Uku

33 2 0
                                    

*Ko da So.....*

*3*

_*In kin karanta ki yi sharing*_

"Wai dan Allah Hafsa ke wacce irin mutun ce?, kin kira mutun kince ya zo ya taimaka ya koya mana, kuma yazo kin ce yunwa kike ji" Bilkisu ta faɗa a fusace cikin faɗa fada.
Juyowa Hafsa ta yi cikin halin ko in kula "Please Hajiya dena mun ihu, kina ji fa ya ce zai je gun abokin sa ɗan level five ya jira mu ai ko addini ya bawa yunwa haƙƙin ta, in coke village ɗinne ba zaki ba ki je gun sa ku fara" ta faɗa gami da yin gaba ba tare da jiran amsar Bilkisu ba.

Ƙwafa kawai Bilkisu ta yi tare da bin bayan Hafsa rai ɓace.

Sai da suka sai lemo da cake sannan suka wuce gun ma su gurasa, Hafsa na son gurasar sosai tun randa ta fara ci shikenan kullum sai ta siya ada ƙyankyamin ta ma take anma tana jin ɗanɗanon ta ƙyankyamin ya bar ta. Suka wuce faculty of engineering ɗin dan can sukai zasu haɗu bilayi suka hau yi har Hafsa ta ɗauki wayar ta tana neman Number ɗin sata jiuryar sa na musu magana.

Shi kuwa zaune yake suna hira da Umar abokin sa lokaci-lokaci yana duba agogo sam baya son jira kawai dai dan yaran sun takura masa ne, kullum ya tuna yaddda suka haɗu sai ya yi dariya, yana zaune yana koyawa Umar Mechanics da yake carrying suka ji muryar ta, ta musu sallama," Ina wunin ku?" ta ce suka amsa da" lafiya ƙalau," ta ɗan sa hannu ta ɗauki takardar gaban su, mintina kaɗan da dubawa ta juya " lah Bilki zo kiga ya iya Physics wallahi" wadda aka kira da Bilkin ta matso "Allah Hafsa ki fita ido na bana son Bilkin nan"
Dariya Hafsa ta yi " sorry Bilkisu"
Kallon takardar Bilkisun ta yi "lah walllahi ya iya kuwa"
Ba tare da wani tunani ba, Hafsa ta ce " kawo wayar ka in sa ma Number ɗin mu dan Allah zaka dinga koya mana walllahi bamu iya ba,"  kasa magana ya yi ya miƙo mata wayar ta rubuta ta ce " na yi saving Suna Hafsa ita kuma Bilkisu me zan sa, dariya yasa "Bashir zaki sa but ni bance zan koya muku ba gaskiya."

"Dan Allah ka taimaka" ta ce
"Oktom ba yanzu ba kumin message ɗim sanda kuke da free time zan duba tamu time table in"
"To mun gode"kawai Hafsa ta ce taja Bilkisu sukai gaba suka bar Umar da Bashir da mamaki.
Umar ne ya taɓo Bashir wanda ke ta murmushi bayan tuna yadda suka haɗu "waɗancan ba yaran da kake jira bane?'" ta taga Bashir ya leƙo kun gann nan wayar ya Hafsa ta mayar suka haura saman.

Zaune suke yana faman bayani yayin da Bilki ta maida hankali sosai har tambaya take jefawa ya yin da Hafsa ta mai da hankalin ta ga gurasar ta da lemon ta, Bashir ne ya kalle ta ya girgiza kai kafin ya ce yace, "ai sam electricity and magnetism ɗin nan bashi da wuya amma Hafsah tafi maida hankali kan gurasar."  Bilkisu ce ta fara dariya " hmm ai in kaga ta mayar da hankali to ta cinye" Bilkisu ta faɗa, amma duda haka ko a jikin Hafsah sai ma kafaɗa da ta ɗage musu, tare da zuƙar lemon dake hannunta tana kallon yadda yake cigaba da rubutun yana bayani.
Kusan awa guda yayi yana koya musu, ba laifi ta dan tsinci wani abun daga ciki. Ita dai burinta bai wuce tayi passing ba. Bata damu sai makin da ta samu yayi yawa sosai ba tunda shi kadai ne course ɗin da bata ganewa ko Organic da 1301 da mutane ke tsoro basa razana ta. Sam bata so ma ta gayawa Abba cewa bata iya ba, yanzu zai ɗaga hankalinsa akan sai ya nemo me nuna mata ita kuma bata so ya nemo. Kusan ɓata lokaci za'ayi don sam bata ƙaunar course din balle ta fahimce shi.

Sai da me tutorial din ya basu assignment suka masa godiya tare da bashi lemo da cake ɗin da suka siyo yaƙi amsa Hafsa ta ajewa Umar gaban sa, sannan suka taso suka tafi.

"Hnmm wallahi gwara ayi test dinnan mu huta. Duk nabi na gaji da mafarkin course dinnan." Bilkisu ta fada suna saukowa daga bene.

"Ke nima." Hafsah ta bata amsa tana hamma. Da alamu ta gaji sosai. Wajen kujeru suke samu suka zauna jiran direban Hafsah.

Ba su wani jima ba yazo ya dauke su.

****

Tunda Inna Kulu taji labarin ya samu aikin nan wani irin farinciki ya lullube ta tana gyara kayan miya tana waƙe waƙen farin ciki, Harira da ta shogo ne ta ce towo kace yau zamu yini da yunwa har yanzu ba'akai markaɗe ba, kinga Malam ya aikon in siya masa Taliya da wake sai dai kenan a zuba masa da mai.
Ɗagowa Inna ta yi tana Murmushi "a'a wannan na gobe ne yanzu nake shirin Hajara ta zo su ɗauki na kaiwa Bakin kasuwar nan kafin rana ta kwalle"

Ko da soWhere stories live. Discover now