Talatin da biyu

19 4 1
                                    

*Ko da So...*

*32*

A rikice ta kalle shi Muktar ni kake kora, miƙewa ta yi duda jirin da ke ɗaukar ta ta ƙarasa gabansa ta hau laluben kwayar idanun sa, akai sa'a suka haɗa ido da sauri ya kawar da idanun sa yayin da tayi saurin kamo hannun sa, "dan Allah Abu Abdallah ka tsaya mu fahinci juna."

Fincike hannayen sa ya yi "na faɗa miki gobe ki tattara su ku tafi na riga na gama magana, kin fi kowa sanin innace bana janyewa," ya faɗa tare da yin gaba.

Tashin hankali tuni ya rikitata cikin ruɗu tace "inje ina da su, inni ka koreni kana nufin suka ka kore su ko me?"

Cak ya tsaya kafin ya juyo, "ai adalci na miki, matsayin uwa, in tani ne ko jariri ne abarmin abuna," ya faɗa cike da kwarin gwiwa kafin ya yi sauri ya bar wurin, yayin da ɓacewar sa da bugo ƙofar ɗakin da ya shiga yasa Hafsa zubewa tare da rushewa da kuka, Abdallah da yake tsaye nesa da su, shigowar sa falon shine dai dai lokacin da Muktar ya wuce ɗaki fuu, yayin daHafsa ta zube da sauri kuwa ya ƙaraso wurin, "Mami mai ya faru?."

Duk yadda taso ta daina kukan kasawa tayi, duda bata son yaranta suga gazawar ta, sai dai yau ita da kanta tasan ta gaza, ta kasa wani kwakkwaran tunani, hannun da Abdallah yasa yana goge mata hawaye ya dawo da ita hankalin ta sosai, ganin ta yi shiru yasa yaron kamo hannun ta, "dan Allah Mami kiyi haƙuri ki cire damuwar Abie a ranki, koma maine nasan ba laifin ki bane, kuma zai fahinci haka in sha Allah zai yafe miki."

Murmushi ta yi tare da cewa, "Allah yasa Abdallah," shima murumushin ya yi "bari inje in bashi haƙuri," kasa cewa kar yaje Hafsa ta yi, sakamakon kwarin gwiwa da ya ziyarce ta, lokaci guda zuciyar na ta faɗamata watakil in yaran sa suka bashi haƙuri ya tuna yanzu fa akwai mutane tsakanin su, watakil ya tuna yanzu fa rayuwar ba tasu bace su kaɗai, bin Abdallah ta yi da ido lokacin da yayi hanyar ɗakin Baban nasu.

Miƙewa ta yi tare da sa hannu ta ɗauki wayar ta kai tsaye ɗakin ta ta nufa, wayar Bilkisu ta hau nema, ta jima tana kallon Number ɗin da ƙoƙarin kira sai dai hannun ta ya kasa danna kira, cilla wayar tayi kan gado tare da kwanciya a dandaryar tiles.

Muktar da ƙafafun sa ke rawa, ƙwarin gwiwar sa ke ƙoƙarin barin sa, na shiga ɗaki banko ƙofar ya yi tare da zubewa a wurin numfashin sa na fita da sauri, yayin da jarumtar sa ta kasa riƙe masa hawayen sa, a hankali yake furta "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un," Allah ma ya sani yana son Hafsa sosai bai kuma san son yakai haka ba bai san ta wuce jini da tsokar sa ba, sai da ya furtar sakin nan.

Abdallah ya jima bakin ƙofar ɗakin kafin ya shiga, kasancewar ba ɗabi'ar su bace shiga ɗakin iyayen su in dare ya yi. Da sallama ya shiga wannan yasa Muktar saurin goge hawayen sa Abdallan ya yi saurin ƙarasawa "Abie kaima kukan kake?"

Girgiza kai Muktar ya yi "ba kuka nake ba," kamo hannayen sa Abdallan ya yi tare da ƙokarin mikar da shi tamkar zai iya wannan yasa Muktar mikewa ya bi yaron nasa wanda ya zaunar da shi gefen gado kafin ya durkusa gaban sa riƙe da hannayen sa tamkar wani ɗan shekaru talatin ko fi, a hankali cikin sanyin muryar sa ta yara yace "Abie dan Allah kayi haƙuri ka yafewa Mami dan Allah."

Kallon sa Muktar yayi kafin ya ce "ita ce ta ce ma ta yi mun wani abu?," Girgiza kai Abdallah ya yi da sauri "ba ita bace kawai tun jiya da mukaje asibiti naga kamar tama wani abu ne."

Muktar yasani Abdallah akwai kaifin basira tun yana yaro, sosai yake gane abubuwa bare yanzu da ya fara zama mutun, a ƙoƙarin sa na son ƙin saka yaran su cikin matsalar su yasa shi cewa "Abdallah cikin kaushin murya dubu agogo yanzu yo 11 bana ce duk inda 10 ta yi ba ya zama kun jima da bacci what are you doing outside?"

"Walllahi na kwanta Aiman ne ya tashen zai yi fitsari da nakai shi yayi shine kuma yace zai sha ruwa, shine na fito ɗibar masa, tsai Muktar ya kalle shi ba alamun ƙarya yaron yake ko da yake yasan Hafsa tama yaran su tarbiyya sun san aibun ƙarya sosai, shi ina Yayan ku Faruk da bazai fito ya dibar masa ba eyyi.

Ko da soWhere stories live. Discover now