Ashirin da biyar

30 4 0
                                    

*Ko Da So...*
*25*

Kamar wasa son uncle Mukhtar ya kama zuciyar Hafsah amma ta kasa ganewa. In tana zaune shi kadai take tunani. In ta na bacci mafarkan hirar su kawai take. Son shi ya ma ta kamun da ba zata iy guduwa ba.

A karo na farko da ta aminta da cewar tana son burge shi yasa yau taji tana so tayi kwalliya don ya yaba. Ya saba yaba yanayin fahimtar ta kuma hakan yana sanyaya mata zuciyarta. Yau so take yi ya yaba da kwalliyarta.

Hoda ta dauko ta shafa a fuskarta sannan ta nemi lipstick ta shafa. Bata so tayi wata kwalliya me hayaniya ba kuma taso yau din ta fito yadda ta saba.

Ta kalli yatsunta taji tana sha'awar tayi musu lalle ko dan yace tayi kyau.

Tashi tayi ta debo littafan ta sannan ta bar dakin. Ko da ta fito ba kowa a falo hakan yasq ta nufi wurin fulawowin ta ajiye littafan ta sannan ta koma ciki don dauko madaidaiciyar carpet din da take shimfida musu. Ta duba ko ina bata ganta ba sai ta nufi dakin mummy. A hankali ta murda handle din taga mummy bacci take.

Sadaf sadaf ta shiga ta fara neman ta amma bata ganta ba.

"Me kike nema a nan duk kin hana ni bacci." Ta tsinci muryar mummy kamar daga sama. Har fa minshari taji mummyn tana yi ya akayi taji motsinta.

"Mummy carpet din lesson din mu." Ta fadi fuskarta ba yabo ba fallasa sai dai haka kawai taji wani nervousness yana lullube ta, ta fara wasa da yatsunta ganin yadda mummyn take kallonta.

Mummy ta mike zaune sannan ta daga labulen gefenta tana kurawa Fuskar Hafsah ido wadda tana gani tasan yau anyi mata kwaskwarima.

Mummy tayi kwafa ciki ciki sannan ta daga girarta. "Carpet din soyayya dai ko?"

Hafsah ta zaro ido. "Mummy..."

"Rufe min baki a nan! Wato kun mayar dani shashasha ke da babanki ko. Yace za'a dakatar da lesson din amma cigaba ma kukayi ko? Toh daga yau na soke wani abu waishi lesson."

Hafsah ta yarfa hannu. "Mummy carryover fa?"

Mummy ta danyi wata dariya da bata da alaka da nishadi sai dai ta nunawa Hafsah cewa ba ta isa ba. "ta zama spill over ma. Fice min a daki!"

Hafsah ta tsaya a wajen da take kamar an dasa ta. Ta kasa gane fushin mummy na menene da kuma dalilin da zata ce ta soke lesson dinsu. Ita fa ba son shi take yi irin son soyyaya ba kawai tana son shi ne saboda yana da kirki kuma yana birge ta. Ta rasa abun cewa amma ta sani a zuciyarta cewa ba zata fita daga dakin ba har sai ta fahimci wani abu.

"Mummy me nayi?"

Mummyn tayi tafi. "Tambaya ta ma kike yi me kikayi ko Hafsah?"

Hafsah bata gane ba. "Toh shi uncle Mukhtar din me yayi?" Ta tambaya tana ware idanuwa akan mummy wadda shock ma yasa ta kasa magana.

"Mu..."

"Kinga fice min a daki kuma wallahi kar naji labarin ya shigo min cikin gida. Ba ma wannan ba..." sai mummyn ta mike da sauri ta bude drawer kusa da ita ta dauko wani mayafi ta yafa. Ta ja hannun Hafsah ta kaita dakinta sannan ta janyo kofar tana huci.

Kai tsaye ta tafi gate ta sami me gadi. Ya russina ya gaisheta. "Wannan yaron, kar ka sake barinsa ya shigo min gida. Duk yadda zakayi, kayi amma kar nuna umarni ne daga mutanen gidam."

"Toh Hajiya in sha Allahu. Allah ya kara girma." Ya fada yana jaddadawa har sai da mummy ta bar wurin.

Ta wuce ta inda Hafsah ta ajiye littafanta. Ta kallesu tayi tsaki sannan ta shige cikin gida.

*****

Wasa wasa zazzabi ya kwantar da Mukhtar don tun da ya dawo daga aiki ranar juma'a ba inda ya sake fita. Kwance yake a kasan bargo yana jin yau da dama dama kamar zai iya fita. Ko kadan baya son yaki zuwa koyawa Hafsah karatun ta na yau.

Ko da soWhere stories live. Discover now