DUNIYARMU-40

463 17 0
                                    

  DUNIYARMU.
          NA.

KAMALA MINNA.

    BABI NA ARBA'IN.

Tsit falon yayi ba abin da kake ji sai muryar mai labarai daga gidan talabijin din kano.
Zaune suke Hajiya Laila ita da Alhaji Kabeer  sai can gefe Adam ne kwance kan kujera kan sa a sama kallo daya zakayi masa ya baka tausayi domin gabadaya ya kara ramewa kamar wanda ya shekara yana cuta idanuwansa duk sun zurma ciki duk fuskarsa duk ta dusashe ta kara ramewa lokaci-lokaci yana sakin numfashi mai wahala idanuwansa sun kada sun yi jajir tun bayan da aka sallamo su daga Asibiti gami da dorashi kan dokoki domin samun lafiyarsa shikenan ya zama shiru-shiru da shi magana ma aiki take zame masa sam baya son hayani ko hira ake sai yaji kamar ihu ake yi masa akai gabadaya ya ji komai ya isheshi na duniyarsa komai ya daina yi masa dadi ba abin da ya ke jin dadin sa cikin duniyarsa ya tsani kan sa da rayuwarsa ya tsani bakar zuciyarsa da irin kitsin da tayi masa na kazamin buri komai na duniya ya daina burgeshi abu daya ya sani zai iya saita rayuwarsa shi samun Bahijja amma kuma ya san tayi masa nisa nisan da har abada ba zai taba samun ta ba ya sani ba shi da wani abun da zai tai maka masa domin samun ta ya sani da son ta zai mutu kuma son ta shi zai yi ajalinsa.
Numfashi Hajiya Laila ta ajje ganin aje hutun rabin lokaci a labaran duniya ta dubi Alhaji sannan ta dubi Adam.
"ban sani ba ko kai zai ji maganar ka, ka yi masa magana akan yawan tunanin nan da yake yi domin ba karamar matsala zai haifar masa ba, likita yayi masa magana akan sa amma ya ki ji sam nima nayi maganar na yi rarrashin nayi fadan amma yayi kunnan uwar shegu dani".
ta ida cikin yanayi na tausayin ɗan nata sosai.
Alhaji kabeer ya numfasa.
"to Laila ya za ayi masa nima kin ga dai iyakar kokarina ina yi amma ya ki ji wannan abun da yake so ya sani ba samun sa zai yi ba amma sam yaki bawa zuciyarsa hakuri na lura so yake yi ya cigaba da rayuwa a haka yana tada mana da hankali".
Kwaɓa tayi tana kokarin yin magana sai kuma ta yi shiru ganin hoton da aka hasko a talbijin da sauri ta sake ware idanu tana kallo ganin abin da take zato hakan ne da sauri ta yafito alhaji tana nuna masa shi kalla yayi da sauri ya dube ta.
"kamar Bahijja ko?".
"ba kama ba ce ita ce ka gani ko Alhaji aure za tayi abin ta".
Sanar wa ake yi cikin talajin din ana gayyatar yan uwa da abokannan arzuki daurin auren Bahijja da Mansoor hotuna aƙe hasko na su kala daban daban fuskokin su cike da farinciki da muradan jin dadi.
Alhaji ya nisa.
"wannan yaron ai shi ne ya ci mana mutunci Mansoor lokacin da muka je neman Bahijja".
Maganar da Hali yayi ta doki dodon kunnan Adam jin an ambaci sunan Bahijja da sauri ya kai kallon sa zuwa talabijin din a kuma daidai lokacin aka sake hasko wani hoton wanda ba karamin kyau sukayi ba Mansoor ne zaune saman kujera Bahijja kuma tana ta bayansa ta dan rankwafo tana kallonsa fuskarta dauke da lallausar murmushi wanda har dimple din ta ya loɓa.
Wani irin katagar tashin hankali ya ji ta ruguzo masa akai zuciyarsa ta shiga buguwa fat-fat da sauri sauri kamar za ta faso kirjinsa ta fito waje idanuwansa suka ƙanƙance suka kaɗa sukayi jajir jikinsa sai ɓari yake yi ya daga hannunsa yana nuna talabijin din. numfashi sa ya shiga sarkewa kamar zai fice daga gangar jikinsa wani nishi yayi wanda ya tafi da karfin numfashinsa lokaci guda ya zube ragwaf kan kujerar da yake hakan ne ya juye da hankulan su gareshi da sauri suka mike sukayi kansa. Alhaji ya shiga girgiza shi amma ina ba alamu rai a jikinsa komai na shi ya saki Hajiya Laila ta kurma ihu tana sallallami kuka take yi tana jinjiga Adam amma ina har zuwa wannan lokacin ba alamun rai a jikinsa da gudu tayi wajan firij ta buɗe ruwan gora ta dauko ta balle murfi tana isa ta dage ta sama ta shiga kwararawa Adam kamar wanda take yi wa wanka shi kansa Alhaji sai da yayi jagaf dashi amma har ta gama tuttule masa rowar ruwan bai farka ba ta sake komwa ta dauko wata mai sanyi ta sake sakar masa ruwan akai wani irin zillo yayi kamar kirjinsa zai tafashe ya saki wani numfashi dauke da hargitsatsan yanayi lokaci guda hawaye suka shiga kwararo masa. Hajiya Laila tace "Alhaji mu tafi Asibiti don Allah kar ya mutu".
magana take cikin muryar kuka da ficewar hayyaci da sauri Alhaji ya fara kokarin kinkimarsa shi cikin tashin hankali da sauri Adam ya dakatar dashi ta hanyar rike masa hannu wani murmushi ne ya wanzu a fuskarsa ma dauke da hawaye ya na duban iyayensa daya bayan daya yana sauke numfashi tashi yayi zaune ya na cizon laɓɓa
"ba sai kun kai ni Asibiti ba Umma, kumar nia gida kawai".
Dukkan su, suka shiga dubansa cikin yanayi na rashin fahimtar inda ya dosa maganar sa ta sake dawo da su hankali.
"na sani son Bahijja ba zai taba barin zuciyata ba, domin halintace Allah yayi min a zuciyata da ruhina a matsayin sakayya akan cutar da ita da nayi ba tare da laifin komai ba na sani asibiti ba za su iya yi mani magani matsala ba warakata tana wajan Allah da Bahijja ni dai roko a gareku don Allah karku manta ranar daurin auren in Allah ya kaimu zan je domin halartar daurin auren tare da neman afuwa da yafiya ga iyayenta da ita kan ta ko da dai bana zaton Bahijja zata yafe min laifin da nayi mata ni nasan na cutar da ita cuta mai mai kona rayuwa da zuciya na san na cuce cuta mai tsanani wanda na tabbata ba za ta taba mantawa da ni ba har ta koma ga mahallicinta".
Tari ya sarke shi yanayi a hankali hawaye na zuba a fuskarsa amma har lokacin murmusho yake yi wanda shi kadai ya san zafi da raɗaɗi da yake ji tun daga kasae ruhinsa har zuciya.
Yayi matukar ba su tausayi su kan su sai da suka zubda masa da hawaye musamman Hajiya Laila da take ji kamar wasiyya ɗan nata ke bar musu ba jimawa zai yi cikin duniyar ba mutuwa zai yi sai dai ta wani fannin tayi matukar jindadi da ɗan nata ya gane macece rayuwa kuma ya gane abin da ya ke aikatawa sam ba daidai bane tabbas ta kara gasgatawa DUNIYA MAKARANTA ce karatu iri-iri ba wanda ba ta koyar da wanda yake cikin ta.
"Adam ka daina fadin haka cuta ba mutuwa ba ce komai tsanani komai wuya sai lokacin yayi ake komawa ga Allah don haka ka yarjewa kan ka wannan lamarin shine kaddararka cikin duniyarka sannan kuma wannan lamari ya isheka IZNA sannan kuma ya isheka ISHARA".
Murmushi yayi mai dauke da hawaye yana mai gyaɗa kai.
"wannan lamarin Momy ni na jawo wa kaina ba ruwan ƙaddara komai ya faru dani nine sila ba wani ba".
Alhaji Kabeer da yayi kasaƙe yana ganin ikon Allah idanuwansa sai kwalla suke kawo wa ya dubi Adam.
"in Allah ya yarda Adam zai kai ka har wajan daurin auren Bahijja domin ka nemi gafararta da na iyayenta hakika ni kaina nasan bakayi musu adalci ba nasani ka cuce su amma son zuciya da makahon sa ya hana na gane haka ban taba zaton rayuwa ya tayi mana zafi haka ba ban taba zaton ukuba rayuwa zata yo mana diran mikiya ba a tunani kudi za suyi maka komai da kake so a duniya ashe ba haka bane kudi ANNOBAR RAYUWA ne ba abin da suke saka mutum sai girman kai da rashin mutunci da biyewa zuciya da ruɗin duniya".
"Dady na ga Ishara a duniya ts kuma nayi Nadama har ruhina da zuciya nidai rokona daya gareku in har ina da numfashi zuwa ranar daurin Auren Bahijja ku kai ni".
Adam ya kareshi maganarsa cikin murya mai dauke da yanayi na neman ALFARMA.
Shiru sukayi suna jujjuya maganganunsa ba wanda ya sake tsinkawa a tsakanin su zuciyoyinsu sai faman lissafe-lissafe suke yi a daidai wannan lokacin Tk yayi Salma ya shigo hannunsa dauke da IV kallo daya zakayi wa fuskarsa ka tabbatar da akwai halin damuwa a tattare dashi a sukwane ya karo so yanayin da ya tadda su ya tabbatar masa da akwai bakon al'amari ko su sun ji abin da ke faruwa ne bai gama tunanin zuci ba ya ji Alhaji ya katse masa hanzarin tunani.
"hala kai ma ka samu labarin Auran Bahijja ne?".
Gyada kai kawai ya shiga yi zuciyartasa na mamakantuwa da yanayin da ya ga Adam ba tare da wani tashin hankali ba IV din ya mikewa Alhaji yana mai ajje numfashin dole.
"ga shi wai in ji Mansoor ya ce a baka Alhaji".
'Mansoor'.
Dukkan su suka fadi cikin hadin baki mamaki bayyane a fuskarsu nan su ka shiga kallon-kallo a tsakaninsu kafin Alhaji ya nisa.
"Mansoor ya ce a bani...shikenan Allah ya kaimu da rai da lafiya dama maganar da muke yi kenan yanzu, Adam ya ce wai zai je daurin auren".
Da hanzari Tk ya dube shi murmushi ya sakar masa shi cikin yaƙe ya yashe baki kamar wanda akayi wa dole yana faman gyada kai.
Nan suka shiga duban IV din kafin kowa ya ajje maganar akan amsa gayyatar.
------@@@-----
maganar Dsp. avva da  Shukura ta kankama domin a halin da ake ciki har magabata sun zo kuma an yarjewa Dsp an bashi auran Shukura ba karamik farinciki da jindadi yayi ba lokacin da yaji wannan kyakkyawan sakon a ranar da yan zuwa NA GANI INA SO suka dawo suka sanar dashi an bashi yana office amma saboda ɗoki ya baro Office ya hau mota ya dire Kauyen Gurmana sai faman rawar jiki yake kamar namijin da aka kargame gidan kurkuku tsayin shekaru hamsin yafito ya ga mace.😁 
A kofar gida ya hangi Shukuranu ya sauka a keke-Napep da alamun wani gun yaje hannunsa dauke da manyan ledoji har uku da hanzari ya isa gareshi yana kokarin baiwa mai Keke-napep kudin sa Dsp ya ti saurin zaro dubu ya mika masa sai faman yashe baki yake yi da mamaki Shukuranu ya dube shi shima yana yi masa murmushi.
"Yallabai ya haka kuma daga dirarka zaka daukar wa kan ka aiki"
Tsuke fuska yayi jin sunan da Shukuranu ya kira shi da shi domin ya jima ya na cewa ya daina ce masa Yallabai ba ya so amma Shukuranu ya ki dainawa.
"Shukuranu Allah zan yage rigar surukanci dake tsakanina dakai".
Dariya yayi da yake ya gano zancen.
"afuwan Dsp Avva".
ganin ya kuma ya san ya Dsp wuce wa ya barshi tsaye da mai Napep yana miko masa canjinsa amsa yayi ya nufi kofar gida inda Dsp yake tsaye ya zaro wayarsa daga Aljihu sai faman lallatswa yake fuskarsa dauke da mayalwacin murmushi Shukuranu ya na iso wa ya ce.
"Angon to ga canjin ka".
Ji yayi kamar ya zunduma shi gidan Aljanna da sauri ya shiga girgiza kai alamun ba zai amsa ba shi Shukuranu ya shiga girgiza kai ba zai barsu a wajan sa nan suka shiga ja in ja a junan su a ka rasa wanda zai hakura kowa na rantse rantse ba zai amsa ba suna cikin wannan muhawarar kawun su Shukuranu ya fito daga cikin gidan ganin su tsaitsaye ya shiga mazurai ya na tambaya lafiya da sauri Dsp ya zube akasa yana kwasar gaisuwa kan sa a kasa hakan ya baiwa kawun Shukuranu damar wafce kudin yana mai cewa
"dan albarka sannu da zuwa kace har manyan naka sun isa sun sanar da kai daddadar labarin ka biyo sahu".
Kasa ya sake yi da kai kunya duk ta rufe sa. shikuwa Shukuranu haushi da bakin ciki ne suka turnuke in da ba dan kanin ba bansu bane wallahi sai sun kwashi yan kallo yanzun nan in ban da rashin kirki da zubda girma maye zai wani kwace kudi a hannunsa ya lura shi dai fa in dai zancen kudi ne yana wajan tun da aka sanar dashi Shukura ta samu miji kuma ga wanda za ta aura shikenan ya mai da gidan su wajan zuwansa komai za ayi sai akan idon sa har yau wajan amsar baki shi yayi uwa yayi makarbiya tun da mahaifin su ya rasu shikenan ya dauke kafa daga gidansu tunda ya ga ba abin mora amma yanzu da ya ga ana batuɓ ne na harkar alheri kuma maganar kudi shikenan kuma lokacin sa yayi tsaki ya ja can katsar makoshi ya raba shi ya wuce yana ji yana kiransa yana tambayarsa kayan dake hannunsa na waye yayi ban za da shi don yayi matukar bata masa rai akan abin da yayi masa a gaban Dsp,Avva.
Yana isa cikin gidan ya shiga gunguni Umma dake cikin daki ita da jama'ar ta yan taya murna ta hango shi da yake labulan dakin a dage yake yanayin da ta ga fuskarsa a cure ta tabbata akwai abin da ke faruwa da sauri ta mike ta fito ta tare shi.
"Lafiya kake kuwa na gan ka duk wani iri kamar wanda ka zage tas!".
tsaki ya ja gami da kwaba.
"Umma tsakani da Allah abin da Kawu yake yi sam ba ya kyautawa ya za ayi a gaban kowa sai ya nuna ba wani mahimmanci muke dashi ba a gareshi ko kuma ya nuna sai ya zubda mana da dan mutuncin da mutane ke ganin mu dashi".
ka sake tayi tajin abin da yake fadi dama ta san a rina wai an saci zanin mahaukaciya dama ita ma yanzu suka gama dashi Allah ya taimaketa bai tsinkata bainar jama'arta ba nisawa ta yi
"me kuma ya yi maka haka har kake tsaki da kwaɓa Shukuranu bana son abin da kake yi ka sani komai yake yi maka dole kayi hakuri shi ne kawai abin da ya dace domin shi kanin Uba ne gareka  ba yarda za kayi dashi".
"Amma Umma ya za ayi yake nuna mana halin ko in kula cikin rayuwarmu ya kamata ace yana nuna shi kanin mahaifinmu ne bawai yake nuna mu da banza duk daya ne b..".
Daga masa hannu tayi tana mai daure fuska hakan da ya gani ya sanya shi tsuke bakin sa ransa ya bace matuka.
"na dai fada maka bana so don haka kadaina kawai kayi hakuri dashi wata rana sai labari in dai abin da yake yi yana ganin burgewa ne ya cigaba dayi duniya ce".
"Umma kin me ma yayi muna tsaye da Dsp Avva fa na sauka a Napep ya biya kudin shine na kawo masa canjin sa sai ya ki amsa shi ne kawu na zuwa bai san meke wa kana ba ya wufce kudin a Hannu na".
zare idanu tayi gami da dafe kirji.
"Innalillahi wai shin me ke damun Bello ne na rasa abin da ke wasa da tunaninsa shi a gaban kowa sai yayi kokarin tsinka min zuria ne kai Allah kyauta ya rabashi da wannan mugun halin".
gyada kai yayi ba tare da ya ce ameen ba ta san halin Shukuranu sarai ba sa jituwa in dai suka hadu
"Yaushi Dsp din ya zo?".
"nima ina sauka a Napep na gannishi".
Ya gyada kai tayi cikin jin dacin abin da Kawu Bello yayi sam bai kyauta ba musamman da lamarin nan ya faru gaban suruki ai wannan zubda daraja da kima ne
"Umma ga kayan na sayo".
Shukuranu ya katse mata tunani da fadin haka. Duban sa tayi tana mai murmushi ledojin hannunsa ta amsa tana buɗewa kaya ne na fitar biki ya sayowa Shukura tare da Salma domin bikin gabadaya za ayi sa rana daya kuma yace komai iri daya za suyi da kan sa ya je kasuwa ya sayo komai.
"kai masha Allah gaskiya kaya sun yi kyau yanzu sai a kai wajan mai dinki kenan don samu da wuri ko".
"ni wannan ba na wa bane tsakaninki da 'ya'yan naki ne ni daina ma fita".
Murmushi tayi tana mai dungure masa kai.
"yo ai shikenan yanzu Dsp  ya tafi ne ko yana waje"?.
" yana nan a waje, ina ita Shukura din take ki rawota yana jiranta a waje don nasan wajan ta ya zo".
ya na gama fadin haka ya wuce dakin sa ita kuma ta juya ta nufi dakin ta nan ta baje kaya ana kallo kowa sai son barka yake yi akan kayan Umma ta shige uwardakanta inda Shukura ke kwance akan gado sai faman malelekuwa take yi tun da taji iyayen Dsp sun zo shikenan ta kunshi a daki kamar mai zaman takaba. Umma ta isa ta zauna bakin gadon.
"wai ke lafiyarki kuwa nifa shirirta ce bana so kin ji ko maza tashi ga Dsp can ya zo".
Zabura tayi ta zauna tana duban Umma kamar wacce taga BAKUWAR FUSKA ta yi sagalo da baki. gabanta taji ya fadi wai Dsp ya zo ba ta gam jajen labarin ba ga mai gayya mai aiki ya wanko kafarsa ya zo ita kam ta rasa ma bakin magana wallahi tunaninta gabadaya ya tsaya cak!.
"magana fa nake yi miki".
baki ta turo gaba.
"yo nima Umma nayi masa me haka kawai kamar wamda na gayyata ya wani kwaso kafa ya zo ni yasin ba in da zan...".
matsar bakin ta da taji Umma tayi ya sanya ta saurin katse maganar ta ta ta kurma ihu saboda zafin da ta ji.
"kisan Allah Shukura in ba so kikeyi mu bata ba zama ki ta shi ki tafi".
Umma ta cikin yanayi na bacin rai amma a zuciyarta dariyar Shukura take yi ta san ba abin dake dawainiya da ita sai kunya.
ganin ta nuna bacin fuska ya sanya ta mikiwa cikin sanyi jiki ta zari hijabi ta sanya dama ba ta ji ma da yin wanka jiki a sanyaye ta nufi kofar dakin har za ta fice daga uwar dakan ta juye ta dubi Umma.
"yi hakuri Umma don Allah".
Yanayin yarda ta marerece ya ba Umma dariya murmushi tayi gami da gyada mata kai alamun ta hakura.
Tana fita falo nan akayi mata acaaa akai ana fadin Amarya Amarya ba shiri ta fici da hanzaei ta zari takalmi ta far cikin gidan a kofar gida ta taddashi tun da ya ganta ya shi yashe baki kau da kai tayi tana mai gaida shi.
"Alhamdulillah nagode wa Allah da ya kawo mu wannan rana mai tarin Albarka naji dadi sosai Shukura Allah ya tabbatar mana da Alheri ya kawo mu wannan ranar mai albarka wacce ba za mu taba mancewa ba a rayuwarmu".
"Ameen" ta amsa cikin sunne kai kasa. Nan Dsp ya shiga barin zance kamar wanda akayi wa Albishiri da gidan aljanna tun bata sakin jiki har ta saki jiki suka sha hira sosai har da yarda bikin nasu zai kasance ranar Dsp bai bar gidan ba sai da ya cinye a wanni uku cir shima kiransa akayi emegency akan case din SAUDAT wacce a wannn lokacin kafafuwanta duk an yanke su saboda daurin da akayi mata bai yi ba ba a lura da hakan ba ashe kafar duk ta rube dole aka yanke halin da ake ciki ma tana kotu domin za a yanke mata hukunci akan laifin da ta aikata na fashi da makami da kuma kisan iyayenta da tayi  dalilin tafiyarsa kenan domin a ranar za a shiga kotu zaman karshe.
A bangaren Salma da shukuranu kuwa ba a magana tunda ta dire  Gidan su wat zazzafar soyayy suke kwasa kamar za su lashe juna a rana sai Shukuranu yayi zuwa uku suna barzar soyayya mai dauke da tsantsar so da kauna wacce tun farko aka gidanata a dubalin gaskiya da kayan alheri tun da kuwa aka ce an saka ranar bikin nasu da yake sai da aka sa nasu sannan akayi na Shukura shikenan fa wani farinciki mara misaltuwa ya shiga shawagi cikin duniyar su aikin kenan musayan kalami da tsara yarda za su zauna gidan aurensu da farincikin da suke rokon Allah ya kawo musu cikin gidan auran su kowa a kauyen Gurmana ya san maganar bikin  Salma da Shukura domin kuwa ko ina Shukuranu yaje sai ya sanar ko da kuwa mutum ba zai zo ba rayuwa tayi musu dadi din wani daci da aka sha a baya ya zama tarihi sai dai a tuna shi in an TUNA BAYA komai ya shafe kamar ba ayi ba Salma ta murje kamar ba ita ba komai nata ya zama daidai ta zama cikakkiyar salmarta kamar yarda take a can baya kafin kaddara baƙa ta fado cikin duniyarta kullum kara godiya take ga Allah da manzon sa da ya barta da numfashinta har ya kai ta lokacin da zata auri masoyinta wanda take so take muradin zama da shi har a gidan Aljanna firdausi taji dadi matuka ba ita kadai ba harta iyaye farinciki kamar me a yanzu inna lubabatu hankali ya kwanta komai ya zama tarihi zuciyarta ta daina zargin kowa da take yi ada nacewa an sace mat 'ya har gida taje ta tadda Umma ta bata hakuri akan zargin da take yi mata nacewa har da hannunta a cikin sace mata 'ya da akayi..
Rayuwa kenan ZUMA DA MADACI

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now