39

10 2 0
                                    

*Ko da So.....*

*39*

_*Rashin Comments yasa typing in ma ya yi sanyi*_

Rabon da ta tsinci kanta a cikin walwala har ta manta. Tun da satin nan ya kama har yazo ƙarshe bata jin ta samu sukuni a ranta ko na sakan daya sai gashi jin muryar Mukhtar gami da ɗora idanun ta kan sa sun sanya ta a cikin farin ciki marar misaltuwa. Ba wani abun yace ba, kawai jin muryarsa babu wannan kaushin ya saka har hardewa take a hanyar zuwa kofar gidan nasu. Tayi sa'a bata tarar da kowa ba a hanyar.

Ta jima tana kallonsa cike da so da kewa mai yawan gaske. Zuciyarta na bugawa da sauri, da kyar ta samu ta nutsu kafin ta ƙarasa.

Kamar budurwar da tayi sabon saurayi ta sunne kai kasa tana masa sallama hade da gaishe shi murya ƙasa ƙasa.

"Mu shiga ciki mana.." ta fada, tana ɗago kanta.

Ya kalleta sannan ya dauke kan sa da kyar. "Nan ma ya isa."

Take jikin Hafsah yayi sanyi saboda jin amon muryarsa da yake nuna sam yanzu bata cikin burikan da yake son cimmawa amma bata haƙura ba.

"Abu Abdallah, we are above all these..." ta saci kallonsa taga ya zaro wayarsa ya duba sannan ta cigaba duk da tana gani ƙirƙiri hankalinsa baya kanta.

"Dan Allah kayi hakuri wallahi ba zan iya..." Kafin Mukhtar ya ankara sai ganin ta yayi ta durƙushe a gaban sa. Takaici ya cika masa zuciya, bai san lokacin da Hafsan sa mai aji ta zama mara zuciya haka ba, da kyar yace ta miƙe.

"Tashi mana Hafsah meye hakan?" Ya maimaita sannan ta miƙe da guntuwar murnar ta. Sai da ta goge hawayen da suka zubo mata sannan ta jingina da jikin motar.

Mukhtar ya kalle ta, zuciyarsa ta karye da ganin yadda duk ta zabge lokaci guda. Don kar ta sake bashin kunya a titi ya ce ta shiga mota akwai maganar da zasuyi.

Ba musu ta shiga gidan gaba shima ya shiga. Sun jima babu wanda yayi magana kafin Mukhtar din ya gyara muryarsa, yana tattaro dukkan jarumtarsa ya dora akan harshensa.

"Hafsah so nake ki nutsu ki fahimce ni. Zama a tsakanin mu ya kare, ba wai don na tsaneki ba. Ke din kina da muhimmanci a gare ni, kuma kin fi kowa sanin bana son naaci da magiya. Daga yau bana son na sake ganin sakon ki makamancin wanda kika turon jiya Hafsah..., Nayi niyar kawai in ƙyaleki ko in yi blocking ɗin ki sai naga ai akwai mutane tsakanin mu innayi blocking ta yaya zan dinga jin wani abu game da yaran, wannan yasa nace bari in zo da kaina zaki fi fahinta fiye da in saƙone"

"Amma Abu Abdallah ko dalilin sakin ai da sai ka...."

Ɗaga mata hannu ya yi " Aure dai lokaci ne kuma raine da shi, namu lokacin ya ƙare ran kuma ya mutu, dan haka dan girman Allah Hafsa karki kuma turon saƙo irin na jiya, ina ma kin kusa gama idda?, ki cireni a rayuwar ki yadda na cire ki, zai fi miki..."

Kallon sa ta yi tsar so take ta gano Muktar ɗin tane wannan kuwa ko wani mai irin muryar sa ne, sai dai idanun ta shi suke gani, bata kuma cewa komai ba ta buɗe motar ta fice har ta fice ya kira sunan ta, juyowa ta yi batare da ta ce komai ba ya buɗe akwatun gaban Motar ya zaro farar takarda ya miƙo mata.

Kallon sa ta yi da alamar tambaya idanun ta na faɗin me zan da ita?, " Naga kamar baki yadda na sake ki ba, nace bari in rubuta miki, duda ma kin kusa gama ida, ina miki fatan samun miji na gari," kamar ba zata amsa ba, ta miƙa hannu ta amsa tare da yin ciki da sauri.

Can bayan gidan ta ɓoye cikin bushiyu tana kuka tana kallon Paper ɗin tabbas rubutun Muktar ne, sharkaf ta jiƙe paper ɗin da hawaye, maganganun Bilkisu kawai ke dawo mata, tabbas bata da hankali da tayi tsanmanin Muktar zai iya mayar da ita, goge hawayen ta tayi tare da miƙewa har ta fara tafiya sai kuma taja ta tsaya takardar hannun ta, ta yayyaga ta watsar aranta tana ji tamkar Muktar ɗin ne ta watsar.

Ko da soNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ