DUNIYARMU-28

388 18 0
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA

BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS.

Al'amarin Adam abubuwa cikin duniyarsa sai kara hargitse yake gabadaya ya rasa abin da kemasa dadi cikin duniyarsa komai ya kwance masa cikin lokaci kankani wanda sam bai taba zaton rayuwa za tayi masa haka ba.
Hankalin sa da natsuwar sa gabadaya sun gushe sun koma can wani waje da yake tsammanin can ne in da abin da yake muradi yake ya rasa jindadin sa ya rasa kwanciyar hankali tashin hankali da tarin damuwa son zama abokanai cikin duniyarsa ya koma zaman kadaici ya koma kamar wani wanda bashi da lafiya yake jinyar kansa da kasan saboda rashin mataimaki.
Zaune yake can kuryar daki karshen gado kallo daya kayi masa ka tabbatar da yana cikin yanayi na rashin armashi takure yake hannunsa dauke da wata kwalba wanda duk wanda ya san me ce giya to zai tabbatar da ita din ce.
Lokaci-lokaci yana daga kwalbar ya na kaiwa bakinsa yana tuttulawa cikinsa idanuwansa gabadaya tun gama rikiɗewa kamar ba na shi ba sunyi jajir sosai fuskar nan tasa gabadaya ta sauya kamanni jikisan sanye yake da T-Shirt fara amma ta sauya kala da alamun tashin hankalin da yake ciki har wanka da tsaftace kai ya hanashi kai shi kuwa kamar dambun karangiya haka yakoma yayi cidin-cidin dashi la66an bakin sa duk sun bushe sosai har wani kanzo-kanzo sukeyi.
Wani irin nishi ya saki wanda ya sanya shi wata irin mika saboda jin da yayi kirjinsa na kartawa da raɗaɗi kamar zuciya zata faso ta fito waje lokaci guda wasu zafafan hawaye suka shiga kwaranyo masa kamar an bude famfo.
Ihu ya kurma tare da fasa kuma kamar wanda aka yiwa sakiya da karfe mai tsananin zafi da tsini kamar da take hannunsa ya daga ya rotsata da kasa yana sakin gunjin kuka kamar wanda aka ce in bai yi ba uwarsa da uban sa za a kashe yi yake kamar ana kara tunzura shi nan ya mike yana faman tangaɗe da nayi duniyar na juya masa gida uku-uku  ya shiga watsi da kayan da duk  ya ci karo da su cikin lokaci kankani yayi kaca-kaca da dakin yana faman kururuwa da ihu.
Ihun da yake zundumawa ne ya janyo hankalin mutanan gidan da gudu su kayo saman dakin sa amma ko da suka iso a kargame su ka tadda dakin kamar ko yaushe ya kulle kan sa a daki ba ya barin kowa ya shi ba ya bukatar kowa ya zo ya same shi ba ya bukatar a gajin kowa sai mutum daya wanda shi ma sai yayi da gaske yake shiga wato Tk
Sun yi matukar razana da firgita jin yarda yake watsi da kaya nan Alhaji ya dubi matar tasa da suka zo a guje tare, ya ce.
"Adam ya na kokarin kashe kan sa wanda hakan ba kan shi ya cuta ba ni ya cuta domin kuwa ba zan iya daukar kaddarar rashin sa ba".
Ya fadi cikin halin damuwa da tsananin tashin hankali da yake bayyane a fuskarsa karara lamarin dan nashi ba karamin girgiza masa rayuwa yayi ba domin kuwa ji yake kamar shine a cikin wannan halin yaro daya tak da yake dashi wanda ya mallaka cikin duniyar nan magajinsa kuma amma ace yana cikin wannan hali dole ya shiga ruɗani matuka zuciyarsa na zafi da raɗaɗi son dan shi da yake yi ba ƙankani bane shi yasa ni ba ya matukar ko ya ya ne ya ga dan nashi cikin halin damuwa amma ga shi a lokaci guda ya tsinci dan nashi cikin wani hali wanda ya kasa gane meye sila yana kallon dan shi rayuwarsa na barazanar tarwatsewa amma ya rasa abin da zai yi domin magance masa damuwar ya rasa mafita cikin lamarin tunaninsa gabadaya ya gama rikicewa yin duniyar nan yayi da ɗan nashi ya fada masa abin da ke damunsa amma abun ya ci tura sanadin takura masa da sukeyi ma ya san ya shi kulle kan sa a daki domin gujewa kowa hakan kuma ya kara tayar masa da hankali domin yana matukar tsoron kar dan sa ya mace numfashi ya ajje gami da sake duban Hajiya Laila.
"tunani ya kasa bani mafita menene abin yi?"
ya fadi cikin raunin murya gami da sakin hannun kofar da ya rike yana girgizawa ya juyo da kallonsa zuwa kan Hajiya Laila hawaye ya gani sai faman zuba suke a fuskarta in da sabo ya ci ace ya saba domin tunda Adam ya shiga wannan halin ta rasa tsukuni da natsuwarta kullun cikin zubar hawaye take amma na yau ya bambanta da na sauran lokutan baya domin jikinta ba abin da yake sai karkarwa bakin ta na ɓari tashin hankali matsananci ga shi nan cikin kwayar idanuwanta da sauri ta kau da kai ganin da tayi kallon da yake mata ya ki karewa ta fara magana cikin rawar murya da muryar kuka.
"in da ina da matsayi da daraja ga iyalan gidan nan da komai bai faru in da ina da kima da za a kalle ni da ita da wasu abubuwa da yawa ba su afku ba cikin IYALINA amma ina an dauke a maras daraja da ɗa wacce zatayi magana a yarda da ita har ayi amfani a dauke wacce ba ta san komai ba wacce ba ta da amfani ga Iyalan gidan nan Alhaji ba zan boye maka ba gaskiya kana da hannu dumu-dumu cikin komai da yake faruwa cikin rayuwar Adam naji ma ina nusar da kai na dade ina karanta maka aibun yanayin salon da kake nuna masa amma ina ka dauke a banza wacce ba ta san abin da duniya take ciki ba  ka dauke wacce bata da Hakki kulawa ga Adam ka nuna kafi ni iko da shi ka manta ita kan ta Uwa ta na da hakki na kulawa da 'ya'yan amma duk ka tauye min wannan hakkin sai abin da ranka ya so zuciyarka take so shi kake aikatawa Alhaji karka mata ita rayuwar nan da kake gani in har kace zaka dauke da zafi to tabbs da zafi za ta zo maka in kuma zafin ya rinjayi naka shi ke harfar da matsaloli wanda ba a taba tsammani ba".
Ta tsagaida ta da maganar tan jan hanci gami da dauke hawayen da suke safa da marwa a fuskarta sannan ta sake duban sa ido cikin ido muryarta a lokacin ta sauya izuwa daci da tsanananin taƙaici da bakin ciki.
"Adam ɗana ne kamar yarda kake ka gasgata kai ma ɗanka ne ina da hakki kamar yarda kake da shi kan sa yarda kake ji zaka iya kula dashi da duk wani lamarin rayuwarsa nima ina da wannan damar amma saboda irin wani banzan so da ka daurawa Adam ya sanka duk ka manta da wannan abubuwa ka nuna kaifa son dan ka shi yafi maka komai cikin duniyar nan ka fifita Adam akan  kowa da komai naka ka nuna ms wani irin MAKAHAON SO wanda yake kan hanyar lalata rayuwa ka nuna masa gata wanda kai kan ka ka sani GATA ILLAH ce in har tai yawa ga yaro kai har ma da babba amma idanunka sun rufe duk ka manta da wannan nayi bakin ciki nayi taƙaici akan irin gatan da kake nunawa Adam ba wai ina nufin ban so ya samu gata bane da kulawar iyaye amma kasa ni wata kusan tafi wata ana barin halak don kunya Alhaji na dade ina nusar da kai amma ina duk kayi kunnan uwar shegu dani ka ba banza ajiyata wofi ta adana ni na daɗe ina guje maka irin wannan lokacin da zai zo ka kasa magance shi na daɗe ina takaicin zuwan irin wannan ranar wacce zata kasance gabadaya iyalan gidan nan kwanciyar hankali zai kaurace musu wata dukiya wata kadara ko wani mukami ko wata isa duk ba za su taka rawa ba wajan magance matsalar a da can baya kana amfani da isar da ikon ka da dukiyarka kana yaga wanda ka so a lokacin da ka so kana karewa Adam duk wani abubuwa da yake aikatawa na laifi kana shigewa gaba da karfin dukiyarka wajan danna hakkin wanda ka cuta ka dade kana abu wanda sam baka tunanin zai dawo maka yanzu ina amfanin haka wa gari ya waya yanzu ga shi matsaloli ne suke tunkaro mu cikin DUNIYARMU wanda Allah kadai shiyasan iyakarsu wallahi na rantse ko da wannan matsalar aka barmu ta Adam ina mai sanar da kai sai mun kwashi kashin mu a hannayenmu".
Tun da ta fara magana Alhaji yayi kasake ya najin ta maganganunta na ratsa shi ta ko ina yana jin su kamar wasiyya ce ake sanar dashi mai dauke da tsagwaron tashin hankali zuciyarsa sai faman amsawa take akan maganganun kunnuwansa kuwa kuwwa kawai su ke jiyo wa da amo na sautin muryar hajiya Laila wani irin gumi  yake ji yana keto masa ta duk wata kafa ta gashi dake jikin sa wasu tawagar katangun tashin hankali yaji suna ta barazanar ruguzo masa akai nan ya shiga girgiza kai lokaci guda hayyacin sa ya fara kokarin barin sa ita kuwa hajiya Laila ta dasa aya a batun ta cikin matsanancin tashin hankali taja jiki idanuwanta na zubda hawaye ta bar wajan zuciyarta na faman tukuki da kartawa kamar zata tsaga kirjinta ta fito.
---------------------------------
Zaune take bakin gado jikinta sanye da doguwar riga mai ƙalar Pink tayi matukar amsar jikinta kan ta ba dan kwalli kayan ya bayyanar sa gashin kanta da yake a ya motse kamar wacce ta yi dambe.
Waya a hannunta alamun kira ne ya shigo take kokarin dauka yanayin fuskarta gabadaya ya sauya izuwa na damuwa ko da yake taji cikin wannan yanayin abubuwa da yawa sun ya motse mata a duniyarta komai ya kwance mata a karan kanta ma tana kokarin rasa gane kan ta.
A hankali ta daga wayar ba tare da tayi magana ba sai faman juya idanu take yi.
Daga can dayan gefen ta a fara magana.
"Bahijja na sani yanzu haka kina cikin halin da kika dauw kanki na damuwa kin kasa fahimtar me cece rayuwa da yarda ake fuskantar ta in kaddara ta shigo cikinta".
Numfashi taja gami da huci ba tare da tayi magana ba jin haka ya sanya shi daura maganar sa.
"Ni sani kina cikin yanayi na abu biyu na daukar kaddarar da Allah ya daura miki da kuma kwadayin daukar fassa na san abin da zuciyarki take so shi ne ki dauki fassa ki ki yarda da kaddara...".
"MANSOOR".
ta katse masa maganar sa da kiran su nan sa cikin wata irin murya mai amo amma da kayan damuwa a cikin ta.
"na kasa ganewa in da kaina yake na rasa abin da ya dace nayi".
ta fadi da muryar son yin kuka jin haka da Mansoor yayi ya kara masa tausayin ta a zuciyarsa da sauri ya ce "Ina ina yanzu haka?"
murya a raunane ta amsa da cewa
"ina daki"
"in har ba matsala ki fito yanzu mu hadu dake".
Kamar jiran umarni take koma da ma can ta na so haduwa dashi cikin hanzari ta amsa masa ga tanan zuwa tana kokarin mekewa nan suka katse wayar a tsakanin su cikin sauri ta zari makullin motarta da jakarta ta dauki wani dan yalolon mayafi ta dora akan ta ta fice daga cikin dakin tana kofar ta kulle can harabar hotel din ta nufa in da motarta take a ajiye ta bude ta shiga ta mat key komai tana yin sa cikin hanzari ne da rawar jiki domin komai nata azancinta kumajinta wat jarumta ta duk tana wajan Mansoor domin kasancewa da tayi dashi cikin kankanin lokaci komai nata sai taji ya fara sauya a cikin duniyar rayuwarta tana ji ajikin ta shi Mansoor ba irin sauya Wasu mazan bane ta naji zuciyarta ta aminta dashi har kasar ruhinta ta yarda a maza ma ba duka bane suka kasance maci amana macuta ta yarkewa kanta cikin maza ma akwai nakwarai akwai kuma bara gurbi amma hakan ba wai yana nufin zata yarjewa kanta dari bisa dari bane domin kuwa namiji ta yada da kikarin da ake masa na Zuma ga zaki ga kuma harbi namiji buhun kaya namiji dangin ajali namiji tabarmar kashi namiji kadangaren bakin tulu ne ba a taba iya masa Namiji...
Girgiza kai ta shiga cikin katse tunanin da zuciyarta ke ta wassafa mata akan maza wanda suka kasance mara tabbas a rayuwarsu komai taji yana dawo mata a kwakwalwa abubuwan da suka guda can baya wata irin muguwar tsanar Adam taji tana kara samun gurbin zama azuciyarta kiyayya mai tsanani da haushi sai kara ruruwa suke akan Adam tsineqa da dibar albarka kawai zuciyarta ke ta yi akan Adam tana rokan masa bala'o'i da su tabbata akan su mara yankewa a duk innda yake masifu da fituna duk roka take su kasance a duniyar sa.
Karar da taji ne ya san ya ta dawo cikin hayyacin ta da sauri ta dubi gaban Ashe danja aka ba su a titin da take wani wawan burki taja saura kadan ta kwashe wani mai adaidaita sahu dake gabanta ajiyar zuciya tayi ganin hakan bai tabbata ta shiga lumshe idanu ta dago ta duba hagunta  sannan ta koma da kallon ta izuwa dama karaf! Idanuwan ta suka sauka kan sa da sauri ta zaro idanuwa waje gabi da sake duban sa sosai gani take kamar gizo yake yi mata kamar shi ma acan ya juyo da kallon sa ga gefensa karaf idanuwansa shi ma suka sauka akan ta wata irin zabura yayi gami da nuna ta da hannu bakin sa sai motsi yake yi hannunsa daya yana karkarwa ya shiga nuna ta yana son yi magana amma sam ya rasa ta ina mazai fara ga shi ba danar ya fito daga cikin motar domin daf ake da ba su hannu nan dai suka shiga kallan kallo a tsakaninsu Bahijja lokaci guda ta tsuke fuska gami da kawar dakai daga kallon sa amma zuciyart sai faman bugu take yi ji take kamar ta je ta shago shi yarda take kallonnsa kamar Adam take gani yana yi mata gizo dakiku biyu suka shuɗe nan aƙa ba su hannun wata irin fizga tayi wa motarta kamar za ta tashi sama zuciyarta ta ji tana zafi ba abin da take buri illa ta ganta gaban Mansoor.
gudu take na fitar hankali cikin rashin hayyaci sam ba ta lura da motar dake bayanta ba kuma ita take bi sai da taje shataletalen kofar dan a gudun sannan nan ma aka ba su danja alamun tsawa nan sannan ta lura da motar mamaki falla a zuciyarta lura da tayi ita yake bi nan t sake daukar hanyar da zata kai sharada in da Mansoor yake domin har gidan sa ta sani tafiyar mintina biyar tayi ta isa gidan nasa horn kawai tayi mai gadi ya bude mata get domin ya rigaya ya san Bahijja sai da tsaya suka gaisa sannan ta kara sa cikin gidan tayi parking ta fito cikin sauri sauri gudu gudu ta isa cikin falon sa nan ta tadda shi zaune yana kallon NTA NEWS jikinsa sanye da jallabiya mai ruwan madara da alamun yau ba inda zak je huta yake yi a gida
Da sallama ta isa cikin falon ta samu guri ta zauna gami da ajiyar zuciya mai karfi kallo daya yayi mata bayan ya amsa mata sallama ya tabbatar tana cikin tashin hankali matsananci ta so wa yayi daga in da yake zaune ya zauna kan hannun kujarar da take ba tare da ya dube ta ba ya fara magana.
"hala akan hanyarki ta zuwa wajena kin hadu da kayan tashin hankali ne naga gabadaya kamanninki sun sauya daga damuwar da na san ta fara raguwa a gareki".
Rausayar da kai tayu gami da sakin huci mai zafi ta numfasa.
"Eh zai iya kasancewa haka domin na hadu da wanda yake kusan ci da mutumin da ya kakaba mani damuwa a duniyata".
ta ida cikin dacin rai ji take kamar da kurma ihu saboda haushi da takaici lokaci guda Tk ya fado mata a rai tabbas ya biyo a baya har lokacin da ta shigo cikin gidan Mansoor to me haka ke nufi bin me yake yi mata ita ya kamata ace tana bibiyar duniyar rayuwarsu amma ga mamaki sai ta ga Tk na bibiyar ta Anya ba wani abun suke kokarin aitawa ba gareta...maganar Mansoor ce ta katse mata hanzari tunani.
"waye kuma haka?".
ya tambaya yana mai kafeta da idanu domin son sanin amsa gamsasshiya.
"Tk".
Ta furta cikin wani irin yanayi na kamar ba ta so furtawa ba ta nisa sannan ta dora da cewa,
"Shine yaron sa wanda muka hadu a Club ranar da nakasance da Adam yanzu haka bibiya ta yake domin ko da na nufo gidan ka na hangi motarsa a bayana mun hadu dashi ne wajan da yale fifa suka ba mu hadu".
Ta karashe tana mai duban sa tana rausayar da kai da alamun akwai abin da yakai wa zuciyar ta hari a daidai wannan lokacin da sauri ta kau da kai daga kallon Mansoor tana faman ajiyar numfashi kamar wacce tayi gudun fanfalaki zuciyarta na bugawa cikin sauri rintsr idanuwa tayi kanta taji ya shiga shawagi da ita cikin duniyarta wasu lamura da ba ta san ko na menene ba su ka shiga zarya cikin zuciyarta da kwakwalwarta.
Sun jima cikin shiru kafin Mansoor ya saita kan shi domin shima ya shiga cikin wani Motion mai wuyae fassaruwa a gareshi shawagi kawai yaji zuciyarsa da kwanyarsa suna yi suna haifa masa da abubuwa da suke kokarin rikita masa tunani da dakusar da jarumtarsa jan numfashi yayi cikin tattaro kumaji da azancin da yake tsammanin yana dashi ya dubeta idanuwansa a dan lumshe kamar mai jin barci.
"me hakan ke nufi, da ya biyo ki ko dai...".
Sai kuma yayi shiru ya shiga sanya hannu a bakin sa ya na ciza wa kamar wanda akayi wa dole idanuwa ta zuba masa jin ya tsinke zaran maganar sa da ya dauko ta shiga jifan sa da kallon tuhuma wanda hakan yayi tsiri azuciyarsa murmushin yake ya saki sannan ya dora da cewa.
"ko dai shi Adam din ya ce a nemo ki".
Wani irin takaici ya kawo zuciƴarta farmaki ba ta san lokacin da ta kwaso wasu tawagr ashariya ba ta dire ta dora da cewa cikin yanayin bacin rai.
"sabo ni kanwar uban sa ce ko matar uban sa  ko ta bace ya zo neman domin kai wa uban nasa da yake zaman jirana".
Yanayin da tayi maganar iyakar gaskiyarta ya sanya Mansoor dariyar da bai shirya ba yana mai kama habarsa yana susa kamar wanda cinaka ya ciza sai faman mitsi-mitsi yake yi da idanu ganin ta kara kulewa da dariyar da yake yi mata.
"Tashi muje kila ma yana waje yana jiran ki".
Haushi ya kara turnuke ta tashiga jan numfashi tana motsi da baki da alamar wasu tawagar ashar din ne suke nukurkusan ta take so Mansoor ya sake tsinkawa ta dire masa su in da hali ma ta hada masa har da bugu tsaki ta dire gami da galla masa harara amma sai yayi kamar bai ganta ba ya fara kokarin mikewa yana mai gyara jallabiyarsa.
"ke fa nake jira".
ya fadi yana mai kau da kai daga kallon ta azuci kuwa dariya ne ke cin sa yarda ya ga tayi kicin-kicin da rai yana jin tausayin ta matuka ya san duniyar mazaje na walagigi da ita ba yarda ta iya ita kuma kalar ta ta ƙaddarar kenan amma ta kasa dauka tayi tawakkali.
Shirun da yaji tayi ne kuma da alamun bata da niyyar mikewa ta bi umarnin nasa ya dube ta karaf sukayi ido hudu ashe tunda idanuwanta na kan sa tsuke fuska yayi ya mai cin-cin magani kamar gaske.
"nifa kallo ne bana so malama ki tashi mu tafi ba sai kin gama gane min munin da Allah yayi min ba ke kuma ga ki ba matata ba balle nace kallon so da kauna ne kike yi mani yasin zunubi kike dauka ni dai ba ruwana".
Yanayin da yayi magana ya dan bata dariya aikam sai da ta murmusa sannan ta koma gidan jiya ta tsuke fuska tana numfarfashi ta fara magana kamar gaske.
"wai don Allah me za muyi masa"
Ya tare ta shima.
"nidai kawai cewa nayi ki tashi muje in kuma ba zaki ba ki sanar dani".
Ba yarda ta iya domin Mansoor ya wuce duk wani mataki na bijewa gareta zuciyarta bin umarninsa take tamkar rakumi da akala ko bawa da uban gidan sa.
Haka ta mike sai faman kumbure kumbure take kamar wacce take shirin tarwatsewa.
Bai sake bi ta kan ta ba ganin ta mike da alamun eh za ta bi umarnin nasa hakan yasan zuciyarsa mamaki ganin Bahijja tana bin maganar sa kuma da alamun ba ta son ganin bacin ran sa sai dai halin mata dole ko a ina ne sai sun nuna haka ya fice daga falon yana tafiya yana jin takunta a bayan shi har suka isa ga maigadi nan ya tsaya suka gaisa sannan ya bude kofar ba tae da ya fita ba amma da alamun ita yake jira lura da tayi da hakan sai ya sanya kara sakin jiki tana tafiya kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki yana kallon ta duk abin da take sai ya kau da kai kamar bai san ta nayi ba har ta iso sai ita ma taja burki ta tsaya hakan ya san yashi saurin kallon ta yana mata alamu da ido da ta tafi mana sai da ta kalle shi sosai san nan ta sa kai ta fice shima ya bi bayan ta.
Aiko suna fita suka hango motar yafito daga cikinta ma ya zo gaban ta ya tsaya ya harde hannu da alamun ya dade da tsayiwa awajan da sauri Mansoor ya dubi Bahijja ita ma shi take kallo cikin alamun mamaki ba wanda yayi magana a tsakaninsu sai suka mai da kallon su gareshi.
Shi kuwa da ga can nesa ganin Bahijja ta fito ya san ya shi muskutawa yana kokarin yo wajan ta amma ganin Mansoor ya san ya shi jan burki ya tsaya ki kam kamar wanda aka dasa yana faman rarraba idanuwa akan su zuciyarsa ta fara sanar dashi ko dai mijinta ne ta sanar dashi yana bin ta ya fito domin tuhumarsa da sauri ya fara ja da baya cikin hanzari ya bude motarsa ya shige ya yi mata key ya bar wajan cike da fargaba.
Su kuwa ganin ya bar wajan nan suka tsaya suna nazarin lamarin Mansoor ne ya nisa ya ce,
"Ina tsammanin akwai fam wani abu a boye tunda ki ka ga haka".
Gyada kai kawai tayi ba tare da ta ce dashi komai ba domin ba ta da abin cewar zuciyarta ne kawai ke zafi ta juya ta koma cikin gidan shi ma hakance ta kasance bin ta yayi a baya.
  Tk tun da ya dauki motarsa yake faman zura gudu ba ƙanƙautawa cikin kankanin lokaci ya isa Dorayi ba in da ya tsaya sai kofar gidan su Adam bai tsaya shigar da motar ciki ba yayi parking cikin hanzari ya bude ya fito yayi cikin gidan da gudu tun falo ya shiga ba tare da sallama ba su Hajiya Laila ya tadda da Alhaji da alamun damuwa tayi nisa da hankalin ba su san ya shigo har ya haye sama wajan dakin Adam ya na isa ya fara kwala masa kira cikin  murya mai cike da tsoro tun yanayi har ya daina ya shiga kwankwasa kofar amma ba alamun za a bude yana jiyo numfarfashin Adam na tar kasa-kasa hakan ya kara sanyashi hanzarin bugun kofar yana kiran sunansa sai da ya shafe kusan minti goma sannan yaji an murɗa hannun kofar kadan hakan ya tabbatar masa da ya bude da hanzari ya fada cikin dakin nan ya ci karo da Adam durkushe hannunsa dafe da kirji sai faman tari yake yi cikin wani irin mawuyacin hali da sauri ya durkushe shima ya tallaboshi a daidai wannan lokacin kuma yayi wani tari mai tafe da jini wanda yayi feshi duk ya bata jikin Tk hakan ya haifar da wata irin ranZ da firgici gareshi...

Hmmm ix life😁😁😁😁

It,x Kamala Minna.😘😘😘😘

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now