Ashrin da biyu

25 2 0
                                    

*Ko da So..*

*22*

"Sabbin kaya zasu iso nan da sati daya saboda haka ya kamata muyi clearance sales don mu rabu da tsofaffin." Hajiya Hadiza, mahaifiyar Hafsah ta gayawa me kula da boutique din nata.

Matashiyar ta amsa. Sannan ta dora da, "how many percent off, ma?"

Hajiya Hadiza ta danyi shiru tana ajiye biron hannunta. "Zanyi lissafi."

Da haka ta cigaba da dudduba kayan tana jotting din abunda ya kusa karewa da abunda yafi yawa. Taku take daidai tana jin dadin nasarar da ta samu a kan kasuwancin nata. Duk abunda ta saka a gaba bata kyale shi sai ta cimma nasara.

Kiran waya ne ya katse mata tunani yasa ta dubi wayar sannan ta tabe baki kafin ta dauka.

"Lafiya, ina boutique ne. Toh shikenan." Ta fadi sannan ta kashe wayar ta jefa ta cikin jaka. Abunda aka fada yasa ta juya zata tafi don anyi mata ba zata. Matar uncle din Hafsah ce ta haihu shine maman Hidaya ta kira ta fada mata suje barka anjima.

"Wani abu ya taso min. Zan shigo da safe." Ta fadawa Saratu sannan ta fice tana nufar motar ta tare da tunanin wacce irin shiga zatayi. Bata son shigar da zata jawo mata raini.

****

Babban gida ne sosai da bangarori da dama. Ko da mummy ta faka motar ta a harabar gidan sai da ta tsaya tana tunanin ko tayi kyau ko batayi ba. Karshe dai ta hakura ta cire mukullin sannan ta fito. Kofar bangaren Amina me jegon tayi tana taku a hankali. Tana budewa sanyin kamshin turaren wuta ya bugi hancinta.

Ta kalli corridor din da zata kaita main parlor din taga yadda aka yi masa ado da frames kala kala. Ga runner carpet nan har karshe. Ta cire takalmin ta ta saka a rack din da aka ajiye a wurin.

Sama sama take jin hirar su har ta karasa da sallamar ta. Cike da takama da nuna ita ma ta isa ta samu wajen zama sannan suka fara gaisawa da mutanen wurin. Dukkan su dai facaloli ne.

Maman Hidaya ta kalle ta ta murmusa. "Hadiza leshin ki yayi kyau wallahi." Kanta ya kumbura, amma sai ta basar kamar ba wani abu ne mai muhimmanci ba tace,

"Kuma kawai na siya ne randomly saboda shan iska."

Ta kyalla ta kalli leshin jikin Amina taga babba ne sama da nata. Haushi ya cika ta wato ita Amina zata nunawa sutura. Ai kuwa dai babu abunda mijinta yafi nata.

"Yayi kyau kuwa." Aminar ta fada itama tana yabawa. Hajiya Hadiza tayi yake tana ganin kamar magana kawai Aminar take so ta yaba mata.

Ta dan kauda kai sannan tace, "ina babyn?"

"Yara sun dauka. Ai ita kam wannan yayyin ta sune iyayenta." Suka kwashe da dariya.

Maman Hidaya tace, "toh abunka da kalan hanji." Aka sake yin dariya. Amina ta maze duk da bata dauka da komai ba. Tunda ta samu cikin ake nata tsiya kala kala wai ta tsufa. Da farko ma taso ta cire likitan yace mata babu wani risks sosai.

"Daga ita na kulle dai balle a samu nayi." Ta fadi sannan suka shiga wata hirar daban.

*****

Ganin a kwana biyu Bilkisu tana ta boye matsalar da take ciki ya saka Hafsah yanke shawarar take gidansu. Ko da ta shirya zata tafi mummy bata ce komai ba hakan yasa taji dadi ta kama gabanta.

A dukkan tsananin mummy bata takura mata idan wajen Hidaya zata je ko wajen Bilkisu. Ta yarda dasu da mu'amalar su da Hafsah din.

Tana isa gidan tayi sa'a bata tarar da kowa ba ta wuce dakin Bilkisu. A kwance ta same ta ta kurawa sama ido hawaye nata fita daga idanunta a gefe kuma wayar ta tana ta ringing.

Ko da soWhere stories live. Discover now