DUNIYARMU-19

594 47 4
                                    

DUNIƳARMU
Na
KAMALA MINNA
BABI NA SHA TARA

Mutuwar tsaye tayi, jin abin da Umma ke fadi wa malam kwanyar ta shiga Safa da Marwa zuciyar ta na faman bugawa da sauri-sauri kamar za ta faso kirjin ta ta fito idanuwanta lokaci guda suka kada sukayi jajir kamar an watsa mata barkonon tsohuwa jikin ta na 6ari fada cikin gidan su kan su sai da gaban su ya fadi ta shiga duban Umma cikin kunar rai tana nuna ta da hannu "kar ya ki ke wallahi ba zaki taba kashe min miji da dadim zance ba tuni ni dama tun da abun ya faru zuciya sam taki amanna akan cewa sace Salma akayi" ta ni sa sa'annan ta saki murmushi mai dauke da kayan takaici ta dora da cewa" kin san Allah sai kun fito mani da 'ya ta tuni na gama yar jewa zuciya ta ku ne kuka sace ta saboda tsabar bakin ciki da kuke yi yanzu dan kun ga asirin ku yana shirin fallasuwa shine ku ka shirya makarkashi domin dawo da ita to Allah ya toni asirinku"ta karashe cikin sakin kuka mai tsuma zuciya duk kan su mamaki ne ya cika musu ciki fal sun rasa ina ma zancen na ta ya dosa idanuwansu su duka sun zube akan ta gani suke kamar hankalin ta ya dan gusa daga jikin ta tsayin mintina biyar suka shafe a haka ba wanda ya yi kokarin cewa wani abu to me ma za su ce bakin su ne kawai ke rawa mamaki ne ya hasu cewa wani abu ko ya ya ne malam ya dubi Umma izuwa lokacin idanuwanta sun fara tara kwalla wanda ita kan ta ba ta san na menene shin na tausayin inna luba ne ko kuma na zargin maganganun da ta fadi ne ta ke tunanin akan ta tayi su nufin ta da hannunta wajan salwantar mata da 'ya kai ta shiga girgiza wa a ran ta ta furta 'ina kar kayi min haka lubabatu kar ki yi min mugun zato kar ki bari hankalin da nutsuwarki su gushe daga duniyar ki har su sanya ki aikata abin da zaki zo kina da na sani akan sa kaicon wannan rana kaicon irin wannan zargi kaicon zuciyar da hankalin ta ke gushe take kokarin dauwa dangin rai da bai ji bai gani laifi ba' hawaye suka shiga zarya masu tsananin zafi da kunar rai shi kan sa malam yanzu ya gama fahimtar in da inna luba ta dosa da zancen ta ran shi in yayi duba ya bace kamar wanda aka tsikara ya miki ya dubi Umma "ina Shukuranu yake?" yanayin muryar da yayi amfani da ita wajan furucin tayi matukar girgiza umma don karara fuskar sa ta bayyanar da bacin rai mara musaltuwa kai ta gyada masa tayi masa nuni da dakin sa bai tsaya jinkiri ya karasa dakin ya yaye labulan kwance ya hangoshi yayi rigingine idanuwansa da suke kallon rufin dakin sun kada sun yi jajir "Shukuranu maza ka tashi ka fito" a bazata ya ji furucin kuma abakin da bai yi tsammani va dom duk wainar da ake toya wa bai ma san ana yi ba daga kwancen ya dago kan sa ya dubeshi yanayin da ya ga fuskar tashi ya sanyashi sauyi tashi zaune kau da kai malam yayi "ta so muje" ya sake fadi ba yar da zai yi haka ya miki jikin sa gabadaya ya saki jiri sai kawo masa farmaki yake yi ya fra kokarin fitowa malam ne ya tsayar dashi gami da cewa "dauko wayarka ka taho da ita" bai musa ba ya dauko daga in take yashe yafito duk yayi wani irin firkai firkai da shi ko ta kan su Umma bai bi ba balle kuma inna luba wacce bai ma san anyi ruwan ta a wajan ba ya ja hannun Shukuranu su ka fice daga cikin gidan tashin hankali aka ce GOBARAR GEMU Umma da Shukura ji suke kamar su daura hannu aka su kurma ihu bakik ciki takaici tashin hankali duk shine ya ke shirin dauke musu numafashi maganar Inna luba ce kawai ke shawagi da kwakwalansu "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un ya Allah mun amsahi wannan k'addarar Allah ka mu ba ikon cin yi ta wannan rayuwa da mai tayi kama kai!kai! Ya ilahi in mutum na cikin duniyar nan ya na ganinmu gashi nan kayan kuncin da na takaici wani ko cin kuma na dadin rai tabbas rayuwar duniyar nan ba ta da mara ba da ZUMA DA MADACI" ta karashe cikin yanayi na som fashewa da kuka ba abin da ke zugurar zuciyar sai tunanin dan ta shikenan ta tabbata shi ne ya sace Salma tun da har iyayen ta suka nuna bacin ran su ai kenan kawai sai yarda Allah ya yi dashi yanayin da taga malam ya nuna da irin kallon da yake mata ta tabbata zuwa zai yi ya kai mata d'a a kargameshi cikin dakin da bata fata ko wani nata ne ace ya shiga daidai da rana daya balle kuma d'an ta ka cikin ta ita kam ta ga ta kan ta cikik duniyar nan wannam wata irin rayuwa ce take shirin tun karo su ba zato ba tsammani hawaye sha6e sha6e kan fuskar ta ta dubi Shukuea wacce izuwa lokacin taci kuka ta koshi har ta godewa mai duka ta juyar da ganin ta zuwa inna luba da take ta shar6an hawaye ta na jan hanci wani mugun kallo ta watso mata da sauri Umma ta dauke kan ta tana mai mai takaici da bakin cikin halin da inna luba take ciki don ta san tabbas takaicin rayuwa ne da na batar 'yar ta ya sanya ta aikata wanna mugun nufin gareta mamakin ta daya yarda shi kuma mijin nata ya hau ya zauna yanuna bacin ran shi akan hakan ya yarda da abin da tace yayi amanna ya dauka mat d'a ya kai shi domin a hukuntashi ko kunyar idon uwa bai ji ba ai ko mutuwa na jin kunyar mahaifiya balle kuma jinsi na Dangin rai ko da dai Allah ka dai ya san gaibu amma ita ba ta tunanin dan ta zai aika ta wannan nufin ga yarda su yaushe ma hakan za ta kasance in kuwa hakan ta kasance tabbad SO bai yi rana ba sai ta ce Allah ya tsinewa so in dai haka yake sanyawa wasu masoyan na aikata kayan takaici a rayuwar su...furucin da inna luba takeyi ne ya yanke mata dogon sharhin tunanin da ta afka in da take cewa "ki sani na wallahi tallahi na rantse da wanda rai na ke hannunsa in har wani mugun abu ya sami 'ya to kafatanin zuri'ar ki sai sun ka sa zama lafiya cikin duniyar nan dom sai na zame musu tamkar gobara daga kogi wajan tayar musu da hankali" ta dasa da jan kwa6a har da tukuicin tsaki kamar harshanta zai tsinke ta juya fuuuuu tayi waje baki sake Umma ta bita da kallo ta na gyada kai cikin takaici zuciyarta ba abin da take sai ta farfasa hawaye kuwa wasu na bin wasu akan kuncin ta Shukur ce ta rarrafo ta isa gareka ta dora kan ta a kafadar Umma idanuwanta na zubar hawaye ta ja hanci "rayuwar nan za ta yuwu a haka kuwa,mai ya sa wasu dangin rai ba sa duba lamarin rayuwar nan ne mai ya sa in suka shiga wani hali suke barin zukatar su da dauko musu kayan da za suyi nadama" "Uhmm" abin da Umma ta kokarta yanjo wa kenan daga kasar mukoshin ta duk maganar ma ji tayi ta na kokarin gagararta shuru ya ratsa su na yan dakiku ba wanda ya sake cewa komai sai ajiyar zuciya da suke saki lokaci-lokaci Shukura ta dago ta dubi Umma gami da cewa " na rasa abin da abban Salma ya ke nufi da daukar yah Shukuranu lamarin ya daure min kar ina tsoron kar abij da zuciya ta take zargi ya tabbata" cikin jan numfashi Umma tace" dama kin gasgata abin da zuciyarki ki miki hasashe akai don ba makawa hakan ce za ta kasance tuni ni na yarjewa zuciya ta abin da ke kike zargi"a razane tadage kan ta daga kafadar Umma ta na duban ta cikin rashin fahimta da rashin in da za ta dosa da zancen har ta bar zuciyarta ta daina zargi ta tabbatar hawaye suka sake balle mata "in kuwa haka ne wasu rayukan ba su san HALACCI ba wallahi" ta fadi cikin cizon la66anta "karki ga laifin su yanayi ne ya zo da haka don haka kawai ki bar furta komai ki bar wa Allah lamarin sa" gyada kai tayi gami da makalewa a kafadarta sukayi shiru suka shiga lissafin rayuwa duniyar nan wai su ne yau cikin WATA RAYUWA mai ciki da tararrabin kwanciyar hankali da natsuwa hawaye da kunar zuci na shirin zamame musu abokan rayuwa tabbas sun yarda duniya ba abin da babu acikin ta sai dai in ba ka zo cikin ta ba.
*** *** ***
"INA SALMA TAKE?" abin da ya ce kenan lokacin da suka hau dan sahu domin kai su station cikin yanayi na daurewar fuska sai ka rantse kiris yake jira ya kaftawa Shukuranu Mari ya rufeshi da duka tambayar ta zo masa a bazata hakan ya kara kidima shi ya shiga jan numfashi cikin karfi da ya ji don ji yake kamar in yayi sake mutuwa zai numfashin sa gaf yake da daukewa ya zakuda daga zaman da yake ya dan ba da tazara tsakaninsu dama su biyu ne kacal hakan ya dan firgita shi ya daga kai ya kalli malam da sauri ya mai da kasa don fuskar yarda kasan ba kayan rahama a cikin ta ko kankanin alamun fara babu balle ya sa ran zai ga hakoran sa waje. 'Ina Salma take' ya maimaita tambayar da akayi masa a kan sa amsa ta gagara ya rasa ma mai je ce me ya dace ya furta a matsayin amsa yanayin salon da tambayar ta zo masa ya tabbatar shi ake zargi da sace ta kenan 'Ina!' ya furta cikin karaji a zuci ya shiga girgiza kai alamun hakan ba zata ta6a tabuwa ba wai bindiga a ruwa in kuwa aka ce shi ya sace Salma to tabbas da ya cika maciyin amana maha'inci da kuwa ya tsine ma son da yake wa Salma don bai ga amfanin da yayi masa ba cikin rayuwa ya nisa cikin jan hanci "BANI NA SACE TA BA" da sauri malam ya dubeshi hakan ya kara kada masa yan hanji ji yayi kamar gudawa zai kunce masa a zuciya ya kama sallallami don gani yake kamar kafta masa mari zai yi saboda irin kallon da yake masa da jajayen idanuwansa "Gaskiya" ya furta cikin murya wacce ba yabo ba fallasa Shukurani ya gyada kai "Gaskiya" shi ma ya fadi cikin sanyin murya wacce take dauke da tararrabi ba wanda ya sake magana cikin su zuciyoyin su suka dauki aikin tunanin da neman mafita a haka suka isa station ba ma su san aikai ba sai da dan sahu yayi musu magana sannan suka dawo hayyacin su malam ya zaro kudi ya biya shi tare da yi masa godiya ya dubi Shukuranu "mu je" bai amsa illa duban station din da ya shiga yi gaban sa ya na tsananta faduwa malam na gaba ya na biye dashi da jan jiki har suka isa gaban sa bai dai na faduwa ba bakin sa ba abin da yake furta sai sunan Allah don ya gama yankewa da lamarin gabadaya ta tabbata shin ya sace Salma tun daga get suka fara cikin karo da ma'aikatan har zuwa ofishin su cikin girmamawa suka gaisa da juna don ganin malam babban mutum ne wani dan kyamurmuri mai gshin baki fari fat dashi mai zubin marasa lafiya ya dubi malam cikin raha da alamun dai har zuci haka yake da farar aniya "baba lafiya dai mu ka gan cikin halin damuwa mai ke tafe da kai?" malam ya nisa "ai tun da ka ganni a wajan ku kasan ai ba kalau ba" murmushi yayi sannan yace "baba kenan ai wajan na duk ba abin da babu na dadin rai da rashin sa yanzu dai sanar damu abin da ke tafe da kai" bai tsaya bata lokaci ba duk ya bashi labarin abin da ke faruwa tun daga batar Salma har labarin da Shukuranu ya zo dashi duk akan su sukayi ajiyar numafshi mai karfi su kan su labarin ya taba su ba kadan ba musamman da suka dubi malam da Shukuranu suka karanci halin da suke ciki "Allah ya kyauta" duk kan su kuratan wajan su ka fadi cikin halin ji mami na dai sukayi musu yan tambayoyi har da fayal sai da ka bude akan kes din ko da dai sun taba samun kes din amma ba ayu nasara waccan lokacin ba wajan babban ogan su su kai su Shukuranu nan zama akayi na sosai gami da tambayoyi akan yarda lamarin ya kasance nan ma ba su boye masa komai ba suka bukaci Shukuranu ya basu lamabar da aka kira shi da ita bai tsaya bata lokaci ba ya ba su su kayan magana kan za su je har kamfa in layin da akayi amfani da lambar domin ita ce kadai hanyar da za a fara bi don ganin abun ya zo da sauki godiya malam ya shiga sheka musu ganin da yayi an amshi kesi din da muhimmanci kuma sun ba su tabbacin za suyi iya yin su da ikon Allah don ganin sun cafke wanda yayi musu wannan yankar kaunar da haka sukayi sallama su fitowa bakin titi Shukuranu yayi ajiyar zuciya tare da godewa Allah akan abin da yake zargi ba haka bane da kan shi ya tsaida musu da dan sahu izuwa lokacin ya fara yin kurin dawowa hayyacinsa suka hau suka dau hanyar KAUYEN GURMANA.
*** *** ***
Cikin tsume fuska ta dubeshi "kasan Allah sai 'ya ta fito da na hakura amma tun da naga lamari akwai son zuciya da mugun hali ba zan lamunta ba dole a fito min da 'yata ko kuma wallahi kauyen yanzu a balle da rigima ta kin kwanciyar hankali" abin da ta ce kenan da malam bayan dawowarsa daga caji ofis ko sallamar da yayi ba ta amsa ba ta tare shi da sababi kamar wanda ya gillewa Sarkin Minna kai.😁 ko duban bai yi don iya kulawa ya gama yin ta zuciyarsa ta zo wuya ya san in har yace zai furta wani abu to tabbas za ayi ba dadi kowa sai ran sa ya kar 6aci ya ja hanci gami da kwa6a hakan ya kara tunzura ta ta shiga duban cikin wani irin kallo ji take kamar ta kafta masa mari don haushi da kunar rai "mahaukaciya ka mai dani malam ya ina maka magana amma ni da banza duk daya a wajan ka" nan bai ce da ita kala ba illa ajiyar zuciyar da yayi yana mamakin Luɓaɓatu tun da yake da ita bai ta ba ganin ta yi masa irin wannan halin ba sai yau tabbas ya yarda 'ya mace karamin tunani gareta abu kalilan ke canza mata akalar natsuwar tunanin ta "Uhmm" abin da ya kokarta cewa kenan cikin jan numfashi ya doshi dakin sa ya na mai kokarin cire bababar rigar sa wacce izuwa wannan lokaci ta gama jikewa jagaf da gumi "malam tsakani da Allah bai kama ka mai dani mahaukaciya ba akan gaskiya ta haba ina dalili ina mafari a cuce kuma a hanaka kokarin kokawa akan cutar da akayi maka"ta karashe magana cikin muryar mai rauni hakan ne ya sanya malam sauri tsayawa da tafiyar da yake yi ya juyo ya dube ta ya nisa "Gaskiya..." sai kuma yayi shiru yana girgiza kai cikin alamun bai ji dadin abin da tayi ba "wa ya cuce ki da kike ikirarain an cuce an hanaki kuma ki fadi" yanayin da yayi maganar cikin bacin rai ya santa ita sake hawa sama don gani take ai wannan rainine ga ga mari a tsinka jaka amma a hakan ma ba za a saurarawa mutum ba..."tambayarki nake waye ya cuce ki" ya sake fadi yana mai kafe da idanuwan sa wanda har a wannan lokacin ba su komai yarda suke ba yatsina fuska tayi sannan tace "ai ba sai na sake mai maitawa akan abin da ya faru sarai ka sani sai da nuna min da kake so kayi iyalan Umma sun fini matsayi a wajan ka tun da har za suyi min laifi amma baka ga bakin su sai nawa ni da ya dace ace ana tausayimi da tayani jimamin" izuwa wannan lokaci ya gama kunburewazuciyarsa kadan ta rage ta har zuko waje "banson salo da rainin hankali kin ji mai ya sa kuma mata kuka fiye karacin tunanin sam ba kwa lissafi kafin ku aiwatar da abu ba kwa ciza kawai kuke amayowa kuma da kike cewa anyi miki ba daidai duk haukar banza ce da rashin hankali yaushe za ace Umma da iyalanta ne za su sace miki 'ya ina aminci da yarda dake tsakaninku...'" sauri ta tari numfashin sa "wallahi dan adam ba abin yarda ba ne ai ba a shedar sa cikin duniyar nan..." da sauri ya tare shima "to ni dai ba za ayi wannan abin kunyar dani ba wallahi tun da ke na lura sam imaninki ragange ne ba kisan kaddara ba" hawaye suka shiga zubo mata " eh dole kace haka mai dani kafira malam sai hankalin ka ya kwanta dama tuntuni na lira kai lamarin batar Salma sam bai dameka ba sabida ba kai neka sha wuya wajan haihuwar taba" ta rushe da kuka mai cin rai iyakar haushi da takaici maganganun malam ya ji su sai dai ba yarda zai yi don ya fuskanci har yanzu ba cikin hayyacin ta take ba gyada kai ya yi sannan ya fada cikin dakin sa cike da tunane tunane masu taba zuciya da sanya rai ba ci duk ya ji duniyar ta yi masa zafi matuka gaya ba abin da yake furta sai 'Innalillahu wa inna ilahir raji'un Allahumma ja'allini fi musifatin' lamari ya kara rincebewa cikin kankanin lokaci kwanciyar hankali da ka samu na dan lokaci ya sake kaucewa Inna luba batar Salma ta dawo mata sabuwa filla ita ala dole zargin Umma da Shukuranu take akan sune suka batar mata da ya malam kuma ya goya musu da baya ya ki daukar mataki tun malam na hakuri har hakuran sa ya kare kullum cikin bata suke ta hana kowa kwanciyar hankali kullum ta na zarya kan haryar gidan umma tana gaya mata ba dadi Umma kuwa ba ta tanka mata sai dau ta bi ta da kallo ta na gyada kai don ta gama hakikance wa Lubabatu batar ta fara zautar da ita sai du'a' kawai abin da ya cancanta da ita kenan cikin rayuwarta Umma macece mi hakuri da kawaici da kai zuciya nesa ba ta dauki abin da Lubabatu ke mata da zafi ba ta hakurkuraar da zuciyar ta don ta gama tabbar da cewa komai daren dadewa akwai ranar da zata zo gaskiya tayi halin ta ranar da zatayi nadamar abin da tayi mata ita dai fatan ta Allah ya bayyanar da Salma ko hankalin kowa zai kwanta natsuwa ta dawo rayuwarsu ta nisa cikin dogon tunanin da ta fada a daidai lokacin Shukura ta shigo jikin ta sanye da kayan makarantada alamun makaranta ta dawo kusa da ita ta zauna bayan ta cire hijabin ta rataye "Wash Allah na" Umma ta dube ta gami da cewa "sannu hala ga jiya ce" "Umma ba dole nagaji ba wannan jarabarwae da muka fara ai ba sauki gareta ba wallahi ji zakayi kamar kwanyar zata tarwatse saboda kawai neman abin da zaka nazarta ka taimakawa kan ka" murmushi tayi "haka rayuwar take Shukura sai an sha wuya akan sha dadi ai karatu duk wuyar sa to mutum ya daure yayi sa domin shine MADUBI a rayuwar nan musamman yanzu da ZAMAƁI YA CANZA sai da karatu komai ke tafiya yarda ake so komai zakayi sai ka kasance kana da dan kwalin nan ko na sankadire ne domin zai taimaka maka a rayuwa shiyasa nake so ki kokarya ki kammala ko da sakandire ne saboda hakan zai amfanar dake saboda rayuwar ya mace da kike gani gajera ce cikin duniyar nan da ta girma ta isa aure anyi mat shikenan kuma in ba wai ta samu miji bane mai son ganin tayi karatu ya bar ta tayi amma dai mafi Alheri ace ya mace tayi kartu ko ya yake kafin ta shiga dakin auran ta" Shukura tayi kasace ta najin bayanin Umman ta duk maganganun ta gaskiya ne ya mace rayuwar gajera ce ba kamar da namiji ba in ta duba yayan in da shi macece da tuni anyi masa aure har ya fara tara 'ya'ya amma da yake namjiji gashi nan har yanzu yana gara rayuwarsa ita kuwa nan da dan lokaci kalilan sai kaji ana cewa gidan wani za akai ta amma ita a rayuwar ta tana da burin ganin ta zurfafa ilminta t zama wata wacce zata kasance mai taimakwa rayuwar wasu duk ta fuskanci maraici a rayuwa bai yi ba mahaifi babban bango ne a rayuwar iyalin sa in kuwa aka ce baka da mahaifi rayuwar ta na raguwa ta wani fanni ko da dai ita ma uwa jaruma ce sosai akan 'yayanta in tayi duba da mahaifiyar su da komai ya dauri akan ta duk yarda za tayi ta taimakawa kan da 'ya'yan ta cikin rufin asiri ta sani tun suna kanana gashi yanzu sun fara mallakar hankalin su girma ya fara zuwa cikin duniyar su sai dai har yanzu Allah na taimaka musu da kuma yayan ta wanda ya sadaukar da komai nashi domin ganin su cikin farin ciki da kwanciyar hankali sai dai cikin kankanin lokaci WATA KADDARA mai dauke da kayan damuwa tana kokarin dauke musi walwalar su Tuna halin da suke ciki yasanya zubda kwalla ta dubi ummanta ba tare da tace da ita komai ba ita ma Umma idanuwanta na kan ta murmushi tayi mai tattare da damuwa ta nisa "Halin rayuwa sai hakuri Shukura na san abin da kike ji azuciyar ki kan lamarin nan da kaddarar rayuwa da muka fada dai mu cigaba da Addu'a Allah ya sassauta mana ya ba mu ikon ganin mun cinywa wannan jarabbatar da yayi mana Shukura ta amsa da " Ameen" ta sanya hannu tagoge kwalla da suka
zubo mata..

Pilis and pilis
Voter and comment
KO yaya ne
kamala din kune dai mai son ku da kaunarku har birnin zuciyarsa

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now