Sha shida

19 1 0
                                    

*Ko Da So....*

16.

_*in kin Karanta kiyi sharing please*_

Kwanakin da Hafsah tayi a gidan Goggo ya saka ta ji daman irin rayuwar da suke yi kenan a gida. Rayuwa ce cikin aminci da kula da juna da bawa kowa muhimmanci. Duk da in aka saka mutum a gaba da fada akan wani abu sai yaji kamar ya gudu, ita dai gidan Goggon yafi mata dadi.

Zaune take tana taya Goggo linkin kaya ta lura Goggon tayi nisa a tunani. Ta kura mata ido sannan tace,

"Tsohuwa ana tunanin mutuwa ne?" Goggon ta murmusa ta kalle ta.

"Ba dole ba. Kowa matafiyi ne." Sai Goggon ta goge hawayen da ya taho mata wanda yasa jikin Hafsah yayi sanyi. Shiru suka yi na dan lokaci kafin Hafsahn tayi magana.

"Goggo kin iya wainar gero?"

Goggon ta kalleta da mamaki. "Wainar gero kuma bebilo?"

Ta gyada kai. "Da ma wasu abincin gargajiyar. So nake na koya."

Goggo taji dadi ganin jikarta ta ta soma wayo da sanin kanta. A iya sanin ta in dai ba so take ta burge mutane ba ko ta nuna ta iya, Hafsah bata kaunar girki. Kai, ko wanne aiki ma ba son shi take yi ba indai ba ra'ayin kanta bane.

"Sai mu fara ai. Dama na kwan biyu banyi ba. Yau sai muyi tuwon dawa amma ki shirya daukar mitar mutan gidan nan. Don ba ruwana."

Hafsah ta saka dariyar da yasa Goggo tayi shiru tana kallonta cike da nazarurruka barkatai akanta. Duk da rabin su alan mahaifiyarta ne ba ita Hafsahn ba.

****

Tana kwance tana duba hotunan wasu dogayen riguna ne kiran Bilkisu ya shigo wayarta. Rabon da suyi waya ma ta manta kuma ita ma bata lura ba saboda yanayin zaman gidan Goggon. Ko yaushe da akwai abun yi ko kuma abokin hira.

"Hnmm." Kawai tace da ta kara wayar a kunne.

"Ke an sa result." Gaban Bilkisu ya fadi. Ta mike zaune.

"Innalillahi, yaushe?"

"Yau dinnan yanzu ake gaya min. Zaki iya zuwa ki dubo mana?" Hafsah ta daga labulen dakin ta leka taga yadda hadari ya hado sosai. Ajiyar zuciyar fargaba tayi sannan tace,

"Hadari ne a garin. Ki zauna kar asthma dinki ta tashi. Bari na kira Ya Usman."

Da haka sukayi sallama Hafsah tana ta tunanin yadda zatayi. Dole sai dai suje su duba don ita bata so wani ya gano mata. Ta jima a zaune tana tunanin Yaya Usman zata fadawa ko Abba.

Shigowar Goggo ya sa ta daina zarya a dakin.

"Goggo an saka mana sakamakon jarrabawa. Don Allah ki min addua." Ta fada idanunta cike da hawaye. Goggon ta kamo hannayenta suka zauna gefen gado sannan tace.

"Ki kwantar da hankalinki. Nasan kwanya ta kika yi. Zaki wuce dukka da sakamako me kyau. Oh jini ba abun wasa ba. Mamanku ma haka take yi duk sanda aka yi jarabawa."

Hafsah ta lankwasa kai tace, "ke kam Goggo kun huta. Ba kuyi boko ba kuma ba wanda zai kalle ku ya muku gorin haka."

Goggon ta yi murmushi me sauti. "Nayi firamare ai kafin a min aure. Lokacin ai mune manyan matan gari."

Sukayi dariya kafin Hafsah ta mike ta kira Abba wanda ya tura mata dreba suje su dubo. Hankalinta yafi kwanciya ta kira shi don ko shi yace zai je ya duba mata yaga da matsala ba zaiyi mata fada ba sai dai ya bata shawarwari akan yadda zata maida hankali. Yaya Usman kuwa suna dawowa mummy zai gayawa wadda zata saka ta gaba tayi ta mata fada kan cewa babu abunda ta sani sai aikin bacci da fita yawo da kawaye. Sannan kuma har Yaya Farida ma sai ta san bata yi kokari ba.

Ko da soWhere stories live. Discover now