41

15 4 2
                                    

https://chat.whatsapp.com/BDPkkYJFDRj94oTZbxOVAN

*Ko da So....*

*41*

Lokaci wani halitta ne da tunda aka hallice shi yake gudu. Baya sauri dan wani, haka kuma baya jiran kowa. Dukkan wani numfashi da dan Adam yake shaqa tafiya yake da lokacin da aka dibar masa a duniya. Haka lokaci ya cigaba da tafiya, rayuwar Hafsah tana sake alkibila. Kamar wasa har ta samu gurbin karatu a jami'ar bayero ta cigaba da karatun da tace ta gama.

Sai dai ita duniya babu tabbas, zaka iya gama tsarin ka kuma ta sauya maka shi.

Zaune suke a ajin suna jiran shigowar malami wata yar ajinsu wadda suka fi jituwa da Hafsah ta kalle ta taga tayi nisa a tunani.

"Umm Abdallah lafiya kuwa?"

Hafsah tayi ajiyar zuciya. Babu abunda yake mata ciwo sama da yadda mummy tasa yaranta a gaba kuma tace kwana uku ta bawa Hafsah ta kira Mukhtar ya kwashi yaran. Tana kallo yadda duk auka takura musamman ma Abdallahn da duk yafi su hankali. Kullum in zata leka su zata ganshi idonsa biyu yana sallah. Da ta tambaye shi me yake nema a wajen Allah sai yace mata bakomai kawai yana mata addu'a ne. Tasan shi da zurfin ciki da son nuna kalau yake.

"Ciwon kai ne yake damuna yau. Kamar ma ba zan iya zaman lecture din nan ba, tafiya zanyi." Ta fara hada littafanta tana saka su a jaka. Zuciyarta cike fam da tunani tana neman mafita. Babu wanda zata yi shawara dashi sama da Yaya Sadiq ko aunty Ameera. A take ta yanke shawarar zuwa gidan nasu.

"Toh Allah ya sauwaqe." Amin Hafsah tace sannan suka yi sallama ta tafi.

Fitowarta daga ajin yayi daidai da lokacin da lecturer din ya iso tare da abokinsa. Dr Karaye. Ba tare da izininsa ba idanunsa suka sauka kan Hafsah. Da yake kuma daliban basu da yawa, lecturer din su Hafsah duk ya san su. Ganin yadda Karaye ya kalleta ya saka shi yin magana.

"Malama Hafsah ina zuwa?"

Ta jiyo ta kalle shi. "Ah Sir ina wuni. Wallahi banji dadi bane shiyasa zan tafi." Tunda ta fara magana Dr Karaye yaji ta kwanta masa a rai. Rabon da yaji wani abu akan mace ya manta. Tunda matar sa ta rasu babu wata da ta taba burge shi. Yau shekara goma kenan yana zaune babu aure. Dangi sunyi mitar har sun gaji. An daura masa aure da wata yarinya amma karshe sai rabawa akayi saboda rashin jituwarsu da rashin zamansa da ita.

"Ayya Allah ya kara sauki."

Saurin da Hafsah take yi bai bari ta bashi amsa ba.

"Don't miss her!" Lecturer din ya dafa kafadar Dr Karaye sannan ya shige aji ya bar shi tsaye nan yana tunanin ko yabi bayan Hafsah ya karbi number ta. Karshe dai yaga hakan bai dace ba tunda duk ba yara bane.

Juyawa yayi ya koma office dinsa yana tunanin sanda abokinsa zai gama lecture. Zaifi ace address sinta ya karba a gun yan ajinsu idan da me shi. A hankali yayi murmushi cike da nutsuwa da kamala irin tasa. Ya sani, ya samu mata!

*****

Kamar wasa kafin ta karasa gidan Yaya Sadiq ciwon kai ya hana ta sukuni. Da kyar ta karasa driving tajw gidan nasa. Kai tsaye ta wuce wajen Ameera ta shiga da yake ta kirata tun a hanya an bude mata kofa. Gidan shiru kamar babu kowa tayi sallama.

"Welcome sis!" Ta tsinci muryar Ameera tana fitowa daga kitchen. Tayi kwalliya sosai kamar ko yaushe, jikinta yana nan da kyaunsa saboda yadda ta yadda da bauta masa. Haka ma kwalliyarta kullum abar burgewa ce kamar bata da wata matsala a rayuwarta.

Suka gaisa da kyar saboda yadda kan Hafsah yake ta ciwo. Karshe dai sai magani tasha ta kishingida a falon don ta samu sauki. Kusan mintu talatin Ameera ta bata ba tare da tayi mata magana ba har ciwon kan ya lafa ta fara bacci.

Ko da soWhere stories live. Discover now