Sha biyu

24 1 1
                                    

*Ko da So...*
*12*
_*In kin Karanta ki yi sharing please*_

Tunda aka rubuta exam din farko hankalinta bai kwanta ba. Ganin yadda exam din tayi mata ya saka ta hana idonta bacci ta dage da karatun sauran courses din. Sam ta cire wasa da bata lokaci a abubuwa marasa muhimmaci ta maida hankalinta completely kan karatun. Bata son failure a rayuwarta musamman ma ta fannin karatun.

Pencil take fikewa wanda zatayi practicing zanen kifi dashi mummy ta shigo falon.

"Hafsah dai ta bace bat. Wannan bamu san wacece ba." Mumy din ta fada tana jawo kujerar kusa da Hafsahn ta zauna sannan ta dubi kan table din inda anan Hafsah take wuni.

"Mummy sannu da dawowa." Haka kawai tace sannan ta cigaba da zanenta.

Kallonta mummyn tayi sannan tayi murmushi. "Allah ya bada sa'a. Daman so nake kije gidan su Hidaya ki karbo min wani lace da na siya."

"Mummy dan Allah. Exam fa nake. Hidayan ta kawo miki mana." Ta turo baki sannan ta juya.

Sabanin yadda suka sabayi, mummyn tace, "Toh shikenan Allah ya bada sa'a. Da ace komai na rayuwarki haka kika bashi muhimmanci ai da ba haka ba. Ni na koma daki. Na dafa abinci ma in zaki zuba."

Yadda Mummy tayi laushi yasa Hafsah taji babu dadi ta kalle ta. "Mummy kinsan zan karbo miki ko?"

Murmushi tayi. "Bakomai. Good luck." Da haka ta bar wurin.

****

Yau ma taje makarantar don haka ta yi saurin zuwa kujerarta ta zauna. Tana ta duba takaardun hannunta, fuskarta cike da damuwa fal wadda ta mamaye fuskartata tun ran farko.

A hankali ya tako, hangota da yayi ya saka yaji wani abu da ba zai kira shi da walwala ba. Kawai he felt something.

Ko da ya karaso, Hafsah taso tayi kamar bata ganshi ba don yau ba ta son yin magana amma sai ta kasa.

"Hi." Tace sannan ta matsa mishi ya zauna. Murmushi yayi ya ajiye flask din hannunsa a tsakanin su sannan ya zauna.

"Hello." Ya amsa mata sannan ya zauna. Sun jima basu ce komai ba har sai da yaga ba zatayi magana ba sannan yace,

"Bismillah: wainar gero." Ta dago ta kalle shi da alamun tambaya yayin da shi kuma yake kokarin bude flask din. Nan take kamshin geron ya cika mata hanci taji tana son ci. Sai a sannan ta tuna da rashin jin abincin safe da tayi a ranar.

Amma da yake bata taba ci ba sai kawai ta kalle shi har ya doni kulikuli ya kai bakinsa. Hankalinsa kwance yake taunawa.

"Ban taba ci ba." Ta amsa shi tana dora indanuwanta akan shi. Duk da tension din karatun da take ciki sai da taji wani abu ya amsa a zuciyarta. Bata san da me zata kwatanta shi ba. Kawai dai in an matsa mata zata ce yana burgeta.

Da mamaki ya kalle ta sannan yayi murmushi wanda bata gani ba saboda dauke kanta da tayi daga kan sa.

"Yau zaki fara. Da dadi."

Ta kai hannu ta gutsuri kadan sannan ta doni kuli kulin. Sai da ta dan kalli piece din hannunta ta kalla taga baya kallonta sannan ta kai bakinta. Taunar farko, ta gaskata maganar sa sai gashi ba tare da tace komai ba ta kai hannu ta sake dauka. A haka suka cinye ba tare da kowa yace komai ba. Ruwa ya mika mata, ba musu ta karba da murmushinta ta sha. Daidai sannan aka kada kararrawa.

"Thanks. Kuma da dadin sosai."

Ya murmusa. Wa ya gaya mata daman girkin Innarsa girkin wasa ne. "Inna tace take yi." Ya fada cike da nuna jin dadin sa a fili.

Ta gyada kai. "Five star."

Mikewa yayi yana kallon yaran da suke guje gujen komawa class.

"Thanks for lunch." Ta sake maimaitawa wanda a daidai lokacin Mukhtar ya sake jin wani abu ya shiga zuciyarsa game da Hafsahn. Kalmar dai daya ce, ta burge shi.

Ko da soWhere stories live. Discover now