33

14 4 2
                                    

*Ko Da So...*

33

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un," Hafsah ta sake maimaitawa a lokacin da kalaman Bilkisu suka daki kunnenta. Kafafuwanta sukayi mata nauyi har sai da ta durkushe a wajen hawaye na sauka daga idonta. Wannan wacce irin kaddara ce wadda ko da wasa bata taba hango ta ba? Zuciyarta ta cigaba da harbawa cike da fargaba da makomar rayuwarta in babu Mukhtar. Har yanzu ta kasa yarda shi ya musu hakan. Har yanzu ta kasa hango babban dalilin da ya ture soyayyarsu ya kawo su nan inda suke a yau.

Ta jima a durkushe Bilkisu tana shafa bayan ta cike da rashin mafita. Bata so ta sake furta abunda zai kassara Hafsahn amma cike take da haushin Mukhtar. Tariq yana ta kallon su daga gefe sai da yaga alamun ba zasu sami mafita ba sannan ya tako a hankali yana nazarin ko me ya faru.

"Ko ma meye matsalar, ciki ya kamata kuyi." Ba'a samu mai bashi amsa ba, sai ma dagowa da Bilkisu tayi ta kalle shi da kyau. Shima zai iya yi mata irin wannan kenan? Sai kawai taki sanar da shi matsalar. Ta kama hannun Hafsah suka shiga cikin gidan a hankali duk da bata san menene mafita a gare su ba.

Sai bayan Tariq ya fita sannan Hafsah ta sake ta dan karya don yunwar da take sakata jiri ba don tana son abincin ba. Sam bata da appetite din cin komai.

"Komai boyewa mummy da zakiyi wataran dole sai kin fada mata. Kawai kamar yadda yace ki kwashi yaran mu tafi. Ni zan mata bayani. Sannan ina so ki sani, it's his loss not yours. Nasan kina son shi kamar ranki amma kuma babu babban asararre irinsa. Namiji? Hnmm..." duk da kalaman Bilkisu don ta sanyayawa Hafsah zuciya tayi, sai Hafsahn taji zuciyarta tana neman kare Mukhtar dinta. Ba asararre bane saboda bata tunanin a hayyacin sa yake. Ko yau ta koma tsaf zata goye shi saboda haka Mukhtar dan goyonta ne. Shi din wani sashe ne na rayuwarta. Da akwai yadda zatayi ma, sai ta sanya jini daya ya dinga gudana a jikinsu ta yadda zai zama nata ko yaushe.

Taja hanci sannan ta ajiye mug din hannunta. "Ina son shi Bilkisu. Duk da yayiwa son tabo, duk da haka my heart beats for him. Bana jin i can move on without him."

Da Bilkisu bata san girman soyayyar dake tsakaninsu ba da taji haushin Hafsah. Shiru kawai tayi saboda bata taba ganin macen da take son mijinta ba irin Hafsah.

"Ko da soyyaya wani lokacin hakura da juna shine mafi alkhairi, ya kamata ki san da wannan. So nake ki zama me tawakkali da rungumar jarrabawar da Allah ya aiko miki a yanzu. Ki daina questioning situation din karkiyi sabo."

Bilkisu ta mike ba tare da ta jira amsar Hafsah ba ta tafi kimtsawa. Ta rasa ma tunanin me zatayi. Zuciyarta tayi nauyi da tausayin Hafsah da makomarta. Wani bangaren kuma haushin Hafsah da Mukhtar din take ji da har zasu bari su zo wannan gabar. Ta tabbatar abunda ya faru a ranar ba wai shine dalilin sakin ba. Ta sani tara abubuwa sukayi tayi a zuci har sai da sukai yawan da suka fashe har suka tarwatsa musu aurensu. Ko da yaushe tana fadawa Hafsah ta dena boye ma Mukhtar abu ko wani iri ne kuma komi kankantar sa. In abun zai janyo fushinsa ba sai ta nemi hanyar yi masa kwaskwarima ta sanar dashi duk dan gudun bacin rana.

Sanda ta fada wanka, kuka ta dingayi na tausayin shakikiyarta ta har sai da tayi mai isarta sannan ta fito ta zura wata atamfa suka fito ita da Hafsah.

Bilkisu ce ta karbi tukin. Shiru sukayi saboda karatun kur'anin da suka kunna. A sannu a hankali nutsuwa take sauka a zukatan su har suka karasa gidan.

Ko da suka karasa gidan Hafsah sai ta tarar yaran duk sunyi wanka sun karya. Matsawa gefe kadan da zatayi sai taga kayan su a akwatuna, mamaki ya kamata.

Bayan duk sun gaida Bilkisu, Hafsah tayi daki don chanja kaya sai ga Abdallah nan yana sallama. Ta amsa mishi ya shigo idonsa duk a kumbure alamar baiyi wani baccin kirki ba. Kafin ma tayi masa tambaya ya soma bayani,

"Abie ne ya hada ma kayan mu wai zamuje hutu gidan Mummy. Mami korar mu yayi ko?" Hafsah ta zuba masa ido, kwalla tana neman ta balle mata.

Da kyar ta samu kwarin gwiwa. "A'a abubuwa sun mishi yawa ne. Zamu je hutu har sai sanda ya warware."

Daidai lokacin Faruk ya shigo shima yana sallamar amma da alama yaji maganarta ta karshe yace, "A office aka kore shi?"

Abdallah ya kalli wansa ya bashi amsa. "Shine muma zai kore mu?"

Hafsah ta murmusa cike da takaicin halin da yaran suka shiga na tunanin mene ne ya faru.

"Duk kunsan yadda rayuwa take cike da kaddara ko? Kuma kunsan akwai akwai me kyau da mara kyau ko and the best of muslims is who?"

"Believe in both. Kenan kaddarar mu ce tayi taking new turn?" Faruk ya fadi yana tsammanin amsa.

Hafsah ta daure, "eh zamu iya cewa hakan. Kawai dai mafitar ko wani yanayi shine addua. In kuna son komai ya daidaita ku dage da addua. Now excuse me zanyi wanka."

Da haka ta shige bandakin dake cikin dakin ta barsu a tsaye wanda sun dan jima kafin su bar dakin ko wannensu da tunanin dake yawo a kansa.

*****

Kafin Hafsah ta fito har sun saka kayan a mota suna jiranta a tsakar gida. Faruk da Abdallah sunyi shiru suna tunanin duk wani karatu da suka sani game da kaddara. Ayman kuwa sai yawonsa yake a tsakar gidan ita kuma Kulthum tana tsaye kusa da Bilkisun.

"Aunty, shima Abie fushi yake yi. Ni kuma banyi komai ba."

Da farko Bilkisun taso ta dauke kanta kamar bata ji ba sai ta kama hannun Kulthum.

"Iyayen mu suma mutane ne and sometimes they are just not perfect as we think. Watakila wani ne yayi wa Abie abu a office ita kuma Mami is worried saboda abunda aka mishi. Amma komai zai wuce. Kema in kunyi fada a school da wani ba yana wucewa ba?" Ta gyada kai kamar ta gamsu sai kuma ta sake tambaya.

"Me yasa to zai kore mu yace wai hutu ne."

Sai da Bilkisu taji wani irin faduwar gaba sai dai Allah ya taimaketa Hafsah ta karaso wajen duk suka nufi inda motar take suka shige.

Saboda gudun kar ma su cigaba da tambayoyin da bada amsar su ga yaran yake da wahala ya sanya aka sake kunna karatun wanda yaran sun san ba'a surutu in anajin karatu.

Cikin motar sai ya zama tamkar makabarta saboda zulumin da zuciyoyin mutanen suke ciki. Ga sanyi amma wani irin dumi suke ji kamar hadari ya hado. Babu salama ko kadan. Musamman ma yaran da tun jiyan suke tunanin menene ya faru suka kuma dora abun a ransu sosai. Hafsah har mamakin su take yi yadda suka lura da yanayin kuma suka dauke shi da girma. Bata taba sanin kular da yara sukeyi da yadda iyaye suke gudanar da rayuwarsu ya kai haka ba sai yanzu.

Ko wannen su kawai kallonta yake yi cike da tausayi. A gefe guda kuma sun damu da dabi'ar Abie din nasu tsakanin jiya da yau.

Har suka isa cikin gidansu Hafsah babu wanda ya tanka. Mummy tayi wanka kenan taji sallamar su. Taso tayi mamakin ganin su da sassafe haka sai ta tuna weekends ne wani lokacin suna zuwan mata haka musamman ma in Ayman yasa rigima.

Kallon farko da tayiwa Hafsah yasa gabanta ya fadi amma ta dake.

"Ha'a Hajiya Bilkisu har dake a gidan namu?"

"Mummy ina kwana." Ta gaishe ta sannan suka shiga ciki. Sai da yaran suka watse sannan mummy ta kalli both of them ta gan su sun kasa samun kwarin gwiwar yi mata bayani.

Hafsah ta mike ta bar su su biyu sannan Bilkisun taja numfashi ta fadawa mummy iya abunda ta sani daga jiya zuwa yau.

Mummy ta jima da kanta rike a hannayen ta kafin ta soma salati.

"Ai kuwa wallahi ba zan rike masa yaran sa ba..."

Abdallah da yazo wucewa kitchen, kunnuwansa suka dauko masa kalamanta. Dama ya sani korarsu akayi. A hankali ya bar wajen wani sashe na zuciyarsa yana samun rauni...

AeshaKabir
FadimaFayau

*ANYA KUWA ZAMU TAFI A HAKA BAKWA FADAR RA'AYIN KU KAN LABARIN, IN BAKWA FAƊA TA YAYA ZAMU SAN ANA KARANTAWA, RASHIN SANIN ANA KARANTAWA KO BA'A KARANTAWA ZAI SA MU DAINA RUBUTUN GASKIYA, TUNDA BA ZAKA DINGA RUBUTU BA MAI BI BA*

Ko da soWhere stories live. Discover now