8

22 1 4
                                    

*Ko da so...*
Book 2
8

Da ace allura zata fadi a cikin falon, tsaf za'a iya jin sautin ta. Shirun da Bilkisu tayi, tunanin mafita kawai take yi. Ya zata yi ne? Kamata yayi ta ji farin ciki amma sam sai taji bata ji komai ba.

Text din ta karanta taga still Hafsah tana fada mata kan zuwan da zasuyi da Dr Karaye. A hankali ta kalli Tariq sannan ta maida kallonta zuwa wayar.

"Tace wurinka zata zo akan karatun ta. Kar kayi kauron baki dai. Hafsahn ka tana son fruits, bari na dan fita ta na samo mata." Da kyar Bilkisu ta gaya masa hakan don so take ta fice kawai ta barsu. Bata son ganin yadda abun zaiyi unfolding. Sannan ita kanta bata gaskata karfin zuciyarta ba. Wani irin haushin Hafsah ne ya cika ta fiye ma da haushin Tariq din. Mafi sauqi shine ta nemi excuse din fita.

Shi kuwa yana jin abunda ta ce, a take fuskarsa ta dau haske ya fara washe hakori. "Dadi na dake kina taya ni son Hafsah. Ina son ki Bilkisu." Ya tashi ya rungume ta. Har ya sake ta bata san me take ji game da shi ba.

"Bari na miki transfer."

"Zanje na shirya." Ta wuce daki sannan ta saka hijab ta fito da saurinta. Bata so ta tarar da Hafsah.

Ganin alert din dubu ashirin yasa ta sake kallon Tariq sannan tayi murmushi. Har gate ya rakata yana cewa ta zabo masu kyau. Da murmushi kawai take binsa har ta bar harabar gidan.

*****

"Ita wannan aminiyar tamu, a ina kuka hadu?"

Hafsah ta kalli gefen titi sannan tayi murmushi kafin ta bashi amsa. "Best friend dita ce tun muna secondary school. Maganar da nake ma friendship din mu ya fi fifteen years yanzu. Ta zama yar uwa a gare ni."

Dr Karaye ya jinjina kai. "Naga alama kam. Ina fata har a aljannah ku sake haduwa."

"Ameen. Tana da kirki sosai, in mukaje zaka shaida. Ta rasa mamanta da wuri amma sai Allah ya bata miji wanda maye mata gurbin komai na rayuwa. Ina alfahari da irin soyayyar daje tsakaninsu. Kamar dai Layla da Majnu."

Dr Karaye bai san sanda yayi dariya ba. Kullum yarintar Hafsah na kara burge shi sama da komai. Sannan kasancewar bata da wani corner a maganarta ko abunda ke ranta, yana sake sakawa yaji ta a ran sa.

"Ashe soyayyar tasu bata kai karshen mataki ba in dai kamar Layla da Majnu suke..."

Kafin ya karasa Hafsah ta karbe tace, "kamar Romeo and Juliet toh."

Ya girgiza kai. "Sam. Dukkan su ba suci moriyar so ba. Duk mutuwa sukayi saboda so. Ni a wurina they are not supposed to be love icons. Ai kaso mutum, ka rayu dashi cikin wannan son, shine riba. Just like us right now. We are about to be bound. In kina son bada example akan love daga yau, sai kice kamar ta mu."

Murmushi ne ya bayyana a fuskar Hafsah. In dai words ne, leave it to Dr Karaye. Ya iya zance. Ya iya karbe zuciya. Mukhtar dinta was more of an action guy and ya burgeta a hakan. Yanzu kuma sai taji ashe all these while tana bukatar kalaman. Yadda Dr ya ke sakata hawa gajimarai a zuciyarta yafi karfinta. Soyyayar sa me zafi ce. Ta Mukhtar me sanyi ce. Yanzu take ji tabbas da Dr Karaye ta fara sani, shi zai cinye da kalaman sa.

Kalaman suka saka mata wata nutsuwa dashi. Ta gama yanke shawara. Bilkisu kawai take jira. Ba za'a wani saka dogon lokaci ba tunda dukkan su ba yara bane. Shiru ne ya cika motar banda nuna masa hanya da take tayi.

Suna isa kofar gidan suka parking.

"Ki fara shiga sai ki min flashing na shigo daga baya. Ko ki zo ki shigar dani. Abunki da me neman shiga, dole naji kunyar introducing dina da za'a yi.

Harararsa tayi cikin sigar wasa sannan ta fita da murmushi a fuskarta.

Tana bude kofar gidan ta hango shi zaune akan plastic chair kamar yana jiran wani abu. Da sauri ya miqe, wanda hakan ya dan tsorata ta ganin yadda yake abu kamar hankalinsa baya tare dashi.

Ko da soWhere stories live. Discover now