Ashirin da hudu

27 2 0
                                    

*Ko Da So*
*24*

"Ashe ma kin iya kika zauna wasa.." Mukhtar ya fadi, yana duba assignment din Hafsah wanda guda daya ne kadai tayi mistake shima daga formula ne. Cike da jin dadi ya sake kallonta yace,

"Kawai dai bakya maida hankali ne."

Hafsah ta sunkuyar da kai tana murmushi sannan tace, "ai malamin ne wallahi abun haushinsa yayi yawa. Wai kaga mutum ya sako wata yellow din shadda ga bakin glass kamar dan daba."

Mukhtar ya kasa rike dariyar sa ya dara. "Allah da gaske. Ni gaba daya sai naji haushi yake ban kuma dama ni ba son physics nake ba."

Ya kalleta cike da mamakin yanayin tunanin ta da yadda ta dauki rayuwa. "Toh yanzu me ya chanza? Nima dai kalli kiga silifas na saka."

Hafsah ta leka kafarsa taga silifas dai da ta sani amma sai taji haushin Mukhtar bai kama ta ba.

"Ai kai daban ne, you're charismatic and just ka hadu kawai..." kamar wadda tayi sabo, sai tayi saurin rufe bakinta ta sadda kanta kasa tana ji kamar ta nutse don kunyar abunda ta fada.

Mukhtar kuwa zuciyarsa ta cika fam da farin ciki. Ya rasa inda zai saka kansa a lokacin, fuskarsa dauke da yalwataccen murmushi ya maida kallonsa kan littafin dake hannunsa. Sun jima a haka ba wanda ya sake cewa komai. Ko wannen su zuciyarsa tana dokawa da sunan dan uwansa.

Mukhtar ya gyara murya sannan yayi kokarin ture yanayin da ya ziyarce su. Hafsah ta dago ta kalle shi, kafin ta dauke kai sai da idanunsu suka sarqe suka yi murmushi sannan kowa ya kauda kai.

Ya sake gyaran murya yana nemo jarumtakarsa da ta gama bacewa a lokacin sannan ya dauki textbook din gefen sa ya bude.

"Tunda kin gane capacitors, inaga yanzu sai mu fara da resistors ko?" Ya fada wanda ya sanya Hafsah tayi ajiyar zuciya sannan ta kalle shi tana gyada kai. Zuciyarta bata daidaita bugunta ba sai ma kara saurin da take yi.

Ta rasa yadda zata yi ta nutsu ta nuna ba abunda ya faru har sai da kalaman da bata san yadda suka hadu ba suka fito ba, tace "uncle Mukhtar wasa nake fa kawai dai ka iya koyarwa ne."

Mukhtar ya gyada kai. "Nagode."

Bata kalle shi ba ta yi shiru. Tunda ya fara bayani kanta kawai take gyada mishi ba tare da ta furta komai ba har suka gama karatun ranar. Daidai sanda yazo tafiya ne yasa yace mata ya kawo mata abu ya ajiye a kofar dakin me gadi.

Cuke da jin dadi da manta wancan yanayin kunyar da ta saka kanta a ciki ta bishi ya mika mata flask madaidaici.

"Wainar gero ce, inji Inna."

Taji dadi sosai kamar tayi tsalle.

"Nagode sosai. Bari na koma. A gaishe su dan Allah." Ba tare da ta jira amsarsa ba ta gudu cikin gida cike da farin cikin da tun kwanaki bata san silarsa ba. Kai tsaye kitchen ta wuce don ta zuba wainar in ta huce kuma tayi warming a microwave.

Bayan Mukhtar yayi sallama da mai gadi shima a hankali ya soma tafiya yana tunanin ta. Wani yanayi yana fusgar zuciyarsa game da Hafsah. Ya sani ya kamata ya dakatar da koma menene. Aiki ne ya kaishi ba sabo ba. Ko bayan haka ma sam ita ba kalar wadda zaiyi sabo bane da ita. Watakila kuma shi yake ganin kamar kulawar ta a gare shi ta musamman ce. Watakila kawai kirki take masa with no strings attached. Ya tsaya a bakin titin yana sake maimaitawa zuciyarsa ta daina dokawa Hafsah ko da kuwa dukan da takeyi ba na neman wata alaka bace ta kawayence ko na so. Maimakon yaji komai ya daidaita sai murmushin Hafsah ya sake fado mishi a rai.

A take zuciyarsa ta shiga harbawa da sauri da sauri tana saka shi shima murmushin.

Mota tazo wucewa ya tsayar ya shiga sannan ya samu hankalinsa ya chanja alkibila.

Ko da soWhere stories live. Discover now