Sha biyar

24 2 0
                                    

*Ko da so....*

*15*

*In kin Karanta kiyi sharing please*

Ruwan da aka tafka jiya da daddare zuwa asubahin yau yasa kayan da Muktar ya wanke basu bushe ba, takaici da ɓacin rai duk yabi ya cika shi sam baya son saka ƙananan kaya gashi kaf manyan kayan jiya ya wanke su, cike da ɓacin rai ya buɗe jakar bakkon da ke gefen katifar sa wadda yake sa ƙananan kayan sa shi bama zai iya tuna yaushe ya sanya su ba.

Rai a cinkushe ya shirya ji yake tamkar bai sanya kaya ba, ruwan da aka maka yasa Inna ta makara batai kosai ba, sai fanke tuni an zuba masa nasa ɗauka ya yi ya musu sallama ya nufi titi.

Sai da ya fara kai abincin sa office ɗin su sannan ya wuce ajin da yake da shi wato SS 2, kamar kullun da yawa sun riga shi zuwa musan man da yake yau ya ɗan so ya makara yana shiga suka sa ihun uncle yau kaine da ƙananan kaya, banza ya musu, ya gaida su suka amsa tare da yin ƙananun maganganu ƙasa ƙasa, girgiza kai kawai ya yi yahau rubutu bisa allo, Khadija da ta doso bakin ƙofar ajin ne ta tsaya turus riƙe da baki tsayawa ya yi da rubutun cikin harshen turanci yace "Hajiya kin makara mai makon ki zo ki fara kwafar aiki kin wani tsaya anan"

Ƙarasowa ciki ta yi tana dariya kafin ta ce " class ku faɗamin ba dai dai nake gani ba, anya uncle Muktar ne?," Girgiza kai ya yi Kadija da Fatima basa ji sam yasan dama ɗaya cikin su sai ya yi magana. Mustapha ne yace ai bari mukai a gama class din mu tambaye shi anya ba twin in uncle Muktar bane.

Fatima da Khadijah ta hango na tawowa yasa ta leƙawa tare da yi mata alamar ta yi sauri, tana shigowa tasa salati kamar wani babban abu ya faru takaici ya cike Muktar, dakyar ya samu suka zauna, sam bai so yau yake da SS 2 ba gashi dai yafi son yaran anma sunfi ko wanne aji takura masa, ko dan yanzu ya fara sabawa da ɗabi'un yaran makarantar na rashin hayaniya sam mutsi mutsin surutun ƴan SS 2 din ya fara damun sa saɓanin da da yake ganin sa ba komai ba.

Yau kusan dai ajin nasa basu wani gane shi ba dan duk ya ƙare a kan batun kayan da ya sako tamkar wani wanda ya sako kayan da basu taɓa gani ba, alla alla yake akada ya fice ana kaɗawa ya bar ajin ta taga suka leƙo Allah uncle ka yo kyau " murmushi kawai ya yi tare da yin gaba.

Ko office baije ba ya wuce SS1 su basu da kula ko damuwa da mai malami yake ciki kamar SS 2 wannan yasa lafiya ya gama koyar su ya fice lokacin da aka buga break, tana tsaye tana duba wasu takardu da ta amso wurin Abban ta, idanun ta suka wulga caraf suka faɗa kansa tsai ta tsayar da idanun kansa yayin da wani abu ke yawo a ranta yar take ji da sauri ta ɗauke idanun ta lokacin da ta fahinci ya gane kallon da take masa.

Jiki ba kwari ya ƙaraso dama a tsarge yake ga kuma uban kallo da ta zuba masa duk sai ya kuma tsarguwa daf da ita ya tsaya har yana iya jiyo ƙanshin turaren ta da bai tashi sosai a nutse ta ce "uncle ina kwana?"

Murmushi ya yi " lafiya ƙalau, yau kin rigani fitowa break?"

Itama murnushin ta yi " ina ta kallon ka ko? Yi haƙuri dan Allah kawai gani nayi kayi kyau?

A ɗan hanzance ya kalleta yana murmushi haka kawai yaji kalmomin nata sun masa daɗi, cikin hanzari bayan ta tuna katoɓarar da ta yi ne ta ce cikin rawar murya " kawai yau da nagan ka da kayan da ban saba ganin ka da su bane naga kayi daban"

Murmushi ya yi " karki damu ai nima nasan nayi kyau, duda dai ban kama ƙafar ki ba" ya faɗa tare da yin gaba dan sam kalmomin fun ƙarfin bakin sa sukayi suka fito.

Tsuru ta yi tana kallon sa har ya kule mata samun kan ta tayi da kasa zuwa kujerar da suka saba ta juya kawai ta yi ajin ta, shiɗin ma kasa fitowa ya yi a office ɗin ya ci fanken sa.

Ko da soOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz