daya ba. Dsp ya dubi yaran sa da ya zo da su, ya ba su umarnin duk su zagaye harabar gidan, lunguda sako shi kan sa maigadin ram akayi dashi. nan da nan hankalin sa ya kara tashi, ya firgice ya tabbatar dara ce ta ci gida yau. Dsp ya dubi sauran yaran nasa tare da su Shukuranu, yace su biyoshi cikin gidan.
Da kansa ya bude kofar falon ya sanya kai ciki. Baban Salma da Shukuranu wata irin faduwar gaba ce ta ziyarce su, ba abin da suke ambata sai 'Innalillahi wa inna ilahir raji'un' a haka har suka isa cikin falon. sosai faduwar gaban ta su sai karu take yi, hakan ya haifar musu da wata irin kalasa ji suke kamar an bubbuge musu gaɓoɓi. Dsp ne ya sanya sauran ya rasa biyu su fara bincike cikin nan falon, shi kuma ya yi cikin sashin ba tare da kowa ba, don cewa yayi su Shukuranu su jira shi nan. ya shiga bincika sakokin gidan ta ko ina har Toilet da su Store sai da ya caje, amma ba alamun mutum. amma duk da hakan bai karaya ba, ya cigaba da shiga cikin ko ina har yakai wani sashi, in da dakuna uku ke jere duk kuma a kulle suke. iya yinsa sai da yayi, amma ya kasa bude ko da daya ne, tsayin lokaci ya shafe yana gwada dabararsa amma ba wani cigaba. fita yayi daga cikin sashin, kicin ya nufa domin samun wani abun da zai bige kofar. aiko ya ci sa'a ya samu wani karfe murtukeke ya dauko ya fito cikin sauri, ya na isa ya shiga bugun dakin farko nan da nan ya bude, amma ba kowa a ciki. nan ya koma daki na biyu nan ya buge, kaya ne ya ga makil aciki nan ya shiga bincike, nan ya gano kayan da suke fashi ne da su suke ajjewa a cikin da duk wani sirri nasu, tsaki ya ja domin ba abin da yake so ba kenan fitowa yayi ya nufi dayan dakin amma sai ya ga yanayin da aka kulle shi ya bambanta da saura shiru yayi yana tunanin ta in da zai fara sai da ya gama karantar kofar sosai ya gane makwancinta sannan ya shiga bugun inda yake tunanin tanan kawai zai isa samun damar bude kofar bugu sosai yayi don sai da yafara fidda rai da buduwarta ya hada gumi kasharban kamar wanda yayi gudun ceton rai jijiyonsa kwanjinsa duk sun mimmike sosai komai na mazantakarsa ga shinan ya nuna alamun karfin kwanji ne tsantsa ya bayyana sai faman numfarfashi yakeyi wani wawan bugu yakai wa kofar cikin tsananin karfi, take kofar tayi fitar burgu tayi cikin dakin wata irin ajiyar zuciya ya saki tare da kai idanuwansa cikin dakin duhu ya gani ba alamun wani haske a cikinsa sai dan kalilan na wajan da yake da ya haska. rarraba idanu yake yi sai ka rantse wani abu zai gani da hasken idanunsa amma ina ba abin da ya hango ko da kuwa alamun akwai wani abune a ciki, mamaki ne ya cika shi ganin duhu sosai ya rasa ya akayi hakan ta kasance bayan sauran dakunan ba haka bane nan zuciyarsa ta fara tunkudeshi da ya shiga ko lalube ne yayi cikin duhu da sauri ya bi shawarar zuciyarsa ya tunkari cikin dakin har yasanya kafar shi daya a ciki, sai kuma yayi saurin jan birki jin wani bangare na zuciyarsa na gargaɗin sa da kar yasake ya shiga cikin duhun nan don bai san abin da zai tadda a ciki ba hannusa ya saka cikin aljihunsa ya zaro wayarsa ya kunnan fitilar wacce ta ke da dan karan haske ya wulla hasken cikin dakin nan take haske ya gauraye ko ina na cikin sa. can kusurwar dakin ya hango tulun abu wanda yake da yakinin wani kullin ne akayi a ciki aka boye da sauri cikin jarumtar zuciya ya fada cikin dakin ba inda ya nufa sai inda zuciyarsa ke sanar dashi yaje yana isa ya sanya hannu domin dogo tulun abun domin ya gana menene amma ina hannusa ne ya tsaya cak tare da duk wani waje dake motsi ajikinsa kwakwalwarsa da zuciyarsa hatta ruhinsa sai da yayi sumar wucin gadi lokaci guda idanuwansa sukayi wani irin fitowa kamar za su fado kasa bakin sa na rawa ba abin da yake ambata sai 'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un' kusan minti biyar ya shafe cikin wannan yanayin kafin ya kokarta ya kinkimo jarumta tun daga zuciyrsa da yaji tana kokarin shiga firgici ya yafawa kan sa gami da sakin wata nauyayyiyar ajiyar zuciya durkusawa yayi gami da yaye abin da yayi wa fuskarta shamaki a daidai lokacin cikin wani irin mawuyacin hali ita kuma ta dago kai sai da ya ja baya ganjn fuskarta ba abin da yayi mara ba da kwarankwal sai fama da idanuwar da suke motsi gabadaya duk wani kwarmi najikinta ya bayyana jikin fatarta idanuwanta kuwa ba ka iya ganin kwayarsu ido ya kura mata sosai gabansa sai dukan uku-uku yake yayi matukar tsora in ba wai don ya ga bata da wata suffar da ba ta bil'adam bace zai iya rantsewa da Aljanna ce wannan ba mutum bane da sauri ya mike cikin matsanancin tashin hankali yayi waje da sauri ba tare da ya taba ta ba jikin sa sai kyarma yake idanuwansa sun kada sun yi jajir gabadaya hayyacin sa ya fara ficewa daga cikin sa da taimakon Allah ya isa falon inda ya tadda su carko-carko yanayin da suka ga Dsp ba karamin razan sukayi ba matuka musamman Shukuranu domin kuwa kamar wanda aka tunkuda sai gashi gaban Dsp jiki na rawa.
"don Allah kace min ka ganta kuma ba abin da ya faru da ita don Allah karka sanar dani mummunar labarin da ba zan iya daukarsa don Allah ko kalma daya kar ka fada min ita in har kasan zata tarwatsa min sauran natsuwata da zuciyata take kalatomin".
Yanayin da Shukuranu ke magana ba karamin tashin hankali bane ya sake ziyartar Dsp kai ya shiga gyadawa kamar mai kokarin fashewa da kuka.
"Na tadda da ita...".
wata irin zabura Shukuranu yayi kamar zai shige jikin Dsp ya rike masa hannu yana mai zubewa akasa cikin yanayi na rashin hayyaci.
"kace min tana raye ba a mace ka same ta ba ka sanar dani ka ganta da numfashi ba wai ya fice daga jikinta na roke Yallabai".
ya karashe maganar ya na mai zuvda kwalla kamar jira yake yi dama Dsp ya dawa ya shiga rusa kuka.
"Shukuranu".
Baban Salma ya fadi lokacin da ya iso wajan da Shukuranu da Dsp suke tsaye kallo daya zakayi msa ka gane kawai ikon Allah ne ke tsare dashi in ba don haka ba da tuni yaje kasa saboda irin yarda jikin sa ke ɓari da karkarwa
"ya kamata ka nemo jarumta ko ya take ka yafawa kanka".
Abin da ya iya cewa kenan yana mai kallon Dsp kamar mai jiran yace masa ga Salma can amma sai ya ga Dsp na gyada kai kmar wanda akayi wa dole hakan ya karawa Baban Salma ruɗu da sauri ya shiga rawar baki yana mana mai girgiza kai saboda abinda zuciyarsa ke sanar dashi akan Salma girgiza kai yake yi domin kar ya gasgata zancen zucin nasa
"Tana ina!?".
Ya fadi cikin wani irin sauti kamar wanda aka shakewa wuya aka ce sai ya fadi kalmar.
Dsp ya fara kokarin saita kan shi yana mai sakin murmushi wanda daka kalla kasan kuka yafi dadi ya shiga gyada kai kamar kadangare.
"Na same cikin numfashi da rai a jiki".
Shukuranu ya mike a firgice cikin hawaye mai hade da murmushi wanda shi kansa bai san lokacin da murmushi ya samu muhalli ba a fuskarsa cikin rawar jiki da zakuwa yace,
"Ta na ina yallabai?".
"kwantar da hankalin ka zaka ganta".
Bai bari dayan su yayi magana ba ya dubi yaransa yayi musu nuni da mutum biyu su biyoshi da hanzari suka bishi ganin shima da hanzari ya fara tafiya domin ba ya so wani daya a cikin su yake tuhumarsa da tambaya Shukuranu ne ya mike cikin hanzari shima yana kokarin bin su da sauri Baban Salma ya riko shi ba tare da yace dashi komai ba ba yarda Shukuranu ya iya haka ya koma lagwas ya zube a kasa kamar wanda akayiwa dukan shan gishiri
Su Dsp na isa inda Salma take suka shiga kuratan na ganin ta ai sai suka zunduma ihu tare da yo waje a gudu har suna turereniya jikin su sai faman mazari yake yi zuciyarsu sai kaɗawa take yi don tsananin tsoro da firgici da sukayi wata irin tsawa Dsp ya daka masu tare da nuna su da hannu.
"becarefull".
Nan suka shiga sara masa suna neman abu ganin da sukayi ya dau zafi lokaci guda amma jikin su bai daina mazarin tsorata ba sai kara ja da baya suke yi don sun rantse ba abin da zai kai su wajan waccan Aljanar ka kawai ta kashe su a banza a wofi suna cikin wannan muhawarar da juna su sukaji ya daka mutsu tsawa nan suka fara kokarin arar ta kare sun dauka Aljanar ce ta iso garesu saboda tsananin tsoro da zuciyarsu ta fada.
"ku zo daga ciki domin mu fidda ita".
Ya fadi cikin yanayi na umarni yake ba su nan suka shiga ture-ture an rasa wanda zai fara zuwa a tsakaninsu hakan da Dsp ya gani ba karamin kona masa rai suyi ba cikin tsananin bacin rai gami da jan kwaɓa ya dube su tare da kau da kai ya isa inda take yashe ba alamun motsi ajikin ta wanda zai tabbatar maka da tana da rai haka ya sanya hannu shima zuciyarsa na ɗarɗar yana addu'ar neman tsari ya sunkuce ta wani irin wari ne da hamami su ka kaiwa hancin sa bugu wanda hakan ya san shi saura kadan ya watsar da ita a lokaci guda yaji cikin sa ya dauka ya fara hawa sama ba shiri ya kira daya daga cikin matsoratan da ya zo ya rufe masa hanci da hankacif din sa a ɗarɗar ya zo ya sanya masa tare da kulle wa shi kan sa sai da yaji kamar zai amayar da kayan cikin sa ya na gama daure masa ya falle da gudu abin har dariya yaso ya ba Dsp amma ya kanne ya shiga sauri domin zuwa ya ajjeta bawai saboda nauyi ba domin ji yake kamar ya dauki yaro dan shekara uku in da ma za a auna kila a tadda yaron da shekara uku yafita nauyi cikin wannan yanayin ya isa falo suna zaune su zabga tagumi suka kurtan nan su shigoa ruɗe sai faman waigen bayan su suke har sun tuntuɓe da sauri suka mike suna faman maza ido su ga ta inda Salma za tafito hango Dsp sukayi dauke da tulun abu nan da nan suka firgice ganin suffar mutum gata nan a bayyane sai dai ba marabar ta da GAWA DA RAI ai da gudu Shukuranu ya kwasa ya isa gaban Dsp yana kokarin kai hannu ya ga waye a hannunsa amma da sauri ya kau ce masa cikin hanzari ya durfafi kofar waje amma kafin ya kai Baban Salma ya tare shi a shammace ya zare mayafin da ya lullubeta ai ya na ganin fuskarta ya baje a kasa sumanme hakan ya ba Dsp damar karas ficewa ba tsaya ko ina ba sai cikin motarsu da sukayi Parking a waje ya dubi dan sanda guda daya ya ce yayi maza ya shiga ciki ya kirawo yan uwan da su Shukuranu shi ya tafi Asibiti su tadda shi acan yana gama maganar sa yayi wa motar key cikin wani irin yanayi ya fizge ta mutanan dake tsantsaye a halin suka bishi da kallo gudu yake yi kamar zai tashi sama yana hawa titi nan ma wani sabon gudun ya kara motoci da yawa sai kaucewa suka dinga yi lura da sukayi da motar jami'an tsaro ne kuma sun hango direban jami'i ne cikin mintina da ba su haura goma ba ya isa General Hospital Parking kawai yayi ya fito ya bude gidan baya ya sungume kamar wata yar tsana in ba lura kayi ba zaka ce wai mai rai bane a ciki gudu yake yi cikin Asibitin yana faman kwalawa likiti kira mutanan dake harabar Asibitin suka shiga dubansa ciki da mamaki yarda yake falla gudu kamar a filin tsare Nurses da suke rarrabe a cikin wajan su ma suka kwasa da gudu suka bi shi bai dire ko ina ba sai wani daki da ya kasance Emengency ya dire Salm a daidai lokacin likitoci kusan su biyar suka fado cikin dakin domin sun jiɓirin kiran da yake yi musu nan ya ba su danar suyi sauri su duba domin ceto ran ta yana magana jikinnsa na kyarma da sauri kuwa suka isa gareta su kan su sun tsorata a yanayin da suka gan ta nan suka cewa ya fice ya ba su waje tare da sauran Nurses da suka cika dakin ba don ya so ba ya fice amma yana like a bakin kofa sai faman Safa da marwa yake a daidai lokacin suka su Shukuranu suka iso dauke da Baban Salma wanda yayi dogon suma nan shiga aka karbe shi domin ceto shi Shukuranu yake a firgice ya durfafi dakin da ya tabbatar nan Dsp ya shiga da abin da ya dauko kuma ya tabbata Salma ce rike shi yaji Dsp yayi gami da girgiza masa kai alamun ba damar shiga ai kamar wanda yake jira ya sake shi sai gashi a kasa yayi zaman yan bori wani kuka ne ya kufce masa kamar karamin yaro ya shiga yin sa muryarsa ba sauti da alamun ta dusashe kallo daya zakayi masa ka tabbatar bayan tahowar Dsp ya ci kuka har ya gaji domin idanuwansa sun yi jajir duk sun kumbura...

Allah sarki rayuwa Shukuranu yo heart ix back now injoy happpy😁😁😁😁😁

IT'x Kamala Minna.😍😍😍

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now