DUNIYARMU

2.1K 81 2
                                    

DUNIYARMU

(c)Kamala Minna.

BABI NA BIYU
zaune yake gaban sa teburi ne girke mai dauke da duk wani dangin kayan maye  masu matukar firgita kwanya da zaunatar da duk Wanda yayi gigin shan su amma ga wajan wannan matashin Wanda yake jin shi duk yafi kowa jindadi rayuwa ba komai ba ne a wajan sa
a hankali ya kai hannu sa ya dauki karan sigari ya ban kamata wuta ya kai wa bakin sa farmaki ya zuka sosai har sai da yayi rabin ta sannan ya daga kan sa sama ya fesar da hakin cikin salo na gwanin ta da gwanancewa a harkar ya sake kai wa bakin sa far maki a wannan karon zuka daya yayi mata ya gama da  kara daya
ya dauki kwalba cikin kana nan kwalaben da ke zube gaban sa ya balle murfin ya shiga kwararawa cikin sa
a daidai wannan lokacin akayi knock din kofar cikin yanayi na fara ficewa daga hayyaci ya ba da izinin a shigo
a hankali aka murda kofar aka turo ta ciki  wata kyakyawar matashin budurwa ce ta bayyana wacce ashekarun ta ba zasu haura ashirin da biyu
Jikin ta dauke da wata riga doguwa mai kalar pink tayi matukar yi wa  jikin ta kyau
cikin salo na Jan hankali ta shiga taku ko ina na jikin ta sai kadawa yake yi kamar iska na kada itaciyar dogon yaro
a haka har ta iso wajan sa
cikin murya mai ciki da kissa tace
"SK mai yasa kake son firgita min rayuwa ne da gigintaccen son ka kasan ba Wanda na mikawa ragamar rayuwata da duniyata kamar kai na yarda da kai na amince da kai na mallaka maka rayuwata kayi yarda kake so da ita amma kai duk wannan SADAUKARWAR da nayi maka ba ka dauke ta wani abin yabo ba mai ya sa haka?"
ta kareshe cikin shagwa6ewar fuska kamar mai son fasewa da kuka
Izuwa wannan lokacin shi kuma kwanyarsa ta fara ficewa daga hayyaci cikin murya mai cike da yanayin maye yace,
"baby Teemah ina son ki duk wanda yace miki yaudararki nake karya yake"
ya kai hannu ya janyota jikin sa ya shiga cakudar ta kamar kayan wanki ita kuwa sai kara narkemasa take ajiki kamar mage.
Haka suka dau tsawon lokaci a haka, duk sun fice daga hayyacin su.
bugun kofar da akeyi ne, ya sanya su saurin dawo cikin duniyar hankalinsu
da sauri SK ya ture Teemah daga jikin sa ya mai cewa
"maza tashi ki mai da kayan ki jikin"
sakin baki tayi tana kallon sa kamar wata sau na mamaki ya cika ta domin  hakan bata taba kasancewa a tsakaninsu ba ko da kuwa ya na tare da wata daban ne amma mai ya sanya shi saurin firgita da tsoro haka don ta fuskanci yanayin tsoro tsoro a game dashi maganar sa ce ta katsemata tunanin ta
"cewa fa nayi ki tashi ki saka kayanki"
Ya fadi cikin daga murya mai zafi
ba shiri ta mike tare da kokarin sanya kayan ta amma  idanuwanta na kansa sai maka masa harara take, kamar idanuwanta zasu zazzago kasa.
bugun kofar aka cigaba dayi cikin sauri-sauri, kamar za a ajiye kofar gefe.
SK daga shi sai gajeran wando da singileti, ya mike ya sake duban Teemah,
"In har kina bukatar ki fita da ranki
Ki cigabada gara rayuwa yar da kike so to ki san yar da zakiyi ki ceci kan ki ga toilet can ki shiga ki kulle ko an buga karki yi gangancin budewa don in har kika bude taki ta kare"
ya fadi yana mai murmushi mai ma'anoni masu yawa
Teemah da tayi tsuro da idanu tana kallon sa tsoro duk ya gama cika mata ciki cikin azama ta Suri ta takalman ta  tayi hanyar toilet cikin sauri ta shige ta maka sakata duk SK na kallon ta sai da ya ga komai ya kammala sannan ya durfafi kofar ya na zuwa ya bude cikin yanayi na kissa ya fara mutsutsuka idanuwa alamun Wanda ya tashi daga barci
sanye take da wani dogon wando Wanda duk ilahirin sa roba ne yayi matukar kama mata jiki komai na jikin ta yafita tsaf!
rigar da ta saka mai kalar pink rabin kirjin ta a waje daga kasa ko cibiyar ta ba ta rufe ba hannun rigar siriri Wanda shi da babu duk daya.
ta dubi sk cikin yanayi na tuhuma sai yatsine fuska take kamar wacce tayi karo da wani abin kyama  cikin izza da Nuna gadara tace "kai da waye cikin dakin nan?"
da sauri ya juya idanuwansa cikin dakin sannan ya juye ya kalle ta
"Ni kadai ne me kika gani?"
girgiza kai tayi tare da murmushi
"Kar fa ka rai nawa kan ka hankali sk kana nufin kai ka dai ne a dakin nan tsawon awanni hudu da na barka aciki?"
Ya mutse fuska yayi tare da watsa hannu sama
"ke kam kin feye zargi wallahi,to nikadai ne cikin dakin kawai turara kai nayi na ban kawa ciki kayan masarufi shine fa na bingire ban tashi ba sai yanzu sanadiyyar bugun kofar da ki kayi"
tsaki ta ja gami da bangajeshi ta kara sa cikin dakin ko ina sai da tabi da kallo ko za ta ga wani abu da ya danganci abin da take zargi har gadon ta hau shinshinar zanin gadon tayi da Sauri ta dago kai ta dubeshi shi ma ita ya ke kallo duk ya hade fuska ya tsare gida alamun bai son wargi
"akwai wacce ta hau gadon nan saboda ga kamshin turaren EL-OPELO kuma na mata ne"
ta fadi ta na kokarin Sakkowa daga gadon gadangadan tayo kan sa ta duban shi tun daga babban dan yatsar kafar sa ba ta dire ko ina ba sai tsaki yar idanun sa
"wallahi tallahi ka kwanta da wata a gadon nan ko SHAKKA ba zan yi ba ka rantse da Allah ba ka kwanta da wata karuwa a gadon nan ba"
shiru yayi amma yanayi da ya nuna a fuskar sa yanayin rashin wasa ya tabbatar mata shakka babu ya aikata sai dai ba yarda zatayi dashi ba dan ta so ba ta tashi ta koma kan kujera ta zauna sai faman cika takeyi ta na batsewa yarda kasan zata tarwatse
"ka shirya mu fita domin ina bukatar hutu yanzu"
a gwale ya dubeta
"gaskiya hakan ba zai yuwu ba dalili kuwa nayi matukar gajiya ke ma in ba fitina da kulafici ba yanzu fa ki kadawo daga waje mai makon ki zauna ki huta shine zaki ce wai a fita to ni dai bani da ra'ayin fita yanzu in zaki hakura zuwa anjima to in kuma ba zaki iya hakuri ba zaki iya fita ke kadai don nidai ba zan fita yanzu ba"
Tun da ya fara magana ta zuba masa idanuwanta kamar zata lasheshi saboda tsatsanin haushi da takaici yanayin da ta fuskance shi cikin yan kwanakin nan duk SK ya gama canzawa daga yarda ta sanshi a da ta rasa dalili ta rasa mai ya haifar da haka amma ba komai ta san yarda zatayi zai sha mamaki ta.
cikin sauri ta mike ta suri jakarta tayi hanyar fita ranta bace
da sauri ya sha gabanta tare da zube mata idanuwansa da suka canza launi izuwa (sexy-eyes) hakan da tagani yayi matukar saukar mata da wani yanayi mai wuyar fassaruwa lokaci guda taji jikin ta ya saki zuciyar ta ta kara ya amma duk da haka ba ta bari haka yayi tasiri a zahirin fuskarta ba ta sake shan mur! Ta dubeshi cikin tsiwa "malam ka ga matsamin in wuce kaji ko nace ina bukatar Abu kace kai ba zaka iya ba na tashi domin in je Neman in da za ayi min amma kuma kana kokarin hanani mai haka ke nufi?"
kau da kai yayi tare da murmusawa yanayin da yaga tashiga ya tabbatar masa ta rigaya ta karaya amma sai yaki ba da kai ya matsa mata tare da Nuna mata hanya alamun ta wuce.
zukudi tayi masa da baki ta na duban sa zuciyar ta tayi matukar cika da mamakin halin da SK ya Nuna mata cikin wannan kan kanin lokaci anya ba wata a kasa kuwa ba wata makarkashi da akeyi.
gyada kai tayi tare da watsa masa wani kallo mai cike da ma'anoni masu yawa sannan ta sa kai cikin sauri ta bar dakin ta ja kofar ji kake gam!!!
SK ya murmusa domin kuwa ta kai makura wajan jin haushi sai dai komin fushi da zatayi ba zai dameshi ba don ya sa tabbas tayi bikon kan ta da kan ta domin kuwa yasan ya gama da ita ragamar rayuwarta gabadaya yana hannun sa sai yarda yayi da ita don kuwa dole ace da mijin iya baba wata mahaukaciyar dariya yayi har ya kai wa iska duka ya fada kan gado sai faman sheka dariya yake yarda kasan wani zautacce cikin hanzari ya miki ya zaro karan sigari ya ban ka masa huta ya zuka ya fesar da hayaki sama cikin salo na gwanancewa ya na gamawa yasake bankawa wata wuta ita ma ya shanye a haka sai da ya sha kara Biyar sannan ya koma ya kwanta.
a daidai wannan lokacin yaji an fara bugun kofar toilet kamar za a karyata da azama ya tashi Sam ya manta da Teemah a kulle cikin toilet da hanzari ya kara sa ya bude cikin sauri tayi waje ko kallon sa ba tayi ba ta bangajeshi tayi hanyar fita da Sauri ya shagaban ta tare da rike mata hannu ya zuba mata idanuwansa masu saurin narkar da zuciyar da ta fada komar sa
"meye haka kikayi sai kace wacce ta fara zare wa"
ban ka masa harara tayi sai faman hura hanci take kamar zata ci babu
"kasan Allah ka sakeni in kuma ba haka ba zan yi maka abin da baka taba tsammani ba wallahi"
ta shiga kokarin kwace hannunta amma ina ta kasa saboda rikon da yayi mata ba na wasa bane tayi yin duniya amma ta kasa nan ta fara matsar kwala hakan da SK ya gani ya sanya shi sakin ta domin shi a rayuwarsa ya ki jinin ya ga hawayen mace domin kuwa su na matukar tayar masa da hankali cikin Sauri ya tallabo habar ta yashiga goge hawayen da su ka fara zuba cikin salon kissa da taushin murya ya shiga rarrashin ta "yi hakuri Teemah ban yi haka don na cuce ki ba ko tozartaki na yi ne kawai don..."
da sauri ta daga masa hannu
"Ya isa haka SK ba na bukatar jin wata kalma ta fito daga bakin ka da sunan ba da hakuri"
cikin Sauri ta zare hannunta daga nashi ta bude kofar ta ficewar ta duk sai yaji baiji dadin haka ba ranshi ya ji ya na daci matuka ba ya kaunar ace ta dalilin sa wata mace ran ta ya baci domin ita mace halin tace ta daban cikin ko wani jinsin dangin rai.
Jikin sa a sanyaye ya juyo ba tare da ya rufe kofar ba da ta bari abude  ya fada kan gado duk sai yaji ba dadi bai kyauta ba da abin da yayi wa Teemah nan dai yashiga lissafe lissafe da nazari tsayin mintina kamar Wanda aka tsikara
Ya tashi ya zauna gami da Jan tsaki a fili ya furta
'nima da damuwar kai akan wasu yo ai bani na kawo ta ba,balle har inji tausayin ta,don ran ta ya baci"
tashi yayi ya fada toilet yayi wanka ya fido ya shirya cikin kananun kaya rigar fara tas mai dogon hannu tayi matukar kama masa jiki gaban rigar an rubuta HEART da ruwan gold wandon ruwan ash kala ne yana da diko-dikon fari shi ma ya kamata shi amma ba can ba ya taje kan sa Wanda yake ta sheki da kyalli sai tashin kamshi yakeyi kafar sa sanye da flatshoes sai da ya duba kan sa cikin dressmirro yayi murmushi mai kayatarwa saboda irin kyan da yaga ya kara fito wa daga gareshi kuma abin da ke taimaka masa wajan yakar yan mata domin ko bai ce yana so ba shi sai ance a na son sa.
wayar sa ya dauka ya rike a hannu tare da kwalin sigari ya zirashi cikin aljihunsa ya dauki makullin motar sa ya fice daga cikin dakin tare da kulle shi.
***   ***    ***
lokacin da Teemah ta fice daga cikin dakin SK cikin yanayi na haushi da kunar rai idanuwan ta duk sun gama rufewa da irin cin mutuncin da yayi mata Wanda a tunanin ta ba ta yi zaton haka daga gareshi ba tabbas ta kara yarda namiji ba abin ayi amanna da shi ba ne musamman Wanda sanadiyyar bariki ta gauraya rayuwarta dashi dole ta san abin yi don wallahi ba za ta barshi haka ba namiji ba abin aji kan sa ba ne ko a tausaya masa saboda shi ma ba tausayi gareshi ba kamar zuma yake shan sa sai da wuta...
Wani irin mahaukacin shaka taji akai wa wuyan ta Wanda yayi matukar rikita ma tunani da hargitsa mata kwanya cikin hanzari ta dawo cikin hayyacinta ta na duban wacce ke tsaya rike da wuyan ta kamar wacce aka aiko ko wacce ta aikata laifi ake neman kama ta a hukunta ta cikin rashin fahimta ta shiga dubanta a mamakance ta ce
"Lafiya"
"kutumar ubanki nace shegiya matsiya wulakantacciya"
abin da ta fadi kenan cikin muryar ihu da kururuwa ta na zazzare ido hakan da Teemah ta gani ta tabbatar mata wannan ba lafiya ba cikin sauri ta yi cilli da Jakarta ta shiga kiciniyar kwatar kanta
Wani gigitaccen mari ta ji an dauke fuskarta da shi Wanda yayi matukar razana da firgita mata tunani lokaci guda ta birkice ta rasa a ina kan ta ya ke
"har ke kin isa har wacece ke uban waye uban ki cikin garin nan wallahi billahillazi sai nayi ajalin ki har ke kin isa muhada inuwa daya dake dube ki dan Allah kazama Kucaka wacce sam rayuwar bariki ba ta mara ba da irin Ku don wallahi in har irin Ku na shigowa cikin ta kashe ta zaku yi sabo rashin wayewar Ku"
Iya shan mamaki Teemah ta kai kololuwa don gani abin takeyi kamar cikin rayuwar film ba ta yarda a gaske ba ne wannan lamarin ke afkuwa ba.
Wata ashariya ta ji an sake lailayowa an cusa mata ita da iyayen ta hakan ya dawo da ita daga duniyar kokwanto
izuwa wannan lokaci harabar otal din ta cika makil da mutane kowa sai kallon ikon Allah yake
wasu na ganin rashin wayewa da gidadanci shi ne ya sanya Teemah sakin baki ake ta kwashe mata albarka ita da iyayen  ta gani wawuya suke yi mata
cikin wanna yanayi Teemah ta kai duban ta wajan ayshanty ido cikin ido suka dubi juna lokaci guda idanuwan Teemah su ka rikide su fara canza kala izuwa kore-kore
cikin tsawa da hargigi
"amma ke karyace ta yi sanadiyyar kawo ki duniyar nan ko, don yanayin zubin ki da haukar da kike nunawa ba kiyi kalar masu hankali ba"
maganganun Teemah sun yi matukar tasiri wajan kara tunzura ta cikin shammata Ayshaty ta dungule hannu ta kai wa Teemah wani wawan naushi amma bi sa akasi Teemah ta kauce ta durkusa kasa ta daki cikin Ayshanty wani wawan ihun kuwwa ta saki ta buga tsalle ta fada can baya ta durkushe tana murkususu hakan da Teemah ta gani ya bata damar dosar ta gadan-gadan ciki zafin zuciya ta kai mata bangara a fuska ta dauke ta da mari hagu da dama cikin yanayin masifa da zazzaro idanuwa waje ta na mai Nuna ta da hannu jikin ta sai karkarwa yakeyi
"Ke har kin Isa duk tashancin da akuyancin ki na dama ki na shaye wallahi, saboda ni da kike gani ba abin a zungura ba ne don bana yafiye bana kyaliya duk Wanda yayi min ba na bari ta kwana sai na keta masa rigar mutunci cikin kasuwa don haka ki kiyaye ki San da wa zaki duk ga mu'amalar rigimar ki"
a daidai wannan lokacin shi kuma SK ya fito izuwa harabar otal din ya ci karo da dandazon mutane duk bai kawo komai a kan sa ba illa tsakin da ya ja yayi wajan motar sa ya na kokarin budewa ya ji amon muryar Teemah da Sauri ya juya ya kai idanuwan sa wajan mai ya ke shirin gani Teemah ya gani duk a hargitse ta ta durkusa tana kokarin daukar jakar ta ido ya zuba mata cikin mamaki bai San lokacin da ya bude baki ya ambace sunan ta ba
"Teemah!!"
ya fadi ya na mai dosar in da take.
sarai taji shi amma sai ta Nuna halin ko in kula ko kallon in da yake ba tayi ba ta suri jakarta ta  durfafi kofar fita cikin hanzari SK ya sha gabanta ya damki hannunta ta shiga kiciniyar kwace wa amma ta kasa ta daga kai ta dubeshi shi ma ita yake kallo
"meye haka Teemah, mai ya sa zaki tsaya ana hauragiya dake a cikin wannan wajan sam haka bai ka mace ki ba"
da sauri ta daga masa hannun dayan da bai rike ba
"ka ga malam sakar ni kaji k.."
ai ba ta kai iyakar zancenta ba ta ji saukar kwalba a kan ta wani ihu ta kurma ta zube a wajan sumammiya jini ya shiga kwaranya saman fuskata.
da hanzari sk yayi kan ta cikin matukar razana da gigita...

DUNIYARMU (Compelet)Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin