DUNIYARMU-23

707 32 2
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA.

BABI NA ASHIRIN DA UKU
  INA SALMA TAKE?
MUTUWA KO RAYUWA?

ɓakar ƙaɗdarar da ta fadowa sallama cikin rayuwa ba zato ba tsammani ba ƙaramar illa tayi ba ta ba cikin duniyarta ta raba ta da farincikin ita iyayenta, masoyinta, danginta, da ƙawaye duk kaddara tayi mata sanadin rabuwa da ita sanadin haka rayuwarta ta juyo izuwa wata irin rayuwa wacce duk wani dangin rai ba zai yiwa ko makiyinsa fatan wannan rayuwar ba da Salma ta koma yi cikin baƙar ƙaddara.

Sanadin soyayya an tauye mata rayuwa an nakasta mata farinciki an sayo mata kayan tashin hankali an jogana mata a rayuwa wanda tunda take ba tayi tsammanin hakan ba duk da dai ance mai rai ba ya rasa motsi a duniyar nan.

ta na rayu cikin wani waje mai dauke da wani gida cikin wani daki mai duhu da kayan takaici ta rayu cikin sa tsayin lokaci cikin zubar hawaye mara yankewa zuciyarta ta rayu cikin tsananin bakin ciki maras yankewa duniyarta tayi duhu haske rayuwa ya kauce mata a lokaci daya tak ba zato ba tsammani ta zama kamar zautacciya wacce ta dau shekaru ba tare da hankali ba ci da sha sun yi kaura daga gareta ta fige da yanƙwane ta lalace ta so ace ta mace cikin duniyar nan amma abu daƴa yake mata shamaki masoyinta ta san tabbas in ta mutu ba tayi masa adalci ba ita kan ta tasan ba tayi wa kan ta adalci ba za tayi wa zuciyoyi da rayuka illa.

"kin jawo wa rayukarki katuwar matsalar da bata da ranar warkewa a gareki. Kin yiwa duniyarki gangacin da za kiyi  da nasanin aikata kuskuren da kika aikata kin siyowa kan ki tashin hankalin da rashin natsuwar rai akaran kan ki sai na shayar dake ruwan ɗaci mai dauke da sinadaran kayan bakin ciki da kunar rai"

Furucin da akayi mata kenan cikin daren da aka rabata da danginta da iyayenta da garinta kuma wanda ba ta san wacece ba kuma ba ta san mai tayi mata ba a cikin wannan halin na rashin hayyaci da gushewar hankali aka rabota da gidan iyayenta aka kawo ta wani waje wanda ba ta san shi ba bata san hanyar da za tabi don ceton kai ba a lokacin da aka kawo ta fuskarta ayi mata kawanya da bakin kyalle wanda zai hanata ganin abin da ke wanzu cikin duniƴar nan mai cike da kayan tashin hankali da kayan ruɗani duniyar da ta kasance cuta da cin amana da salon mugunta iri-iri suka zama abin ado a cikin ta za ta so ace ba ta tare da dangi da yan uwa da masoya a daidai wannan lokacin da ta roki Allah ya dauki ranta cikin duniyar nan don ba ta tsammanin rayuwarta na da amfani a cikin ta duniyar ta rigaya ta gama lalacewa ta gama gurba cewa rayuwar dangin rai ba a bakin komai yake ba duk yarda aka so a sarrafa shi za ayi musamman in dangin rai ya kasance ba wani ba ne a cikin duniyar nan kaicon wannan rayuwa kaicon duniyar nan mai cike da kalubale masu muni da tarwatse tunanin duk wani mai rai kaicon duniyar da aka canza mata salo da kayan cutarwa kaicon rayuwar da ake kashewa da shiga hakkin duk wani dangin rai kaicon Al'umman da suke tauye hakki junansu a salon rashin Imani da tausayi ina ma ace duniyar nan za ta tashi ina ma ace tashin alkiyama ya zo ina ma ace a nannaɗe duniyar nan ina ma ace rayuwar ta kare cikin yan dakiku ina ma ace duniyar ta ta tashi cikin dakiku ina ma ace taji numfashin ta ya dauke a daidai wannan lokacin rayuwar duniyar nan ba ta da amfani ba da da abi yabo sai na ki a cikin ta kaicon wannam rayuwa

Numfashin ta na wanzuwa cikin duniyar nan amma kuma ta rasa a wani mataki take tsakanin RAYUWA KO MUTUWA? tunanin ya daina dauko mata abin kirki zuciyarta ta daina yi mata nazari na kirki zuciyarta ta daina yi mata amo mai armashi da alamun su ma sun gajiya da banzan tunanin da su keyi maras mafita zuciyarta da zafi idanuwan ta sun dai hawaye wanda a wani lokaci can baya in tayi kukan tana jin sauki amma ina yanzu babu kukan ma kan sa babu zuciya ta kekeshe ta daina wahalar da kai sai dai wasu HAWAYEN ZUCIYA da suke zuba wanda da alamun ba ranar tsaywar su suna kekketa mata sassa na cikin zuciya suna kokarin farka mata kirji da mugun zafin su mai radadi da firgitarwa.

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now