DUNIYARMU-17

545 51 1
                                    

DUNIYARMU
Na
KAMALA MINNA
BABI NA SHA BAKWAI
SHARATON HOTEL.
Tun isar Heejat birnin kano ta yada zango cikin hotel din sharaton daki guda ta kama na musamman domin aiwatar da komai ba tare da ta fuskarci WATA MATSALA ba komai ta zauna nayi nazarin sa da lissafe-lissafe yarda komai zai guda na domin yarda ta fuskanci rayuwar Adam yarda yake gudanar da ita akwai cakwakiya domin kuwa NAMIJIN DUNIYA rikanken kadangaren baki labarin sa dabtaji ta yi matukar shan mamaki domun ba ta taba zaton tattirancin nasa ya yi tsamari haka ba cikin kano da kewayan ta ba wanda bai san Adam Tanga ba rayuwarsa gabadayan ta kasar waje yayi ta mahaifin sa karatu ya tura sa amma ba karatun sai ya bige da neman mata acan mace mai amasa suna mace ba wacce Adam bai sani ba duk cakwakiyar da yake yi mahaifin sa bai da masaniya sai da domin mahaifin yarsa ta rasu shi kuma mahaifin nasa ba mazauni bane kasashen waje yake fita bai fiye zama a gida najeriya ba Adam ya fara lalata rayuwarsa ne tun ya na firamare bisa sakin mahaifin nasa bai ganin laifin sa ko daya ko mutanan unguwa ya bata wa in aka kawo kara sai mahaifin yace an sanyawa dan sa ido sai kace shi ka dai ne d'a  cikin unguwar rashin mutunci iri-iri ba wanda vai yi mahaifin Adam da ya ga an ta kurawa dan nasa ya na gama firamare ya fidda shi waje wai zaman najeriya sam bai yu ba an fiye takurawa da tsangwamar 'ya'ya to dai garin neman gira sai aka rasa idanu har da girara kan ta domin kuwa ko kammala sakandire bai yi ba Adam ya fara har karmata domin kasancewar sa kyankyawar matashin saurayi (black beauty) mai suffar tsari na halintar ingarmar maza hakan ne yaƙe firgita mata ko bai ce yana so ba za a taya masa kai yan masu jajayen kunnuwa da yan matanmu na gida najeriya hakan rayuwarsa ta kasance har ya kammala sakandire din sa amma bai dawo gida ba sai da ya daura digiri bai laifi kwanyar sa na ja sai dai fa sharholiyar da yake yi ta shallake tunanin mai tunani matuka gaya yana aji biyu a digiri din sa ya ziyarci gida najeriya in da wannan zuwan ne SILAR ƘADDARAR bahijja.Zaune take cikin harabar otel din ta fito domin shan iska jikin ta sanye da wasu bakaken kaya riga da wando wanda su kayi matukar amsar jikinta duk wasu surori na daukar hankali duk wani namiji mai lafiya sun bayya ko ina jikinta motsi kalilan za tayi su shiga kadawa musamman kirjin ta da mazaunan ta fuskar na kuwa taji kwalliya na fitar hankali idanuwanta darara masu launi fari sun fes dasu tsakiyar su kamar an zuma ruwan gold a ciki in ka kalla za ka ga kamar ruwan ne kwance ga girar ta da tayi gazargazar bakin nan nata kamar an yanka mata shi da reza dan tsut dashi mai dauke da la66a jajaye hancin ta dan zir dashi mai daukar hankali.kallo daya zakayi mata ka tabbata zaman da take akwai abin da take tunani akan sa bi sa lakari da fuskar tata yarda ta nuna rashin walwala hausa sun ce LABARIN ZUCIYA a tambayi fuska to hakan hejjat take numfashi ta aje lokaci guda ta juyo izuwa bayan ta jin motsi kamar kusan to ta ake yi matashin saurayi ne wanda akiyas ce ba zai hau ra shekaru talatin ba dogo kyankyawa mai dauke da kyankaywar fuska komai ya ji rabajau😜 kau da kai tayi lokacin da ta lura wajan ta ya yo ta sake tsuke fuska don abin da ta ki jini kenan wani namiji ya tunkaro ta abin yake hanata fitowa kenan daga cikin dakin ta tun zuwan ta cikin otel din don mafi yawancin lokaci in ta niyyar fitowa domin shan iska sai taki dan ta san tabbas in ta fito sai mazaje sun yo kan ta da sunan ke mantuwa takuma hakan sam! ba ya gaban ta don abin da ke gaban ta bashi da gami da wannan harkar a yanzu ba ma wannan ba in tayi wani tunanin sai ta tuna ita MATAR AURE CE ko da dai hakan ba ya zuwa cikin tunaninta sam! ta daukar hakan a wani abin yabo cikin duniyar ta...maganar da taji kunnuwanta sun jiyo ya sanya ta sauri katse tunanin ta da sauri ta dago kai ta dubeshi ya na tsaye gabadaya hankalin idanuwansa da nutsuwarsu suna kan ta ganin irin kallon da yake mata ya sanya ta kara tsuke fuska kamar ba ta taba yin FARA'A ba ta sunkuyar da kan ta kasa ba tare da ta yi wani kokarin magantuwa ba hakan ya kara bashi da ma ya sake tsinkawa "rayuwa fa ba ta son haka ko baka san mutum ba in har ka ga ya zo gareka kar kayi saurin yanke hukunci don baka san da me ya zo maka ba" jin furucin sa ya sanyata dago ta dubeshi ta nisa gami da kau da kai "amma kasan dai a duniyar da zamani ya sauya salo ba kowa dangin rai ake saurin amanna dashi ba" murmushi yayi mai kara wa fuskarsa kyau da kwarjini sannan yace "nasan da hakan amma ai ko sallama ya ci ace kin amsa ko?" ya fadi ya ami kannne mata idanu hakan ya kars ba ta haushi namiji akwai dan banza namiji akwai iya salon yaudara da rikita kwanya mace kai namiji sai Allah NAMIJI KENAN! bai cika kunya ba shi ba ruwan sa in dai ya ga abu ya burgeshi bai tsaya bin wasi hanyoyi kawai gaba gadi yake yo wa ko da kuwa  kwa6e wa za tayi nisa tayi sannan tace "to na amsa sallamar taka" zama yayi ganin fuskar da ta saki sannan ya sake kallon ta yace " sunana MANSOOR GALADANCI" duban sa ta shiga yi cikin mamaki kamar wanda ta tambaya ya saki baki yana fadi mata sunansa ikon Allah shi fa namiji duk yarda zai yi ya ga ya samu shiga ya iya sa murmushi ta saki "ikon Allah tambayarka nayi da ga zama sai kace mani ga sunan ka ni fa ba bukatar hakan nayi ba" lemon dake gabanta ya jawo ya kai bakin sa sannam ya aje "nima wai cewa nayi kin bukata ba akaran kai na nayi niyya kawai na fadi" "shikenan" ta fadi gajarce don ta lura dashi yana da surutu in har ta biye masa to tabbas ita za ta kwana ciki ya bata mata tunanin da take ciki wayar ta ta dauka ta mai da hankalin ta kan ta kacokan
Domin ba ta muradin wata hira ta shiga tsaƙanin ta da mansoor don ba ta bukata wani namiji ya kutso rayuwarta cikin wannan yanayin da take ciki na muradan aiyukan daukar fansa tsayin minti goma suka shafe a haka ba wanda ya yi kokarin tsinkawa mansoor da ya lura sam ba ta son magana shima sai ya biye mata ya ga iya guɗun ruwan ta amma da alamun in ya biye mata wankin hula zai kai shi har dare ya muskuta "zaman shiru sam bai da ce da mu ba wallahi ya kama ta ko yar hirar duniya ne muyi da wannan shirun da muka kinkimowa kan mu" ta ji shi sarai amma sai ta nuna sam ba ta san ma ya nayi ba wayarta ta zubewa ganin ta "ban san sunan ki ba ya dace izuwa wannan lokaci ke ma ki fada min naki ko da dai kin ce nawan da na fada miki ba bukata kikayi ba" ya sake fadi cikin son dai ta yi magana amma har zuwa wannan lokacin ba ta da niyya ba tare da ta sani ba ya kai wa wayar hannunta cafka da sauri ta dubeshi cikin wani irin kallo na ban so abin da kayi min ba murmushi ya saki duk da ganin sauyi a fuskar ta hakan yake so don ya san zata tsinka ko da kuwa ba ta so ba don shi maganar ta kawai ya ke so ya ji  hannu ta mika masa cikin daure wayar fuska don ta lura dashi dan shisshigi alamuran da bai shafeshi ba hakan ita kuma ba ta mata yayi "ban waya ta" ta fadi cikin murya mai son shiga bacin rai kafada ya make mata alamun ya ki ya sake cewa "ban waya ta" nan ma ya nuna alamun yaki t sake bukatar ya bata wayarta karo na uku nan ma ya nuna alamun ya ki izuwa lokacin ta gama tunzura ta mike rai bace ta kare masa kallo tun daga kan sa har zuwa kafarsa ta ja wani mahaukacin tsaki kamar harshan ta zai tsinke ta suri jakar ta ta na kokarin barin wajan ya yi saurin mikewa ya riko mata hannu hakan ba karamin bata mata rai yayi ta na juyo ta dauke shi da mari tare da nuna shi da hannu "bana cikin sahun matar da ake yin galaba akan su a ko wani lokaci ka kiyaye" ta fadi tana mai karkada dan yatsanta ta sanya hannu ta fizge wayarta ta wuce ta barshi tsaye sake da baki da hanci mamaki da tu'ajibi sun cika masa ciki ya shafi kuncin da ta mareshi gami da kissing din wajan ya yi murmushi irin na su na yan duniya  ya juya ya dauki key din sa da ke saman teburin.
Rai ba ce ta isa dakin ta t yada zango bisa gadon dakin ta yi rigingine ta mai tunanin lamarin yan mazaje komai ya sa su ba su da kunya ne a rayuwarsu ba sa jin kunyar ko ke wacece su tunkareki musamman maza yan duniya ba su da burin da ya wuce su ga sun mori ya mace ko wacece su ba su dauki mace a bakin komai ba sun mai da ta kamar riga sai wacce suka ga damar sanyawa ba ruwan su domin su duk abin da sukayi a ado ne a garesu ba kamar ya mace ba abu kalilan me zai tarwatsa mata rayuwa amma ba ayi mata uzuri sam ba a lura da raunin ta shin me aka mai da 'YA'YA MATA ne cikin duniyar nan sam ba a ganinsu da wani mutunci ko yanci ba a lura da raunin rayuwarsu gidan aure ba su huta ba haka ko a waje su hakan ba zai hana maza su yi musu abin da su ke so ba kai jama'a duniyar nan abin a ji tsoron ta ne da mazajen dake cikin ta...tunanin ta ne ya katse sanadin kiran wayarta da akayi ba ta tsaya duban wanene kawai ta kai kunnan ta muryar Mubasheer ta ji ya na mai cewa "hejjat ya dai dafatan kina lafiya yake ciki ne?" nisa tayi sannan ta ce "lafiya lau wallahi, ys kuwa ake ciki komai na tafiya normal ina tunanin yau akwai target din da zan hada domin akwai party da za ayi cikin otel din da nake kuma na musamman ne ina tsammanin zuwan sa wajan" Mubasheer ya ce "kina nufin har yan zu ba ki hadu dashi ba ne?" "na hadu dashi amma ba muyi wata alaka ba ina dai bibiyan sa ne domin ganin komai yard yake gudanar dashi domin in san ta yarda zan je masa" "ok to shikenan ina tsumayen ki zuwa safiya duk yarda ta waka na zan ji" ya na fadin haka sukayi sallama ba tare da sun wa ni batun ba dama ita ta fison haka
NIGHT CLUB.
ba abin da yake tashi cikin harabar otel din sai kide-kide da raye-raye na wakokin zamani na mutanan kudancin kasarmu ba wata waka da za kaji wai kace da dan bahaushe ne kallo daya za kayi wajan ka kau da kan domin maza da mata ne matasa masu ji ajika su ke rawa ta tsinancewa da wasu irin sutturu na fitar hankali wanda sam wani mai tarbiya ba zai so ace ya san ya su ba gefe guda kujeru aje wanda ba da bukatar yin rawar ko kuma sun yi sun gaji suna zazzaune su huta hayaki da hamamin kayan maye kawai ke tashi gabadaya wajan ya turnuke da wani irin wari wanda sam ba dadi shakar sa sautin da ake saurara ne ya dauke wajan ya dauki ihi da kururuwa da kunduma kundumar ashariya da alamun masu shagalin ba su ji dadin haka ba wanda suke cikin hali maye har kwalaban da suke hannayensu suka shiga rotsawa da kasa alamun dai ran yan maza sun baci sautin ne yasake wanzuwa mai matukar kara da gigita kunnuwan wanda bai sama sauraro ba haba kamar wanda aka cikara suka cigaba da rawa ta tsinancewa da lalacewa yarda kasan wadanda bakin duniya ya kama su ko daya yake duk wanda ka gani cikin wajan nan ba za ka daukehi mutumim arzuki ba mai mutunci domin duk wata lalacewa da rashin kunya da zubda mutunci ya tabbata a gurin  motar Hejjat ce ta sanyo kai cikin wajan ita ma na ta sautin na ta shi amma ba zaka taba ji ba in har ba cikin.motar kake ba domin sautin da ke tashi cikin club din kamar zai tarwatsa wajan haka yake gefe daya ta samu tayi parking sannan ta sauki gilashin motar ta ta ta shiha duban wajan tsayin minti biyar sannan ta fara kokarin fitowa daga cikin motar kafar ta ta zuro mai dauki da wani takalmi mai matukar tsinin dunduniya mai kalar baki da fari yantsun kamar nan nata zara zara sun sha jan lalle sai kyalli su da daukar ido duk da dare nr hakan bai hana kyawu da gogewar kafar ta ba ga wani fitinan nan kamshi da ke fitowa daga motar lokaci guda ta fito doguwar riga ce a jikin ta mai hannun bes wacce tayi matukar kama ta daga kirjinta zuwa kugun ta daga kasa kuma ta bude anyi mata cin baki da wasu duwatsu masu ruwan gold haka ma daga samar rigar surarta gabadaya ba abin da ta buya kan nan nata kuwa ya ji gyara yayi bakinkirin sai kyalli yake yi ta zuboshi saman kafada sai reto yakeyi daga gaban goshin ta nan ma anyi parking din wani wanda shi ma ya sha ado da wasu duwatsu mai kyalli da daukar ido kamshi kuwa ba a maganar sa ajikin ta don kamar cikin turare aka tsoma ta ka fitar hannuta rike da jaka kalar takalmin ta haka wayarta an sanya mata condum kalar jakar hakan sai ya kara ba da Fashion a dreesing din nata hankulan maza da mata da ke kan kujeru duk yayo kam ta sun zuba mata ido ko kaftawa ba sa yi wasu jarababun ma har lasar la66an su sukeyi kamar mayunta iya haduwa BAHIJJAT ta hadu ba abin da bai ji ba na tsarin ya mace ajikin ta taku ta fara cikin salo na fizgar hankali ko ina na jikin ta kadawa yake yi kamar iska  na kada fishiyar dogon yaro hakan ya kara firgita mazaje matuka gaya can nesa kadan ta samu kujera ta zauna ba tare da ta kulawa ko kallo wasu ba hakan ya kara tunzura mazaje domin wajan zaman da za tayi sai da tayi wani salo don ta da hankalin wadanda ta burge don ita kan ta ta san daban ce cikin maza ita a bar so ace ga ko wani namiji tsarin halinta ta na dashi kyau ta na dashi iya kwalliya kuwa ba a magana masu kula da wajan ne duka iso gareta suna tambayarta abin da take bukata hannu kawai ta musu nuni dashi alamun ba ta bukatar komai suka runsu na su yi gaba duk abin da takeyi idanuwa ne baje akan ta kowa ita yakr kallo mazaje dake zaune a wajan kowa su yake yi ya ga ya je gareta kowa sai shiri yakeyi domin tunkurar ta amma tsayin lokaci ba wanda yayi wani yin kuri na azo a gani Zip din jakar ta ta zuge gami da leka cikin ta ganin komai ya na nan yarda ta aje shi ya sanya murmusawa wanda da ka kalli murmushin zaka san akwai gayya a cikin sa karar parking din da kayi ne ya sanya ta dago kai ta dubi in da ake parking din gaban ta ne taji ya buga sa'ilin da ta kalli motar tun kafin ta ga waye ma mallakinta kafe motar tayi da ido kamar ba za ta kyafta ba domin ji take ajikin ta wannan motar mamallakin ta shine wanda take cigiya take nema tunanin ta lokaci guda ya sauya akala izuwa faruwan komai da ya kasance a rayuwarta kamar yanzu ta fa hasko lokacin da take zaune bakin get din makarantarsu izuwa lokacin da ta shiga motar Adam da faruwan komai zuciyar ta tayi wani yin kuri gami da tokare mata kirji wani tawagar kayan dacin rai su ka yo wa makoshin ta kawanya idanuwanta suka ka kada kayi jakir kamar ba farare ba ganin da tayi komai na shirin jagule mata ya sanya sauri kinkimo jarumta ta yafawa kan ta tashiga saita kan ta a fuska ta nuna kamar ba komai amma zuciyarta kuwa kamar ta tarwatse saboda dacin rai idanuwan ta ta sake kai wa izuwa motar amma bisa akasi har mai motar ya fi ce daga cikin ta ya bar wajan da sauri ta shiga rarraba ido ko zata ga wanda take tsammanin gani amma ina ba alamun sa hakan ya sanya ran ta kara baci matukar tayi kwa6a gami da tsaki kamar harshanta zai tsin ke cikin wannan yanayin ta shafe a wani biyu cur amma ba alamun sa sam haka dai ta cigaba da zama tun tana tunanin ganin sa har ta fara YANKE TSAMMANI akan sa ta duba wayarta don gannin lokaci ganin da tayi lokavi ya fara ja ya san ya ta kokarin fara hada ina ta ina ta domin har bacci bacci ta fara ji ta miki wajan motar ta ta tunkara ta na kokarin bude mata ta ji an riko murfin mota han da hannunta aka hada da sauri ta juya wani yarrr ta ji jikin ta yayi gami da shock kamar an jona mata wutar nema tana kokarin zuke mata jinin jiki idanuwanta warwaje zuciyarta na wani irin logudan bugu kamar za ta faso kirji ta yo waje in ya rike mata ji take kamar garwashin wuta aka daura mata bakin ta gami da jikin ta suka shiga rawa kamar wacce ruwan sama yayi wa dukan tsiya su ka shiga kallo juna ido cikin ido kiyayya ta gaske ota ce take taruwa cikin idanuwanta suka zuwa gareshi amma shi kallo daya zakayi masa ka san ba haka bane domin wani murmushi ne mai dauke da muradan sha'awa akan ta suke SAFAH DA MARWA ida idanuwan sa zuwa na ta da sauri ta dauke ganin ta daga gareshi domin abin da take hangowa zai iya nakasta mata zuciya ba tare da ta sani ba tsakanin su aka ras mai numfasawa duk jikinsu ya shiga wani irin yanayi mai wuyar fassaru musamman shi da idanuwan sa izuwa wannan lokaci sun gama kwadaituwa da ita hakan ya kara tunzura ta tayi kokarin cin zarafin sa amma wani bangare na zuciyarta ta gargade ta akan hakan domin ita mai nima ne wani wahalallan murmushi ta saki wanda da ka kalleshi zaka tabbatar bada son rai akayi sa ba yafi kuka zafi da radadi ji take kamar ta kurma ihu don bakin ciki wai makiyin ta wamda ya kashe mata rayuwa ya kinkimota bakik ciki da kayan tashin hankali cikin rayuwa shi take yi wa murmushi wasu kwal masu radadi kamar za su dauke fatar fuska suka fara kokarin zubo mata da saurit dauko wa kan ta jarumta ta mai da su don ta san tabbas ta sake su ita zata kwana ciki duk wani alkadarin ta ya karye akan namiji namijin ma wanda ya nakasta mata rayuwa mai yafi wannan tashin hankali da bakin ciki a duniyar ta duban sa t sake yi gami da sakin wani murmushin ta nisa cikin takaicin zuci da kunar rai tayi farrrrr da idanu kamar gaske ta fara kokarin kwatar kan ta amma irin rikon da taji yayi mata ya sanya jin fuduwar gaba domin riko ne ba na sauki ba ya numfasa gami da kara fidɗo da idanuwan sa wanda tun dazu suke kan ta "kallo daya nayi miki nasan ke ta daban ce cikin yan matan bariki domin kuwa tun shigowarki wajan nan ba wanda ya kula ki saboda tsoro da fargaba duk da mazajen bariki da suke wajan nan amma sun yi shakkar ki na rasa dalili hakan amma ban yi mamaki ba domin kin cancanta da matsayin daki ka taka tun zuwan ki aka sanar dani domin ke sabuwar fuska ce a nan wajan kuma tun da aka ganni a san ke kalarmu ce ba ta kananun KADANGARUN BARIKI ba ne sai irin mu manya kuma masu fada aji a wannan harkar dafatan za ki ba ni damar kasancewa dake a matsayin ki tabbba kuma mai madafun iko a wannan harkar ta bariki musamman da na lura ke ma cikakkiyar 'YAR BARIKI (Rufaida Omar) ce" duk cikin kalaman sa da take jin sun kamar saukar ruwan dalma cikin jikita yana ratsawa ba ya kamar kalmar YAR BARIKI da ya ce da ita tabbas ta yarda namiji akwai mugu macuci kuma maha'inci NAMIJI BUTULU,NAMIJI KUDAN ZUMA,NAMIJI KANIN AJALI, kai wasu mazan sam ba suyi ba a rayuwa tabbas namiji ba abin yarda ba ne a rayuwa sam ba shi da kayan farin ciki sai na takaici da bakin ciki ti kam ta fara yanke tsammani namiji na da imani a rayuwarsa a gidan auran sa ba ta huta ba haka ma a waje ba ta huta ba kai namiji sai a barshi shi KOMAI YAYI ADO ne ba kamar ya mace ba wacce abu kalilan ne zai kashe mata rayuwa da duk wani farin ciki na duniyarta yar bariki kalmar tayi mata tsauri matuka wai ita ce yar bariki kuma sunan sai ya fito a bakin wanda ya zama sanadi komai wannan wata irin rayuwa ce a WATA RAYUWA da tayi can baya sam ba ta tsammani akwai wanda zai kirata da suna makamin ci haka ba tabbas dole ta dauki fansa mai matukar girma kan da domin sam bai kamata ace ta sassauta masa ba  duban sa tayi gami da cewa "shin shi namiji kalmar DAN BARIKI ba ta kyau dashi ne da ban ji ana yawan kiran sa sai 'ya mace?" ta fadi cikin yanayi na dacin rai da kunar zuci murmushi yayi mata ba tare da yace da ita komai ba yayi mata nuni da su karasa su zauna ba musu ta bi bayan sa can ne da mutane suka zauna ya ja kujera ya ce da ita ta zauna sannan shu ya zauna mutanan wajan ku sai aka fara magana kasa kasa da nuna burgewa gareshi lokaci kankani a cigaba musu gaba da kayan ciye ciye da tadde tadde tun da suka zauna idanuwanta ke kan shi kallo takeyi masa na kwarrilla ta kasa dauke ganinta daga gareshi shi kan sa ya lura da haka amma bai yi mamaki ba shi a tunanin sa duk cikin fadawa komarsa da tayi ta nutsu cikin shaawarsa matsa mata hannu yayi hakan ya sanya ta sauke ajiyar zuciyata kau da kai shi kuma sigari ya bankawa wuta ya dora a bakin sa yana zuka ya na fesar da hayaki...

Heyy vote voter voter line by line

Kamala din kune 😘😘😘😘

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now