Ashirin da bakwai

65 9 1
                                    

*Ko Da So*
*27*

Ganin shiru shirun da Hafsah ta dauka kwana biyu ya damu mommy sosai. Duk yadda ta kada ta raya kuma Hafsah ta nuna mata sam shirunta bai da alaqa da Mukhtar. A zuciyarta taji sanyi amma duk da haka bata jin zata iya barin sa ya cigaba da hulda da Hafsah saboda gudun bacin rana.

Mug din tea da take sha ta ajiye tana hamdala. Shirun gidan ya mata yawa yau saboda bata da niyyar fita ko ina. Hafsah ta kwalawa kira wadda ta fito tana hamma.

Mummy ta kalleta ta tabe baki kadan. Yau hira takeji shiyasa ma ba zatai mita game da yadda Hafsahn take ba.

"Mummy ina kwana."  Ta samu waje ta zauna. Ta kalli TV taga a kashe sannan ta kalli mummy wadda sanye take da wata doguwar riga mara ado sosai. Hannunta kamar ko yaushe dauke yake da zobunan gwal guda biyu da awarwaro uku wanda sai zata kwanta da daddare kawai take cire su.

Yanayin shigar mummyn ya tabbatar mata da yau ba inda zata je.

"Lafiya lau. Kin tashi lafiya?"

Hafsah tayi murmushi. Yau wace rana ba'a fara amsa gaisuwarta da mita ba. Ta gyara zama tana matsawa kusa da mummyn.

"Lafiya lau mummy."

Suka danyi shiru cike da rashin abun fada don basu saba hira ba haka kawai sai dai in wani abun ne ya tashi.

"Yau ba zaki fita ba?"

Mummy ta gyada kai. "Hutu nake. Gyaran daki na zanyi daga nan inyi tsifa na wanke kai."

Hafsah ta murmusa. "Toh mummy muje in taya ki gyaran dakin sai in miki tsifar ma."

"A'a gara dai ki tayani gyaran dakin. Ba ruwanki da gashi na. Haka kawai a yanke min dan abun adon nawa?" Suka kwashe da dariya.

Abu ne da dukkan su basa mantawa. Akwai lokacin da mummy ta taba saka Hafsah da Hidaya suyi mata tsifa lokacin basu kai haka ba. Da yake tana da cika da tsawon gashi sai yasa suka dade sunayi har suka gaji. Hafsah ta kalli Hidaya tayi qasa da murya sosai don kar mummy taji,

"Dama akwai reza mu dan rage tsahon jelar." Karaf kuwa sai a kunnen mummy wadda ba shiri ta kwace kanta ta hau su da fada. Tsifar da basu karasa ba kenan kuma basu sake ba.

"Mummy an fa dade. Kuma gajiya ce tasa na fada haka."

Mummy ta girgiza kai. "Ba zan yi wannan gangancin ba. Tunda kika furta, zaki aikata. Ki ja min asara ki jawa babanku." Suka sake yin dariya wanda tayi daidai da shigowar Sadiq.

Sallama yayi basu ji ba sai da ya sake yi. Ganin rahar da suke ciki ya faranta masa rai sosai har shima sai da ya murmusa.

"Ya Sadiq ina kwana."

Hafsah ta gaishe shi.

"Ba wannan ba. Hado min shayi." Mummy ta harare shi. Ya za'ayi mutum ya fito daga gida yazo neman abinci. Sai da Hafsah ta wuce sannan mummy ta amsa gaisuwarsa tana cewa,

"Ina Amirar take?"

Ya sosa keya. Kwana biyu abun nata kara gaba yakeyi don ko kwalliyar jikin ma da take bata lokaci tana yi masa bata yi yanzu. Bar ta dai tayi ta kwanciya tana ta gaji. Abun yaso ya dame shi musamman da yaga in zasu fita tana yin kwalliya iya kwalliya sannan ta ware sosai amma da sun dawo gidan sai ta sauya kamar ya kawo ta makabarta.

Boyayyiyar ajiyar zuciya yayi sannan ya niisa. "Bata jin dadi ne." Da gaske kuma yau yaji alamar zazzabi a jikinta shiyasa ya danyi share sharen da zaiyi ya barta tayi bacci ta huta sannan ya fito.

Mummy bata wani gamsu ba tace, "Toh Allah ya kara sauki."

Daidai sannan Hafsah ta shigo dauke da ruwan zafi a flask ta ajiye. Mummy ta kalle ta tace,

Ko da soWhere stories live. Discover now