DUNIYARMU-31

375 20 0
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA.

BABI NA TALATIN DA DAYA.

Ba su gama dawo wa hayyacin su ba Bahijja tayi kukan kura ta dire gaban Adam dake kwance amma idanuwansa a buɗe duk ya na kallon abin da ke wakana idanuwansa sun kafe kan Bahijja gani yake kamar ba gaske ba kamar gizo take masa kokarin tashi yake amma ina! ya kasa dalilin kirjinsa da yayi nauyi matuka ko numfashi kirki ba ya iya yi.
Wani irin cafka ta kaiwa wuyansa da duk hannayenta biyu wani karfi da kuzari gami da kwanjinta duk ta ji zuciyarta ta kara mata karfinsu idanuwanta a zazzare kana kallo yanayi na kiyayya a cikin su cak ta dage shi daga kan gadon ta hadashi da bango tana mai girgiza shi kamar wacce take so jikin nashi ya watse gabadaya duk wannan abin da take yi kallo daya zakayi mata ka gane ba ta cikin hayyacinta shaƙa sosai tayi masa wanda sanadin haka duk idanuwansa suka warwaje sai faman zubda hawaye su amma duk da hakan idanuwansa ba su bar nuna masa surar Bahijja bai damu da abin da take aikata masa sam shi dai kawai ganinta da ya yi ya rage masa raɗaɗin zuci sosai.
Hajiya Laila ne ta kurma ihu gami da dora hannu akai ganin abin da ke faruwa Alhaji kuwa bai san lokacin da ya dire gaban Bahijja ba wani wawan cafka yayi mata gami da wulli da ita can gefe sai ga ta warwas akasa amma ko gezau sai ma sake mikewa da tayi tana kallo Alhaji a wulakance cikin yanayi na kaskanci sai faman ya tsine fuska take tana hirji kamar za ta ci babu jikin ta sai faman bari yake yi suka shiga kallon kallo da Alhaji shima zuciyarsa ta zo wuya yana dubanta a wata mahauciya wacce sam ba ta da hankali bai san wacce ba bai san daga ina ta fado ba take kokarik karasa masa ɗan nashi da hannu ya nuna ta cikin murya mai sauti dauke da ɗaci da takaicin abin da tayi.
"ke! 'yar gidan uban wanene, kina da hankali kuwa,uban me ya kawo ki nan dakin, har kike kokarin kashe min ɗa to wallahi duk dan banzan da ya turo aikata wannan DANYEN AIKIn wallahi sai na daure ku ke dashi da duk wanda ya dangace ku".
ya karashe cikin dacin rai da tunƙaro inda Bahijja take tsaye amma ita ko gezau sai ma wani banzan murmushi da ta saki gami da kure Adam da idanu da yake kakari kamar ran sa zai fita wani murmushi ta sake yi a daidai lokacin Alhaji Kabeer ya iso wajanta yana mai nuna ta da hannu sai faman cin-cin magani yake yana ya mutse fuska ba abin da ke cin sa sai masifa da fitina dungure mata goshi yayi gami da cewa "Uban wa ya turo ki, ki kashe min ɗa wani dan iskanne ko wani gantalalle ne ya turo ki ki fada min nace tun kafin na kankaryaki na watsar!".
ya fadi yana naɗe babbar rigar sa kamar wanda zai shiga filin dambe har izuwa lokacin Bahijja ba ta wani tsorata ba saboda zuciyarta ta gama kekeshewa taga ficewa daga yanayi na tsoro ba ta fargaba ko wani firgici akan abin da zai faru.
Tk da yake can gefe sai fama kyarma yake yi domin duk yana kallon abin da ke faru cikin tashin hankali ya lura su Alhaji ba su san wacece ba, ba su gane ita wacece ba ce, cikin yanayi na ganin tashin hankali karara ya kokarta janyo jarumta ya yafawa kan sa yace,
"Alhaji ita ce fa yainyar da Adam ya gani yake so a sanadin ta ne ya shiga wannan halin...".
Ai bai kai karasa maganar sa ba Alhaji ya dauko Ashar ya dire gami da duban Bahijja.
"akan wannan tsinanniyar yarinyar fa kace wannan mai suffar yan fashi da makamin wannan mai suffar masu daukar rai kake danganta ɗana da ita kake cewa ita yake so".
duk maganganun nasa yin su yake yi cikin firgici da tashin hankali yana duban Bahijja da takaicin duniya ya isheta jin ana maimaita kalmomin da take jin su kamar saukar ruwar dalma a cikin kunnuwanta.
Hajiya Laila ne ta iso wajan Bahijja ta roko mata wuyar riga kamar za ta tsinke mata wuya idanuwanta na zubda hawaye tashi ga magana murya na rawa.
"Tukur wannan sam ba maganar dauka bane wannan sam ba maganar da hankali zai dauka bane har yayi nazari akan sa wannan makashiyar rayurka kake nufin ɗana ke so ƙana nufin wannan maras imani da tausayi ɗana ke so..."
wata irin fincika Bahijja ta yiwa Hajiya Laila a zafafe sai ga ta ta baje a kasa ta shiga nuna ta da yatsa.
"ke har kina da bakin cewa wani maras imani bayan ke ga ki kin haifarwa duniya kasurgumin mara imani Annoba kuma cikin duniyarmu, ke har kina da bakin cewa mani makashiyar rayuka bayan ga shi nan kin haifi makashi rayuka tun da nake a duniya bamn taba ganin annoba ba sai akan dangi ban taba ganin mai dauke farin cikin mutane ba sai a kan ɗanki ban taba ganin mai tarwatsa farin cikin iyali ba kamar dangi wallahi na rantse miki da Allah a duniyar nan ban taba ganin mutum mai kashe rai ba ta hanyar son rai da son zuciya ba sai ɗanki...".
"Saboda ya ce yana son ki?".
Alhaji Kabeer ya fadi cikin tsawa
Duban sa tayi cikin dacin rai.
"kasan Allah ko za a dinga sassara nama na a konawa an tayar dani don in so ɗanka wallahi ba zan taba son shi meye abin so a jikin sa meye abin so jikin fasiki macuci maha'inci sam ni maganar kalmar da naji kuna hagaga akan ta ban sani ban san wannan tsinannan yace furta kalma mai muni akai na ba wai so to ko da uwar sa yake Kwana Hajiya Laila ba abin da zai sa na kula shi ni fansa  na zo dauka".
"FANSA"
duk kansu su ukun su ka fadi cikin alamun mamaki da daure kai murmushi Bahijja tayi ganin irin halin da suka shiga.
"kar fa kuyi mamaki don na fadu haka musamman kai Alhaji na lura kana da son ɗan ka ko kuma kai ne kake kara masa kwarin gwuiwa akan duk abin da yake aitakawa to yau ranar daukar fansa ne kuma na rantse maka da Allah sai Adam ya ban duniyar nan cikin yan dakiku".
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"
abin da Hajiya Laila ta fadi kenan cikin ruɗani da tashin hankalin da ya kara bugar da ita lokaci guda
Haka shi ma Alhaji tsayawa yayi yana jujjuya maganar Bahijja kai shi yayi matukar daurewa hakan da Bahijja ta gani ya bata damar fallewa a guje ta isa wajan da Adam yake wanda har lokacin idanuwansa ba su daina kallon Bahijja ba abubuwa ne ya ji suna tayi masa shigar sauri cikin zuciya suna haifar masa da WANI AL'AMARI mai wuyar fassaruwa gareshi wata yar karamar wuka ta gani kan wani faranti da sauran magunguna da Allura da alamun na Nurse da take can bakin kofar bayin dakin jira kawai take taji kes ta shige ta kulle kan ta don tayi matukra tsora da ganin abin da Bahijja ta aikata fitsari a tsayene kawai ba tayi ba.
Bahijja na daukar wukan nan ba inda ta dire sai wuyar Adam wani wawan yanka tayi masa saboda wukar akwai kaifi sosai ta sake daga wa za ta caka masa a kirji caraf taji an rike mat hannu da sauri ta juya Tk ne wanda a lokacin da ta yanki Adam ya ga alamun da gaske take bai san lokacin da ya buga tsalle ba ya dire gaban ta yana mai faman numfarfashi cikin azama ya gayyato jarumta ya yafawa kan sa ya shiga kiciyar amshe wukar amma ina ya kasa saboda wani irin ƙarfi da yaji Bahijja tana dashi sai da yayi da gaske san nan ya samu nasarar amshewa amma sai da ta yanke shi a hannu da wukar Nurse ce ta kurma ihu ganin abin da yake faruwa da sauri ta falle da gudu tayi waje tana kururuwar neman ɗauki Alhaji kuwa ba a maganar sa don gaɓadaya ya ruɗe ya rasa ma abin da zai yi haka ita ma Hajiya hannu ta daura akai ta kurma ihu tayi wajan da Adam yake yana faman numfarfashi jini sai fita yake yi ta wuyan sa dan kwalinta ta zare jiki na ɓari ta san ya a saitin in da jinin ke fitowa Tk ya Bahijja.
"wallahi in har Adam ya mutu ke ma sai kin dandani zafin mutuwa"
ko gezau ba tayi ba illa harara da ta yi masa gami da sakin murmushin yake Adaidai lokacin Doctor Kamal ya shigo tare da wasu securty na cikin Asbitin ba karamin kaduwa yayi ba lokacin da ya ga abin da ya afku da sauri ya isa wajan Adam ya cire dan kwallin da hajiya ta san ya masa da sauri ya kau da kan sa ganin irin yankar da akayi wa wuyan Adam juyo wa yayi ya dubi Bahijja ita ma tashi take kallo  ya dubi Securty ya ba su damar su yi suka Bahijja cikin Azama suka doshi in da take ganin suna kokarin kama ta ba zato ba tsammani sai ga bindiga a hannunta ta zaro daga kugunta a bazata ta saita su tana mai cewa "duk wanda yayi gangancin isowa gareni sai na fasa masa kai".
cak suka tsaya domin su daia ba su da wani makami a hannusu gabadaya mutanan cikin dakin sukayi tsuru-tsuru ganin Bahijja da bindiga a hannu Doctor Kamal dake kokarin gyara inda ta yanki Adam da sauri ya mike ya na dubanta.
"karki soma kar ki kuma fara kokarin daukar ran wani a cikin dakin don in har kika aikatawa hakan ba abin da zai hana a dauki naki".
murmushi tayi sannan ta yi masa kallon na raina maka.
"yo ai ni dai in har buri na zai cika ko a yanzu na mutu".
ta nuna Adam da yake cikin halin ha'ula'i
"mutuwar wannan bakin mugun shine burina wallahi".
mamaki ne ya wanzu a fuskarsa sosai ya shiga dubanta yana duban Adam gabadaya kan sa ya kulle zuciyarsa tana shiga tunanin abubuwa akan maganar Bahijja tuni kwakwalwarsa ta hango masa wasu lamura da yake kokarin gasgatawa Ihun da Adam yayi ne ya dawo da shi hayyacin sa duk kan sun sukayi kan shi gani yana fizge-fizge wani shu'umin murmushi Bahijja ta saki cikin hanzari ta balle daga cikin dakin ba tare da sun sani ba sai jan kofa da tayi ta kulle su a ciki ne ya dawo da su hayyacin su ai da gudu securty sukayi kofar amma ina gam suka ji ta alamun ta kulle su a ciki nan suka shiga bugun kofar kamar za su karya ta da sauri Doctor Kamala ya mike ya nufi windon dakin ya leka a guje ya hango ta ta doshi wata bakar mota tayi mata key ta fice da gudu kamar fitar burgu hannunsa ya dinkule gami da sakin naushi cikin iska yana cizon La66an sa da sauri yayo kan Adam wanda yake ta faman fizge fizge Hajiya da Alhaji da Tk duk suna kan sa cikin tsananin tashin hankali da yanke tsammanin samun Adam ba abin da Hajiya Laila ke fadi sai 'Ta kashe shi Alhaji Adam ya mutu shikenan na rasa ɗana'
Doctor Kamal ne ya fara sanar dasu ba mutuwa yayi ba nan ya shiga gyara wajan dinki yayi masa sannan yayi masa Allura domin rage raɗaɗi da zafin wajan domin ya lura ba karamin yanka tayi masa ba a wuyan nan ya shiga kwantar musu da hankali tare da tambayar wacece wacce take kokarin kashe musu ɗa nan Tk ya sanar da shi ita ce yarinyar d yake so ba karamar kaɗuwa Doctor Kamal yayi jin abin da Tk ya fadi nan ya shiga tunani da nazarin lamarin tabbas akwai wani abu a kasa akwai wani BOYAYYEN SIRRI da ba su sani ba akwai abin dake faruwa a tsakaninsu ba karamin babu bane zai sa mutum ya nemi ran dan uwan sa nisawa yayi gami da duban su Alhaji da sukayi carko-carko.
"Anya kuwa Alhaji ba wani BOYAYYEN AL'AMARI a tsakanin ɗan ku da yarinyar nan?".
ba karamin haushi Alhaji ya ji ba akan maganar Doctor Kamal jin yana neman dauko musu wani zancen banza ya jogana musu da wannan lamarin da bai kamata ace an sayon wasa a ciki ba kamar ba zai yi magana ba ya shiga yatsine fuska kamar bire da lemon tsami.
"Ba wani abu kawai iskanci ne muraran za ta nunawa mutane ita yar duniya ce rikankiyar 'YAR BARIKI tun farko dama sai da na zargi haka tun da naji ance Clube ya ganta ni fa ina zargin anya ba asiri tayi masa ba kuma take neman ran sa tsinanniyar yariya daga ganin ta yar fashi ce domin in ba yar fashi ba, ba yarda za ayi a ganta da bindiga".
sakalo Doctor Kamal yayi yana jin batutuwan Alhaji na son zuciya da son kai wato shi ɗan sa ba zai ga laifin sa ba kuma ba zai tambaye shi dalilin da ya kai shi Club tun da ya san Club ba wajan mutanan arzuki bane kawai ya take laifin ɗan sa ya dauki na wani yana zuzutawa tare da tsinewa duban Alhaji yayi sosai ya ga alamun da gaske yake nisawa yayi sannan ya ce.
"amma Alhaji ya kamata ka fuskanci wani abu 'ya mace da ka ke ganinta rauni gareta sosai tana tausayi da jin kai ba kasafai za ka samu 'ya macen da za ta iya aikata hakan ba, ba wai ina goyan bayan wannan yarinyar ba ne a,a ya dai ka mata ka bincika domin sanin takamaiman abin da ya an assasa hak...".
da sauri Alhaji ya tare shi.
"ni ba abin da zan bincika kawai dai  don yace yana son ta ita kuma ba ta son sa shiyasa za ta kashe shi kuma wallahi na rantse da Allah duk in da tashiga sai na binciko ta sai na shayar da ita mamaki wallahi tun da ta nemi ran ɗana".
Shiru kowa yayi ya na sauraron maganganun Alhaji wanda ba komai a ciki sai son zuciya da MAKAUNIYAR SOYAYYA da yake yi wa ɗan sa Hajiya Laila tagumi tayi tana ta kasafi da lissafe-lissafe akan wannan lamarin da take yi wa kallon ALMARA Tk kuwa maganganun Doctor Kamal kawai yake ta nazari a kan su tabbas ya san halin Adam zai iya aikata komai na rashin Mutum ci maganar Doctor za ta iya tabbata cewar Adam akwai abin da yayi mata.
------------@----------
12:00am Night-Dare.
Gari yayi alamun kowa ni dangin rai ya nemi makwancin sa domin huce garin yini da akayi da aikace-aikace ba sautin da ke tashi sai na karnuka da gyare.
Karar harsashe ne kawai ke safa da marwa cikin wannan salusun daren adaidai lokacin da agogo ya nuna karfe shabiyu daidai motoci ke gudu cikin wani irin yanayi na rashin tsammani abin da zai faru falla gudu suke kamar za su tashi sama jerin gwano sukayi bakar motar dake gaba dauke da bakin glass ba abin da ake hango na daga cikin ta daga bayan tkuwa motar yan sanda guda biyu sai sakin jiniya  suke yi lokaci-lokaci yan sanda kusan takwas ne jere reras bisa motar da gefen windinan motocin lokaci zuwa lokaci suna sakin harbi ga motar dake gaban su sanda kallo daya kayi mata ka tabbatar mai tukin ta ba karamin gwani bane a harkar domin kuwa tuki yake na ganganci da neman tsira daga yan sanda.
Sama da mintina talatin suna abu daya cikin garin Minna amma ba wani alamun nasara a tattare da yan sanda har suka fara ficewa daga cikin gari suka naushi bayan gari in da dazuka suke sun yi nisa sosai da cikin gari kamar daga sama wannan bakar motar  tayi wani irin wulwuli tayi sama gami da dawo kasa a take a wajan ta daki wata bishiyar gamji gamjejiya wani kara da ya tashi daga cikin motar ya amsa kuwwa cikin dajin a daidai lokacin yan Sandan suka iso saura kadan suma suyi sama amma da yake direban ya ga abin da ya faru yayi hanzari taka burki amma duk da hakan sai da ya daki dutsen da waccan motar ta daka tayi sama Allah ya taimaka motar ta su ba tayi sama sai dai glass din gaban motar ya dagargaje sosai cikin sauri duk suka dindire gami da gyara bindigunsu jira kawai suke su ji kes su saki wuta amma tsayin mintina biyar ba alamun motsi daga cikin waccan motar hakan ya tabbatar musu sun yi mummunar haɗari da sauri suka isa gareta daya daga cikin su ya  ma yan uwansa alamun su shirya saboda zai buɗe motar saboda gudun kuskure nan da nan ji kake sautin bindugu na tashi sai kace wanda za suyi gangarumin yaƙi sannu a hankali ya rike makirin motar ya ja amma yaji shi a kargame ya sake ja a karo na biyu nan ma dai ko alamun motsi babu ya dubi yan uwan nasa cikin maganar idanu yace ko a fasa glass din saboda sun lura Securty-key ne akayi amfani dashi wajan kullewa su amsa masa nan ya sanya kan bindigarsa ya bigi glass amma ko motsi nan ma bai yi ba ya sake kai masa wani wawan bugu nan take ya tsake gida biyu amma bai bude ba wani wawan bugu ya sake kaima masa nan take ya tarwatse duk kan su sukayi kan motar gami da saita bindigun su cikin ta.
Shafe shafe su ka hango su cikin motar duk jikin su sanye da bakaken kaya haka ma fuskoƙin su a rufe yake da bakin abu nan daya daga cikin yan sanda ya sanya hannun ya dago direban wanda kan shi ke kan sitiyari ba alamun  motsi ya zare abin da suka kulle fuska da shi wata irin razana yayi ganin fuskar mace ta bayya da sauri ya juya ya dubi yan uwan nasa suma hakan ne ya san ya su zare idanu waje da sauri ya zaro key din motar yayi amfani da remove din ta ya bude nan suka fiddo da macen dake ma zaunin direba sannan suka buɗe gidan bay suka fito da sauran duk kan su suka zare musu abin da ya kare musu fuskoki ma karamar mamaki sukayi ba da suka gan su duk 'YA'YA MATA ne nan suka shiga kallon kallo tsakanin su suna mamaki da tu'ajibi.
  daya daga cikin yan sandan da ya kasance babba ya dubi sauran  cikin muryar raɗa.
"wannan wani irin lamari ne?".
dayan wanda da alamun shi bai yi mamakin ganin matan a matsayin yan fashi ba ya ce,
"ai ba kan su farau ba oga wannan ba bakon lamari bane a duniyar nan".
nan ya shiga gyada kai yana mamaki da tu'ajibi lamarin wanda ya daure masa kai sosai wai 'YA'YA MATA da fashi wannan wani irin zamani ne muke ciki wani irin zamani ne ya sauya DUNIYARMU da abubuwa masu daure kai. maganganun da ya shiga yi da zuciyarsa kenan lokaci guda ya basu umarni duk su caje su har da cikin motar domin gujewa faruwan wani abubu nan suka shiga cajin su ko wacce suka duba sai sun same ta da bingudu a kugunta uku ko biyu bayan wukaƙe nan suka tare su waje daya bayan sun tabbatar da yawancin su ba sa numfashi nan daya daga cikin yan sandan ya shiga motar domin fiddo da ita gefe guda dakyar ya samu ta kunnu domin ba karamin farfashewa tayi ba nan suka kwashi matan suka saka su motarsu dayar motar kuma yan sanda biyu suka shiga suka juyar da akalar motocin zuwa gari cikin wannan daren wanda lokaci ya nuna karfe biyu har da kusan rabi.
Henkwatan su suka zarce ta cikin garin Minna dake Unguwar tunga a nan suka ajje gawarwakin Yan sanda da suke aiki a cikin wajan ba karamin mamaki sukayi ba da suka 'ya'ya mata suke fashi da makami kuma su ne suke ta faman ba su wahala tsayin lokaci nan kowa ya shiga duban su a daidai lokacin kuma daya daga cikin su ta fara motsi cikin hanzari suka isa wajanta gami da jawo ta gefe a hargice suka ji ta saki wata kara mai amo sosai nan gami da bude idanuwanta wata irin razana tayi lokacin da ta ga yan sanda akanta ta tabbatar an ka masu nan ta fara kokarin ta shi amma ina ji tayi bayanta kamar zai rabe gida biyu saboda a zaba da raɗaɗi ta ji dole ta koma tayi lakwas tan duban yan sanda daya bayan daya tana lura da irin kallon da suke yi mata hakn ya kara hargitsa mata tunani nan ta shiga tunanin abinnda ya faru da yarda akayi har aka kama su wasu hawayen takaici ne taji sun ziyarce ta bakinciki ya turnuke ta ba ta so haka ba ta so aka kama su ji take kamar ta hadiyi zuciya don takaici ta mutu.
Misalin ƙarfe shida na safiya yan sanda suka kwashi gawargwakin sauran da suka tabbatar su tasu ta kare sukayi babbar asibitin Minna da su (General Hospital) cikin ƙanƙanin lokaci aka tabbatar musu da zargin su na cewa mata su shida duk sun mutu ita kuma dayan nan suka shiga dubata da bata kulawa saboda irin matsalar da ta samu a bayan ta domin kafafuwanta duƙ sun ƙarye dukka biyun lokacin da aka sanar da ita yan uwan nata sun mutu ita kuma ga abin da ya same ta ihu ta shiga zundumawa da kururuwa tana kallon kafafun ta da suka kumbura sukayi suntum hakan ya kar firgita ta wani dan sanda ne ya daka mata tsawa amma ko alamun za tayi shirun ba tayi ba sai ma kara kware baki da tayi nan ya sa hannu ya zabga mata mari har guda biyu ba shiri ta tsuke bakinta domin kuwa ba karamin gigitata marin yayi ba ta dafe kumatun ta idanuwanta sai zubda hawaye su ke yi.
"yi wa mutane su in ba haka ba wallahi nasa takalmin dake kafata na sake karya kafafuwan banza kawai wacce bata da hankali kina 'Ya mace ki na irin wannan aikin 'ya macen da aka sani da rauni da jin kai amma ke duk ba ki da wannan jibeki don Allah wa zai kalle ki ya ce zaki aikata wannan mugun aiki ke da yan uwanki"
Dan sandan ya fadi cikin zafin zuciya da takaincin abin da ya same su suna aikatawa kallo na yake yi mata na kiyayya da tsana ji yake kamar ya shaketa ta mutu saboda bai ga amfanin barin iri su cikin duniyar nan ba.
likitin da ya duba ta ne ya shigo ya dubi dan sandan da yake tsare da ita.
"yallabai yanzu ya ake ciki da wadancan gawarwakin da ita kuma wannan?".
cikin dacin murya da takaici yace,
"mutuware za a kai su dominnsai an gama bincike kafin a san abin yi akan su ita kuma wannan ba abin da za ayi mata wallahi yanzun ma abin da ya ka ga an barta a cikin asibitin na kawai so muke sai ta sanar damu komai da muke son sani kafin nan musan abin yi a kanta".
rausayar da kai likitan yayi cikin matukar tausay mata da kuma halin da suka je fa kan su ita da yan uwanta ya ji labarin duk abin da suke aitawa kuma yayi bakinciki matuƙa da takaici cikin muryar tausayi ya dubi dan sandan
"Amma yallabai barin ta cikin wannan halin ba karamin illa zai yi wa rayuwarta b...".
wani kallo da dan sandan yaƴi masa shi yasa ya shi saurin tske bakin sa.
"illa fa ka ce yo ai ta kama yi wa rayuwarta illa kuma ba ta da wani amfani cikin duniyar nan ni na tabbata wannan kisa  shi ya fi cancanta akanta domin barin ta a duniyar nan ba karamin illa bane".
Jin abin da ya fadi ya sanya likitan gyada kai gami da ficewa daga cikin dakin cikin wani irin yanayi na rashin dadin zuciya..

Oga Saudat your ar in matsala fa
Kin hadu da mugun Dsp Avva berayeeeee😁😁😁😁😁

IT'x Kamala Minna.😘😘

DUNIYARMU (Compelet)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon