Book 2: 1

18 3 1
                                    

*Ko da so...*

*Book 2*

*1*

Da gudu Aiman ya shige ɗakin Hafsa tana kwance bisa gado idanun ta na duban fanka da alamu ta yi nisa a tunani Aiman ɗin ya gaji da magana taɓo ta ya yi ta ɗan firgita da girgizawar da karamin hannun ya mata a ɗan nutse cikin muryar damuwa ta ce "Aiman bana hana ka girgiza ni ba."

ƙasa yaron ya yi da idanun sa " I am sorry Mami, my mistake, anma ba ke ce ba ina ta magana kinmin banza nama ɗauka kurmancewa kikai" yadda ya yi da yadda sautin Muryar sa yake ya sata yin murmushi tabbas ɗa rahama ne, ita tasan damuwar da take ciki ta yi mata yawa ma ta ma ƙarfin kwanyar ta sai gashi yaron ta yasa ta pure murmushi kuma har cikin ranta taji nishaɗin.

Yunƙurawa ta yi ta zauna tare da kamo ƙaramin mutun ɗin nata da duka hannun ta kafin ta ce "toh ayi haƙuri baccin zomo nake shi yasa ido na ke a buɗe anma bana jinka" dariya yaron ya yi "nifa in ce ya faɗa kamar babba" kallon sa ta yi tamkar mahaifinsa ya koma mata kusan da shi da Abdullahi sunfi kowa yanayi da Muktar.

"Au har na manta" ya faɗa tare da dafe goshi haka dai ta kuma ganin Muktar a yaron dafe goshi ya yi da bai yi wani abu ba ɗabi'ar Muktar ce.

Murmushi ta yi kafin ta ce towo me kuma ka manta, wani ne yace ki zo yana kiranki yaya Abdallah ya ce ba kyananan bacin Abie ya hana mu ƙarya.

Gaban ta ne ya faɗi ita ko tana budurwa batai wannan yayin na a turo ana kiran ta ba ballantana kuma yanzu da girman ta da komai, "maza geka kace banan kaji ɗan albarka," ƙuri yaron ya yi yana kallon ta da alamu so yake yace mata baya son ya yi ƙarya, fahimtar hakan da sanin halin yaron yass ta tsuke fuska tare da faɗin zaka tafi ko kuwa sai na sakko na make ka.

Rai ɓace ya fice wanda ya yi dai dai da kawowar jikin Mumy wurin har ya ɗan buge ta a tsorace ya hau bata haƙuri, sosai yake tsoron dattijuwar kakar tasa, "Mumy ki yi haƙuri mami ce ta min tsawa inje in ce wau bata nan, bacin tana nan"

Mum da batai niyar ce ma yaron komai ba ta yi saurin cewa "waye kuma yake kiranta?," a fusace ta faɗa dan tsammanin ta Muktar ne kafin ta samu amsar yaron tuni zuciya ta tunzura ta yin bakin tagar da ke iya hasko mata farfajiyar gidan, can ta hange shi tsaye cikin manyan kaya jingine gikin motar sa, irin sirikin da Mum take so kenan nan take taji hankalin ta ya kwanta da shi kamalar sa daban yake duda daga nesa ta hange shi, da sauri ta saki mayafin tare da cewa "Aiman" yaron da ke gab da fita ya ja ya tsaya rai duk a cunkushe "maza jeka kace masa ta zuwa" da fara'a yaron ya fice dan shi kam ya tsani ya yi karya bacin Allah baya bacci yana ganin sa, yana jin tsoro yana kuma jin kunyar Allah.

Da han zari Mum ta shiga ɗakin Hafsan tana kwance sangalalun hantunta bisa goshin ta idanun ta da ke fuskantar fanka a limshe sai dai kallo guda zaka mata kasan ba bacci take ba.

"Ke Hafsa ki tashi ki fita kina da baƙo" shurun da ta yi ne yasa Mum fusata, nasan ba bacci kike ba zaki tashi ki fita ko sai na tsinka miki mari" rai a cunkushe ta buɗe ido "Please mum.." Hajiya ki ta shi ki fita kin bar mutun na ta tsaiwa, ina kin gama idda, ko kina nufin wancan ɗan iskan kike kuma jira? To wallahi badai ina da raiba, in wancan karan kunmin ƙarfa ƙarfa na yadda yanzu ba zai yuwu ba, in koma gidan sa to wallahi cikin biyu ne kodai na mutu ko kuma nabar gidan nan dan wallahi in kika ce sai kin koma gidan sa to ni kuma nawa auren sai ya mutu in kuma ya mutu ki ɗaura ɗammarar neman wata uwar.

Jiki ba kwari kice da ɓacin rai Hafsa ta zari mayafin doguwar rigar da ke jikin ta, kamar yadda ɗabu'ar ta na sanya abaya kusan ko yau she ma tsayin kayan ta yake tana budurwa yanzunma sune dai kayan nata sai dole take sa atamfa leshi kuwa tunda tabar gida bama ta da shi dama Mum ke sai mata.

A fusace take da zummar taje ta mass rashin kirki ta fito sai dai kwarjini da haibar sa sun sa mata girman sa a idanun ta, bata saki fuskar ba ta ce ina wuni, ajiye idanun sa daga kanta ya yi zuwa ƙasa zuciyarsa na harbawa da sauri tun fitowar ta idanun nasa suka maƙale kanta, sanyayyar murta ta dawo shi, a nutse ya ce lafiya ƙalau ya kuma haƙuri da ni. Ya faɗa yana kallon ta. Kallon sa shi ta fara ji ya fara bata haushi sam bata son kallo ita kam.

Ko da soWhere stories live. Discover now