Ashirin da tara

12 2 1
                                    

*Ko da so....*

*29*

Yau cike da farin ciki ya tashi ji yake tamkar ya janyo ƙarfe uku domin ya tafi gidan su Hafsa sosai yake missing ɗin ta, Kasancewa yaji sauƙi sosai yasa shi tashi da niyar komawa koyarwar da yake mata, ta ko ina ya yi missing ɗin yarin yar, bayan ya karya ne ya hau duba kayan da zai sa, muryar ta ce ta dawo kunnunwan sa a lokacin sa ya sanya ƙananan kaya "Uncle kayi kyau" tamkar a lokacin ta faɗa haka ya ji sautin nata, murmushi ya yi tare da ture jakar bakkon da yake sa manyan kayan sa ya janyo ledar da ƙanana suke, shiɗin ba gwanin ƙananan kayan bane, kwata kwata basu fi shida ba, wata blue ɗin riga mai haske ya janyo gami da baƙin dogon wandon sa, baki yasa ya cinge tag ɗin rigar tunda Ibrahim ya nana masa ita ya siya bai kuma bi ta kanta ba.

Aje kayan ya yi a bakin katifar sa wadda ya gyare ta tamkar mace, ɗakin ya share tare da fita ya ɗebo garwashi tare da ɗan turara ɗakin sam Muktar baya son ƙazanta mutun ne gwanin son ƙanshi.

Dariya Juwairiyya tasa lokacin da ya fito riƙe da kasko " kaima dai yaya sai kace wani mace, ni ban taɓa ganin inda namiji ke turara turaren wuta ba sai kanka"

Banza ya mata tare da aje kaskon can gefe ya leƙa ɗakin Inna, ganin ɗakin wayam yasa shi cewa "ina Innar?"

"Ka manta yau ake sunan Balaraba ta je taya su aiki" juwairiyar ta faɗa lokacin da take juya miyar da ke kan wuta, jira kawai take ta karasa ta fita da abincin.

"Kingani ko na manta shaf walllahi, bari ma kawai inna fita in leƙa" ya faɗa tare da yin waje ba tare da ya jira amsar Juwairiyya ba.

Gida ne matsaikaci kai yasa ya shiga bayan ya yi sallama, matan da ke ta faman aikace aikace suka amsa, ɗaya cikin masu ɗaura zoɓo ne ta ce "ah Muntari ashe jiki yayi kyau jiya nake cewa zan komo in kuma duba ka."

Murmushi ya yi "walllahi kam jiki ya yi sauƙi, ina kwana" ya gaishe ta.

"Lafiya ƙalau, to Allah ya ƙara sauƙi" ta faɗa lokacin da ta kamfaci zoɓon ta kurɓa.

"Ina mai jegon?" Ya tambaya bayan ya gaggaishe da matan da ke aiki, daga ciki Balaraba tace shigo mata Muntari, a nutse tare da sallama ya shiga, daurewa yayi dan wani irin ƙamshi ko ƙarni zance ya daki hancin sa, kamshin turaren daban ƙarnin jego daban, a daddafe suka gaisa ya ɗan riƙe Jaririyar na mintina kafin ya bawa mai jegon dubu guda ya taso ya fito.

Ƙarfe biyu dai dai ya dawo sannan ya shirya kafin ya bar gidan su, cike da walwala sam fuskar sa ta kasa ɓoye farin cikin da yake ciki, a ƙofar gidan ya tsaya mintina kaɗan da bugun sa aka buɗe Malam Musa ya fito, ganin Muktar ya washe baki "oh ashe ba'a gama karatun ba, har ina cewa Malan ko sallama"

Murmushi shima Muktar ɗin ya yi "walllahi ba'a gama ba banji daɗi bane sam"

"ayya to Allah ya ƙara sauƙi" Malam musa ya faɗa yana bawa Muktar wuri alamun ya shiga, duru duru ya yi da ido yana tunanin ya za'ai Hafsa tassn ya zo, kamar ance juya suka haɗa idanu da Usman wanda ya fito riƙe da makullin mota da alamu fita zaiyi, ƙarasawa Muktar ya yi suka gaisa.

"Malamin Hafsa ko?" Usman ya tambaya.

Gyada kai Muktar ya yi "eh, Allah yasa dai tana na?"

"Eh tana nan but naji tana cewa zasu fita bari in mata magana" ya faɗa tare da juyawa ba tare da ya jira mai Muktar zai ce ba.

Momy na zaune a falo tana kallo, ganin Usman ta ce "ya kuma ka dawo kasan Hajiya Hasina bata son jira fa"

Zama ya yi kujerar da ke kallon ta, "Dama malamin Hafsa ne yazo nace ba inzo in faɗa miki, dan naji kamar zata fita rannan kuma naji kina cewa an dai na," ya yi ƙarya dan in yace mata Hafsan ta faɗa masa faɗa zatayi mata tace tana kai ƙarar ta gun yaran ta.

Ko da soWhere stories live. Discover now