DUNIYARMU

1.3K 59 0
                                    

DUNIYARMU

(c)Kamala Minn
BABI NA HUDU
Tun bacewar dabon da salma tayi tsayin watanni uku ba ta ba labarin ta cikin kauyen gurmana hankula sun yi matukar shiga yanayi na rashin armashi dadi lakari da yarda rayuwar kauyen da mutan kauyen ta sauya Sam ba wani kuzari da abin darawa a tare da su kowa kagani fuskar sa da cikin zuciyarsa ciki take da kayan damuwa cikin kan kanin lokaci rayuwa tayi juyin bazata ga wasu dangin rai da su ka kasance wata katanga abin jin gi na ga rayuwar salma rashin kwanciyar hankali shiga damuwa rashin sukuni rayuka sun shiga duk a dalilin batar salma kaddara mai matukar gigita rayuwa ta fado duniyar rayuwarsu musamman iyayen ta mukusanta a gareta
"In dai haka rayuwa take sauya wa mutum wata rana wani ba zan iya daukar ta ba in har bai yarda da kaddara ba"
malam ne ya fadi wani yammaci bayan ya dawo daga wajan sana'ar sa ta faci ya zo ya tadda inna luba ta buga uban tagumi duk ta jeme ta yankwane sai kace wacce tayi shekara ta na cuta cikin halin magashiyan.
hawaye ne suka zirnano mata ta sanya hannu ta goge su sannan ta dubi malam da kodandun idanuwanta sun kada sunyi jajir ta nisa murya a raunane.
"mai yasa rayuwa tayi min a tishawar tsaki ne mai ya sa rayuwa ta kinkimo min abin da ba zan iya jurar sa cikin duniya ta ba mai ya sa rayuwa ta dauko min WATA KADDARAR da ba zan iya daukar ta ba"
ta karshe cikin muryar kuka mai tsuma rai duban ta ya shiga yi cikin hali na jajantawa halin da take ciki tabbas ko shi ba don ya na hakurkurtan da zuciyar sa ba Allah kadai ya san halin da zai shiga na rashin armashin kwanciyar hankali da rashin abin yabo girgiza kai yayi sannan ya nisa
"Ita fa rayuwar duniyar nan dauke take da kayan irin biyu kwanciyar hankali da  rashin jindadi dole sai ko wacce rayuwa ta saba da wadannan bangarorin biyu in har ta na bukatar nasara cikin ta"
cikin rashin jarumtar zuci inna luba ta sake duban malam.
"na kasa ba zan iya daurewa ba zuciya ta zata iya tarwatsewa a ko wani irin lokaci in har tunani salma ba zai bar duniyar rayuwa ta ba"
"zaki iya rayuwa da tunanin salma a ciki duniyar rayuwar ki ba tare da kin gamu da wani illah ba han yar guda daya ce ki mikawa Allah lamarin ki ki cigaba da addu'a zaki samu saukin zuciyar ki ko wani irin tashin hankali bawa ke ciki in har ya mikawa Allah lamarin sa ya yarda da kaddara mai kyau da akasin ta to tabbas zai ga kayan nasara cikin rayuwa don haka ki cire damuwa da kulafici a rankin domin tun fil'azal Allah ya kaddara sai hakan ta faru"
jikin ta yayi matukar saki da jin maganganun malam.
rayuwa ta cigaba da tafiya cikin wannan halin da ake ciki na janjan rayuwar batar salma Shukuranu yayi wa kauyen su tsinki zuciya da ruhi cike da farinciki maras misaltu abubuwa biyu suke masa shawagi wanda suke kara rura ruwan farin cikin sa iyayen sa da masoyi yar sa Salma
Ya fado cikin kauyen su da buruka da kudurori masu matukar amfani rayuwarsa ya ci burin ace ya na sauka bayan haduwarsa da iyayen sa ace ya  hadu da masoyi yar sa Salma wacce ya ke hango ta cikin shiga a kowani lokaci in yana tunanin ta ta nayi masu wani murmushi mai cike da armashi da sanya duniyar rayuwar sa nishadi da burgewa a ko wani lokaci ya kance
"duk ranar da allah ya tabbatar da mu cikin inuwa daya a matsayin ma'aurata zan Nuna miki kulawa da tarairaya Wanda ba wani d'a namijin da ya taba Nuna wa matar sa haka cikin duniyar auransu sai mun zama abin kwantance da burgewa ga duk sauran mutane sai sun so ace DA MA A CE duniyar auransu ta kasance irin tamu"
a duk lokacin da yake wadannan kalaman sai ya ga ta fito masa a gizo ta mai yi masa murmushi kana tace "zan fi kowa farinciki da wannan ranar har in ta kasance fata na da kudirina da burina duk suna kan ka Shukuranu Allah ya kai mu cikin wannan ni'imantacciyar duniyar mai cike da kayan alheri"
duk lokacin da ya jin zanzakar muryar ta na Sakar masa amo mai sauti da sanya nishadin farinciki ciki duniyar sai  yaji kamar shi kadai ne yayi dacen da budurwar mai tsananin son sa.
lokacin da bakin labarin batar Salma yayi wa Shukuranu marhabin lale cikin rayuwa
bayan ya iso ya gaisar da kowa anyi masa ya hanya ya fiddo da tsabarar da ya dawo da ita ya raba gida uku ya dubi Mahaifiyar sa da ta kure shi da idanuwa zuciyar ta sai faman fargaba takeyi in har ta tuna da batun Salma ta yaya zata sanar da Shukuranu batar Salmar sa ta yaya zai fuskanci al'amarin shin wa ni irin tashin hankali ne zai sake fadowa rayuwarsu don ta San tabbas Allah kadan yasan halin da za su shi ga musamman Shukuranu don yarda ya mace akan Salma ya kwallafa rai akan ta ganin ko da mutuwa ce ta zo daukar Salma zai iya ce wa ta dauke su tare in har zai fa mutuwar.
maganar da yayi mata ne ta katse mata tunani
"Umma ga wannan naki ne wannan kuma a rabawa su Shukura  wannan kuma na Salma tace"
ya fadi fuskar sa na kara bayyanar da murmushi
lokaci guda tausayi dan ta ya darsar mata a rai wasu guntayen hawaye su ka kawo wa idanuwanta farmaki da Sauri ta tare su ba tare da ta bari ya gani ba
"mun gode, Allah ya kara budi  yanzu abin da za ayi, ka bar kayan kai kaje ka kara huta wa in Shukura ta dawo daga makarantar ta sai a bata kayan Salmar taka sai ta kai mata"
ta karashe maganar tana duban sa ta na mai sakar masa murmushi shi Wanda da ka kalleshi kasan na dole ne.
duban ta yayi cikin hanzari cikin rashin fahimta
"ban fahimta ba umma, ni fa ba wata gajiya da ta addabe ni wallahi, kawai ba sai an kai mata ba ni da kai na zan kai mata"
Ya mike ya na mai kokarin daukar kayan da niyar tafiya.
da sauri ta tsayar dashi
"Shukuranu zauna ina son magana da kai"
ta fadi murya a sake lokaci guda damuwa ta bayya na a fuskar ta
Yanayin da tayi magana da yanayin da fuskarta ta sauya sun yi matukar tasiri wajan kashe jarumta da kuma jin sa duban ta ya shiga yi cikin yanayi na tuhuma
jiki a sake ya ajeyi kayan kasa sannan ya samu guri ya zauna ya fuskanci mahaifiyar ta sa cikin yanayi na zakuwa da son jin abin da za ta fada masa Don ya matsu ya Ganshi yayi wa Gidan su Salma masoyiyarsa tsinke.
"Shukuranu a rayuwa ka kasance mai yarda da kaddara a duk yarda tazo maka ka amsheta domin hakan na karawa mutum karfin imani"
cikin nuna rashin fahimta da kuma alamun fargaba suka dirarwa Shukuranu ya shiga duban mahaifiyar ta sa ita ma shi take duba
"tashi ka tafi Allah ya kiyaye hanya ka gaidamin da mutanan gidan"
wani irin yanayi ya ji kansa ya fada Sam ya rasa gane kan maganar mahaifiyar sa me take nufi da hakan me take nufi da cewa ya amshi kaddara ko ta yaya ta zo masa tana nufin kenan zai ci karo da WATA KADDARAR kenan ko yaya
da wannan tunanin ya mike jiki a sake ya suri kayan ya fice bayan ya ce mata sai ya dawo.
fitar sa ke da wuya hawayen da take rikewa suka zubo mata ta sanya habar zanin ta ta dauke tare da cewa
"Allah ka ji kan mu cikin rayuwar duniyar mu ka yi mana da kyau a lahirar mu"
***  *** ***
tashin hankali GOBARAR GEMU in da Shukuranu ya  san irin wannan bakin labarin zai tarar da ya roki  Allah ya dauke masa numfashi.
lokacin da ya isa cikin gidan su Salma yayi sallama bayan an bashi izinin shigo ya na sanya kafar sa daya cikin soron gidan gaban sa yayi wani irin mugun bugu hakan ya sanya shi saurin ambaton Allah tare da dafe kirjin sa cak ya tsaya ya na nazarin abin da ya haifar masa da irin wannan mummnar faduwar gaba mai barazanar haukata zuciya cikin wannan yanayin ya kokarta ya fada cikin gidan.
Inna luba ya tarar zaune ta zuba uban tagumi kallo daya yayi mata ya tabbatar ba lafiya ba don bai saba ganin ta cikin wannan halin ba a tare da ita ba mutuniyar da ta mai dashi kamar dan ta ba ruwan ta zama take suyi hira duk lokacin da ya ziyar ce ta ko wajan Salma ya zo cewa take ya shigo daga ciki sai dai in shine ya ki
gaban ta ya zube ya na mai kwasar gaisuwa a daidai lokacin kwallar da ta taru a idanuwan ta zubo hakan ba karamin tashin hankalin Shukuranu ya shiga ba
da sauri yace "umma lafiya kike zubar kwalla haka, ko dai wani abin Bacin rai ne ya sa me ki?"
duban sa tayi cikin yanayi na son shanye abin da ke nukurkusar zuciyarta ta saki wani yakunannen murmushi wanda yafi kuka ciwo
"Shukuranu yaushe aka iso garin namu daga tafiyar da ba sallam?"
sunkuyar da kai yayi gami da susar keya alamun rashin gaskiya
"umma ayi hakuri wallahi tafiyar ce ta zo a bazata shiyasa ban samu damar sanar da ku ba"
"shikenan, dafatan ka dawo lafiya?"
gyada kai yayi gami da cewa "lafiyalau umma ya kuke dafatan kowa ya na lafiya?"
lokaci guda wani irin gurjejan ajiyar zuciya ya faru gareta hakan yasan ya Shukuranu saurin duban ta a hanzarce yace "akwai wani abu da yafaru ne umma?"
Ba tare da ta bashi amsa ba ta sanya hannunta ta dauke gumin da ya fara tsantsafowa
"k'addara ta fado rayuwarmu lokacin da ba muyi tsammani ba tashin hankali da rashin walwalar rayuwa shi mu ke fuskarta cikin duniyar mu"
ta karashe cikin raunanniyar murya mai son fashewa da kuka
cikin rashin fahimta Shukuranu yashiga dubanta gaban sa na faman duk kan uku uku cikin sauri sauri zuciyar sa ta fara harsaso masa wani abu ya faru kuma ma rashin armashi dadi maganar ummarsa ce tayi wa kwanyar sa tsine ke in da take cewa 'ya amshi kaddara ko wacce iri ce ta shigo rayuwarsa'
tabbas akwai wani lamari Mara dadin ji da ya afku bayan tafiyar sa da sauri ya dubi umma a daidai wannan lokacin gabadaya ta fara ficewa da hayya cin ta jikin ta ba abinda yake sai kyarma idanuwanta sun kada sun yi jajir
"umma shiga tashin hankali ko halin damuwa ba shi ke nufin igiyar rayuwar mutum ta tsinke ba don girman Allah ki bar wannan shiga halin tashin hankali hakan ba karamin gurguntar da jarumta ta yake yi bs nima zan iya shiga rudu matukar ina ganin ki kin fada halin damuwa"
"SALMA Shukuranu Salma ta mutu an sace Salma an dauke min farin cikina an dauke min dariyar duniyar rayuwa ta an dauke min walwala da nishadi rayuwa...!!""
sunan Salma shi ya amsa masa kuwwa cikin kwanyarsa jin abin da umma take fadi lokaci guda numfashin sa ya dauke na wucin gadi tunanin sa nazarin sa ya tsaya cak! magudanan jinin jikin sa suk dai na tafiya zuciyar sa tabar aiki idanuwan sa sun kankafe ba alamun wani bangaren na jikin sa da ke motsawa duk sun tsaya caji da aiki.
duk abin da ke faru inna luba bata lura ba sai da takai matsaya a zancen ta sannan ta fuskanci abin da ke faru cikin razana da tsananin firgici ta mike jiki na karkarwa tashiga sallallami a daidai lokacin shi kuma malam ya sanyo kai cikin gidan da sallama sa amma dalilin abin da ya kagani ya sanya shi saurin cinye maganar da yayi niyyar yi da hanzari ya karaso ya mai tambayar ta lafiya amma ta kasa bashi amsa sai kada kai kawai takeyi da sauri ya ruko Shukuranu wanda a daidai lokacin yake kokarin bajewa kasa ya kwantar dashi sannan ya dubi inna luba cikin yanayi na damuwa
"duk mai ya haddasa hakan?"
"maganar Salma"
ta bashi amsa a gajerce
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un allahumma aj'alni fi musifatin"
Iya abin da ya iya ambata kenan da sauri ya tashi ya suro buta cike da ruwa ya shiga kwararawa Shukuranu amma kamar dutse yake shekara ba alamun motsi a tare dashi hakan ya kara firgita shi da sauri ya turkusa ya sanya hannunsa na dama ya dafe kirjinsa na yan sakanni da Sauri ya cire tare da mikewa yana yarfe gumin da ke jika masa fuska yayi hanyar waje.
mintina daya biyu sai gashi ya dawo da sauri yana fadin
"ku shigo daga ciki"
wasu matasa biyu ne su ka biyo bayan sa a hanzarce suka nufi wajan da Shukuranu yake yashe cikin yanayi na rashin tsammanin sake WATA RAYUWA cikin duniyar nan suka sungumeshi sukayi waje malam na biye dasu inna luba  dai idanuwa ta zuba musu ba abin da jikin ta yake yi sai kyarma
"wannan wacce irin rayuwa ce take kokarin tun karo mu wannan wani irin tashin hankali mai girgiza muradan kwanciyar hankalin dangin rai" maganganun da tashi ga yi kenan cikin rashin hayyaci da yanke tsammani akan wannan lamarin rayuwar.
***    ***  ***
tun fitar su malam daga cikin gida su ka isa in da aka ajiye Babur mai kafa uku (keke napep) a ka sanya Shukuranu cikin da ya daga cikin matasan  da suka fito dashi da hanzari ya shiga a matsayin direba sauran biyun suka shiga suka tallabe Shukuranu Wanda iya wannan lokacin ba wani alamun motsi jikin sa.
hankulan mutanan unguwar  duk yayon kan abin da ke faruwa sai tambayar malam suke amma ya kasa basu wata amsa ta azo a gani saboda yanayin  da yake ciki ba karamin tashin hankali bane tunanin sa daya kar  a kuma Salma ta bata ace kuma ta sanadiyyar batarta an rasa Shukuranu in kuwa haka ta kasance rayuka da yawa za su shiga tsananin da rashin walwala a duniyar su..
"malam da kai zamu tafi ko a gida zaka tsaya"
cewar direbar napep din da sauri malam ya tsinke igiyar tunanin sa
ya dubi matashin cikin murya mai rawa yace "e..eh da..ni za..aaa"
da sauri ya kokarta ya shiga matashin ya ja napep din mutane sai fatan samu waraka sukeyi musu fuskar su cike da jimami.
***  ***   ***
da gudu ta fada cikin gidan sai faman haki takeyi hannunta dafe da kirji sai faman kiran 'umma' take yi cikin yanayi na matsananciyar tsorata.
cikin hanzari umma dake daki zaune tana lazimi tayo waje tana mai duban Shukura da ke durkushe sai kokarin daidaita  tsayuwar numfashinta take
"ke lafiyar ki kuwa, kika shigowa mutane gida kina kwala musu kira kamar wacce ake kokarin salwantar wa rayuwa.?"
cikin yanayi na numafarfashi Shukara tace
"umma to meye bambancin maganar ki da wannan kayan tashin hankalin da ya tunkaro rayuwarmu"
cikin yanayi na nuna rashin fahimta umma tace
"ke Shukura  bana son jin mugun abu daga bakin ki,wai shin me ke faruwa ne na ganki haka har kike ikirarin kayan tashin hankali ya tunkaro rayuwarmu?"
Shukura ta numfasa sannan ta dubi mahaifiyar ta cikin yanayi na damuwa.
"umma yaya na"
"me ya sa meshi"
ta fadi cikin nuna rashin bawa maganar ta ta abin yabo.
Shukura  ta sake ni sawa
" ya na can an tafi dashi asibiti wai ya fadi gidan su anty Salma"
tun kafin ta dasa aya umma ta shiga sallallami da tafa hannu
"muhammadu dan aminatu, nikam na ga  ta kai na Allah ya sa yaron nan ba kan shi ya salwantar ba"
gaban Shukara ya buga ta zaro idanu waje tare da cewa cikin hanzari
"umma me ya faru da yaya Shukuranu?"
zaman dirshan tayi a kasa gumi ya shiga tsantsafo mata a goshi ta dubi Shukura
"maganar batar Salma ita ce yaji"
Idanuwa waje Shukura ta dafe kirji
"umma dama bai sani ba, ai na dauka kin sanar dashi"
girgiza kai tayi cikin jimami
"ba zan iya ba shiyasa na kyakeshi ya tafi ba yarda ban yi dashi ba kar yaje gidan don nasan komai  zai faru ba mai dadi bane har cewa nayi ya bari ki dawo makaranta sai ki kai mata tsabar shi ya huta ban nuna masa komai ya faru ba"
ka sake Shukara tayi tana kallon ummanta.
da sauri umma ta tashi ta dubi Shukura
"wani asibiti su ka tafi dashi?"
girgiza kai tayi alamun bata sani ba
umma ta fada daki ta dauko mayafin ta hannunta rike da karamar jaka ta dubi Shukara da tagama tsinke wa da lamarin
"maza tashi muta fi"
mekewa tayi jiki a sake su ka fice daga gidan gami da kullewa...

DUNIYARMU (Compelet)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant