Ashirin da takwas

21 2 1
                                    

*Ko Da So...*
*28*

Tunda suka shigo suka gaishe ta sukayi daki don su chanja kaya, Hajara ta yatsina fuska tana kallan Juwairiyya. "Wai me ya kawo ta?" Juwairiyya ta watsa hannu gefe alamun bata sani ba. Ita kuwa Hajara sai haushin yayar duk yabi ya cikata da yake daman sakuwar ta ce ga fada, ga kazanta. Yanzu Inna sai tace daki daya zasu kwana wanda babu yadda zatayi. Amma in akace kwanan zatayi, wannan karan sai dai ita ta dinga kwanan tsakar gida. Gwara taji da sauro da taji da aikin gyaran fitsarin kwance na yaran Yayar.

Hajara ta linke hijab dinta sannan ta daura zani tana tunanin me zai kawo yayar tasu gida. Ita kuwa Juwairiyya kawai daga labulen dakin tayi ta fice ba tare da ta bata amsa ba.

Kusan a tare suka nemi wajen zama kusa da ita suna zama. "Sannu da zuwa Yaya, ya gidan?"

Juwairiyya ta tambaya tana kallon fuskar yayar wadda duk ta fada.

"Hnmm ya akurki zaki ce min dai. Wannan wajen har kya kira shi da gida? Allah na tuba ba gara kwanan bakin titi ba." Yarinyar ta ta zuba mata ido kamar tana so ta fahimci me uwar tata take fada. Juwairiyya ce ta lura hakan ya sanya ta kama hannun yarinyar.

"Muje in miki wanka..." da haka ta bar wajen ta barsu da Hajara dan ita ba zata iya tankawa yayar ba.

Hajara ta tabe baki. "Toh me kike nufi yaya?"

Rashida ta sosa kai har dan kwalinta yana zamewa gefe wanda yasa Hajara ta lura da tsohuwar kalbar dake kanta. Hajara ta kalle ta da mamaki kamar yadda Mukhtar yayi mamakinta. A gidan ita da Hajara sune yan gayu da kwalliya kuma ba abunda yake hana su yi. Ko rashin lafiya take sai tayi kwalliyar nan. In bata da kudi kuwa a cinikin Inna take sayar hoda da turare dan zubi.

Kullum tas take amma sai gashi lokaci guda ta rikide. Dole ma tayi nesa da aure yanzu.

"Yaji nayi. Ai wallahi ba zan koma ba sai anyi magana da shi. Ace mutum ba ci ba sha kullum sai dai ya dimama katifa?"

Hajara ta sake tabe baki. "Toh dama ai kinsan baya aiki."

"Ai da yana nema yanzu kuwa bacci yasa gaba. Ni wallahi ba wahalalliya bace. In ya ga zai gyara toh, in ba zai gyara ba wallahi yazo ya debi yaransa ya bar takarda ta na kara gaba. Ai da saura na."

Hajara ta zuba mata ido. Bakinta yayi nauyi ta rasa abun fada duk haushin yadda Rashida ta zama ya cikata. Ta cigaba da kallonta har ta mike ta dauki buta.

Ta kalli gefe taga yaronta yana bacci har yanzu. A nan take ta lula duniyar tunani. Garba yana da sana'a, shin watarana haka shima zai daina? Shin haka rayuwarta zata koma ita ma? Tab di jam. Ai wallahi ita sana'a zata nema. Ba zata iya zaman wahala ba. Ba zata yarda ta yarda wannan kwalliyar a gidan su ba. Ta ja numfashi saboda nauyin da taji zuciyarta tayi. Tana son Garba, amma bata son rayuwar talauci ko zaman kauye. Bata son ya dauke ta ya kaita nesa. Dole ma ta masa magana tun yanzu suyi yarjejeniyar inda zata zauna.

Rashida ta tako a hankali tana shafa cikin ta wanda babu tsammani ta dauke shi. Ta ja tsaki sannan ta sake zama.

"Wai Inna ba zata dawo bane?"

Hajarah ta murmusa. "Dawowarta kam sai bayan Isha. Gidan Kawu taje." Su ka danyi shiru na wani lokaci ko wannen su da abunda yake sakawa aransa.

"Yaya wai auren ba dadi ne? Duk soyayyarki da Nura ina ta tafi?"

Rashida ta tabe baki. " Wace soyyaya kuma babu kudi. Ai wallahi duk yadda zakiyi kiyi aure gidan kudi. Nima kaina sai da mukayi auren naga duk wasu kadarori da yace yana da ita karyace. Kinga kuwa dole ma na kaso auren nan yasin. Ya nemi yar wahala irin sa."

Sallamar Mukhtar ta saka Hajarah ta hadiye amsar da zata bayar. Har ya shigo da ya zauna gefen su da yar ledarsa a hannu ya ajiye basu sake cewa komai ba.

Ko da soWhere stories live. Discover now