Ashirin da daya

29 1 1
                                    

*Ko da So....*

*21*

Cike da ɗoki Hafsa ta tashi, kaya kala biyu ta ɗauko in da ta shirya ta saka doguwar abayar ta golden ne kalar ta, a falo ta tarar da Momy tana ta famar mitar jikokin ta da aka mayar da alamu har lokacin Usman bai yadda sun haɗu ba wannan yasa Hafsa saurin wucewa Dinning area ta zubo abincin ta tare da komawa ɗakin ta dan bata son taka sawun ɓarawo tasan kure kaɗan zatai Momy ta hau ta da faɗa.

Tana zaune tana duba wasu formulas dan bata son in Muktar ya zo ya tambaye ta basic abubuwa na course ɗin ta hau zare ido, Sallamar Hidaya yasa ta maida littafin tare da sakin murmushi, "yanzu nake mita a raina kinƙi zuwa bayan na faɗa miki in uku tayi inada abinyi"

Duban agogo Hidaya ta yi kafin ta ce " ai ban makara ba, tashi muje Allah dai ya sa Bilkisun ta shirya"

Mayafin ta da ke gefen gado ta naɗa a kanta kafin ta ce "amin dai" Sallama suka yiwa Momy suka fice.

A ƙofar gate ɗin su Bilkisu suka tsaya ko minti uku basuyi ba ta fito, sai da suka hau titi sannan Hafsa ta ce " gidan Gwaggon zamu fara zuwa ko kuwa kasuwar kurmin?"

Hidaya ce ta ce "no it's better mu fara zuwa kasuwar in ya so ko irin munga wani abin ma yi mata tsaraba"

Murmushi Hafsa ta yi Haka ne kuma ta faɗa kafin ta maida kallon ta ga Bilkisu wadda ta maida hankalin ta sosai ga bakin hanya tana tunani.

Hafsa ce ta ce " Maddam mai ke damun ki tunda kika shigo ina kule da ke you are not on your usual self"

Murmushi ta yi tare da ƙara kallon gefe, kafin tace ba komai kawai banjin daɗi ne"

Shiru Hafsa ta yi sai kuma tace "Tariq ne?"

Ɗan kallonta ta yi kamar zata ce eh sai kuma ta kalli Hidaya wadda idanun ta ke a kanta, girgiza kai ta yi "no kawai banjin daɗi ne"

Kafun Hafsa ta ce wani abu Hidaya ta yi caraf tace " tunda dai sabida ni ba zaki faɗi damuwar ki ba sai ki dawo normal in mun rabu kya cigaba da damuwar"

Hafsa ce ta yi dariya " No badan ke bane dan Malam Musa ne, kar yaji ta mato kan namiji" dariya sukai Har Malam Musan wanda ya ce "ah in dan nine sai in toshe kunnuwa" ya faɗa yana ƙokarin faka motar suka fito zuwa kasuwar shi kuma ya fito ya samu tebur ya zauna.

Sosai sukai siyayya kusan rabin kayan na Hidaya ne sabida makaranta da zata koma, yayin da Hafsa da Bilkisu kusan kayan girki ne sai akushi da ya burge su suka siya, Bilkisu ta fara siya sabida Tariq nason har kar gargajiya tana gani ta tuna da shi in yazo wannan satin ciki zata zuba masa abinci abinda ta fara ayyanawa a ranta kenan.

Kusan sai wurin ɗaya suka bar kurmi suka wuce gidan Gwaggo tunda suka baro kasuwar Hafsa ke duba agogo bata son uku ta mata a waje kar Muktar yazo bata nan ya zama stranded dan tasan Mum ba lallai ta wani yi welcoming din sa yaji normal ba.

Tunda ta hango kofar gidan ba tabar Malam taji daɗi dan shine kawai zai tsayar da ita yace sai sun tsaya sunci abincin rana kan su tafi ganin ba tabarmar tasan bayanan.

Hannun ta rike da kayan da ta sayo musu gefen ta Bilkisu ce Hidaya na daga ɗan bayan su, a hankali ta ce "kin ƙi dai faɗan meke damun ki ko?"

Itama shigen irin yadda ta yi maganar ta kwata " zamuyi waya anjima," ta faɗa tare da yin sallama sakamakon zauren da suka shiga.

Halima na tuƙa tuwo Gwaggo na yanka alayyahu da alamu na miyar tuwon ne, suka shiga "lale maraba da ƴar gudun hijira" Gwaggo ta fada tana murmushi.

Murmushi Hafsa ta yi ba tare da ta ce komai ba ta aje ledar Hannun ta ta shige ɗaki Halima ta ce "to walllahi karki mun ta'adi", ta faɗa cikin ɗan ɗaga murya.

Ko da soWhere stories live. Discover now