DUNIYARMU

1.6K 61 1
                                    


DUNIYARMU

(c)Kamala Minna

BABI NA UKU
Teemah kwance sai nakar barci takeyi hankali kwance kallo daya zakayi mata kasan adon gari an ji jiki ba kadan ba.
kan ta daure yake da bandeje kimi guda kamar gammo fuskarta ta tasa kadan alamun ta bugu sosai akai can gefe guda SK ne zaune ya buga uban tagumi kamar Wanda akace uwar sa da uban sa sun mace yake zaman jimami da jaje lokaci lokaci yana duban Teemah da ke kwance ta na narkar barci fuskar sa gabadaya ta sauya damuwa gami da Bacin rai duk sunyi wa duniyar rayuwarsa kaka gida zuciyar sa na azalzala gami da kunar rai lokaci lokaci sai ya ja tsaki can kasar makoshin sa sannan ya kalli Teemah.
a hankali ya sanya hannu cikin aljihunsa ya zaro dankareriyar wayar sa wacce kallo daya zakayi mata kasan ba kana nan kudi aka turmushe kafin a mallake ba.
Ya shiga lallatsa ta cikin yan dakiku ya kai ta kunne da alamun kira ya ke son yi.
can ya nisa hadi da kara daure fuska hakan zai tabbatar maka da cewa wayar da zai yi ba ta muradan jindadi ba ne
"sannu kin kyau ta Ayshanty,ban ta ba zato ko  tsammanin ba ki da hankali ba sai yau Ashe ke mahaukaciya ce  wacce ba ta San abin da takeyi ba kin ba ni mamaki wallahi..."
da sauri ta katse shi cikin hargowa "kaga ba na bukatar wani sauki burutsun ka nifa lamarin ka ya fara shallake tunani na na lura borin kunya ne kake son nade tabarmar sa da hauka, to bari kaji na gaya maka, wallahi tallahi bilalhilazi kaji na rantse ba zan taba barin wata yar iska karamar kilaki wacce a barikin ma ba ta san komai ba mu na hada mu'amala a inuwa daya ba kai da kake gani don ni kadai aka halince ka ba a halinceka don in raba ka guda biyu ba ni kadai ce zan mallake ka har karshen rayuwar ka..."
"dallah rufe min baki karya kawai maras tunani"
SK ya fadi a kufule da tsawa
amma hakan bai razana ayshanty ba illah wata irin mahaukaciyar dariya da ta saki daga cikin wayar ka na jiyo sautin tafin hannu da ta ke yi sai da tayi mai Isar ta San ta fara magana cikin izza da Nuna gadara.
"haba SK duk wanda hauragiyar taka ba zata tsorata ni ko firgita ni ba kai kan ka ka San ni ba na shayi ko shakkar duk wani Abu da zakayi min don na San ba iya wa zakayi ba kawai shafcin gizo ne da zancen kila wa kala duk maganganu na ka daukar su nake kamar tatsuniyar gizo da koki"
Iya kuluwa SK ya kulu ji yake kamar Ayshanty na gaban sa ya turmushe ta ya shaki wuyanta har sai numfashin ta ya fara barazanar daukewa ya nuna mata shi namiji ne mai ZUCIYA DA KWANJI bai ya daukar rai ni ko don ta ga ya na sakar mata fuska ta gane makwancin sa shiyasa za ta dunga yi masa abin da ta gadama to sai ya nuna mata shi namiji Wanda ba wata 'ya mace da ta isa ta juya shi son ran ta zai nuna mata asalin mazajantakar sa.
ba tare da yayi yin kurin sake yin mata magana ba ya sauke wayar gami da kashe ta ba ki daya Wani dogon tsaki ya ja a daidai wannan lokacin Teemah ta farka daga nauyayyan barcin da take yi
da sauri ya tashi ya isa gareta cikin marerecewar murya da idanuwa sannan ya ce
"Teemah don Allah kiyi hakuri ki ga farce ni na san duk ta dalili komai ya faru dake duk ni na ja miki da na kasa kwatar miki yancin ki kuma na hanaki kamar da kan ki..."
a wahalce ta daga masa hannu
"ya isa haka SK ba na bukatar wani ban baki ko hakuri daga gareka saboda duk abin da ya faru ba laifin ka ko kankani"
bin ta yayi da kallo cikin Nuna rashin fahimta a zancen ta yanayin da tayi maganar ba ta nuna wani alamun bacin rai ba amma shi dai yasan dole a cikin zuciyar ta akwai haushi gami da takaici abin da ya faru ko da kuwa ba ta bari fuskarta ta bayyana ba.
duban ta yayi tare da nisa wa
"please Teemah.."
"don Allah kayi shiru bana bukatar jin wata magana da ga gareka infact surutu sam ba na bukatar sa a irin wannan halin da nake cikin don Allah kayi hakuri"
tana gama magantuwa ta juya ta bashi baya alamun tabbatuwar abin da take fadi
shiru yayi tare da kama ha6a tabbas dole Teemah tayi fushi domin kuwa an ya ga mata rigar mutunci amma in yayi tunani ta wani bangare rayuwar bariki ta gaji haka tamkar alalar gero take in ka iya ka fidda kan ka in kuma ba ka iya ba ta kwa6e maka.
"TEEMAH" ya kira ta cikin murya mai matukar taushi da jajantawa zuciya da take cikin halin fushi.
Sai da ya numfasa sannan ya nisa ya cigaba da cewa
"ya kamata duk wannan fushin ki aje shi gefe yanzu ba lokacin yin sa bane kamata yayi ki bukaci lafiya jikin ki domin ita tafi komai muhimmanci a rayuwarki don Allah Teemah ki mai da komai ba komai ba"
da hanzari ta juyo ta dubeshi gami da tashi zaune ido cikin ido suka shiga duban juna tsayin mintina kamar uku sannan Teemah ta nisa
"tafiya zan yi gida ka kira likita ya sallameni"
shiru yayi bai yi mata magana ba hakan yayi matukar tun zura ta da sauri ta zare allurar Karin ruwan da akeyi mata ta mike cikin yanayi na rashin karfin jiki tashiga rarraba ido alamun ta na son ganin wani abu na ta can ta hango jakarta da sauri ta kai hannu ta sungume ta tayi hanyar fita hakan da SK ya gani tayi yayi hanzarin mikewa ya tare gaban ta tare da ware hannu alamun ba za ta wuce ba
Kau da kan ta tayi dan ta lura in ta cigaba da kallon sa zai karya mata alkadarin ta
"bani hanya na wuce"
ta fadi rai ba ce
"In naki fa?"
shiru tayi ba tare da tace masa komai ba
tun ta na jure tsayuwar har taji kafar ta ta fara karkarwa alamun ta fara gajiya da tsayuwar a wahale tace
"In kana yi wa Allah ka bar ni na wuce in ba so kake ka haifar min da CIWON RAI  ba, kamar yarda aka kakabamin wannan"
ba tare da yayi yin kurin cewa wani abu ba ya kauce ya bata hanya da sauri tayi ficewar ta hakan ya bashi damar bin bayan ta da kallo har sai da ya ga ta fice sannan ya numfasa cikin yanayi na jajantawa kai.
***   ***      ***  ***
horn din motar da ke amsa kuwwa shi ya fargar da mai gadin gidan da sauri ya aje rediyo dake hannun sa wacce ta dauke masa hankali da hanzari ya mike har yana kokarin yin tuntu6e ya isa bakin get din ya dan bude yar karamar kofar da ke jikin get din ya leka domin ganin wanene lokaci guda ya watsa idanuwansa waje alamun tsoro da sauri ya fara kokarin bude get din, tun kafin ya isa matsaya ta cinno hancin motar cikin gidan da sauri ya ja gefe don saura kadan tayi ciki dashi ido ya bi motar da shi yana mai girgiza kai alamun damuwa da haushi ya mai da get din ya rufe duk idanuwansa na kan motar can gefe guda tayi parking sannan ta fito daga can in da take ta watso masa wata uwar harara gami da tukuicin tsaki, sannan ta yi hanyar da zata sada ta da cikin gidan baki daya ta na isa tayi knock din kofar da zata sadata da babbar falon gidan tsayin mintina biyu amma shiru ba alamun za a bude cikin yanayi na jin haushi ta sake knock din kofar amma wannan karon da karfi tayi sau uku ajere
daga can cikin falon ta ji an tanka cikin daga murya da kwakwazo
"wanene?"
Ya tsine fuska tayi sannan cikin izza tace
"ni ce"
ba ta ji an sake tsikawa ba illa tsaki da  taji anyi can kasa-kasa nan ma sai da aka dauki akalla sakanni arba'in sannan taji an fara kokarin bude kofar ji tayi kamar ta dauke mai bude kofar da mari in ya bude saboda tsabar haushi da takaici da taji in ba rainin wayo ba menene wannan mutum na kwankwasa kofa amma abude masa amma sai an gama wulakantashi tsaki taja a daidai lokacin aka bude kofar
bin ta tayi da kallo a wulakanci sannan ta fara kokarin shige wa cikin falon har ta na bangazarta.
"sannu maras kunya fitsararriya wacce ba ta san mutunci ko darajar mutane ba"
da sauri Teemah ta ja burki ta tsaya ta juyo cikin mirgina kai gami da yatsine fuska.
"ai in kika ga an  mutunta mutum ko an ga darajar sa to shine ya fara daraja kan sa sannan zai samu takomashin wasu su karrama sa"
ta na fadin haka ta juya tayi cikin dakin ta da sauri.
kwa6a hajiya deenah ta ja gami da cewa
"zan yi maganin ki ne yarinya duk ki gama jalla Ku jallan ki zaki shigo hannu na zaki gane baki da wayo"
Komawa tayi ta zauna kan daya daga cikin luntsuma-luntsumar kujerun da sukayi matukar kawata falon kallo daya zakayi masa ka tabbatar an kashe daloli wajan wanzar dashi duk wani Abu na more rayuwar jindadi da armashi an ta naje shi cikin wannan falon babu ce kawai za ace ba ta samu muhalli acikin sa ba.
hajiya deenah ta dauki abin canza tashar talabijin tashiga sauya wa har ta kai tashar da take muradin gani AREWA24 a daidai lokacin sun fara gabatar da shirin DADIN KOWA hankalin ta gabadaya ya raja'a kan kallon da takeyi amma zuciyar ta tana hasko mata Wani abu na daban Wanda ya yi matukar daure mata kai matuka gaya tambayar da takeyi wa kan ta shi ne: 'shin me ya sami Teemah har ta ji wannan mugun ciwon akan ta?'
Ta na cikin wannan tunane-tunanan ta ji sallamar Alhaji Muktar da sauri ta yaki ce tunanita taje gefe ta mike cikin kissa da salo na Jan hankali ta nufi in da yake tsaye ya zuba mata idanuwa kamar Wanda aka cewa in ya dauke ganin sa daga gareta za ta gudu.
tafiya take ta na faman kada duk wani sassa na jikin ta har ta isa gareshi ta watsa masa wani kallo mai saurin firgita duniyar Wanda ya dulmiya cikin duniyar son mai kallon sa sannan tace cikin kashe murya.
"dear sannu da isowa"
ta shiga kokarin amsar jakar dake hannunsa
"sannu da gida deenah dafatan komai lafiya ba wata matsala"
ya fadi ya na murmusawa gami da daga mata gira.
ya tsine fuska tayi tare da cewa
"bakomai sai dai abin da ba a rasa ba"
da sauri ya dago ta daga durkushen da take gaban sa ya kafeta da idanuwa
"wani abu ya faru kenan ko?"
ta gyada masa kai ta shi kokarin zare jikinta daga nashi ta na mai cewa
"zo mu shiga daga ciki ka huta kayi wanka sannan kaci abin ci ko naga alamun yau ka gaji matuka duk kayi laushi da yawa da alamun sai nayi maka tausa sosai yau baby ya ji jiki wajan aiki"
Ta karashe maganar cikin sigar zolaya tana mai kyalkyala dariya shi ma sai ya biye mata a haka sukayi hanyar dakin kwanan sa domin taimaka masa yayi komai kamar yarda suka saba.
**   **   **
gudu take zabgawa kamar wacce zata tashi sama,kallo daya zakayi wa fuskarta ka tabbatar ba karamin tashin hankali bane yayi wa duniyar rayuwar ta k'awa.
Idanuwanta sun kada sunyi jajir kadan ne ya rage ba su zubda ruwan hawaye ba azahiri amma abadinance zuciyar rugugi take tare da tarwatsi gami da Bacin rai kirjin ta na wani irin bugu kamar zuciyar zata faso ta yo waje.
Wani mahaukacin birki ta ja ta tsaya dalilin kaiwa wata mota mafarmaki da tayi har sai da ta tayar da kura hankalin mutanan dake kan hanyar ya juyo garetaa yanayin da ta Nuna ko ajikin ta illa tsaki da ta ja gami da kaiwa sitiyarin wani wawan bugu sannan tasake yi wa motar key ta ja da baya da gudu ta fincike ta bar mutane tsaye da sakanken baki.
cikin wannan yanayi ta isa cikin unguwar sarki duk da mutane da suke kai kawo bisa hanya bai sanya ta ta rage gudun da takeyi ba har ta isa kafcecen get din gidan ta tun kafin ta isa ta fara horn sai ka rantse wani gida na kusa da ita take wa horn amma akwai gida kusan uku da zata wuce sannan ta kai nata gidan haka masu gadin gidajen suka fara kokarin lekowa don ganin wanene amma da sun ga ita ce sai su ja tsaki su yi komarwa su.
ta na isa tayi wani mahaukacin horn Wanda in har kana kusa da ita sai ta tarwatsa maka kunni ta kashe maka ji a banza a hofi
lokacin da mai gadin gidan ya leko a razana ya na ganin ta ya ja burki ya tsaya idanuwansa waje ganin irin kallon da takeyi masa ya sanya shi saurin kaiwa get din cafka daidai karfin sa ya shiga turashi tun kafin yayi rabi ta iso get din yana ganin haka cikin yanayi na ceton kai yayi tsalle ya ja gefe ya tsaya jikin sa na kyarma kamar wanda aka yi wa juyen ruwa mai tsananin sanyi.
Wata uwar harara ta cilla masa gami da daka masa tsawa wanda yayi sanadiyyar kadawar kayan cikin sa cikin barin jiki ya dawo ya karasa bude get din a tsorace ta fizgi motar tayi cikin gidan ko in da ake aje motocin ba yakai ba tayi parking nan tsakar gida ta fito cikin hanzari hannunta rike da jaka da mayafi ta zaro wata doguwar riga daga bayan motar ta ta sanya bisa matsiyantan kayan da ke jikinta ta yafe dan yalolan mayafin rigar sannan tadoshi cikin gidan duk abin da takeyi akan idon mai gadi mamaki duk ya gama ciki masa zuciya da kwanya ya kamata ace in da sabo ya saba da wannan bakin halin na uwar dakin sa gyada kai yayi gami da cewa "allah ya ganar dake gaskiya"
ya koma mazaunin sa ya zauna ya cigaba da nazarin irin wannan kazantacciyar rayuwar da ta addabi duniyar mu.
ta shigar cikin falon ke da wuya ta yi arba da Khalil kwance bisa kujera ya hada hannayen sa duk biyu ya daura bisa Kansa idanuwansa sa na fuskantar saman dakin.
burki ta ja ta tsaya cikin alamun mamaki amma ba na tsoro ba da sauri tayi wajan sa tana isa ta yi cilli da Jakarta da ke hannunta gefe ta zare dan yalolan mayafin da ke kan ta ta sanya hannun ta ta shafi goshin sa tare da fadin
"Allah sarki my K kai kadai acikin gida sai kace maraya"
ta karashe cikin shagwa6ewar murya da alamun tausayi gareshi
da sauri ya tashi zaune ya kafeta da idanuwansa dara-dara masu launin ruwan rose sai sheki sukeyi
"kin wahalar dani da yawa, tun dazu na dawo na samu gidan ya zama kango dalilin baki aciki"
murmushi tayi sannan ta janyoshi jikinta kamar wani dan karamin yaro "yi hakuri kaji my K gani na dawo yanzu komai ya wuce aiko"
Ya mirgina kai cikin rashin kuzari yace"ji be ni sai tsami nakeyi tun da na dawo ko wanka ban yi ba dalilin rashin ganinki"
cikin yanayi na tausayawa tace"kayya my K tashi tashi ba  zan yarda ka zauna da tsami ba kar wani ya shigo yace mijin gidan ma tsami yakeyi wannan ai abin kunya ne"
cikin sauri ta mike ta ja hannunsa alamun ya tashi ya kokarta ya miki ta ja hannunsa sukayi ciki dakin barcin su suna shiga ya zube zaman gado cikin rashin fahimta ta dubeshi "me nene haka kuma?"
luuuu ya tafi kamar zai fado kasa daga kan gado murya a kasale yace "barciiii"
zaro ido tayi gami da tsuke fuska
"ka na nufin haka zaka kwanta ba tare da kayi wanka ba to Sam ba zan yarda ba kuma in har kace barci zakayi yau ba za ka kwanta min kan gado da tsamin jiki ba don haka sai ka zabi daya barci ko tsaftace jiki?"
tun da ta fara magana yake bin bakin ta da kallo yarda take sarrafashi cikin salo da  kalamai masu matukar Sauti da burgewa, hure masa ido tayi ganin ya kafeta da kallo firgigin ya dawo haiyacin sa ya mike gami da zare kayan da ke jikin sa da taimakon ta ya rage daga shi sai gajeran wando Wanda iyakar sa gwuiwa sai singilet ita ma zare doguwar rigar ta tayi wata irin zabura khalil yayi ganin irin fitinannun kayan da ke jikin ta Wanda dasu da babu duk daya
ta lura da haka amma sai ta nuna kamar ba ta san yanayi ba ta ja hannunsa sukayi cikin toilet zuciyar khalil har zuwa lokacin ba ta rabu da razana da firgici ba ganin irin kayan da ke jikin Ayshanty kuma wai da su tafita unguwa ba ma wai acikin gidanta ta sanya su ba wani bangaren na zuciyar sa ta sanar dashi 'ka lura da wani Abu mana ai ba haka ta fice ba sai da ta sanya doguwar riga a sama Wanda ba ta bayyanar da irin kayan da ke jikin ta ba kai ma in ba don tacire doguwar rigar ba ba za kasan wani irin kaya ne ajikin ta ba'
wannan zancen zucin da yayi ya yi matukar tasiri a zuciyar sa har ya yayi Amanna da cewa ba wata matsala ga hakan tun da ta na suturta kan ta ko da kuwa ta sanya wadannan fitinannun kayan.
      a nashi fahimtar falsafar sa kenan

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now